DAN HAKIN DAKA RAINA???? COMPLETE NOVEL
Futa tayi taka ma hanyar xuwa gida
Lokacin dataje gidan sun gama share ko’ina sun wanke ko ina dan tayal ne ako ina acikin gidan
Sunsa tsunman dasuka gani sun goge ko ina ya tsane
Kayan kiching ma sun wanke sun goge komai Doya, da dankalin dasukaga sun lalace suka futar suka saka abuhun shara
Dan watan ta d’aya da tashi Amman saboda yanayin sanyi ga iska ga 6ura kota ko ina shiyasa gidan yayi futu futu sosai
Yadda kasan an shekara ba’a shiga gidan ba
Mamaki tai ganin sun gama komai har wankin kaya sunyi shaya
Tarar dasu tayi suna iban ruwa dayake akwai rijiya acikin gidan kuma akwai guga aciki
Wai harkun me
Mun gama Ummerh
Sai kace wasu injina gaskiya kun aykatu sosai Allah yasaka muku da gidan aljannah
Amen yarab Ummerh
FAHAT ne yakalleta sai kuma yace Ummerh mujefa cigiya har INDA RANKA, BBC NEW’S MUJE
Amman shiru bamu ji bayani ba
Murmushi tai tace Allah yashirye ku wlh
Ummerh munjefa sai kafun nashiga naji ana cewa kizauna kidan huta shine nadawo nace masa kina nan muci gaba da aikin mu
Au ainazata bakuje nemana ba
Haka kawai kuke ta zaune
Haba mu mafara
Dariya sukayi gaba d’aya suka cigaba da dibar ruwan tana tayasu cika wasu abubuwan
Atare sukayi jeran kicin din dakuma sauran ayyuka
Kallon su tai tace toh yanzu mezamu siyo muci kuma ice zaku siyo muhura wuta azaure ko kuma magal zaku siyo mana da gawayi dan naga acan kofar gidan wasu makera anayi
FAHAT ne yace Ummerh ga gass nan aisaimu kunna muyi amfani dashi
Gass kuma ni Hapsatu ina na iya aiki dashi ko kunnashi ban iyaba
Hh Hh Hh ummerh ni na’iyafa wlh agida nikeyin girki kullum
Toh maza shiga kayi
Meza’adafa ma Wai
Ai sai abunda kikace
Tohhh???????? kubaku da za6i sai nawa
Ey mana Ummerh kifada
Toh nikam banasan komai
Nauphal ne yace toh muyi shinkafa da wake tunda akwai
Saimu daka yaji koh yayah
Yawwa kumafa hakan yayi mudaura
Hapsatu ce ta tafi dakanta tasiyo barkono da salat, tumatir, kokumba, da albasa duk sannan tasiyo musu kankara daruwan sanyi leda daya, da tiara, da so6o, cotta, kanin fari da danyan kifi na dari biyar sannan tadawo gida
Lokacin sun zuba wake
Adayan kuma sun daura ruwan zafin wanka har Nauphal yashiga yayi Fahat kuma zai shiga ta shigo
Zuwa yay zaitayata aikin tace a’a maza kayi wankanka bari ingyara
Tafiya yayi yay wanka yashirya
Lokacin ta gama komai ta tattare gurin ta gyara
Itama wankan tashiga
Lokacin harya sauke abuncin yajuye akula Nauphal yakama wanke-wanke shikuma yahad’a sauran kayan abuncin yakai daki ya ajiye
Kifin yasoya sannan yasoya man dazasu ci abuncin dashi
Saida suka kammala komai sannan suka zauna cin abuncin ababban plate ???? tazuba musu abuncin suka saka hannu suka faraci
Koda suka gama saida suka tattare komai sannan suka dawo dakin suka zauna
Hirar su suke
Sai Hapsatu ta kalli Fahat tace nikam Fahat inane gidan ku
Saida yanayin fuskarsa yacanja dakar ya kwa’kulo murmushi yace Ummerh meyasa kika tambayar gidan mu
Haka kawai kuma yakamata musan gidan ku dan mumaidakai koh yakake gani
A’a Ummerh dan Allah karki maidani gidan nan wlh banasan komawa gidan nan ko amafarki wlh
Meya faru haka Fahat?
Kabani labarinka in babu damuwa?
Toh Ummerh bazanki gaya miki koni waye ba da kuma asalina ba…………..
*** *** ***
A6angaren su fauziyya kam
Mama Balaraba anugun razane ta tashi tace ciiii meeeeee na shiga uku yanzu fauziyya cikine dake inna lillahi wa inna ilaihi raji’un nabani
Tayaya akayi fauziyya tasamu ciki
Am nace ba dan Allah tayaya za’ai acire wannan cikin
Zaro ido Baba iyabo yayi yace minana kike cewa hajiya
Kazubar mana da cikin nan nakeso
Niii nini nii Wlh bazan iya aikin sa6an nan ba badani ba hjy
Nace kadauka d’anka kubarmin chamist Wlh konayi maka ihu yanzu jama’asutaru
Haka kawai ni nace d’anka yaje yayi ciki
Tashi Balaraba tai tace katai makamun karkamun ihu yanzu zamu tafi
Yawwa yafi dai kam
Amman kaban kudina maza kafun nama rashin mutunci Wlh kagane ko?
A’a Baba iyabo basaikayi rashin mutunci ba yanxu zan baka kudinka nawane
Yawwa yika kawo maza dubu biyar da d’ari tara da hamsin da biyar
A’a nashiga uku harda biyar Baba iyabo baza’abar mun biyar dinba
Ey bazan bari ba dan tashegen zan yiwa ragi kaban kud’ina tsaf sannan kafuta anan Wlh
Balaraba saida ta irga masa kudinsa tass sannan takama hannun Fauziyya suka futo daga chemist din
Kama hanya tayi sukayi wani chemist din ma nan ma babu wani sauki sai wula ‘kanci data tarar
Saida sukaje chemist yakai 5 amman babu wani bayani haka suka dawo akan zasuje cikin garin kano gobe dan samun mafuta
Mama Balaraba kuwa tashiga tsananin tashin hankalin daba’a zato bare tsammani dan ta gigice ta razana dajin wannan zancen har yakai kunnen……….
Ina ganin comment dinku masoyana ina godeeyah sosai da sosai
ALLAH yabar kauna
Love you all my fan’s ????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????❤❤❤????????????????????????????????????
Hallmarth ce????????????
[04/02, 7:56 AM] Ummuh Fateemah????????????: ????✨????✨????✨
✨????DASHEN ????ALLAH????✨
WRITTER’S✍???? ASSOCIATION
https://chat.whatsapp.com/BHqoOEHjWQz26cyXRvt9V7
????ALKALAMI ✍????YAFI TAKOBI????️
بسم الله الر حمن الر حيم
✨DAN HAKIN???? DAKA RAENAH???? ????✨
*????NAH????*
SADIYA ABDULLAHI UMAR
????UMMUH FATEEMAH????
????—
Page 3⃣3⃣&3⃣4⃣
Danjin zancen yakai kunnen Anas da kannensa shiga sukai cikin gidan ad’arare suka wuce d’akinsu
Zaunar da Fauxiyya tai tace dan uwarki a ina kika samu ciki nace miki eyeeeee
Uban waye yayi miki ciki
Kifad’amun nace kafin yanzunnan in yanka ki wlh kinajina ko
Cikin tsananin tashin hankali da rud’u take maganar
"Dan tuno da maganar da likitan nan yamusu akan karta kara samun ciki dan in takara samun ciki tofa saidai tarasa mahaifarta gaba daya"
Ma’ana bazata kara haihuwaba kwata kwata yanzu kuma gashinan tayi wani cikin wannan na 4 kenan
Kuma ita gaskiya bata da burin "yarta taja mata abun kunya acikin garin toh yanzu yayah zatai kenan
Haka Balaraba taita masifa tana tambayar Fauziyya wayay mata ciki amman ko ajikin ta tayi mata buruss
Tana zaune kamar bada ita take ba
Saida Balaraba tadauko wata katuwar wu'ka tace wa Fauziyya koki gayamun waya miki wannan cikin ko kuma na yankaki
Sannan cikin rawar baki tafara fad'in wlh mamah zan gaya miki ki ajiye wukar nan wlh zan fad'a
In kinga na ajiye wu'kar'nan toki tabbata kin fadamun Gaskiya wlh inba hakaba Wlh saina yankaki, kinjini koh ba kijiba
Tunkarota tai gadan gadan da wukar zata luma mata
Tana fad’in kin manta abunda doctor yace koh akan karki kuskura kisake daukar ciki sbd mahaifarki bata da lpy in aka ‘kara yimiki abortion zaki rasa mahaifarki
Yanzu yaya kike so inyi
Kuma dawani idon kikeso in kalli yayyenki da jama’ar gari eyeeeee
Ma..... Ma.... Ma.... M... Mama..... Wlh wannan cikin na jaz.... ja...... z.. u.... l.. i... J.. azuli..... ne Wlh
Jazuli….. jazuli…. kuma bangane ba jazuli…. dana bawa kudi yayiwa Hapsatu fyade
Eyy Eyy Wlh shine
Yanzu kuma haukar taki kan jazuli takoma
Inna lillahi wa inna ilaehi raji’un kice hauka nake tayi nice keda abun kunya agari
Toh wlh daga ke har Jazulin saina kasheku
Kan Fauziyya tayo da gudun
Ihuuuu taraf ka tana fadin atai makamun jama’a
Za’ai kisan kai Wayyo Allah n…………
*** *** ***
ALHAJI UBAH SHEHU
Shine mahaifina yakasance mutum mai tarin dukiyane
Dan shahararren d’an kasuwa ne shi babu abunda baya siyarwa kama daga kayan abunci sutura motoci mashina da kekuna da saida gidaje yana siyan fili yagina yasiyar
Wannan dalilin ne yasa shi yin suna acikin garin kano kota ko ina ansansa har wasu suna masa kirari da
SANA’A GOMA MAGANIN MAI GASA
Aharkarsa ta kasuwancine yahadu da mahaifiyata
Wato hjy Maryam macece wadda take da hkr da kuma neman nakanta bata dogara da mijinta yana dashiba
Ita bata zama wai sai abunda miji yay mata
“Tunda suke da daddy na bata ta6a tambayar sa kud’i ba saidai idan shine yad’auka yabata”
Neman kudin ta take dan ita lauya ce babba sannan kuma tana saida atampopi da shaddoji da less kala2 order su ake mata daga waje
wannan dalilin ne yasa kowa yatsaneta a family dan tunaninsu duk shi yake Mata komai
Ita kuwa dukkan wulakancin dasuke mata bata ta6a tanka musu ba
Haka sukayi suka gaji amman bata ta6a tanka musu ba koda sunyi habaici saidai tayi murmushi kawai