DAN HAKIN DAKA RAINA???? COMPLETE NOVEL
Ummerh ni dan asalin garin Abuja ne kuma anhaifeni acikin unguwar WUSE 2 anan nagirma nayi karatun primary school da secondary dina
Ina rayuwa cikin jin dadi da kwanciyar hankali kafin family dina su tar watsamun rayuwa ta hanyar saka daddy na ‘kara aure
Lokacin da daddy yafara shirin ‘kara aure nikuma awannan lokacin ne nake ‘ko’karin fata zuwa Makarantar gaba da secondary
Akwai wata rana dana dawo ina murna mun gama ajin farko anbamu hutu
Naahigo gida dan sanar da mom dina sai na iske hajiya babba dasu hjy kareema da uncle saminu sunzo inda suka saka daddy na agaba saiya ‘kara aure
Hajiya babba harda cewa idan bai amun ceba zata tsine masa ta sallama shi daga cikin “yayan ta
Haka suka saka daddy na yayi aure badan yana soba yayiwa mom dina kishiya
Koda wasa bata ta6a nuna musu 6acin ranta ba
Ita ta had’a masa kayan lefen ma tayi komai na bikin
Lokacin da akai biki gidan su d’aya da amaryar daddy wanda shiba santa ma yake ba
Akwana atashi amaryar daddy hartakai shekara 2 bata ta6a ko 6atan wata ba
Sun shiga cikin tashin hankali sosai Sannan taga komai tace yay mata bayayi intace tagani agurin mommy na sai yace mata bashi yay mata ba
Ita taiwa kanta itama ta kama sana’a intanaso tayi
Abun yana mata ciwo sosai hakan yasa tafara neman yadda zatai tarabasu
Tafara shiga malamai tana neman magani kota ko ita
Tun bata nasara har Allah yabata sa’ata yi nasara
Ranar wata juma’a wadda bazan manta da itaba ranar mom d’ina tafara rashin lpy sannu sannu ciwo yaringa gaba2 kamar wasa komai na mom yakoma gun amaryar daddy ita take duk wani kasuwanci da mom takeyi dan mom yakai yakawo har bata iya Tashi saidai in mata komai
Daddy baya kulamu komai ni nake mata duk wani magani ko abunci
Takai tun munacin kud’in mu harsun ‘kare saida nakoma saida komai namu har yakai sai naje kasuwa nayi dako sannan muci abunci ko insai mata magani
Kullum mom acikin yi mun wa’azi take akan inyi hakuri in yi biyayya akan duk umarnin da akai mun kazamo mai biyayya
Ranar wata lahadi da safe natafi kasuwa bayan nayiwa mom komai nayi wanka nasaka kayana
Tayimun nasiha sosai sannan tabarni natafi haka naji jikina yayimun sanyi kamar kar inje kasuwar
Amman haka natafi dan babu kud’in dazan siyo mata magani kuma nata yakare
Bayan nadawo da yamma naganta tana zaune akan sallayar ta da Al lkur’ani akan ‘kafarta
Murmushi nai na ‘karasa na ajiye ledar dana siyo mata abunci da kuma maganinta
‘Dauko plate nai najuye nadauki kunun gyadar shima najuyeshi acikin cup na ‘karasa na ajiye mata akusa da kafarta na ajiye mata maganin ta
Natashi zuwa wanka duk tuna nina karatun datake ne yasa batayimun magana ba
Har nafuto nasaka kayana nadawo naga komai yana gurin kamar yadda nabarshi ‘karasawa nai na ta6ata amman me sai naga t…………….. ✍????
Ina ganin comment dinku inajin dadi sosai my fan’s
Allah yabar ‘kauna????
Hallmarth ce???? ????????
[04/02, 7:56 AM] Ummuh Fateemah????????????:
????✨????✨????✨
✨????DASHEN ????ALLAH????✨
WRITTER’S✍???? ASSOCIATION
https://chat.whatsapp.com/BHqoOEHjWQz26cyXRvt9V7
????ALKALAMI ✍????YAFI TAKOBI????️
بسم الله الر حمن الر حيم
✨DAN HAKIN???? DAKA RAENAH????????✨
????NAH????
SADIYA ABDULLAHI UMAR
????UMMUH FATEEMAH????
????—3⃣5⃣&3⃣6⃣
Ta fad’i gefe ina ‘kara ta6ata naji jikinta ya saki duddubata nafarayi naji babu numfashi atare da ita sam
Kuka nasa nafuta nakira kishiyar mom ina gaya mata amman abun mamaki saima wata dariya tasaki tana gud’a tana fad’in burinta yacika
Futa nai nakira masu mana aiki na ari wayar mai gadi nakira daddy na nagaya masa amman sai cewa yay Allah yajikanta yakashe kiran naji haushi sosai
Haka akai wa sutura aka kaita gidanta nagaskiya amman babu kowa namu
Haka rayuwa tacigaba da tafiya yau fa dad’i gobe akasinsa
Harna kammala degree na A6angaren karatun likita lokacin ina da shekara 17 kowa yakanyi mamakin yadda d’an shekara 17 yakammmala degree amman babu mamaki aciki saboda tun ina 3years nake zuwa Makaranta kuma ansha kaini ajin gaba idan akaga ‘ko’karina wannan dalilin ne yasani kammala degree na asaukake
Bayan wannan lokacin nahad'auki takarduna dan zuwa neman aiki ne ban samuba nadawo nazauna agida ad'akina sai naji ana magaba 'kasa 'kasa nad'an la6e inaji anan naji amaryar daddy ita taiwa mom d'ina asiri kuma ita tahana daddy na yayi mana komai
Dariya suka saka anan suka fara shirin sawa a kasheni
Nan hankali na Yatashi sosai dan bansan yadda zanyiba
Da dare yayi kulle d’akina nayi na kwanta amman sam nakasayin bacci saboda yanayin tashin hankalin danake ciki
Ina cikin wannan tashin hankali wasu mutane suka cire window glass din dakina suka shigo fuskarsu duk arufe suka yo kaina
Dasauri natashi dan guduwa suka rikeni wani abu suka d’auko suka sha’kamun ahanci daga nan bansan inda nakeba sai ganina nai acikin wannan shagonai ‘kosan ana cinikin mu aka bata kud’i akace za’a zo ad’aukemu
Saina had’u da Nauphal wanda yakasance yanata kuka yake gayamun yadda akai suka daukesa suka rabashi dake natausaya masa hakanne yasa nayi masa alkawarin zamu gudu in sha Allah kafun sud’aukemu
Kallonsa tai tana murmushi tace amman kayi namijin 'kokari sosai arayuwarka Fahat
Kuma ka dage dayiwa mahaifiyarka addu’a
Sannan kuma kasani dukkan abunda mahaifinka yayi maka yayi maka ne badan yana soba tunda aikin asirine
Natabbata wata rana zai nemeka kaji d’an ‘kanina kadaina kuka
Sannan kuma bazan maidakai gida ba harsar ranar daka bu’kata da kan ka
Rungumeta sukai su duka suna kuka sosai da’kar ta iya lallashinsu
Tace toh yanzu maza atashi ayi abunyi dan yamma tayi sannan munemi guri muzauna dan inasan muyi shawara gaba daya dan gane da sabuwar rayuwar da zamu fuskanta
Toh Ummerh bari mud’an tattare gurin muyi sallah
OK maza
Tashi sukai kowa yakama aikin dazaiyi, bayan sungama suka shiga d’ankin kusa da ita suka zauna
Takallesu tace inasan gobe da safe bayan mun gama karyawa mud’an futa mu duka sbd inasan muga yanayin garin sannan musan wace sana’a zamu kama
Sannan kuma musan a ina zamu farayi agidane ko akasuwa sannan musis siyo abunda muke da bu’kata nadaga kayan sawa sabulu da mai
Toh Ummerh ke atunanin ki meyakamata mufara saidawa dan gina goben mu
Toh Fahat nidai da tunanin danai mushirya muje kasuwa sai musan mezamu siyar
Nauphal ne yakalleta yace Ummerh kinga unguwar nan babu gurin da ake saida kayan shago akusa kuma abuncima nasiyarwa sai anje kasuwa mezai hana mufara siyarwa kawai
Fahat ne yace tabbas Ummerh Nauphal yayi gaskiya yakamata mufara saidasu kuma Allah zamuyi ciniki IN SHA ALLAH
Toh amman me yakamata musissiyo goben
Ummerh duk kayan da ake daidawa ashago mana
Toh bari in d’auko kudin inga nawane
Jakar kud’in tadauko tacirosu gaba d’aya tafara ‘kirgawa tana mikawa Fahat yana ‘kirgawa shima yana ajiyewa
Saida suka ‘kirga dubu tamanin da tara da d’ari biyar
Sai wayar da gara yabata
‘Dauko wayar tai taga babbace sosai zatai kud’i da yawa
Tacewa Fahat gobe zamuje kasuwa amman bamusan inda ake saida wayoyi
ba damun sayar da wannan
Amman kaduba mana kaga ko menene about dinta
Toh Ummerh amsa yayi ya duba yace kai Ummerh babbace wlh kinsan yadda zamuyi cewa zamuyi nawa suke saida ta sakan in suka fad’a saimuce musu nawa zasu siya tamu sai muji
Toh shikenan yanzu dai muyi niyyar Kwanciya da wuri dan gobe mutashi da wuri
Toh Ummerh d’akin suka tafi tarakasu saida ta tabbatar da sun kwanta sannan ta rufe musu kofa takoma itama ta kwanta ad’ayan dakin
*** ***
Kanta tayo da gudun masifa tace jazuli kuma wlh kin cuceni Fauziyya yanzu kirasa wazaki bi sai jazuli shine uban shegen cikin nan naki aikam yazama dolema acire wannan cikin dan bazan iya renon cikin shegeba
Kuma dad’in da d’awa babanshi d’an shaye shaye wannan wace irin mummunar ‘Kaddarah???? ce
Dukanta tafara da dukkannin ‘karfin ta tana fad’in kin cuceni wlh kin gama dani faiziyya
Abban Hafsatu ne yajiyo ihun kukanta da gunjinta shine yataho yana buga d’akin da karfi, yace kibud’e Balaraba kinajina koh kibud’e maza
Kin budewa tai
Saida taji yace idan bata bud’eba abakin aurenta shine ta taho da sauri ta bud’e kofar
Shiga yay yatarar da Fauziyya kwance cikin jini, yace Subhanallahi
Wannan wani irin danyen aikine kika aikatawa yarinyar nan yanzu idan ta illata fa Balaraba
Hmm niba wannan bane yadame ni tajecan taita jigatarta indai wannan jarababben cikin zai zube ban damuba na nemaata magani
Cicc… Ciiccc…. Cciiiikkkkkk…….. Cik…… Ciiccc… Ciiii… kiiiii kuma Balaraba ban ganeba
Aaaaaaa..aaaa…. Aaa….. Aaaaa’aaaaaa…. Baka fahimta bane ina jimamun yadda Hapsatu ta tafi da cikin shegen nan ne batare da’an zubar dashiba
Ok Bari Allah yakyauta kawai nima wannan kayan bakin ciki yana damuna
Amman kuma me Fauziyya tai miki kike dukanta yarinya mai biyayya
Wlh ina takaicin yadda akai tabar Hapsatu tabar gidan nan ne saikace wata sakara takasa tsaydata daga tafiyar datai
Wlh inajin kewar ta sosai wlh ina tunanin yadda za’ai muyi da abun kunyar datai
Yanzu ko ina tayi oho????
Alhajine yace hakane Allah yashiryata
Yanzu abunda yakamata mukai yarinyar nan asibiti sbd kinga yadda take zubar da jini sosai
Toh bari in samo d’an sahu sai mu tafi
Futa tayi tasamu anas awaje kallonsa tai ta had’e rai tace kazo ka kaimu chemist
Toh tashi yay badan yana soba suka tafi chemist din
Koda sukaje da’kar aka kar6eta suka dubata akace mata cikin……….