DAN HAKIN DAKA RAINA???? COMPLETE NOVEL
Yau yakama ranar asabar and’aura auren jazuli da Fauziyya wanda hakan yabawa su Anas da Baban su Hapsatu mamaki dan yashiga rud’ani dajin wannan auren
Dan duk cikin su babu wanda yasan da auren saidai d’aurin aure
Gida Anas yadawo afusace yashiga d’akin mamah Balaraba, ganin ta yay azaune tana shirya Fauziyya wadda duk ta gala baita sbd maganin datakesha na kwantar da ciki ta rame tayi ba’ki sosai
Kallon su yay yace abunda aka fad’a gaskiyane kenan
Mm Balaraba ce tace kamar yadda, me aka fad’a?
D’aurin auren Fauziyya da Jazuli amasallaci
Ey kaji dai2 kam, menene kuma?
Kobakasan auren ne sai inji
Aa amman dai mamah a rasa kowa za’a aurawa Fauziyya sai jazuli
Ey mana shi tagani kuma shi take so ko zaka hana ne eyeeeee sai inji
Yarinya tafutar da wanda take so amman kai zakace ga zance ga magana
Allah yabaki hkr, futa yay zuciyarsa tana masa ‘kuna ganin ‘kannen sa yay suma duk rai a6ace suna tsaye abakin ‘kofa cirko2
Matsawa sukai shikuwa yayi gaba abunsa
Alhajima koda yatambayeta shima d’iban albarkar tai masa haka yahakura yafuta abunsa
Kamar dai yadda yakamata haka akakai Fauziyya d’akinta kamar ko wacce mace
Anyi mata kaya na dai talakawa dan daga gado sai kwaba da kwanon cin abunci na silba guda biyu sai copi da tukunya tuwo da miya
Sai wajen 1:47 sannan jazuli yashiga cikin gidan abug………………….
Sadiya A Umar
Ummuh fateemah
Hallmarth ce ????????????
Love you all my fan’s ????????????????????????????????❤️????????????????????????????????????????????????????????????????????????????
[04/02, 7:56 AM] Ummuh Fateemah????????????: ????✨????✨????✨
✨????DASHEN ????ALLAH????✨
WRITTER’S✍???? ASSOCIATION
https://chat.whatsapp.com/BHqoOEHjWQz26cyXRvt9V7
????ALKALAMI ✍????YAFI TAKOBI????️
بسم الله الر حمن الر حيم
✨DAN HAKIN???? DAKA RAENAH????????✨
????NAH????
SADIYA ABDULLAHI UMAR
????UMMUH FATEEMAH????
????—4⃣1⃣&4⃣2⃣
Abuge yashigo gidan yana zuwa yazube abakin gado yana tan gad’i
Amai yarinka kwarawa abunsa yana gamawa yayi bacci agefe
Ita kuwa data rufe kanta haka ta sakko jin wannan amai dayake kwarawa, haka ta tattare gurin ta gyara komai sannan ta kwanta tana dana sanin wannan aure
Koda gari ya waye hakan ce ta kasance dan bai tashiba sai wajen 12:00pm sannan yayi wanka yaci abunci yafuta
Sai wajen 3:00pm sannan yadawo lokacin tayi bacci ta Tashi yafi sau akirga saitaga bai dawoba
Lokacin daya shigo dai kamar jiya haka yashigo cikin d’akin yayi amai ta gyara ya kwanta yayi bacci da safe yayi gaba abunsa
Kamar wasa haka jazuli yake shigowa gidan har tsawon wata d’aya bata ta6a tanka masa
Ranar tsautsayi tace waikai meka maidani ne kamar wata ‘yar aikin ka tunda nazo gidan nan saidai inyi maka wahala wannan wace irin rayuwace
Ni kike gayawa haka eyeee
Anfad’a makan ai nayi hakuri wlh bazan iyaba
Wata waya yad’auko mai kaurin tsiya yafara lafta mata ajikin ta saida yay mata rud’u rud’u da jikin ta tun tana iya tashi harta kasa tashi
Saida yaga tajigata sannan yafuta yabarta agurin
Kota kanta bai biba yayi waje abunsa yana fad’in gobe ma ki ‘kara mun irin wannan maganar
Futa yay abunsa hankali kwance
Da’kar ta iya tashi daga gurin tad’aura ruwan d’umi tayi wanka ta gargasa jikinta tad’aura girki haka da rarrafe tayi girkin ta gama sannan ta ‘kara gasa jikinta sannan ta d’an kwanta wayarta tad’auka takira mamah Balaraba ta sanar mata da komai
Aikuwa Balaraba amugun razane tace dume?
Duka wlh mamah
Lalle kahaifu jazuli ina nan zuwa d’auka miki fansa wlh bai daki banzaba gani nan zuwa
shiryawa tai tafuto, suka kama hanya ita da ‘kannen Anas suka tafi
Ajigace suka tarar da ita har zazza6i yafara kamata
Chemist suka kaita anan aka dudduba aka bata magun guna sanan suka dawo
Har suka gama zamansu Jazuli bai dawo ba ran Balaraba ya6aci matu’ka amman babu yadda zasuyi haka ta koma gida dan ranta a6ace yake tama rasa yaya zatai
Washe garima da sassafe taje gidan amman baya nan haka ta wuni amman ko d’uriyar sa babu
Tajera kusan kwana uku tana haka amman basu ta6a had’uwaba
Yau kam da masifa yatashi akan bata wanke masa kayan saba sbd jiya da zazza6i ta kwana
Amman ko duba halin da take cikinsa bai ba dukan ta yafarayi kamar an aykoshi, suna cikin haka Balaraba tashigo gidan rai 6ace tayi kansa ta fuzge bulalar wayar wutar tai ta zabga masa tasa ‘kannen Anas suka fara dukan sa da ita
Aikuwa Jazuli yace indai suka ‘kara dukan sa to sai yasaketa yanzunnan, babu arziki suka daina dukan shi, tashi yay yace, jeki gida nasakeki saki d’aya
Dasauri Balaraba da Fauziyya sukayo kansa dansu bashi hakuri amman ina, tum kan su’karaso yay fucewarsa yaya wani yad’aukesa amashin sukai gaba
Har dare suna jiransa amman bai dawoba
Bashi yadawo ba sai wajen 1:47 sannan yashigo gidan abuge kamar kullum
Kanta yayo yafara surutai anan yayi amansa ta tashi ta gyara komai sannan sannan ta gyara masa kwanciya itama ta kwanta mama Balaraba kam tana cikin Kiching anan ta kwana da gari yawaye Jazuli yashiga kicking zai ibi ruwa yaga mutum akwance aikuwa ajiye butar yay ya’karasa yafara shafa mata fuska yana fad’in dama na dad’e inasan in sha wannan ro……………….
Wajen su Hapsatu kuwa amaryar daddy tacigaba da masifa tana fad’in
Nace meya kawoku cikin gidana ajiya kuka ban waya baku izinin shiga
Hafsatu ce ta kalleta sai tace hjy mun zone mutai makeka
Muna bada maganin mallaka ne dana farin jini, dana kasuwa
Kai kowanne irin magani muna bayar wa har na korar kishiya
Murmushi tafarayi tace kai masha Allah bari inzo kuwa dan kunzo a lokacin daya dace, dama ina neman magani sosai, “da har ina cewa zanje gurin mlm mai magana d’aya ashe basai najeba ga sau’ki nan yazo”
Haule…. Haule…. Haule…… Kina inane, Na’am gani nan hjy
Amman kinajina dan wula ‘kanci kikai shiru, bakiga ba’ki bane
Nagansu hjy nakawo musu ruwa da lemon, okkkkkk haka kikewa ba’ki dama ko bazaki kawo musu abunciba da nama da snacks ba, sai ruwa da lemo, sai kace uban kine yake siyan kayan, a’a hjy ayi hkr bari in kawo, Banza shaa shaa shaa kawai mazakije ki kawo musu
Tashi Haule tai takawo musu komai da aka lissafa mata
‘Kawayen tane suka dawo sukace, ai ba’ayi bamuba muma bari mudawo mu amshi na mallaka,Heeeee here heeee tafawa sukai suna shewa atare suka shigo zama sukai suma
Amaryar daddy tace kuci mana hjy
Murmushi Hapsatu tai tace, hmmm mun ‘koshi ai, bari mubaku maganin ku kawai mutafi dan akwai inda zamu da yawa, kema watace ma da muka bata magani alayin baya shine tace muzo kema tasan zaki bu’kata, ayyaaa aikam nagode
Toh yanzu hjy nawa kuke bada na mallakar nan
Toh yadan ganta da yanayin abunda zaku biya akwai na mallakar miji har dangin sa, danashi shikadai, dakuma na ra’kumi da akala dana bita zayy2
Aaaaaa nikam duka za’a had’amun, toh nawane amman ai za’amun sau’ki koh tunda dayawa zan siya
Toh hakane kibada dubu d’ari 5 sai in baki, toh shikenan bari in d’auko ahad’amun kafun in futo
‘Dadd’aura maganin Hapsatu ita da Fahat suka fara sannan suka ajiye mata aguri d’aya
Ta amshi nakasuwama dana farin jini, shikuma dubu d’ari 2
Suma ‘kawayenta sun amshi magani sosai dan sunyi musu cinikin dubu d’ari 7, sosai suke ta musu godeeya itako amaryar daddy harda basu atamfofi guda 6 da shadda guda 4 tace mata, keda mijinki hjy
Toh shikenan ngd sosai hjy, babu komai gashi bakuci komai ba bari ajuye muku snacks din da naman soyayye koh hjy, irin wannan tai mako da kukamun aikamata yay nima kud’anci wani abun ko kad’anne
Toh shikenan, tsaya wa sukai aka juye musu shi , harda ‘karin wani acikin babbar leda mai ba’ki da yellow aka sako musu, amsa sukai suna godeeya
Har lokacin zuciyar Hapsatu data Fahat bata daina bugawa ba