DAN HAKIN DAKA RAINA COMPLETE NOVEL

DAN HAKIN DAKA RAINA???? COMPLETE NOVEL

Nanfa mama Balaraba tayi tsalle ta dire akan saiya saketa, aikam da dance masa kasaki Fauziyya saiduka baya bada amsa saidai duka kawai

Haka dai tarinka shiga tana futa har aka raba auren nan, ba'adad'e da raba aurenba dan watanta biyu aikam sai ga doctor faruq nan 

Yasamu Alhaji yace yanasan auren “yarsa Fauziyya, yakuma gaya masa bayasan ad’auki lokaci
Amsa masa yay ace amman yabari ta gama iddah kafun nan sai ayi maganar auren

Ahaka suka rabu inda aka yi masa farfesu kamar yadda Boka nakan dutse yalabarta musu

Yaci kuwa sosai, aikam sunji dad’i ba kad’an ba
dan suna ganin burin su yakusa cika akan sa

Bayan wata d'aya da tafiyar doctor yadawo su Mm Balaraba ma anzata aiki baiyiba


 Saigashi da manyan ledoji da kud'i yakawowa Fauziyya, itakam sai yau'ki take tana wani rangwad'a alamar ta isa d'in nan
 Saida tagama yau'kin sannan taje, doctor faruq kuwa kamar zai haukace sanda yaganta haka yayta zuba yana yaba kyan ta(wanda nikam dana ganta kamar nayi kuka dan rashin had'uwa????????) 

 Wasa² soyayya mai 'karfice tashiga tsakaninsu inda take samun kud'i yadda take so tayi mai ta'kara fari, gashi tasha, shaka fashe tayi wata irin 'kiba sosai

Anas kuwa tun abun nabashi mamaki har yadaina, yazuba musu ido kawai dan dai yasan wannan abun bana Allah bane

Babu abun da yake damunsa kamar rashin jin labarin Hapsatu dabaiyiba

 Yau tun safe su Mm Balaraba ke shiri ita da Fauziyya dan yaune za'a saka ranar auren su akuma kawo lefe dakud'in nagani inaso

Sai wajen 12:09pm sannan suka iso Alhaji da kakah hajja sai gyaran gida ake anata gwalli za’a “yarsu zata auri mai kud’i
Shidai Alhaji sbd kar kaka hajja tace zata tsine masa yasa yakeyin wasu abubuwan amman badan ransa yanasoba
Kuma abunda yafi d’aga masa hankalinsa shine yanasan yatambayi ina su Hapsatu suke amman saiya kasa kwata²

Koda family 'n su faruq sukazo sun raina wannan gidan da faruq yaketa rawar 'kafa akansu
Saida sukaga amaryar ma sannan sukai dana sanin zuwan dasukai, dan waye baisan family d'insuba wajen bin bokaye da malamai har la'kabi ake musu da "ya"yan Allah bani sbd dukkan su halinsu d'aya

Hakadai sukai duk abunda yakamata inda suka kawo lefe akwati 8 da bakko guda 2 anzuba kaya sosai
Nan aka saka sati biyu dan haka faruq yace kuma yace kar akawota da komai yasaka komai acikin gidan sa

In kukaga Fauziyya abun saiya baku mamaki sosai dan babu kunya tazo tanata dudduba kayan tunkan ba’kin sutafi

Haka aka tafi da ita abaki anata zaginsu
Itakam ko ajikinta saima shewa take da bud’a

yarone yayi sallama, aka amsa yace kawu Anas yana nan
Akace ey
Yace ana sallama dashi awaje
Toh, kace waye
Futa yay, bai dad’eba yadawo
Ance wai ansamu labarin wanda yagansu zasu hau mota subar gari
Suwa fa inji Mm Balaraba
Anas ne yafuto dasauri yace A’a wannan zance nane
Muje ko tasa yaron yay suka futa daga gidan ashirin yabashi yace ngd kaji yaron kirki

Amsa yay yana ta murna yace angode kawu

Yana futa yaga wani mutum abakin kofa dasauri ya'karasa suka gaisa

Mutumun ne yace yawwa wannan yarinyar daka bamu cigiya anganta amman kuma wanda yaganta yace ansaidasune gawasu mutane
Masu siyan yara a garin Abujah 

Mekace wannan yarinyar fa tacikin wayata
Tabbas ita nake nufi dan har hotunan su yanunamun suna cikin adai-daita za’asiyar dasu kuma dama mai adai-daitar Saida yara suke shida mahaifiyar sa, suna zaune ne atashar kaduna, kuma sunyi hatsari sun mutu gaba d’aya
Shine nazo in gaya maka maka dan kar ka cigaba da neman su
Tunda antabbatar da duk yaran da suka d’auka yankasu akeyi

Wata juwace tad'auki Anas yayi baya luuuuuuuuu..................... ✍????✍????✍????

Keep waiting my fan’s????????????????????
Hallmarth ????????????
[04/02, 8:02 AM] Ummuh Fateemah????????????: ????????????????????????????????????
????????????????????????????????
DASHEN ALLAH
WRITING ASSOCIATION

‘DAN HAKIN????DAKA RAINA????????
Story and written by

*SADIYA •A• UMAR*

{UMMUH FATEEMAH}

????—5⃣3⃣&5⃣4⃣

……………luuuu yay yafad’i ‘kasa sumamme mutanen gurin da kuma d’an sandan ne suka taimaka aka saka masa ruwa yafarfad’o bayan sun yayyafa masa

Sosai Anas yaji wannan batun danji yay kamar yagama samun farin ciki dajin dad’i kenan arayuwarsa taduniya dan yana matu’kar san Hapsatu amman kuma yakasa fad’a mata sbd gudun karya ja mata masifa

Sai yau yake daya sanin dabai auretaba yabar garin da itaba, dayanzu tana tare dashi

Hakadai akai ta ban baki anata yi musu jaje, su Mm Balaraba kuwa kamar mutuniyar kirki harda kukan munafurci itada Fauziyya

Alhaji kuwa jiyay kamar ancire masa wata laka daga jikinsa, duk jiyay yarasa duk wata nutsuwar sa da kwanciyar hankalin sa  

Balaraba kam da Fauziyya ji sukai wannan labarin yafimusu ko wane albishir dad’i dan ji suke kamar yau sallah, sai juyi suke suna shewa abunsu, kamar ba gobe

Wasa² saida aka had’awa kawu Anas da addu’oin samun nutsuwa sannan yadawo hayyacinsa

Sosai yarame yayi ba'ki gaba d'aya yacanja kamar ba kawu Anas d'an gayu da kwalliyaba

Abu kamar wasa bikin Fauziyya sai ‘kara sowa yake inda Jazuli babu alamar lpy atare dashi sam kullum haukar tasa cigaba take, daga ”karshema gidan mahaukata aka kaishi, dan zaifi samun kulawa acan

Tun saura sati biyu aka kai Fauziyya gidan gyaran jiki anata gwalli, duk, ‘kauyen su babu wadda ta auri mai kud’i kamar ta intabiyo hanya kokai waye saika caya ta wuce sannan kawuce

” ya”yan gidan Alhaji Hamisu d’an kakah hajja sune suka dawo ‘kawayen ta, dan sune suke da kud’i suma a ‘kauyen

Yau ce takama ranar d’aurin aure kamar yadda yakama alissafi
Ansha faty anci DJ angaji sosai tun jiya yau kuma za’ad’aura aurene da kuma kai amarya

Ahanyar su ta zuwa d’aurin aure su sani ‘kannen Fauziyya suka had’u da wan mijinta b………………….


A6angaren su Hapsatu kuwa saida ta kammala aikin komai sannan tasallami kowa sannan tazauna akan tabarma dan jiran “Baba mlm idi”

  Yajuma sannan yafuto wajen gaf da magriba dan haka saida yaje sallar Isha'i sannan takai masa wani abuncin da ruwa yaci yasha


Sannan tai musu shimfid'a atsakar gida dayake akwai wutar nefa dan haka suka zama idan yaranta suna nan

Saida yakammala, sannan ta bashi gurin zama yazauna, suka ‘kara gaisawa sannan, yace mata Rabi’atu maiya kawoki nan garin ne keda kike aure agarin kano, can ‘kauyen rano

Baba mlm ba rabi’tu bace “yar tace Hapsatu wadda suke kawo muku kunu ko fura idan Ummerh ta dama

A’a dai A’a dai A’a dai, karki ce mun Hapsatu ce, itace baba

Kuka yasaka yana tafa hannuwa yace kuma kinyi kama da ita sak dan wlh baku da maraba, keda RABI'ATU

Allah kenan mai yadda yaso da bawan sa
Ina ita innar taki tak?
Aurene yakawoki nan?
Ina sirikin namu yake?
Tunda nazo bangan saba

Sunkuyar da kanta tai 'kasa taji wata kwallah tacika mata idan ta, tace baba, ai Ummerh na ta dad'e da mutuwa


Mekikace Hapsatu ban fahimce kiba , Rabi'atu d'ince tarasu, kuka ya'kara sakawa harda shar6ar majina



 Kayi ha'kuri baba haka Allah yaso, Tooo yaushe akai aurenki Hapsatu 
Baba ba aure nayi ba, zaro ido yayi yace ba aure kikai ba, mekikeyi agidan nan zaman kanki kike yi Hapsatu 

Ey, baba
Innalillahi wa inna ilaihi raji’un Hapsatu inashi Alhajin yake da Kakah hajja menene amfanin su dazasu barki kina zaman kanki bazasu ri’ke kiba

Kuka tasaka tana yinsa da'karfin ta kanaji kasan tun daga 'kar'kashin zuciyarta yake zuwa, abdad'e ana danneshi, na zallar ba'kin ciki ne da 6acin rai, duk wanda yake sauraron sautin kukan ta saiyajishi acikin jikinsa sbd rad'ad'i dazafin da sautin ke futarwa

Baba malam idii ne yace Hapsatu daina kuka kinji gaya mun meyake faruwa inji

Babah dan Allah suwaye dangina kuma a ina suke inasan zuwa cikin su nima inji dad'in da mutane sukeji idan suna tare da 'yan uwansu


  Zan fad'a miki Hapsatu amman dafari dai kidaina kukan kifad'amun meyake damun ki inji
 Nima sai in baki labarin 'yan uwanki yanzunnan


Rage sautin kukan tai tad'ago idanunta dasukai jaaa jaajirrr tace baba, nidai tunda nataso naganni tare da ummerh ta acikin Wannan gidan kuma ban waye dakuba sosai lokaci d'aya muka rasa BAFFA tun banda wayau daga baya kuma muka rasaka, kullum natambayi  Ummerh sai tace mun inyi hakuri zataban labarin inda kukaje, kuma BAFFANA yana kawo mana sa'ko dan yana samun labarin mu daga baya kuma yadaina kawo mana komai 


 Tiryan tiryan Hapsatu tabashi labarin komai daya faru arayuwarsu bata 6oye masa komai ba har wahalar dasuka sha da kuma shekarun da suka d'auka acikin garin kaduna



Sosai Baba mlm idiii yatausaya musu wani gurin ma saida yay kuka yace meyasa ya'auro wad'an nan ahalin, wanda ake musu take kala²,   "kwar kwasa fidda na kogo" ai indai sukai shiga saisun fitar dana ciki, in kuma babu to baka isa kashigoba


Baba Kakah Hajja ce tasashi yay auren ai, kakah Hajja ita awa kuma
Baba ai ita kakar muce

Inji wa yace miki
Inji Abban mu

Hmmm ???? murmushi yay yace a’a wannan batun ba haka yake ba Hapsatu

Yaya yake Baba ban gane ba sam
Zan baki labari komai yanzu Hapsatu

gyara zaman ta tai ta maida nutsuwarta kansa dan tanasan taji labarin Ahalinta itama


  ALHAJI IBRAHIM MAI SHADDAH

shine kakan Ummerh ki
An haifesane agarin kano acikin unguwar yakasai alayin ‘kofar mata anan ne gidan su yake

Susu biyu iyayen su suka haifa inda suka basu ilimi da tarbiya dai² misali kakan Ummerh ki yayi makarantar primary dashi da ‘kanin sa musa wanda daga nan suka tsaya sai suka kama kasuwanci sosai

 Sana'ar shadda shine kasuwancin gidan kakan nin ummerh ki susu biyu suka taso Ibrahim da kuma Musa suna san junan su sosai dan idan babu d'aya to d'aya bazai iya koda zaman kasuwa bane


Sun ginu akan sana'ar saida shadda sosai sannan Allah yay wa iyayen su rasuwa wanda hatsarin mota yakashesu ahanyarsu tadawowa daga YAMAI sunkaiwa danginsu ziyara


Sosai mutuwar iyayen su ta gigitasu wanda kakan JAURO mahaifina kenan  yaso yad'aukesu amman sukace abarsu suci gaba da harkar kasuwancin su anan kawai

Babu yadda suka iya dole suka barsu inda kakan JAURO yadawo kano da zama badan yana soba
Saidan yakula da yaran d’an uwansa tunda iyayensu d’aya

Kakan Ummerh ki shiya sha nono yabawa kakan JAURO

Yataho da JAURO lokacin shima baifi sa’an suba inda suka cigaba da kasuwanci tare sosai suke girmama junan su wanda daga ‘karshema kakan JAURO yayi aure ya auri HAJIYA TABAWA

HAJIYA TABAWA macece mai hkrn gaske wadda bata da saka ido ko kuma ba'kin ciki akan abun wani


Kuma duk iya abunda zaka mata bazata ta6a nuna kayi mata laifiba tsakaninta dakai addu'a kawai da kuma nasiha akan ka gyara

Haka ta kwashi shekaru amman bata ta6a haihuwa ba har su IBRAHIM da MUSA da JAURO sukai aure

Basu dad’e dayin aure ba tasamu ciki inda wannan ciki shine yazama ajalinta dan tunda tasamu cikin nan kullum cikin ciwo take yau da lpy gobe babu lpy

Randa ta haihu kuwa ranar tarasu inda tahaifi d’anta namiji aka saka masa suna NAZIRU

Sosai su IBRAHIM suke kula da yaron nan wanda kakan Jauro badan yasoba ya’kara aure inda ya auri Kaka Hajjah

Hjy mashid’a kenan iyayenta ‘yan kano tu jiddane shiyasa idanunta suke abud’e zam²

   Bata ganin kowa da arzi'ki shigowarta wannan gida yafara haddasa bala'i wanda kakan Jauro yasha yi mata fad'a da kuma takara amman bata gani


Matar Ibrahim da musa sun haihu rana d'aya inda matar Ibrahim tahaifi namiji, matar musa kuma ta haifi mace

Namijin aka saka masa suna Hashim, macen kuma fauxiya wadda akeceda Mamie, Hashim kuma ake ce masa Baffan

  Matar jauro bata samu cikiba saida aka yaye yaran Ibrahim da musa


Sannan tasamu ciki sunyi murna sosai inda tacigaba da renon cikin ta harta haihu d'anta namiji aka saka masa idiris

Bayan ta haihune babu dad’ewa Allah yay wa kakan Jauro rasuwa
Inda wannan rasuwa ta girgiza wannan family sosai

Sunyi kukan rashin baban su sosai da kuna kewarsa

Kakan Jauro bai dad’e da rasuwaba kaka Hajjah tace tanada ciki wanda wannan cikin nata ma ba’asan dashiba yakai kusan wata 4

Alokacin ne kuma IBRAHIN mai shadda shida 'yan uwan sa suka gida makeken ESTATE acikin garin RANO


Wanda gidane nagani nafad'a acan suka tare suda matansu da iyalinsu baki d'aya inda suka baje gidan su nagado suka gina wani katafaren gida agurin 


Haya suka saka suka cigaba da rayuwarsu acikin garin RANO

Tun daga wannan haihuwar da sukai basu ‘kara haihuwa ba sudukan su Kamar had’in baki

Yau tun safe kaka Hajjah take……………. ✍????✍????✍????✍????✍????✍????✍????✍????✍????

Keep waiting my fan’s????????????????

Hallmarth ce ????????????

[04/02, 8:02 AM] Ummuh Fateemah????????????: ????????????????????????????????????
????????????????????????????????
DASHEN ALLAH
WRITING ASSOCIATION

‘DAN HAKIN????DAKA RAINA????????
Story and written by

*SADIYA •A• UMAR*

{UMMUH FATEEMAH}

????— 5⃣5⃣&5⃣6⃣

………. Tun safe kakah hajja take na’kuda inda bata haihuba saida ta kwana asibiti ta haifi “yara mace tana haihuwar ta kuma yarinyar tarasu

Ba’karamun ba’kin ciki tajiba narasuwar yarinyar taba wanda saida ta dad’e tana jinya sannan tadawo dai²

Haka rayuwa taci gaba kakah hajja tana kula da Naziru amman kuma wahalar dayakesha takai intaha
Wanda daga ”karshe wajen Aunty Safiyya yakoma matar Ibrahim
Inda tahad’ashi da danta Hashim take kulawa dasu

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40Next page

Leave a Reply

Back to top button