DAN HAKIN DAKA RAINA COMPLETE NOVEL

DAN HAKIN DAKA RAINA???? COMPLETE NOVEL

Haka rayuwa taci gaba da tafiya yau dad’i gobe akasinsa harsu Hashim suka kammala karatun degree da matter’s d’insu

Inda aka had’a auren Hashim da Fauziyya
Shikuma idiris ya auri wata wadda ake ce mata maryam
Naziru kuma ya’auri karima

Acikin garin RANO iyayen su suka gina musu suma nasu makeken estate d’in suka fara tasu rayuwar mai tsafta dan bala’in kakah hajja kullum ”karuwa yake
Suma kasuwanci suke dan iyayen su basu ‘kyalesuba suna aikin gomnati kad’ay ba

Sana’ar shadda da kuma wasu sana’oin duk sukeyi ba wasa

 Matar Naziru ita ta fara haihuwar d'an ta namiji aka saka masa sunan kawu Ibrahim 

Sai matar idiris itama ta haifi d’anta namiji itama, aka saka masa sunan kawu musa

Saida Ibrahim da musa suka girma har sukai shekara 11 sannan matar Baffan ki tasamu ciki tahaifi yaranta guda uku biyu maza d'aya mace ake ce musu hasan da usaini ita kuma macen aka saka mata Rabi'atu 
Sosai suka taso cikin gata daso da 'kauna wanda bazai misaltuba agurin iyayen suba da kakan ninsu



Ranar wata wata talata ranar dabazamu manta taba itace ranar da wuta takama acikin estate d'in su kakan Ummerh ki wanda da dare ne kafun motar kwana-kwana tazo gidan nan ya'kone sosai, dukkan su babu wanda aka futar da rai acikin su

Amman abun mamakin shine wutar bata ta6a 6angaren kakah hajja ba ko kad’an itace ma ta futo take ihun wuta²

Haka akai musu sallah aka sallaci gawarsu wanda duk sun 'kok'kone sosai



  Babah Ibrahim Ashe kafun yamutu yabawa Hashim da Fauziyya dukkan takaddun dukiyarsu da komai wanda kaka hajja bata sani ba

Kuma yace karsu gaya mata dan ba alkairi bace wannan matar ba

Bayan sun rasu ne taji har yau ba’ai zancen dukiyarsu ba gashi sun doshi shekara hankalinta yatashi dan tai tunanin za’ai maganar kuma taji shiru

Taso tai magana amman sai taga idan tai maganar za’ace wazata bawa tunda itadai bata ta6a haihuwa ba acikin su

Ahaka tayi hkr ta share amman kuma daga ‘kasa tanata yi musu bita da kulli danta gane ina suka ajiye wasu takaddu na dukiyar tasu

Tunda tayi bugun cikin dai duk abanza dan bataji wani labari ba

Ranar wata juma'a da safe Naziru yatashi daciwon ciki wanda aka d'aukesa zuwa asibiti kafin suje yaras





Ba'a dad'eba itama matar sa tarasu

Abun mamaki sai Kakah hajja tace abata d’an Naziru tari’ke sbd yanzu bashi da iyaye ita kuma bata da d’a abar mata shi

Dafarko nida baffan ki bamu yaddaba amman saita rink’a kuka harda hawaye wai zamu nuna mata wariyar launin fata dan munga bata ta6a haihuwa ba

 Haka tacigaba da ri'ke Ibrahim awajenta tun yana d'an shekara 2 tari'ke Abban ki wanda yafara basa wahala daga farko 

Aikuwa Baffan ki ya ‘ke’keshe idan sa yace tabashi d’an sa inba hakaba hukuma ce zata rabasu
Taji tsoro sosai anan tace bazata ‘karaba yayi hkr dan jan ido yanuna mata sosai akan Ibrahim

  Daga ''karshe tayi hkr ta rikesa amman kuma idan yay mata abu kad'an sai masifa da bala'i zatai tai masa

Shekarar Ibrahim 6 agurinta tayi aure ta auri wani mai kud’in gaske bata dad’e da auren saba tasamu ciki ta haifi d’anta namiji aka sama masa suna Hamisu

  Sosai take nunawa d'an nan nata soda 'kauna da kuma sangartasa datakeyi sosai da kud'i sbd kasancewar mahaifinsa yana da kud'i


Hamisu yanada shekara 10 mahaifinsa yarasu inda kaka Hajjah tayi ba'kin ciki amman kuma tayi murna dan yabar musu dukiya mai yawa

Takama kasuwanci Kamar babu gobe

Anan harkar kasuwancin ta tahad’u da mamar Balaraba hjy kaltum wadda ta ‘kara bud’e mata idan ta tass suke bin malamai da bokaye

Sosai suke shan sha'anin su yadda suka ga dama
 Baffan ki bai ta6a kula taba saidai daga ''karshe yad'auko Ibrahim yadawo dashi wajen Fauziyya 

Tahad’ashi shida su hassan da rabi’atu taci gaba da rainon su

Haka rayuwa taci gaba da tafiya inda kowa yake cin gashin kansa

Sam bama shiga safgar kakah hajja dan tunda tayi aure ta 'karo wula'kanci sosai 



Bare yanzu kuma datake zawarci

Ita irin matan nan ne masu ‘karamun jiki, suci zamaninsu suci nawasu, sannan kuma tunda ba haihuwa takeba tsufanta bai nuna ba sam gakuma kud’i sun zauna mata kota ita, sai she’ke aya da kuma bariki

 Hamisu a'kasar waje yayi karatunsa na primary da secondary har university ma acan yayi shiyasa ya'kara kangarewa gashi kuma yahd'u da abokai marasa ji 

Sai suka had’u suka kangare babu wanda zai kwa6esu idan suna abunsu

Wani lokacinne ma idan abun ya ishi baffa saiya kirasa yay masa fad’a amman abanza dan baji yake ba

Daga ‘karshema yafuta sha’aninsu gaba d’aya

Baffan ki mutum ne mai yawaita kyauta da sadaka dan kullum sai anyi girkin almajirai agidan sa masu dafa musu abunci yad'auka na musamman, sannan kuma dukkan 'karshen wata sai yay rabon kayan abunci daga company sa kuma baya ta6a gajiya

Yakan kuma shiga makarantar islamiyya da allo da boko yaga abunda basu dashi yay musu sannan kuma yad’auki nauyin karatun yara dayawa harsu kammala

Shiya gina asibitin garin Rano dakika ganta

Dan haka suma yaransa suka taso da wannan tarbiyyar basu da rowa ko kad’an, sannan kuma uwa uba Aunty Fauziyya itama bata da rowa sam hannunta abud’e yake

Lokacin da ummerh ki ta girma takai shekarun aure, lokacin ne kakah hajja tazo akan lalle lalle saita auri Hamisu d’anta inda Baffanki yace atambayeta tana sansa itakam tace aa batasan sa

Ba’karamun ba’kin ciki kakah hajja tajiba ba, alokacin taso aimata auren dole amman Baffan ki yace A’a sam shibadashiba za’ai wannan rayuwarba

 Alokacin ne kuma IBRAHIN yanunawa Baffan shifa yanasan Rabi'atu kuma itama tana sansa

Aikam babu 6ata lokaci akai auren su anyi biki nagani na fad’a inda suka tare agidan su wanda baffa yagina musu gidane babba sosai na “ya”yan…………………….✍????✍????✍????????

Keep waiting my fan’s????????????????????

Hallmarth ce ????????????

[04/02, 8:02 AM] Ummuh Fateemah????????????: ????????????????????????????????????
????????????????????????????????
DASHEN ALLAH
WRITING ASSOCIATION

‘DAN HAKIN????DAKA RAINA????????
Story and written by

*SADIYA •A• UMAR*

{UMMUH FATEEMAH}

????— 5⃣7⃣&5⃣8⃣

…………. Na “ya”yan manyane sosai duk wanda yashiga gidan sai yasan yashiga gida mai kyau mai rai da lpy sosai ma

Ranar da kakah hajja taje gidan banda ba’ka’ken magan ganu da habaici babu abunda takeyi

Tana samun nasarar juya Ibrahim sosai sbd yana bata girmar uwa dan ganinta yake Kamar mahaifiyar sa

Ba’a dad’eba tasa Hamisu yayi aure ya’auro wata yarinyar yar wani mai kud’i sosai

Inda tasaka dole sai Baffan ki yagina masa gida irin na Ibrahim acewar ai duka d’ayane

Haka yasa akai masa shima gidan sa amman baikama ‘kafar na Ibrahim ba sam anyi masa shima dai dai² gwargwadon iyawarsa

Sosai wannan abun ya’kona mata rai akan yaya za’ai baza’ai masa irin na Ibrahim ba

Amman ganin shima gidan na kece sa’ane yasata hkr kawai Amman badan taso ba

Haka akaci gaba da rayuwa inda shikuma musa yaron wajena shima yayi aure

Baffan ki bai gajiba yayi masa gida shima mai kyau sosai inda suke zaune shida matarsa

Akwana atashi babu waha sai gashi ummerh ki tasamu ciki wanda tahaifi d’anta namiji wanda ranar data haifesa aka samu wani yasacesa da dad dare a Asibiti sosai hankalin mu yatashi muka shiga wani irin tashin hankali, abu Kamar wasa²

Har akai satuttuka babu labarin wannan jariri sam




Tun ana nema har aka hkr aka fawwalawa Allah komai dan yakai shekara 8 Amman ba'a gansaba hotonsa kawai muke dashi sai kuma wata sheda da mukewa Ahalinmu zarar an haifi yaro to ana masa wanka muke yiwa yaro ita abayan sa za'a yayyanka shi sau uku  amasa tabo


Sbd koda ya6ata in aka gansa ana duba wannan shedar za'a gane sa

Haka muka hkr muka cigaba da addu’a koza’a gansa

Amman dai shiru kakeji
Haka rayuwa taci gaba tun daga wannan haihuwar kuma ummerh tadad’e sannan ta haihu inda tahaifeki aka saka miki suna Hapsatu wanda alokacin kuma Hamisu yanada raya 3 mata

 Musa kuma matar sa bata ta6a haihuwa ba
 Saida kika kai shekara 2 sannan matar musa ta haihu mace yarinyar ta itama kamarki tunda dukkan mu asalin buzayene Amman farare

Duk wanda zaiga “ya”yan zuri’armu to babu mummuna kaf d’in mu dan har wasu suna cewa family’n mu family’n aljanu, sbd kyau da Allah ya azurtamu dashi

Haka kuka taso Kamar tagwaye komai naku iri d'aya ake muku shi mukan zauna abakin wata bishiyar tsamiya nida baffan ki, dayake shi ma'abocin shan furane ko kunun tsamiya, to idan Ummerh ki tayi saita aikoku keda khadija ku kawo mana 




Anan zakuyi tawasa har sai mun tashi sannan kuma musa akaiku gida
 Tin ban iya shan furaba da kunu harna koya sosai sbd kullum ne sai ankawo mana ita




 Ranar wata asabar wadda takasance mun ba'kar rana ranar ina zaune nida baffan ki da yamma sai kawai yacemun shifa kawai so yake yabar garin nan kuma sam² bayasan yadawo koda wasa

Abun yad’auremun kai amman sai nace masa meyafaru yacemun babu komai amman shidai kawai tafiya zaiyi

Da’kar na lalla6ashi aka kwana washe gari kuwa yagama had’a komai nashi yace tafiya zaiyi nida Mamie kakarki munyi munyi amman ina yace shi sam tafiya zaiyi kuma da yaransa su hassan

Haka suka had’a kayan su suka tafi musa ne yashiga motar danya ja yakaisu tasha subar gari, aikuwa khadeeeja tasaka kuka saita bisu

Haka suka tafi tare inda nidai bansan ina suka tafi ba yace dai ko a ina yake idan ya nutsu zai kirani

Ahaka muka rabu kowa yana kukan wannan tashin hankali dan agurin mu tashin hankali ne dan tunda muke dashi baya iya tafiyar kwana d’aya batare da mu ba

Amman haka kawai baka tatan yace tafiya zaiyi kuma fur ya'kijin lallashi bare ban baki


Haka suka tafi munaji muna gani

Bayan musa yakaisu tasha ne ahanyarsa tadawowa yayi accident yarasu

Lokacin da mukaje gurin munshiga tashin hankali sosai dan duka motar sa takama da wuta da'kar aka ciroshi daga ciki muka d'aukesa aka kaisa asibiti 

Da’kar aka samu yadawo hayyacin sa anan ne muke tambayarsa khadeeja yace ‘kin biyoshi tayi tace ita agurin baffa da kawu hassan zata zauna

Da misalin ‘karfe 11:00pm na dare yace ga garin kunan

Sosai muka shiga rud’ani haka mukai gida dashi inda kuma har akai sadakar bakwai 7 bamuji labarin baffan kiba

Kuma gashi bamu tambayi musa wace tasha yakai suba bare muje garin cigiya

 Wadda kika kar6o sa'ko awajenta wannan mai d'inkin itace matar kawunki musa 




   Bayan tafiyar baffan ki da kamar shekara 3 babu shi babu labarin su gaba d'aya

Anan kakah hajja tafara baza nata mulkin inda bamusan hawa ba bamusan sauka ba kawai saiji mukai ankawo mana sammaci daga kotu

Mudai munsan bamuyi wani laifiba amman haka muka shirya ranar zuwa kotu mukaje
Inda aka fara gabatar da shati’a akan Baffan ki

Tace abunda yasa Baffan ki guduwa wai sbd yaciyo bashi ne yayi masa yawa

Kuma ita take ta biya sannan kuma yanzu ya gudu takawo wasu takaddu wanda ga yarjejeniya nan duk sun suna yaci bashin kuma tabiya
Dan bamu yaddaba amman da mukaga saka hannunsa da sign d’insa sai muka yadda dan ko mafarki nake zan gane saka hannunsa

Haka munaji muna gani aka saka gidajen sa danamu na gado nagarin kano aka siyar aka bata kud'inta

Duk da hakan ma saida aka yanki wani gurin daga cikin gidan ku aka siyar aka cika mata kud’inta

Daga nan kuma d'an sauran 'yan canjin dasuka rage mana muka ci gaba da siyarda shaddar mu kamar yadda muka saba




 Ana nan wata rana kakah hajja tashigo gidan danake haya tace in tashi nace mata ai kud'ina bai 'kare ba tace ita sam saina tashi inba hakaba kuma yanzunnan nima taga bayana 

Anan take gayamun dukkan abubuwan data aikata tun daga mutuwar kakan Jauro wanda tabuga tabuga danta samu ciki bata samuba sai daga baya tana ganin tasamu ta kasheshi da kuma mutuwar Alhaji Ibrahim mai shadda na wutar data kama agidan sa da kuma mutuwar d’ana Ibrahim da kuma karayar arzi’kin mu

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40Next page

Leave a Reply

Back to top button