DAN HAKIN DAKA RAINA COMPLETE NOVEL

DAN HAKIN DAKA RAINA???? COMPLETE NOVEL

Kama hanyar d’akin yay, sai Baba mlm yataresa, aikam mom d’in Nusaiba tun kud’esa tayi yakusa fad’uwa tace maza jeka d’auko min ita

Shiga yayi d’akin yaga tana sallah
Juyowa yay yafuto
Kallonsa tai tace tana ina
Cewa yay sallah take
To tagama ta futo maza

Hapsatu ce tayi sallama ta futo da hijab d’inta da carbi a hannunta tace lpy hjy mekuma yafaru wanna d’iban albarkar yayi yawa haka

Uwar kice banyi miki kashedin karki 'kara siyarwa da 'yata wannan gur6a taccen abuncin ba kuma bana gaya miki cewa ba tunda bazakiyimun aikiba banasan sakejin kina saida wani abu ba

Nusaibace, tace haba mom wai meyake damun kine
Tayaya zakice tadaina san’arta, adalili dame yasaka

Adalilin ubanki nace adalilin ubanki,inaga yanzu kin fahimta ko, ina han’koro akan lpyr ki ke kuma kina neman cimun mutunci agaban mutane, saboda kinuna ban isaba

Hapsatu ce tayi Murmushin takaici tace, kiyi hkr in sha Allah zan kiyaye, Nusaiba kidaina yiwa mahaifiyar ki musu su iyaye lalla6a su ake arabu lpy

Banasan in ‘Kara ganin kinzo gidan nan siyan abu ko gaisheni, kinji ko

Toh Ummerh
Ummerh kan ubanki Allah yasuttura
Wuce mutafi

Baba mlm ne yace Allah mai iko
Allah yasa mucika da imani………..

Ai bai kammala fad’aba yaji wani saukar wawan mari wanda tunda yake bai ta6ajin irin saba

Yana d'agowa yaga babar Nusaibace, cewa tai Allah dama ai da iko yake, kuma kullum zakana ganin sababbi indai kana raye
Ina sake sanar daku indai baku fita harkar "yataba, to yanzu muka fara nidaku wlh

Kuka Nusaiba tasake fashewa dashi ta tako zuwa gaban mom d’in tata tace, “yata³ saida tafad’a sau uku sannan tace Allah yakiyaye ni da’kara zama “ya agareki, wlh nayi ba’kin cikin kasancewa “ya agareki nayi dana sani da nadama wlh nazamanki uwa agareni, ina takaici da ba’kin cikin hakan wlh

Allah yamun tsari yakuma kiyayeni daga irin wannan arzi'kin mara anfani
Indai wannan shine arzi'ki bana fatan samunsa har izuwa 'karshen rayuwata

Arzi’ki dabakasan darajar kowaba saita kud’i² wanda ake samunsu aduniya abarsu kuma aduniyar ummmm

Dattin duniya, daud’ar duniya, wanda bazaka ta6a tafiya dasu kabarinkaba
Saidai inkayi aikin alkairi dasu sai yabika
Amman kud’in baza’a ta6a sakaka acikin kabarinka dasu ba

Kuma daga yau nayanke duk wata ala’kata dake karki ‘Kara tunanin kina da “ya Nusaiba arayuwarki, ragowar “ya”yanki sun isheki rayuwa amman nikam nagama daga yau

Kuma zama agidan nan yanzu nafara, daga yau wanan gidan shine gidan mu, kuma family na, dangina, ahalina kuma, abun alfaharina, kuma zanyi tutiya dasu agaban kowa afad’in duniyar nan

Daga yau niba “yarki bace ko family d’inki
Kuma wanda yace miki nazo ganin saurayina to yayi ‘karya danni bani da saurayi agidan nan

Nazo siyan abunci ne agidan nan, amman tunda ance miki harda saurayi nazo gani to nazo ganin saurayin, kuma saina aureshi kodan tabbatar miki da zargin ki

 Juyawa tai takama hannun Baba mlm tace Baba muje sakashi tai ad'akin datake zaton nasane tace kayi hkr baba ni naja muku

Babu komai 'yar nan haka rayuwa take dama yau da dad'i gobe kuma akasinsa

Hakane baba ina zuwa
Futa tai ad’akin ta kalli mahaifiyarta
Tace ina kinji menace
Sannan takama hanya danta shiga d’aki
Jitai andan’kota zuwa baya, mom d’intace tace daga kikace kinyanke ala’ka dani ko
Ey tace babu tsoro atare da ita
Toh kisani karki ‘kar………………….. ✍????✍????✍????

keep waiting my fan's ????????????????

Hallmarth ce ????????????
[04/02, 8:02 AM] Ummuh Fateemah????????????: ????✨????✨????✨
✨????DASHEN ????ALLAH????✨
WRITTER’S✍???? ASSOCIATION
https://chat.whatsapp.com/BHqoOEHjWQz26cyXRvt9V7
????ALKALAMI ✍????YAFI TAKOBI????️
بسم الله الر حمن الر حيم
✨DAN HAKIN???? DAKA RAENAH????????✨

          ????NAH????

SADIYA ABDULLAHI UMAR
????UMMUH FATEEMAH????

????—

     6⃣3⃣&6⃣4⃣

………………….. Toh karki ‘kara kusantar koda hanyar gidanane
Kuma dukkan abunda nake miki najin dad’in rayuwa nayankeshi daga yau
Dukkan wani kud’i danake baki daga yau nadaina baki

Sannan makarantar islamiyya koh boko duka najanye hannuna daga biya miki kud'in makarantar ki
  Kuma komai wahala karki sake kidawo cikin family na

Babu ni ba ke sannan karkiyi tunanin kina da iyaye arayuwarki kodai-dai da minti d’aya
Kisa aranki wad’annan sune iyayenki nahar abada, kinajin na ko ina fatan kin fahimta sosai

Cikin rashin tsoro ko nadama tace nafahimta sosai

 Dukkan abunda yadanganceki zansa ayi waje dashi akawomiki shi gidan ahalin matsiyatan nan kuma koda pics d'inkine sai nasa akawo miki dan bana bu'katar ko tsinkenki, zan fahimtar da mahaifinki, ragowar yaranmu sun ishemu rayuwa, ke kuma kije na sallamaki wa ahalin matsiyata har abadaaaa

Na yadda na amince kuma wannan ahalin da kike ciwa mutunci kika RAINA WATA RANA ZAI TSONE MIKI IDO, Kobadad’e ko ba juma nasan wataran zakiyi nadama mom

Fuuuuuuuuuu tajuya tafuta tana banda other akan ayi sauri atashi mota

Suna shiga takama hanyar gida babu 6ata lokaci tasa aka rin’ka kwaso mata kayan Nusaiba ana shiryawa a akwatunan ta, dukkan wani abu daya danganceta saida aka kwasheshi tsap aka saka mata shi ajakunkunan ta da akwatunan ta


Suna tafiya tashiga d’akin da Hapsatu ta futo, binta Hapsatu tai dan ita takasa magana ma sam

 Zuwa tai ta zauna akusa da ita ta d'aura kanta akan cinyarta tace yarinyar kirki meyasa kikaiwa mahaifiyar ki haka bayan kinsani Kuma kin karanta alittattafai da dama illar bin umar nin iyaye musamman ma uwa, wadda Annabin rahama dakansa saida ya ambaceta sau uku tukunna ya ambaci uba

Meyasa yarinyata, dakin sani bakiyi mata hakaba kin kyaleta tayi dukkan abunda tai niyya inta gama sai abata hkr

D’agoda kanta Nusaiba tai ahankali ta kalli Hapsatu fuskarta tayi jaaa jaaajurrr idanunta sun kumbura sunyi luhu² saboda tsabar kuka da ba’kin cikin abunda yafaru abunka da farar fata duk tafuta hayyacinta sosai, cewa tai Ummerh nah, mom bazata fuskanta ba kikalli yadda ta bangaje Baba ta tunkud’esa sannan hakan bai ishetaba ta wanka masa mari
Koba komai yaci ace taduba girmansa sannan taduba yanayinsa dakuma yaddda yake bata hakuri ko kaffara bazanba wlh nasan baba yagirmeta yayi jika da ita tunda kakana baikaisa girma ba

Ita gaba d’ayanta mom wahaka take bata ganin girman kowa ko mutuncin kowa asangarce ta taso ita kad’ay ce awajen iyayenta sam bata jin nauyi ko Kuma damuwar ta wulakanta mutum matu’kar akace miki bashi da kud’i to zance ya’kare

Ita awajenta mutuncin ka kud’inka shine kad’ay darajarka idan baka da shi wlh zakasha wula’kanci ba kad’anba

Ummerh ki kyaleta watarana zatayi nadama mukuma zamu zame mata
‘DAN HAKIN???? DAKA RAINA
In sha Allah Ummerh karki damu
Hawayenta tashare mata tace kidaina kuka kinji yar Ummerh, gani nake kamar bazaki iya rayuwa acikin wannan gidan namuba, sbd mu Talakawa ne bamasu ‘karfiba

Murmushi Nusaiba tayi tace karki damu Ummerh ta in sha Allah zanyi rayuwa tare daku komai wahala komai d’aci bazan guduba

Allah yasa yarinyar kirki “yar Ummerh ta shafa mata kanta takeyi tana kuka tanata lallashinta

Sallamar kalis ce ta katse mata kukanta dantamanta ma tare suke, shigowa tai har cikin d’akin dataji su suna magana

“Karasowa tai ta rungumeta suka ‘kara saka kuka, kalis ce tace meyasa kikai haka Nusy

Kinsan halin mom kalis ki kyaleta Allah yasa hakan shiyafiye min alkhairi arayuwata

Amman kalis batun makarantar ki fa kinga bamu dad’e da fara zuwa lecture ba

 Murmushi tai tace zancigaba da zuwa har kud'in wannan shekarar ya'kare daga nan saina ha'kura kawai
Haba Nusy kiyi hakuri ki koma wajen mom d'inki kodan karatunki 
A'a ilimun da nake Dashima ya isheni haka, indan dan tabiyamun kud'in makaranta ne bazan komaba wanan ma ilimun danake dashi Allah yasanya masa albarka



Kuka suka cigaba dayi, Hapsatu ce tabasu hakuri da'kar suka ha'kura sukai shiru

Tom ‘yanzu kitaso mutafi makaranta kinji
A’a bazani yauba kikai muku abuncin kawai nisai gobe zani
Gaskiya indai bazakiba nima babu inda zani

 To shikenan, dawowa da Ummerh abuncin kawai, dan nidai babu inda zanje yau ina tare da Ummerh ta sainaji d'umunta

Murmushi Hapsatu tai ta’karaso gurinta kama mata hannu kawai tai suka ”karasa bakin fanfon da aka saka musu atsakar gida tacire mata hijab d’inta tasa’kale akan igiya sannan ta tsugunnar da ita awajen ta saka sabulu ta wanke mata face d’inta tsap sannan tasa Hanki ta goge mata ita tsap

‘Dankwalinta ta kunce tagyara mata yarwatacciyar sumarta ta’kara yi mata parking da band sosai sannan tagyara mata d’aurin d’ankwalin tasaka mata hijab d’inta

 Lip gloss tad'auko ta shafa mata sannan tace maza kutafi makaranta kinji "yar Ummerh ta, karkice a'a kinji indai kinasan Ummerh ki maza kutafi makaranta ayi karatu banda wasa banda tunani Kuma kinji ko

Murmushi tai tarunguneta tanajin wani dad’i da sanyi aranta dan tunda take ba’a ta6a yi mata abunda Hapsatu tai mata ba

Thank you thank you thank you soooo muchhhh Ummerh na

Rakosu tai suka hau adai-daita sannan tayi mata kiss agoahinta tace akula sosai fa yarinyar kirki
Toh Ummerh ta saimun dawo
Allah yay muku albarka gaba d’aya
Ameen Ummerh

Saida taga tafiyarsu sannan takoma gida, tattare komai tayi tashare sannan ma masu aikinta aunzo sukai mata wanke² tad’aura musu fried rice wadda taji vegetables da naman rago
Sannan tasaka turaren wuta mai ‘kamshi tashiga wanka

Bata dad’eba ta futo shiryawa tai tana sauri dan kar abuncinta yakama zuwa tai tajuyesa acikin kularta sannan ta wanke tukunyar

Tadawo tana had'a musu so6o kenan taji anbanko 'kofa,gabanta ne yafad'i ta tashi tana kwashe kayan juice d'in tad'aura akan fridge d'inta wanke gurin tai taji anan duddure akwatuna kamar za'asauke akanta



Kallonsu tai saita d'auke kanta suka gama ajiyewa sannan suka futa, mom d'in Nusaiba ce tashigo itama tana fad'in kina ina, danki tabbatar da da gaske nake kuma kinsanni idan nayi al'kawrin yin abu bana fasawa dan haka gashinan babuni babu ke komai naki nahad'o mikishi

Itakam Hapsatu tama kasa magana dan gani take anya kuwa wannan matar tanada hankali, kodai tasha wani abun

“Yarta tacikinta takewa wannan d’iban albarkar, kai Allah yakyauta

 Kina inane wai

Hapsatu ce tace sun tafi makaranta ai tun d’azu
Toh gashinan kisanar da ita ahalin matsiyata kawai
Fuuuuuuuuuu kamar wata iska tayi waje

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40Next page

Leave a Reply

Back to top button