DAN HAKIN DAKA RAINA???? COMPLETE NOVEL
Itakam Hapsatu tattara akwatunan tai tashiga dasu cikin ad’akin ta tana mamakin wad’an nan kaya saikace lefen ‘yar birni akwati har goma 10 da bakko 4 saida takaisu uwar d’akinta sannan tadawo taci gaba da aikinta
Saida tagama sannan tadawo tashimfid’a tabarma tafara karatun al’kur’aninta
Basu d'auki wani lokaci ba suka dawo, dan lecture biyu garesu suna gamawa kuma suka kamo hanya suka dawo gida, abakin 'kofar gida suka rabu ita da kalis me nafef yayi gaba da ita, ita kuma tashigo gida da sallamarta abakinta, wani dad'i taji jin sautin 'kira'ar Ummerh ta
Wanda tunda take acikin gidansu bata ta6a ganin mom d’inta tayi ba saidai daddy’nta taji yanayi da asuba koda yamma ranar da babu aiki
Shiga tai ta zauna kusa da Hapsatu tana Murmushi, itama tana kai aya ta rungumeta tace andawo kenan
Umm Ummerh
Sannu da dawowa
Maza garuwan wankankican a flask kije kiyi wanka ad’aki, kayanki suna nan ankawo miki kisaka saikizo in baki abunci maza
Kinga yamma ta kusa 5:00pm yanzu harda yan mintina
Toh Ummerh ta ngd sosai
Tashi tai taje tana duba kayan taga ankawo mata komai harda littattafanta da dukkan wasu tarkacenta, wankanta tafara yi sannan tashirya cikin doguwar rigar atamfa blue da fari tayi kyau sosai
Lokacin data gama ma anata kira sallar magariba dan haka ta futo sukai salla itada Hapsatu
Karatun suka cigaba dayi saida akai sallar isha’i sannan sukai sallah
Abuncin su tad’auko musu takaiwa Bb mlm nasa sannan tazau tafara bata abaki, tun lomar farko talumshe idanta sbd dad’in dataji sosai
Haka taita bata harta ''koshi sannan tabata juice d'in tasha sannan itama tafara ci saida suka 'koshi sannan suka tashi
Nusaiba ce ta wanke kwanukan harda na Bb mlm sannan tadawo kusan Ummerh ta ta zauna
Hira suke mai dad'i sosai anan take gaya mata in sha Allah komai zaiyi normal
Koda dare yayi ad’akin Hapsatu suka kwana atare, da’kar ta kwanta akan bed d’in Hapsatu shima saida taga tayi mata jan ido sannan
Washe gari kwa tin sassafe suka kama aiki inda Hapsatu tari’ka mamakin yadda Nusaiba take aiki kamar ba ‘yar masu kud’iba
Itada ‘yan aikinta suka kammala komai suka gama kafun 7:30 sun gama komai, sa6anin da dasai 9:00pm suke gama wasu ayyukan
Sallama sukaji anayi abakin ‘kofa, gaban Nusaiba ne yafad’i rass dan ko amafarki tasan mai wannan muryar………. ✍????✍????✍????
Keep waiting my fan’s????????????????
Hallmarth ce????????????
[04/02, 8:02 AM] Ummuh Fateemah????????????: ????????????????????????????????????
????????????????????????????????
DASHEN ALLAH
WRITING ASSOCIATION
‘DAN HAKIN????DAKA RAINA????????
Story and written by
*SADIYA •A• UMAR*
{UMMUH FATEEMAH}
????—
6⃣7⃣&6⃣8⃣
……………laaaa Ummerh kingan su, mamaki ne ‘karara akan fuskar hapsatu tace too???? Kuce kuna kan hanya
Murmushi sukai suka shigo shikam gogan naka babu alamar wasa akan fuskar sa mamaki yake meya kawota gidansu da daddare kuma harda wani kwanciya akan 'kafar kummansa
Ajiye jakar datake bayansa yay akusa da Hapsatu
Kallonsa tai ta kauda kai tasan halinsane muskilanci
Fahat ne yashiga d'aki da kayan nasu yace waya gaya miki mu mukeyin girki da kanmu
Ey mana baku damai muku ai ku kukeyi, ba boarding school ???? bace bare Kuce za'ai muku
Wannan university ???? ce fa
Ai dai muna siyane ko kuma musaka adafa mana
Hmmm ???? ???? lallema brother waye zai muku biyansu kukeyi
Ey mana
Waya baku kud’in dazaku biyasu to
Allah ne yabamu
Kaiii
Kamar daga sama taji yace
Keeeee kin ishemu da zance da Allah tunda mukazo sai zuba kikeyi tsayyy³
Kallonsa tai ta watsar sannan tace "NI INBAN DAMU DA KASUWA BA KO SAUTUN CIKINTA BANA BAYARWA"
Kai ni kike gayawa haka
Ko kallonsa bataiba tace brother wanka zakayi ko kuma abunci za’akawo maka
Aa baridai afara wankan ko
Sai aci abuncin
Toh
Mamaki Fahat yake dan shidai sau d’aya yata6a ganinta amman kuma tana masa hira kamar sunsan juna
Kuma baisan maiya zaunar da ita agidan ba
Amman komadai menene yasan Ummerh ‘nsu bazata 6oye musu ba
Haka sukai tayi har sukayi wanka sukaci abuncin, su amman magana bata 'kara had'asuba saidai harara kawai
Hapsatu kam saidai ta kallesu ta girgiza kai kawai
WASHE GARI
Koda gari yawaye tunkan sutashi tayi ayyuka dayawa dan lokacin da suka dawo daga masallaci ma ta kammala wasu ayyukan saura kad’an
Mamaki suke sosai akan yadda take aiki babu kasala ko nuna gajiyawa
Saida tagama sannan tai wanka tai shirin tafiya makaranta, kalis kawai take jira
Tana zaune itada Hapsatu suna hira tana nuna mata wasu pics d'in 'yan ajinsu da sukai birthday ???? d'insu sunyi kyau sosai
Hapsatu ce tace kefa yaushene aka haifeki
Ummerh awannan watanne 23 gawata
Kice anyi naki ma
ey Ummerh
To Allah yakai mu shekara mai zuwa sai musakeyin wani koh
Ameen Ummerh na
Sallamar kalis ce tasasu suka katse hirar tasu
Tana shigowa tagaida Hapsatu sannan tace bestie wlh wannan d’an iskan mlm chemistry d’in yaturo assignment kuma yace duk wadda bataiba bazatai test d’insaba ta gobe kuma agoben zai amsa inkika bashi kishiga d’akin test inbiki bashiba kuma shikenan kiji asalansa
Tooo fa yanzu yazamuyi
Mugani, mi’ka mata wayar tai tagani tace ta6 mun bani wlh yanzu yaya zamuyi
Kuma yasin niban ganeba
Kodai muje mucire masa kawai
Haka za’aima
Amman fo komun cire yace shi bayasan na computer
Na rubutu yakeso
To kawai muyi Googling mana
Hakane kam
Fahat ne yace muga aikin naku
Yawwa kagani brother amsar wayar yay yafara dubawa
Ok bari Nauphal yayi muku
Kubada paper guda biyu
Cirowa sukai suka bashi sunata murna
Yanzu kunada lacture ai ko
Ey bro
Toh maza kutafi tunda bayau zai kar6a ba inyaso in kuka dawo yagama
Kusaka sunayenku akan paper’s d’in
Amsa sukai sunata jin dad’i suka rubuta sannan suka tafi
Ummerh zamu tafi
To yaran kirki, Nauphal maza jeka sakasu a nafef katabbata sun shiga sun tafi sannan kadawo
Ummerh kuma ni
Haka nace ko bazakaba
A’a am sorry ???? mom
Oya maza kutafi
Mom yanzufa nashigo gidan bari ind’an d’auki ruwa saimu tafi
Ok
Tafiya yay yad’auki ruwan sannan suka futa yana gaba suna binsa abaya
Sai murgud’a masa baki Nusaiba take
Shikam baima san tanayiba
Saida yatsayar da me nafef sukai masa bayani sannan yabiya suka shiga sannan yajuya yatafi yanata sakin tsaki
Fahat ne yabashi assignment d'insu yace yay musu
Yeahhh meyasa ka amsa daka bari an mata dukan tsiya ai
Duka sai kace wata pri-sec
University fa sukeyi waye zai dakesu kuma
Amman yaya saidai inyi na ‘kawarta amman bazanyi na mara kunyar nan ba
Ni nace kayi ko itace tace kayi
Shagwabe fuska yayi yace haka yeahhhh Allah bata da kunya jiya kanajin takama mun rashin kunya amman bakace komai ba
Ajiye masa takaddun yay yafuta yace in kaga dama kayi inkuma bakaga damarba kabarshi zanyi musu
Tashiyay yasha gabansa yakama kunnensa yace am sorry ???? my big bro
Allah zanyi musu kamar yadda kace kaji bro
Ok yayi matsamun to
Cikin muryar shagwa6a yace A’a am sorry fa nace
Toh naha’kura mana
Amman ka’kiyimun dariya
Kama kunnensa yay yamurd’a sannan yace naha’kura to
Ashhhh yeah akwai zafi ba wlh
‘Dan dukan kansa yay yace ai gwara kaji zafin
Rungumesa yay yace yeah to mukoma ciki kaji karka tafi
Yanzu zan dawo wajen Ummerh zani
Ok tom kadawo da wuri
Matsawa yay yafuta shikuma yakoma yafara aikin daya sakashi
Zuwa yay yaga tanata lazimi kamar yadda tasaba in bata da aikin yi
Zama yay kusa da ita yace Ummerh ta
Na’am d’an ummerh ya akayi ne
Murmushi yay yace Ummerh wai ni Ummerh meya kawo wannan yarinyar gidan nan naga alamar kamar tadawo nan ne da zama
Lpy dai koh
Wlh lpy ba lpy ba
Tofa meya faru Ummerh
Toh fahat abunda yafaru shine……….
Saida tagaya masa komai daya faru sannan ta numfasa tace amman naso takoma wajen mahaifiyar ta danta fahimtar da ita komai to gaskiya yanayin yadda takene yasaka ni na’ki mayar da ita gidan
Hakane Ummerh Allah yasa hakan yazama alkhairi
Nauphal duk akan kunnensa akai komai yaji tsap amman sai yaji tausayinta
Haka sukaita hirarsu har Nauphal yagama yazo shima suka cigaba
Anan ne suke sanar mata da idan suka koma wannan hutun babu dawowa saidai surin’ka waya
To Allah yay mana jagoranci
Ameen
Haka suka cigaba dayin hirarsu har wajen sallar la’asar sannan suka tafi masallaci ita kuma hapsatu takama ayyukanta na girkin dare
Lokacin dasu Nusaiba suka dawo ankusa kiran magrib, abakin 'kofa taci karo da Nauphal yatakata bai saniba
Aikam data zumduma ihuuuu tana fad'in ya kasheta
Dur’kushewa tai abakin ‘kofar tafara rera kuka, ummerh kinga wannan yaron yakaryamun ‘kafa ko, ummerh kitaimakeni wayyo ummerh taaaa
Wai menene
‘Kafata mana ka karyamun wlh bazan yaddaba
Yaro dakai sai muguntar tsiya Allah saiya sakamun, kuma wlh saina gayaka da Ummerh ta
Wayyyo Ummer zoki gani bayan karyani dayay harda jini ma wlh wajen yakeyi
Mugani wai
Bazan nunaba
Ri’ke ‘kafar tai tanata juyi awajen
Fahat bayanan
Hapsatu datake sallah
Allah Allah take ta idar tazo tagani meyake faruwa
Shikuwa Nauphal daya gaji da masifar kukanta saka hannu yay ya d'auketa tsalak yashiga da ita cikin gidan
Sabon kuka tasaki tana cewa yasaketa yana fama mata ciwon ta
Banza yay mata yaje ya ajiyeta akan kujerar tsakar gudan yana cije le6ensa na 'kasa
Mugani
A’a bazan nuna makaba ka’kara jimun wani
Hapsatu ce ta futo tace menene yake faruwa daughter
Wani sabon kukan ta'kara saki
Tace Yawwa Ummerh kin gani yadda yakaryani yafutarmin da jini ajiki na
Hapsatu ce tace mugani
Duba ‘kafar tai kawai d’an kurjewa tayi awajen yatsun ta jini kad’an ne yafuto
Innalillahi wa inna ilaihirraji'unnn wannan ciwon haka ina kake kallo Nauphal kadaketa haka
Cije lip d’insa na ‘kasa yay yace Ummerh n………………✍????✍????✍????
Keep waiting my fan’s????????
Hallmarth ce ????????????
[04/02, 8:02 AM] Ummuh Fateemah????????????: ????✨????✨????✨
✨????DASHEN ????ALLAH????✨
WRITTER’S✍???? ASSOCIATION
https://chat.whatsapp.com/BHqoOEHjWQz26cyXRvt9V7
????ALKALAMI ✍????YAFI TAKOBI????️
بسم الله الر حمن الر حيم
✨DAN HAKIN???? DAKA RAENAH????????✨