DAN HAKIN DAKA RAINA???? COMPLETE NOVEL
Allah yakiyaye wlh wannan yazama saurayina, ta6
Wannan yazama saurayina ai rainonsa zanyi saiya bala…………….. ✍????✍????✍????
Keep waiting my fan’s????????
Hallmarth ce ????????????
[04/02, 8:02 AM] Ummuh Fateemah????????????: ????????????????????????????????????
????????????????????????????????
DASHEN ALLAH
WRITING ASSOCIATION
‘DAN HAKIN????DAKA RAINA????????
Story and written by
*SADIYA •A• UMAR*
{UMMUH FATEEMAH}
????—
7⃣9⃣&8⃣0⃣
………………Shida wata yarinyace kuma ko kamun kai bata da sai rawa take yana mata li’ki
Abun yabawa Hapsatu mamaki tooo wacece wannan yarinyar kuma ina yasamota
Yi shiru 'yar Ummerh taso muje kiyi wanka, kicanja kayanki, kici abunci
Zaizo yasameni wlh
Tashi tai idanta yayi luhu² fuskar tayi jaaaa sosai abunka da farar fata
Da'kar Hapsatu ta lalla6ata tayi wanka taci abunci tasaka kayan bacci, bata panadol tai tasha sannan ta lalla6ata ta kwanta
Har lokacin Nauphal bai dawoba
Itakam inna fakaici idon Hapsatu saita share kwallarta
Yitai kamar tayi bacci sai Hapsatu taja mata bargo sannan ta futo
Sai alokacin ma takula da kayan data shigo dasu da wayarta duk agurin tabarsu har hand bag ???? d’in tama
Kwashe kayantai taga babu abunda zai lalace aciki takai matasu d’akin ta ajiye
Saida akai sallar Isha'i sannan yadawo shida Fahat
Da sallama suka shigo
Da’kar Hapsatu ta amsa musu sallamar
Zama sukai akusa da ita suka gaisheta
Nam ma ada’kile ta amsa tana tashi daga gurin
Nauphal yasan dashi ake wannan fushin sbd yata6a mata ‘yar gold d’in ta
Shikuwa Fahat dabaisan komaiba tashi yay yabita yace Ummerh me mukayi kuma
Nauphal kansa yana ‘kasa baice komaiba
Shiii bai gaya maka ba
Ummerh bai gayan komai ba
Tunda lokacin da muka had’u da magriba ne munayin sallah aka shiga karatu
Da aka kammala kuma akayi sallah, sannan muna idarwa akai addu’a kowa yataho gida
Kaje yafad’a maka
Ummerh nifa bansan menaiba kiyi hkr dan Allah ko wani abun akace namiki
Ban saniba
Kasamun yarinya kuka
Kun tafi tare meyasa bazaku dawo tareba shine kazauna kanawa wasu shasha shayyy li’ki ko
Sannan harda rawa da tafiya hira kabarmun yarin yata ita kad'ay
Wayace kabita inkasan bazaka zauna tare da itaba
Ummerh budur watace fa
Ok budur war taka tafita kenan ko
A’a Ummerh
Hakane mana gashinan kafad’a
Toh bari kaji zan aurawa yarin yata wanda yafika komai kuma zaka gani
Itakam Nusaiba akan kunnenta akai komai jitai gabanta yafad’i da Hapsatu tace zata aura masa wata
Dama jibi hutunku zai ‘kare koh
To yau kashirya kayanka
Gobe ka kama hanya katafi banasan ganinka agidan nan kaji na fad’a maka ko
Ummerh Allah ni......
Banasan jin komai kuma koda wasa kadawomun gidan nan ba Bayan 2year ba sai ranka ya6aci kajidai nagaya maka koh
Kallonta yay atsorace yace Ummerh na dan Allah kiyi hkr mana Allah nifa ba wani abu naiba
Itace tace batasona ni yarone
Kuma Ummerh nasamu wadda take sona,shine fa muke hira
Allah ni babu abunda nai mata kuma cewa nai tajirani
Shine fa tai tafiyarta nibanma san ta tafiba Allah
Ina zaka sani tunda kasamu wadda kakeso
Ummerh Allah ni fa babu abunda nai mata
Kumafa ita tace batasona
Kumani aure nakeson yi
Ita da bakinta tace maka batasan ka
Ey wlh Ummerh tace nai mata ‘kan’kanta
Bangaya maka metaceba tunkan wannan lokacin
Ummerh toki tambayeta wlh kiji
Allah itace tace batasona
Nikam bansan menai mataba ta tsaneni
Har gayawa ‘kawayenta takefa
Ummerh dan Allah kiyimun afwa Allah bazan ‘karaba
Kuma kitambayeta indai tace namata yaro shikenan bazan ‘kara kula taba
Banza Hapsatu tai masa shikuwa fahat dariyace take cinsa kamar me
Abuncinsu yad’auko dan yaga yau Ummerh tasu bazata basu ba
Itakam Nusaiba kukan ta tacigaba har bacci yad’auketa
Hapsatu ma d’akin ta tafi tayi shirin kwanciya tai bacci abunta
WASHE GARI
Koda gari yawaye ma daurewa tai tayi ayyukanta tayi komai yadda tasaba ta nunawa kowa babu komai aranta
Yau babu Makarantar boko saidai islamiyya dan haka tashirya tai tafiyarta ahanya suka had’u da kaliss sukaita hirarsu, tasha mamaki kaliss dan batai tunanin zatazo Makaranta ba
Lokacin da aka tashi daga makaranta abakin get suka had'u da wani kyankyawan farin saurayi yana tafiya zai shiga motar sa
Kallon su yay yaga Nusaiba tana murmushi, jiyay har cikin zuciyarsa
Binsu yarin’ka yi har bakin gidan su Nusaiba, yayi parking
Sallama yay musu suna ''ko'karin shiga gidan
Amsawa sukai suna Juyowa
Kallon kaliss yay yace dan Allah inasan ki aramun “kawar mu kona 5m ne please
Ok
Kallon ta tai ta had’e rai dan badan kaliss tari’ke mata hannu bama da tuni tashiga ciki
Besty ana magana fa
Inaji ai
To amman kije mana kiji dame yazo kinga dai wannan ba yaro bane bakuma tsoho bane
Murmushi tai tace ke kooo
Kije nidai dan Allah
Juyawa tai ta taka zuwa inda yake
Sallama tai masa kawai ta tsaya
Amsawa yay yana murmushi yace gimbiya sarautar mata
Hmm
Barka da yamma
Hmm
Yagida, ya makaranta kuma
Alhmdllh tace ada’kile
Masha Allah
Nidai sunana muktar kuma nagankune yanzu anan zaku futo daga makarantar islamiyya nabiyoku, nazo gurin wani abokinane naganku
Kuma gaskiya dagaske nake ina sanki aurenki zanyi
Dan Allah kitai makamun kar kice a'a
Ni d'an gidan mlm sulaiman ne
Wanda akafu sani damai shadda
Yana aikine a company alhaji Ibrahim mai shadda baban hassan da husaini
Kuma ashirye nake da in aureki ba wasa yakawoniba Allah
Nayi karatuna a6angaren business ne
Kuma ni banada wata matsala da iyayena dan burinsu guda d’aya yarage musu suga nayi aure kawai
Dana Allah karki watsan 'kasa acikin idona
To dan Allah kabani lokaci zanyi tunani kaji
Toh shikenan kamar zuwa yaushe kenan zan dawo
Toh kamar rana ai tayau
Haba gimbiya ta so kike in mutu
Zuwa dai gobe dan Allah
Gobe kuma
Umm mana dan Allah karkice a’a
Toh bada wuriba
Kamar yaushe kenan
Bayan mundawo daga makaranta
Toh Allah yakaimu naga ai 5:00pm kuke tashi ko
Ummm
Toh nagode ga number ta nan
Kibani taki kinji
Ai….
Tarar numfashinta yay yace ai meee
Dan Allah karki hanani kibani number kinji gimbiya ta
Murmushi tai ta karanta masa yarubuta
Amman daaa batai niyar basaba
Murmushi yay yace ngd gimbiya ta Allah yabar ‘kauna
Hmm natafi kar anemeni
Ok agaimun su mom
Ummerh dai
To agaidamun su
Duk abunda akai akan kunne Nauphal akayi jiyay kamar yamutu dan ba’kin ciki shiyayi mata nawasa ita nagaske zatai masa kenan
Gida tashiga abunta ta tarar da kaliss sunata hira da Ummerh ta atsakar gida
Ummerh ce ta kalleta tace sirikin nawa yatafi
Kunya taji tashiga d’aki kawai
Haka sukaita tsokanarta
Bayan magriba ta taraka kaliss tahau nafef ta tafi gida azaure tazo shiga taga mutum atsaye yahad'e rai fuskar nan babu annuri
Kallonta yay yace keeeee……………✍????✍????✍????
Keep waiting my fan’s????????????
Hallmarth ce ????????????
[04/02, 8:02 AM] Ummuh Fateemah????????????: ????????????????????????????????????
????????????????????????????????
DASHEN ALLAH
WRITING ASSOCIATION
‘DAN HAKIN????DAKA RAINA????????
Story and written by
*SADIYA •A• UMAR*
{UMMUH FATEEMAH}
????—
7⃣7⃣&7⃣8⃣
…………….Sai ya Balaga sannan sai mufara rayuwar aure dashi
Kallonta sukai suka kwashe da dariya, yanzu wannan gayen meye aibunsa ai wannan sune nafuta shopping wlh, nazuwa taron kece raini
Aaaaaa kudai gaya mata
Dan Allah inkika rasa wannan damar zai wahala kisamu yaro mai jini ajika irinsa
Wannan sabon jinin ai saida sabon jini, irinki, inkikayi wasa kyaji asalansa wlh kiga yasamu wata ke kuma ki losing wlh
Wata wadda ake cewa sumy itace tace aikam ni yamun ahakansa wlh bari kiga inje musha love
In mi’ka masa sa’kon dayake zuciya ta dan tunda nagansa bugun zuciyata yasauya alamar yasamu mahad’insa kenan
Kallonsa Nusy tai sai tace aranta inkinjema zakisha wula'kanci sosai
Tafiya sumy tai
Sukuma su Nusy suka ‘karasa wajen wani table suka zauna amman suna hangosu
Shikuwa tun tafiyar Nusy gurin yasan maganar sa sukeyi
Amman yau saiya ‘kuntata mata itama zaiyi abunda zaiga tana sansa ko kuwa
Lokacin da sumy taje gurin gaban Nusy sai fad'uwa yake dan bata ta6ajin irin hakaba
Amman saita daure ta basar tacigaba da safgar ta kawai jira take yaci mata mutunci taji dad'i
Shikuwa lura da yadda take satar kallonsu yasakashi fasa yiwa sumy wula'kanci
Tanayin sallama ya amsa yacigaba da danna wayarsa
Cewa tai Ammm dan Allah inasan yin magana dakai yayan mu
Uhummm
Yawwa inbazaka damuba inasan number wayarka
Kallonta yay yayi murmushi yace kiyime da ita
Inkiraka, sabida tunda naganka naji babu wanda nakeso da ”kauna aduk duniyar nan kamar ka kuma zan iya rayuwa dakai acikin kowane hali
Ngd sosai da wannan karamcin amman ansamun rana kiyi hkr
‘Dan had’e rai tayi
Yayi murmushi yace sorry ???? mana ‘yan mata yana had’a hannunsa guri d’aya
Yace amman inasan mubuga wani game dake dan Allah
Ok wani irifa
Inaso akoda yaushe kinunawa Nusaiba soyayya muke sosai dan haka yanzu zan amshi number d’inki kuma zamu fara daga yanzu
Toh babu damuwa zanyi hakan sbd kaid’in farin ciki nane
Dama Allah zai bani damar mallakar ka amatsayin miji danaji dad’i duniya da lahira
Kallon su dayaga Nusaiba tanayine yasashi sakin wani lallausan murmushi yace karki damu Allah zai baki wanda yafini koma, yana nuna kansa
Wani dad'i taji
Yace to tashi mud’an zagaya
Tashi tai tanata gwalli tana rangwad’a ita adole mai saurayi
Wani tu'ku'kin ba'kin ciki ne yatokare Nusaiba jitai kamar tayi hauka dan ba'kin ciki da takaicin dayake damunta
Daurewa tai ta kauda kanta tacigaba da kallon masu rawa
Ta gabanta suka wuce zuwa kan step d'in da ake rawar
Sumy tafara takawa
Hannunsa yasaka a aljihunsa yaciro “yan 200h yafara li’ka mata yanata murmushi yadda kasan masoyan gaske
Sosai Nusaiba tacika tayi fammm saida sukayi mai isarsu sannan suka futo
Zama sukai akan table d'in dayake opposite danasu Nusaiba suka cigaba da hirarsu
Murmushi yake sakar mata yana tayata hirar shima
Servings d'in mutane aka fara cikin lokaci 'kan'kani aka kammala sannan aka saka kid'a mai dad'i anaji
Abunci sumy tad'auka kad'an tayi wajen bakin Nauphal dashi tana fad'in my dear kaci mana
Uhummm juyar da cokalin yay zuwa bakinta yace faraci, tukunna idan kika 'koshi sai in ci nima
Ok
Bata yarin’kayi tanaci tanata wani kwar kwa sa da shagwa6a abunta
Takaicine yazowa Nusaiba wuya ita kanta batasan kona menene ba
Tashi tai taje wajen dayake zaune tace nagama katashi mutafi
Amm ni kuma ban gama ba kozaki tafi nataho daga baya
Bazan tafiba katashi mutafi
Aaaa kinga mutum yace bayanzu zai tafiba kibarsa mana shida ba yaro bane bare kice zai 6ata
Ina ruwanki ne dake nake magana koda d’an uwana karki ‘kara sakamun baki alamarina
Aaaa d'an uwa manya nikuma miji nane kinga tsakanin nidake wayafi mahimman ci yaba kulawa
my dear tashi mu koma can ko mad'an samu sukuni ko
Ok dear muje
Tashi yay suka jera suka fara tafiya
Nusaiba jitai dama ta sani tasaka ni’kaf d’inta datayi kuka yanzu ta gode Allah babu wanda yaganta