DAN HAKIN DAKA RAINA???? COMPLETE NOVEL
Toh amman ai bakice kinyi al’kawrin ba, zakiyi komai dana saki
Hmmm I promise you I will do everything that you positioning me to do
Hmm Allah yashiryeki
Yanzu babu rakiya
Nace maka bazan iya zuwabafa
Yanzu zantafi har tsawon 2years hubbi amman bazaki rakaniba
Kika sani ko Acan ma in mutu bazaki sake gani naba
‘Dago kanta tai dasauri jin abunda yace wai yamutu
Girgiza masa kai tayi idanta nacikowa da kwallah tace Uuuu’ummm
Bakyasan in mutu
Ummmm
Meyasa to
Shiru tai
Murmushi yay yace saboda kinasan yaron mijinki ko
Tureshi tai tajuya masa baya
‘Dan takowa yay yace ko ‘karya nayi
Shiru tai masa
Yace toh nizan tafi, hubbie taaa
Adawo lpy Allah yatsare ka yakaika lpy yadawo dakai lpy
Wowwwww ngd sosai dear
Shammatar ta yayi yasakar mata kiss awuyanta yace byeeee
Wani numfashi tasauke dan ba 'karya taji Wannan kiss d'in sosai
Juyowa tai ta kalle sa yana futa daga gidan
Acikin nafef yasamu su Hapsatu sunata jiransa
Kallonsa tai tace waimeka manta naga baka d’auko komai ba
Ummerh banganshiba fa
To menene shi d’in
Ummerh…… Ummerh…
Fahat ne yay saurin cewa ko P-cap d’inka kaje nema
Ummm…. Ummm…. Ita naje nema
To ai nad’auka tana cikin kayana inasantane
Ok amman baka gayamunba
Nasan kanasantane shiyasa na’ki gaya maka
Itakam Hapsatu kallonsu tai kawai tayi Murmushin dan tasan ba haka zancen yake ba
Amman tunda sun nuna sunajin kunyar sanar da ita bari ta kyalesu karsu dainajin kunyarta kuma
Haka suka kaisa tasha yahau mota sannan suka dawo bayan sunga tashin su
Koda suka dawo Nusaiba takammala gyaran gidan tana ta sallamar masu siyan abunci wanka tashiga tabar mai Mm suwaiba agurin tunda tazo
Aikin suka cigaba dayi ita da Hapsatu dan haka ake wuni kullum tun daga safe har dare
Washe gari suka raka fahat shima yatafi makaranta duk da tasa acikin garin take
Haka ma……..
Wazan gani su doctor faruq ne suka futo da waliyyansa
Shiga sukai cikin gidan harda wani namiji wanda a'kalla zaiyi 47-48,kyaky kyawane ajin farko shima
Shiga sukai cikin gidan suna kallon gidan sosai azauren gidan suka tsaya ganin Alhaji yana shirin futowa
Yana kallonsu gabansa yafad’i nuna wani yafarayi acikinsu hannunsa yana karkarwa sai kuma yafad’i yasuma
Salati suka fara suna d’aukar sa zuwa cikin gidan su kuma wakilan doctor faruq suka futa
Anjuma kafun Alhaji yafar fad'o kallonsu yay yace ina yake
Waaaa fa baba, inji doctor faruq
Wannan saurayin yana ina
Wanene baba
Wanda naganku tare yanzu
Sun futa ai
Dan Allah kiramun su
”ko’karin tashi yafarayi
A’a baba kahuta bari inkira makasu
‘Daukar wayarsa yay yace dasu Alhaji magaji su shigo
Ok gamunan
Kashe wayar yay sannan yamaida dubansa akansa yace gasunan zuwa
Toh zama yay yana zubda kwalla acikin ransa sai ro'kon Allah yake Allah yasa hasashensa yazama gaskiya
Suna shigowa
Yaga babu shi aciki, harzaiyi magana sai yagansa yashigo
Dasauri yatashi yarungume sa yasaki kuka
Mamakine yakama su
Shikansa Ibrahim mamakin yake dan dai baisan saba bai ta6a ganin saba amman kuma yarungume sa
Ba nuna ‘kyama ko wani abu shima yarungume sa yana bubbuga bayansa ahankali yaji gabansa yana tsananta fad’uwa
Sakinsa yay yakalli doctor faruq yace doctor Wannan d'anane wlh d'anane ba 'karya zan mukuba Allah d'anane shi
Sosai abun yabawa kowa mamaki amman sai sukace haba baba daga ganin yaron mu sai kace d'ankane Wannan d'an mune kuma jininmu family'n mu
Shid’in gudan jinin d’an uwanane
Meyasa zakace haka Baba
Wlh Alhaji wannan d’a nane kuma ni nahaifesa
Zan iya nuna muku shaida idan baku yaddaba
A’a bari akira baban sa tukunna dan abun da d’aure kai
Kallon faruq yayi yace kira baban ku maza, kace masa muna san ganinsa agidan Alhaji Ibrahim mai shaddah kaji
‘Daukar wayarsa yay yakira shi kamar yadda aka umar cesa haka yafad’a
Lpy meyafaru faruku naji kamun irin wannan kiran
Daddy, Uncle ne yace ince maka haka
Ok yana ina, bashi wayar
Mi’ka masa yay kamar yadda yace
Amsa yay yagaya masa komai daya faru, jummmm yay kafun yace gani nan zuwa
Aransa yace wannan shine ranar wanka ba’a boyon cibi
Tashi yay yakalli hajiya habiba yace mata kishirya muje idan su Alhaji Ibrahim mai shaddah
Inna lillahi mezamuyi musu
Hjy tashi muje kawai
Tashi tai tafara Shiryawa
Shima yashirya sannan suka futo
Mota suka hau driver yakaisu har ‘kofar gidan nasu dan sunga Motocin suma agurin
Tun kafun su futa hjy habiba tasaka kuka tana fad'in shikenan yau za'a'kwacemun d'ana
Da'kar Uncle sulaiman yalalla6ata tayi shiru sannan suka shiga sallama tai tashiga sannan aka basu izinin shigowa
Shiga sukai suka zauna a d’akin Alhaji, yasaka anas yakawo musu ruwa da lemo dama
‘Karowa akai harda cincin
Amman babu wanda yaci ko yasha
Zama Uncle Sulaiman yayi itama hjy habiba tazauna
‘Kara mai maita musu komai akai kamar yadda Uncle yagaya masa
Kallonsu yay yace naji kuma nafahimta, shikuwa Ibrahim In banda kuka babu abunda yake dan yakasa gane komai
Tashiyay yadawo kusa da daddy Sulaiman yace daddy kagaya musu gaskiya niba d'ansu bane
Kuka daddy yasaka dan tausayin d'an nasa sosai
Dakewa yay yakalli Alhaji yace, Alhaji Ibrahim wace shaidace kake da ita wadda kace zaka nuna
Tashi Alhaji yay yabud’e durowar sa yad’auko…………………✍????✍????✍????
????????????????????????????????????
????????????????????????????????
DASHEN ALLAH
WRITING ASSOCIATION
‘DAN HAKIN????DAKA RAINA????????
Story and written by
*SADIYA •A• UMAR*
{UMMUH FATEEMAH}
????—
8⃣5⃣&8⃣6⃣
…………Tashi yay yad’auko wata jaka sannan yarufe yadawo yazauna
Bud'ewa yay yad'auko wani pic d'in sa na ranar da aka haifesa ansaka masa kayan sanyi a asibiti ne ma yana kwance kusa da Ummerh'n sa
Mi’ka musu yay yace wannan hotonsane lokacin da aka haifesa da daddare
Kallo sukai sannan Ibrahim ya amsa yaga tabbas yanada wannan photon amman nasa akwai mom d'in sa agurin ba wannan matar bace sannan kuma dasu daddy agurin dawasuma
Kallonsa yamaida kan daddy Sulaiman yace dad wannan hoton iri d'ayane danawa amman kuma anawa babu wannan matar saidai ku dasu mom
Kwallace tazubowa daddy Sulaiman yace kayi hkr d’ana yau zan gaya maka abunda naita 6oyewa sama da shekara 47
Kallonsa su Uncle sukai da mamaki dansu kansu basusan komai ba
FLASH ???? BACK ????
……Akwai wata ranar laraba wadda bazan manta da itama mun taho da family na zamuzo garin kano akan hanyarmu ta zuwa sai motata tai facii
Sai nai parking agefen titi natsaya ina jiran wani abun hawa yazo wucewa in hau motarsa inje cikin gari inkai faci
muna tadai zaune shiru kuma gashi ita uwar d’akin nawa bazata jure zaman motaba dan bansan bata da lpy bama saida muka taho, sbd tanada tsohon ciki
Sannan kuma awatan ta na haihuwa muke
Wani mai mashing ne yazo wucewa natsayar dashi, shiya taimaka mun muka kunce tayar yakaini akai faci sannan muka dawo muka sakata
Amman gamamakina sai naga babu hjy habiba amotar dan nai tunanin ko bacci tayi abayan mota
Dan haka saida muka gama na lura, gayawa mutumun nayi nan muka juya dan nemanta
Hangota mukai tana tahowa da yaro ahannunta sai kuka yakeyi sosai yana 'karawa
Kallonta nai da mamaki kuma ga cikin tanan ajikinta amman kuma gayaro ahannunta
Saida ta 'karaso nace mata ina kika samo wannan d'an
Sai mai machine d'in yace aikam dai a ina kika samo sa
Zama tai acikin mota sannan tace mun
Bayan tafiyarku ba’a dad’e ba naji inajin futsari saina sauko nazagaya dan inyi futsari
Bayan nagama sainaji kukan yaro kamar an muntsilesa
Dabazan jeba sbd nai tunanin ko aljanune tunda gurin jeji ne sosai
Amman saina daure nafarabin sautin kukan yaron
Abakin wani ruwa nagansa an kwantar dashi wanda da alama ba’adad’e da haihuwar saba
Saina d'aukosa nafuto daga gurin inata sauri inzo ince maka kutaho masa da madara sainaganku kuma
Toh Alokacin mukace da mutumun ko in basa yaron amman saiyay fafur yace a’a sbd bashi da aure
Sai nace kozai kaimu wajen mai gari
Yace a’a shibaisan mai garin wannan unguwarba
Nandai yace kawai bari ya amshi number wayar mu koda zaiji masu d’an saiya kiramu
Muma muka amshi tasa
Saina sallamesa nabashi dubu 30 yatafi mukuma muka shiga mota
Zamu cigaba da tafiya sai hjy habiba tacemun karmu sauka a family house ???? d’inmu mutafi gidanmu kawai
Haka na amsata koda muka shigo garin kano agidanmu muka sauka dayake sharad’a
Bamu dad’e dasaukaba itama tafara na’kuda dan haka na d’auketa zuwa d’akin haihuwa nan akaita fama abu kamar wasa saida takai wajen 12:30pm sannan ta haihu d’anta namiji
Bayan komai yalafa angyarata itada baby sai muka yanke shawarar inkira "yan uwana ince musu habiba tahaifi 'yan biyu
Haka kuwa akai nagaya musu ta haifi ‘yan biyu kuma suka yadda
Saboda shaida yasaka bamu sauya maka kayankaba mukai hoto dasu
Haka taci gaba da shayar daku amman tunda muka tsinci Ibrahim bayashan nonon habiba saidai madara kawai
Bayan suna da kwana uku sai Allah yayiwa d'anmu rasuwa munyi kewarsa sosai
Amman babu yadda zamuyi haka Allah yaso sai muka rufe sirrinmu muka cigaba da kula da Ibrahim
Saida Ibrahim yacika shekara 6 sannan habiba ta 'kara haihuwar d'anta namiji sai muka saka masa UMAR ake kiransa da faruq
Haka muka cigaba da rayuwa muna d’an binciken sirri ko zamuji ina iyalan ka suke amman shiruuu
Anan nan sai akamun canjin gurin aiki nakoma England ???????? da zama tunda muka tafi bamu dawo Nigeria ???????? ba saida mukai shekara 27 sannan muka dawo
Muna zuwa sai faruq yace shi agarin Rano yakesan muzauna sbd yanasan yarin’kayin aiki a asibitin nan danya tai makawa marasa lpy garin
Haka akai muka tare atsohon gidan mu sai muka saka aka fara gina mana babbar estate Acan saida aka kammala sannan muka dawo
Haka muka cigaba da zama gaba d'aya family d'inmu
Amman kusan koda yaushe muna bincike wajen ganin mungano ina family d'inka suke
Lokacin da faruq yazo mana da zancen auren sama Ibrahim baya GARI da tare zasuzo, dan cemana yay “yar gidan Alhaji Ibrahim mai shaddah zai aura
Saida d'aurin aure yarage saura kwana 1 sannan mukaji ashe "yar da yake ri'ko ce "yar Mm balaraba dangin bala'i, shine muka rasa yadda zamuyi akaucewa wannan auren, sai kawai mukace muce muku faruq ya6ata kawai sai afasa auren bayan haka da d'an kwanaki sai muzo muyi muku jawabi akan dalilinmu
Toh shine fa su Uncle d'insu waliyyansa kenan sukace zasu taho sai sukace faruq yabiyosu
Sai shima Ibrahim yace zashi, sai suka taho gaba d'ayan su
Sosai abunda Uncle sulaiman yafad’a yasaka Ibrahim da alhaji kuka dan sunyi masa ri’kon Allah da Annabi basu ta6a nuna masa wani mugun haliba ko kuma su nuna masa wani abu nacewar basu suka haife saba
Alhaji ne yace Tabbas wannan shine 'DAN HAKIN????DAKA RAINA???????? Tabbas zai tsone maka idooo
Allah mai iko
Akunnen Mm Balaraba akai komai dan anfuto da ita tsakar gida tasha mamaki sosai da sosai
Abunda sukai gashinan duk taji dan itada kakah Hajja suka kai jaririn nan bakin ruwan nan suka ajiyesa sannan sukai tafiyarsu
Kuma harda su amasu neman sa suna kukan munafurci
Alhaji ne yace kosuwaye sukai mun haka bazan yafe musuba har abada wlh dansun cutar dani sosai
Fashewa da kuka yay
Ibrahim yataso yarungumesa yana kukan shima
Da'kar suka samu sukai shiru sannan Alhaji yace wa Ibrahim babana inga bayanka
‘Daga rigarsa yay saiga wannan SHAIDAR TASU TA FUTO RAMMM
Yawwa kunga shaidar danake nuna muku, sannan akwai ta ajikina ma bari in nuna muku
Haba Alhaji aibasaika nuna ba komai yatabbata Ibrahim d’an kane dan haka babu abunda zamuce mu
Sallama akai ana saka kuka kuma muryar namijine babba kuna
Futowa sukai dasauri suna kallon bakin ‘kofar d’an gidan Alhaji H……………. ✍????✍????✍????
Keep waiting my fan’s????????????????