DAN HAKIN DAKA RAINA COMPLETE NOVEL

DAN HAKIN DAKA RAINA???? COMPLETE NOVEL

Anas ne yashigo da sauri dan yajiyo karar dukan tunda yaxo kofar gidan kayan ya ajiye yakarasa gurin dasaurin tsiya shiga tsakanin su yay yace haba Abba me hapsatu tae maka yarinya mae hkr da ladabi da biyayya Abba kayi hkr

Huce Abba yake yace inyime hkr fakace anas wannan yarinyar ita kadae baxata samun hawan jiniba wlh tashi kitattara kayanki maxa kisan inda dare yay miki

Kuka take sosae takarasa kusa da Abba takama kafarshi tace abban kayi hkr wlh babu abunda naewa kaka hajjah gaesheta kawae nae, Abba karka koreni inka koreni ina xani ina nasani, abban bansan kowaba, Abba kaeda Ummerh kawae nasani, Ummerh kuma tamutu Abba yaya xanyi ina xanje

Rufemun baki munafukar kawae toh nabaki nanda wata daya kisan inda xaki kinji ni kobakijiba

Abbah kae mata hkr dan Allah hakurin uwar wa Anas ina ganin mutuncinka kamatsamun aguri tun kafun indaena gani kaji ko

Kukan nauphal ne yakara karfi haryanayin kamar xae shide dan tunda aka fara dukan hapsatu yafarka daga baccin dayake

Tashi hapsatu tae dasauri tashiga dakin daukoshi tae tana jijjigashi tana masa addu’a sassauta kukan yafarayi yana ajiyar xuciya ruwa tadauko tabashi na faronsa datake xubawa afida yasha kuwa sosae

Jinin goshintane yadigo masa afuska dan taji ciwuka sosae Anas ne yay sallama abakin kofar falon amsawa tae tace yayah shigo shigo mata yay da kayan yace innalillahi wa inna ilaehi raji’un hapsatu kinga jini kuwa a fuskarki da wuyanki kalli kafarkima sae xubar da jini take tashi muje asibiti maxa tashi muje

Tace aa yaya kavarshi kawae yanxu vavu kudi agurina kuma ma aiki nakewa mamah gashi inasan tace kunun nauphal dan vashi da abunci

Tashi nace var wadannan aiyukan xan miki inmun dawo tashi kafun kiga 6acin raena

Tashi tae tasaka hijab sannan tadauki nauphal xata goya kar6arshi yay yace muje dakar take taka kafarta dan ciwo take mata sosae haka suka futa har tsakar gida lokacin ma kakah hajjah da balaraba suna bakin kofa sae shewa suke

Hade rae Anas yay yace xamu wuce malamae ganin fuskar nan babu annuri yasa Balaraba matsawa kakah hajjah ma matsawar tae suka futa adae dae ta sahunsa yay wa key yace shiga muje hapsatu

Shiga tae yamika mata nauphal ta amsheshi yaja suka tafi

Koda sukaje sunsha wahala kafun akar6esu dan cemusu akae wannan accident ne saesunxo da police

Likitan dayake duba hapsatu ne yaga taji ciwuka sosae saeda yay mata dinki a goshinta da kuma hannunta wajen kafadar ta gakuma kafarta takumbura sosae yana dubawa yace tsagewar kashi ce da ita nan yagyara mata sannan yadaura mata ruwa dawasu allurae ta kwanta

Nauphal kuwa lokacin yayi baccin wahala ga yunwa kwantar dashi yay akusa da ita sannan ya jah musu kofar yafuta saeda yabiya kudin komae yasiya duk avunda akace yasiyo sannan yakoma gida lokacin babu kowa atsakar gidan

Surfen da hapsatu takeyi yaga ankarasa an kwashe daki yashiga yay mata tatar kunun ta sannan yatattara mata dakin yashare dukda badatti yayba yadauko mata kaya kala 7 dana nauphal yadauki dukkan avuvuwan daxasu vukata sannan yahada acikin gana masgo yafuto kulle dakin yay yashiga adae daetarsa yakoma asibitin

Lokacin daya shiga dakin yasha mamakin gani ruwan yakare ta tashi xaune tana rike da nauphal daketa faman tsala kuka amsarsa yay yace mata bari in samo masa madara ashagon waje wace iri kike bashi

Tace yaya kowacce irima sha yake yace toh futa yay, bae dadeba yadawo dauke daleda guda uku ahannunsa yunkurawa tae xata tashi yace aa yixamanki vari in kawo miki kiduba

Amsa tae taduva ledojin madarace katon gwangwani guda daya da kuma fida da madae daecin tea plats sae cokali guda daya,
Dayar ledar kuma man shafawa ne da sabulu da detol da makilin da brush da aizal da kuma omo viva babba guda daya,
Dayar ledar kuma naman kaxane da yoghurt wannan tun akan hanya yasiya da kuma bread da lemo

Sallama akae wata Norse ce ta shigo da babban boket naruwan Xafi da kuma wani acikin karamin mika mata nauphal yay yakar6i na karamin boket din sannan ya dauki plast din yacika matashi da ruwan xafin sannan Norse din tace yawwa kitashi ahankali garuwanan muje kigyara jikinki akwae wadda xataxo tahada madarar bebin aa varshi kawae xanyi

Ok futa Nurse din tae anas ne yashiga toilet din yawanke matashi tsaf da aizal da omo sannan yasa mata detol yakara daurayewa kana yakae mata ruwan wankan yasurka mata abahon dayaxo dashi daga gida xuwa yay ya amshi nauphal yaci gaba da bashi madarar ita kuma ta shiga wanka da kayan daxata canja

Lokacin data futo Anas yanata jijjiga nauphal dan da’alama anci an koshi kuma Xafi yakeji

Amsarsa tae tahada masa ruwa tae masa wanka sannan tashiryashi tinkan tagama ma yayi bacci abunsa kwantar dashi tae sannan taxauna tace yayah nag…. Tunkafin takarasa yace indae ni yayan kine tobasaekin godemunba kinji hapsatu ina kallonkine amatsayin kanwata kicigaba da hkr komae xae wuce maxa kici abuncinnan gamaganinki nan yana jiranki kinji ko vari inje in wanke kayan nan naku abaya inda naga ana wankewa

Aa yaya kabarshi inna samu sauki xan wanke aa kyale kawae nurse ce tashigo da sallama tace gashi wannan inji likita mika masa tae ya amsa budewa yay yaga maganin ciwon idone yamanta daxu

Ok ngd
Ok
Am please anan a ina ake wankin kaya xanyi inji anas
Aa akwae masu wankewa abiya su kavayar akae musu da safe xasu xo sukawo maka saeka basu kudin

Ok toh gasunan hada kayan yay yamika mata ta amsa

Saeda yay da gaske sannan hapsatu taci naman nan dayawa saeda yatabbatar data koshi sannan tasha magani yace toki kwanta dan likita yace sae nan da kwana uku xa’a sallamemu kinji nibari indauki tabar mar nan in kwanta abakin kofa tunda naga ana kwanciya koh

Toh yayah saeda safe yawwa Allah yakaemu futa yay yayi shimfida ya kwanta abakin kofar daga gefe

 ****** ****** *******

Agida kuwa Balaraba taxaga kofar hapsatu yafi akirga amman shiru kuma Abba ma ya duba yaduba nan ma shiru sun kira wayar Anas sam baya dagawa daga karshema kin shiga tae sae hakura sukae suka kwanta badan Balaraba tasoba dan taso sudawo taci uwar hapsatu daxarar Anas yatafi gidan dayake kwana shida kannensa

Koda gari yawaye har dare Anas bae xoba hapsatu ma haka saeda sukae kwana uku basa ganin hapsatu bare Anas

  *** *** *** 

A asibiti kuwa inyayi musu duk abunda suke bukata saeya kama hanya yatafi aikinsa na adae dae ta baxae dawoba sae dare amman yana kiran hapsatu awaya dan yasiya mata karamar waya Nokia

Haka suka kwashe kwana uku a asibiti dan har hapsatu wata kiba tae farinta yakara futowa sosae

Yau ne yakama xa’asallamesu da yamma gaban hapsatu sae faduwa yake sosae dan tarasa meke shirin faruwa da ita yau haka suka shirya suka tafi gida lokacin da suka shiga gidan shiru kamar anyi shara gashi dattine acikin gidan kamar me ko ina yakoma juji gatulin kayan wanke wanke ga kayan wankinsu nan adaure tuli guda da sallama abakinsu suka shiga da mugun dubu Balaraba tafuto daga daki kamar haukaciya tace Anas Anas ina kaje ne katafi kavarni inata tunanin ka Anas wani laefi nae maka
Babu komae dan matsa in wuce dan nagaji sosae
Sakin baki Balaraba tae ta matsa masa yawuce ahankali hapsatu takebin bayansa jikinta duk babu kwari gashi gabanta sae faduwa yakeyi sosae

Bude kofar yay yasaka mata kayanta aciki taga ko ina pes angyarashi mika mata naera dubu biyar yay yace gashi ko xaki nemi wani abu saeda safe

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40Next page

Leave a Reply

Back to top button