DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL
Duniya biyu mabanbanta[11/1, 11:41 PM] Re@l???? K@usy ????: ????TWO DIFFERENT WORLD????
DUNIYA BIYU MABANBANTA
BISMILLAHI RAHMANIR RAHEEM
✍️ M SHAKUR
1️⃣
FREE PAGE
Ahankali yake saukowa daga stairs katafaren falon dako gidan shugaban kasa sai haka, yana sauka ahankali yana gyara zaman necktie din wuyanshi da hannu daya kasancewa dayan hannun na rikeda wata briefcase brown, daidai lokacin wata babban mace da a kalla zatai 57 tana sanye da shiga na alfarma tabude kofar wani daki wanda ga dukkan alamu kitchen ne sabida kamshin girke girke daya cika ko’ina tafito bayanta kuma wata maid ce dake sanye da uniform din masu aiki tana rike da babban warmer da alamu abinci ne aciki ta tsaya a bayan matan ganin uwar dakin nata ta tsaya itama, ganin matashin yasa batare data kalli maid dinba tace “kai kulan dining Shafa” sanan tacigaba da tafiya daidai matashin yakarasa saukowa daga stairs yakaraso gabanta, kafinma yay magana ta mika hannunta takai kan necktie din dayaketa fama dashi da hannu daya ta shiga gyaramai, dan murmushi yasaki cikin wata yar karaman natsassiyan murya yace “Barka da safiya Ammi” batare data amsashi ba ta sauke hannayenta kasa ganin tagama gyaramai ta kalli fuskarshi damuwa karara ya bayyana akan fuskarta amma saitai shiru batace mai komiba, kallon datake mai yasa adan shagwabe yace “Ammi, menen…..?” wuceshi tayi tai dinning taja kujera tazauna tadau mug tareda bude flask ta tsayaya ruwan zafi sanan ta waigo ganin har lokacin yana tsaye inda ta barshi yasa tace “anan zaka tsayane kana kallona ko ba break zakayi ba?”
Ayanda tamai maganan yasa yagane fushi take dashi kuma yasan dalilin fushin, karasowa yayi yaja kujeran gefen ta ahankali ya ijiye briefcase din hannunshi kan dayan chair dat is next to him sanan yazauna ahankali, mug din shayin dayasha kayan kamshi ta turomai gabanshi cikeda fushi tadau plate mai kyau fari kal kal ta debamai soyayyan Irish sanan ta kallai babu alamun wasa akan fuskarta tace “pepper soup ko ketchup? Wanne zan samaka?” murya chan kasa yace “ketchup” daukan bottle din ketchup tayi tabude tazubamai a gefen chips din dayawa dan tasan Allah yazubamai son ketchup sabida shi kadai agidan nan takesa ayo cefane harda na ketchup dan shi kadai kesha ita haryau abin baimata bane ko dandane batayi. Turamai plate din tayi gabanshi zata zare hannunta daga jikin plate din yakama hannunta yarike hakan yasa tadago idanunta ta kallai, dan shiru yayi yana kallonta sanan yadan sauke ajiyan zuciya asanyaye, murya chan kasa yace “I promise bazan dade ba kinji Ammi please” dan lumshe ido tayi cikeda takaicin shi sanan tabude su, batason tamai masifa hakan yasa ta sassauta murya tace “gobe fa bikinka haba Waleed bazaka iya daukan break kahakura da zuwa aikin nan ba, yakamata kaje kaga Ilham ko, you suppose kaje kaganta kaji medame dame take bukata, yaufa dinner ku mesa kake hakane? Kai baka gajiya da aiki, safe aiki, rana aiki dare aiki dukkai kadai bakagajiya?” tai maganan sounding a bit harsh sanan tai shiru tana kallonshi, ahankali ya saukar da kanshi kasa kaman bazaiyi magana ba saikuma yace “am doing all wat am doing for Dad Ammi, I’m doing it for him” yay maganan tareda dago kanshi ya kalli mahaifiyar tashi sosai yaga jikinta yay wani irin sanyi, hannunta takai ahankali ta shafa full sajenshi dakeda mugun laushi yana kyalli sosai tace “Waleed, Boy listen” tai maganan ahankali tace “I know u are doing all this for your father and trust me, I know duk inda mahaifinka yake he is proud of you cus he gave birth to such eloquent hard working youngman da burinshi shine yataimaki Al Umma, but in this Life Waleed you need to balance somethings, bazaiyu kullum aiki aiki aiki ba, u are needed awasu wajajen, za’ayi bikinka but bikin baya gabanka kwata kwata kabar su Khaleel da Hammad sumaka komi that isn’t right kagane?” gyadamata kai yayi ahankali, sanan tace “abinda nakeso dakai yanzu, I know how much this work means to you dan haka bazan hanaka zuwaba, kaje but ana tasowa daga sallan juma’a kadawo kazo kafara shirye shirye, take a break of 2weeks aure zakayi kaji” gyadamata kai yayi amman harga Allah yasan yanada rai da lafiya bazai iya yaki zuwa wurin aiki harna tsawo kwana goma shahudu ba but bazai iya gardama da Ammi ba. “now eat karkai latti” maganan Ammi ya katse shi hakan yasa ya karbi fork din datake bashi ya shigacin Irish din yana dangwalawa a ketchup, yadanci badayawa ba yadau shayin ya shanye sanan ya goge bakinshi yatashi yana kokarin daukan briefcase din yace “ina Mum Ammi? Naje dakinta bata ciki” murmushi Ammi tayi tace “Mum dinka nachan ana harkan biki, ni banmasan ina tanayi ba, wuce katafi sabida kadawo dawuri” gyadamata kai yayi yadau briefcase din yafito waje, babban compound ne mai bala’in girma sai amsa gaisuwan masu aiki yake, gaban wata jeep yayi da wani mutumi katoto ke tsaye agabanta yana sanye da bakaken suit, yana ganinshi yabude mai baya hakan yasa ya shiga ya zauna, yamaida kofar ya rufe sanan yawuce ya shiga mazaunin direba ya kunna motar aka budemusu Gate suka fita.
Tafiyan wajen minti talatin sukayi kaman zasubar garin Abuja sanan direban yay horn agaban wani tangamemen Gate wanda sojoji guda hudu ke tsaye agaban wajen rike da bindigogin su da alamu gadi suke an rubuta WARBAI ORPHANAGE HOME AND HOME OF THE DISABLED (Gidan Marayu da Gidan Nakasassu) asaman tangamemen Gate din, sojoji na sarama motan alamun gaisuwa, aka bude gate din akayi daga ciki direba yaja motar suka shiga, titi ne har titi kaman sun shiga wani gari daban suka hau tafiya, manyan fulawowi sun ratsa dan dandamalin tsakiyan titin daya raba titin shiga da titin fita, babban wurine da girman shi zaiyi girman wani babban University, daga farko farkon babu wani gini ta wajejen sai sport yard, wajen kwallon, wajen buga long tennis, basket ball sune awajen, almost tafiyan 5 min sanan sukakai wajen wani tangamemen masallaci mai kyau gaske an rubuta WARBAI MASJID ajiki da larabci, sanan sai wani katon story building da aka rubuta Boys Section ajiki mai girman gaske, babu kowa agaban wajen sai wasu yan yara haka dake sanye da uniform na makaranta su kusan goma da wasu ma’aikata maza ke taredasu suna sanye da jeans saikuma riga dayakasance uniform ne dan yanada logo WARBAI ORPHANAGE HOME AND HOME OF THE DISABLED rubuce ajiki, yaran nakasassu ne dan wasu hannun guragu ne dasu, wasu idanunsu wani kala, wasu nada katon kai, wani kuma shanyayyen hannu saidai dukkansu atsaftace suke fes fes, kallo daya zaka musu kagane suna samun special kula, suna sanye da clean uniform da white sucks dinsu ga jakunkunan makarantan suke goyedashi da ko wanne akwai sunanshi ajiki sabida a dinga ganewa dan jakunkunan iri dayane sanan ajikin school bag din shima akwai logo orphanage home din akai, agogon hannunshi ya kalla ganin tara saura yasa anatse yace “stop the car” parking direban nashi yayi baijira yafito yabude mai ba yabude motan yafito cikin dan fushi dan yanayinshi ya nuna haka, yaran suna ganinshi sukahau ihu suna tsalle irin na yaran nan sukai wajenshi da gudunsu. “Teacher, Teacher, oyoyo” kowanen su burinshi yakamo hannunshi yarike kosu kamashi, murmushi yayi daya karama fuskarshi wani irin kyawu da cikan haiba, ahankali ya tsugunna dan tsayinsu yazo daidai cikin harshen turenci yace “Hello Children” suma cikin harshen turenci sukece “Hello Teacher” sosai yaran ke tsalle tsalle banda mutum daya cikinsu da yake kuka mara sauti sai hawaye yake sharewa da bayan hannu, maaikatan dake kallonsu cikeda girmamawa suka gaidashi. “Barka da shigowa Dr” bai tsaya amsa gaisuwan suba strictly yace “why are this children late? Maiya faru ba’a kaisu school dawuri ba?” daya daga cikin ma’aikatan ne yace “Dr gabaki dayansu basuyi homework bane antsaya amusu ne” “what happen da baku zauna dasu kun ko yamusu ba jiya? Kunzaci am paying you all ne dan kuyi yanda kukaga dama?” yay maganan babu wasa dan inhar kan yarane or duty nasu he can question, baya daukan raini, saisa suke mugun tsoronshi, cikeda girmamawa daya daga cikinsu yace “mun shafa’a ayakuri Dr, hakan bazai kara faruwa ba in sha Allah, dan Allah kayakuri” “sorry teacher” yaran suka fada ganin yanayin fuskarshi yanuna he’s a bit angry, kasa magana yayi sabida sun bashi hakuri yadauke kanshi yamaida hankalin shi kan yaron dake kuka, tashi yayi ya daukeshi yace “why are you crying namiji?” murmushi yaron yayi yadaura hannunshi kan necktie dinshi yana kallo abin yama daukemai hankali, necktie din yakama yana kallon fuskar yaron yace “you like it?” gyadamai kai yaron yayi da sauri hakan yasa yay murmushi yace “okay zansa akawo muku naku anjima okay” washemai baki yayi yaron yayi cikeda jin dadi hakan yasa ya saukar dashi kasa yace “a tafi school to, bye” “bye Teacher” suka fadi dukansu atare sanan suka wuce school ya tsaya yana binsu da kallo, babu abinda yake so kaman yaga he’s the reason behind this innocent children smile, yakai kusan 5min yana kallon yanda suke tafiya suna wasa suna tsalle tsalle maaiktan na tattarosu sanan ya kada kai yawuce yashiga motar da direban yabude mai sanan yamaida yarufe yakoma gaba yaja motar sanan suka tafi.