DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

Suna saukowa falo daidai shigowan wata yarinya fara itama tarr doguwa tana sanye da bakin doguwan riga tadaura gyalen rigan akanta batare datai rolling ba ana ganin blonde gashinta hannunta rike da jakan makaranta, Widad na ganin ta washe baki tai wajenta da gudu tai kissing checks dinta starting from the left one taima right din sanan ta rungume ta tace “marhaba Sabeeha” hada ido Sabeeha tayi da Aby daya tsaya yana kallonsu murmushi tayi ta dago Widad din daga jikinta itama tai kissing din kumatun ta sanan ta shafa fuskarta cikin harshen larabci tace “iyye Widad kin kara kyau abinki, kin kara girma kaman bakeba, ya makaranta?” gyadamata kai Widad tayi tana murmushi tace “kema kinyi kyau Sabeeha” “Sabeeha” sukaji muryan Umm daga sama ta kwaloma Sabeeha kira hakan yasa ahankali Widad tasaketa duk suka dagokai harda Aby suka kalli Umm din dake gaban bene, dan murmushi tayi tace “abu zatamin ne sorry na katse musu hira, bari taci abinci saita sauka afara shirye shiryen da ita” gyadakai Aby yayi cikeda gamsuwa yace “hakane, wuce kije kiyi salla Widad bari naje masallacin nima” juyawa Widad tayi kaman yanda mahaifin nata ya umarceta tai dakin Amah itakuma Sabeeha ta gaida Aby ya amsata cikeda fara’a yanai mata barka da zuwa sanan yawuce yafita dan zuwa gabatar da salla a masallaci.

Har daki Sabeeha tabi mahaifiyarta jakan makarantan ta tacire ta ijiye ranta adan bace tace “Umm maisa baki gayamin yarinyar nan zata dawo ba yau?” kofi Umm tadauka ta tittila mata madara a cup din sanan tajuyo ta mikama Sabeeha tace “nima uban nata bai gayamin ba nadaiga anata saka flowers ana gyara gidan nazaci ko yauma iyayen yaron nan zasu sake dawowa ne ashe itace shine dazu dasafe wai na shirya zamuje mu tarbo yar gaban goshinshi daga Airport” cikin fushi Sabeeha tace “shine ke kikawani je, ni wlh Umm bazan yarda Aby nawani treating naki kaman wata nani ba, ke nani yarshi ce kema ai matarshi ce mai matsayin da daraja, ni wlh bazan yarda ana wulakanta min keb…..” da sauri Umm tace “ke jinan inhar zai mallaka miki dukiyarshi all his property yakoma naki ai zan iya komi, kinga daga Widad sai ke ku kadaine y’a y’a agidan nan, banda haka ke accounting ma kika karanta kuma yanzu ma final exams dinki kikeyi ke kikafi chanchanta da zama in charge of dukiyoyin shi ba yarshiba” dan murmushi Sabeeha tayi ta mikama maman tata Cup din milk din data shanye tace “Umm inabadai yau Widad zata fadi ta mutuba ta ina Aby zai mallakamin dukiyarrshi nida ba yarshi ba” murmushi kawai Umm tayi ta ijiye cup din tace “leave everything to me, tashi kije kiyi wanka kici abinci saiki sauka kasa wajenta, so nike kiyi amfani da ita hakan zaisa Babanta yakara miki wata daraja na musamman a fadanshi” dan yatsine fuska Sabeeha tayi tace “I can’t stand that gurl Umm am so jealous of her wlh, I wish nikeda mahaifin mai sona irin Aby, I wish nikeda all abubuwan data mallaka” tai maganan tana bude dakinta tana shiga ta maida kofar ta rufe cike da rashin jin dadi, yayinda Umm tabi bayanta da kallo, wasu hawaye ne taji sun tarun mata a ido, tarasa maisa Aby baison yarinyarta kaman yanda yakeson Widad, kome Sabeeha take bukata yana mata, shike biya mata kudin makaranta ya ijiye mota na musamman da ita kadai ake kaiwa duk inda zata dashi, babu abinda Sabeeha ta nema tarasa kawai dai wanan son da kaunar da affection dayakema Widad baima yarta shi dudda Sabeeha ce kullum agidan but baitaba jinta kaman Widad ba, baima janta jiki, daukan tray din madaran tayi tawuce ta shiga kitchen din dake falon ta dashi ta ijiye.

Shirye shirye akahau yi sosan gaske abunku da babban gida, ma’aikata ne daban daban kowa na aikinshi, shidai Aby na zaune a falo kan tattausan kujeranshi yana kallon Widad yanda take murmushi dimples dinta na lotsawa duka biyun tana kallon hannayenta da ake mata hadaddun lalle akai, kowani hannu da wanda ke mata lalle akai, itakuma Sabeeha ganin idanun Abba na kansu yasa ta shiga gyara mata dogon gashinta tana applying hair treatment din da aka gama hadamata na gashinta tana shafawa tana bama Widad labarin yanda take fitsari ajiki datana yarinyar Widad sai dariya take kaman cikinta zai kulle.

Sosai Abba ke murmushi yana kallonta deep down jiyake kaman karyama aurar da itan wlh baisan ya ai iya rayuwa ba itaba amman abu daya ke kwantarmao da hankali inya tuna shine yanda yaga tanason Ahmad din shima kuma Ahmad din na sonta, dafa kanshi dayaji anyi yasa yadago kanshi ganin Amah ce da sauri yatashi yazaunar da ita zama tayida kyau sanan ta kalli tsakar gidan dayake kallo tai murmushi tace “Widad kake kallo ko?” murmushi yayi yasake kallon inda Widad din take ya zubamata idanu yana murmushi yace “Amah she smiled just like her mother, Widad dina is so happy Amah” murmushi Amah tayi tana kallon Widad din da Saheeba ke saka mata gashinta cikin shower cap tace “nasan duk inda mahaifiyar ta take she’s happy yarta is getting married” murmushi dukansu sukayi atare suka cigaba da kallonsu.
Gama zana mata lallen akayi sanan ta mike tsaye tana murmushi tahau rawa irin na yan mata dinan su Sabeeha namata tafi tana juyawa blouse dinta nasake zama umbrella, sosai Aby ke kallonta suna murmushi mawakan nasake rera mata waka duk wanda zai ganta sai yaji kaman ya saceta ya gudu she looks so adorable and so sweet and happy, ta gefen ido Sabeeha ta lura har yanzu Aby kallonsu yake hakan yasa ta tashi itama ta shiga filin sukahau rawa itada Widad din sosai Aby da Amah nata dariya.

Wuraren magrib aka gama raye raye aka wanke mata gashin ana wake akai drying gashin aka gyarashi tsaf bayan yasha maiyuka akamata parking sanan akasata taje tai wanka, wanka tayo sanan aka shiryata cikin wasu ubansu kaya long kaftan ne milk color dake dauke da stones da bids ta ko’ina masu shining kaman na diamond, djellaba (kaftan mai long lose robe) da aka daure mata igiyan ta wajen waist yay kaman belt, kayan kaman kayan yan India, aka yafamata gyalen kayan aka bayan an gyaramata gashi anyi parking ansaka mata wata sarka ta gaban gashin anmata makeup mai kyau lips dinan anshafa mata red janbaki dayasa tai kyau kaman ita takera kanta, gusan sarewa da wakoki dasukaji yana tashi na welcoming groom’s family yasa Sabeeha tace “Ahmad and his family are here, iyye ta Ahmad kinyi kyau” akunyace ta lullube fuskarta tana kara daure fuska ita adole Sabeeha tadena tskonar ta, Sabeeha tai dariya tace “ina platan dake dauke da zoben sa ranan?” ahankali tace “yana wajen Amah” gyadamata kai Sabeeha tayi tace “tom bari naje naga ya ake ciki awajen” fita tayi daga dakin tai dankareren compound dinsu ta tsaya tana kallon kowa, iyayene aketa gaishe gaishe family su Ahmad ne da taasu tawagar yayinda wani kyakkyawan balaraben guy yana sanye da sherwani hadadden gaske milk color kaman kalan na Widad, sai fararen kafanshi sanye da Babouche (traditional morrocan shoes) hadadden gaske shima milk, fuskarshi na kyalli bakin sajenshi da gemunshi a kwance yana murmushi yana kallon kowa kanshi ya kafa wata yar karaman hula milk color dake dauke da bids design tsayamai a tsakiyan kanshi, dan tabe baki tayi ta tsaya daga inda take tana satan kallonshi kaman yaune tafara ganinshi. “Sabeeha” Aby ya kwalamata kira da sauri ta waigo Aby ne da Umm tareda iyayen Ahmad, cikeda fara’a kana ganinshi kasan yau cikin farin ciki yake yace “jeki kawo yar uwanki afara lokaci natafiya” gyadama Aby kai tayi tajuya takoma ciki, bude dakin tayi ta shiga ta tarar da Amah ma natare da Widad din tana kara gyaramata fuska, ganin yanda Amah ke kallonta yasa tace “Aby yace afito da itane Amah za’a fara” dago Widad din Amah tayi tana gyara mata zaman gyalen sanan ta kalli Sabeeha ta nuna mata farantin da jajayen flowers ke cike aciki sai akwatin zoben tace “biyomu da wanan, muje Widad” ahankali Widad ke tafiya idanuwanta akasa har suka fita tsakar gidan inda wakokin larabawa ke tashi taresu maman Ahmad tayi ta rungume Widad din da takasa daga ido ta kalleta tamata kiss akumata tace “masha Allah Widad kinyi kyau” mahaifin shi ma haka yamata kiss akumatu sanan Amah tawuce da ita har zuwa inda Ahmad yake azaune wanda nanne aka tanada dan zaman Amarya da ango Amah ta zaunar da ita akan kujeran gefen Ahmad sanan ta cupping face din Ahmad tace “dan saurayina kai kyau” dan dariya yayi yace “Amah nifa nagayamiki bani sonki jikanki nakeso” dariya tayi tamai kiss akumatu tace “ko kaki ko kaso yaro soyayyan mu ba fashi” tai dariya tareda wucewa tabarsu awajen shiru sukayi Widad taki juyowa ta kallai dudda takosa ta kallai dan tasan yay kyau jikinta na bata hakan. Yana kallon masuyin rawa kaman hankalin shi na wajen yace “tayaya zan fara bawa wacce zuciyata ke bugamawa hakuri?” yadanyi shiru yace “nasan Ahmad mai laifi ne amman da ace Widad zata dan juyo ta kalli Ahmad koda sau dayane da Ahmad yasami natsuwa dan zuciyarshi dab take data buga” dan juyowa tayi ahankali ta kallai saida kirjinshi yabuga baitaba ganin tamai kyau irin na yauba kasa daina kallonta yayi hakan yasa ta dauke kai abinta tanadan murmushi zaiyi magana yaji muryan Aby nabada izini akashe wakan dan zasu fara ceremony din, wani ne yazo yabude taron da addu’a sanan akasa Ahmad da Widad din sufito fili, dan wake aka fara yi ana zubamusu flower kafin abokin Ahmad din dake gefenshi yamika mai farantin zoben daukan akwatin zoben yayi yabude yaciro wani hadadden diamond ring ya kalli fuskar Widad din kaman yanda take kallonshi yace “inason ki Widad and I will love to spend the rest of my life with you, kin yarda muyi taking this relationship a step forward ta hanyar engagement?” ahankali ta gyadamai kai, hannunshi yasa yakamo hannunta ahankali yana kallon fuskarta ya zuramata zoben a yatsa ihu aka dauka da tafi ana jefamusu fulawowi, ahankali Widad ta juya tadau akwatin zoben ta daga farantin da Sabeeha tarike tabude ta ciro zoben sanan ta kalleshi cikin tattausan sweet muryanta tace “Ahmad you’ve been the source of my happiness and joy inhar ban aureka na zauna akarkashinka ba Menai achieving a rayuwan nan, yes I love you also and I don’t have any greater wish daya wuce yin rayuwa dakai” ahankali ta ziramai zoben a yatsunshi hawaye ya cika idanunta saikuma tajuya ta rungume Aby da gudu dake gefen ta yana kallonta tahau kuka, watsa musu fulawowi akahau yi Aby na jijjigata dan tai shiru shikuma Ahmad na satan kallonta Widad is so soft, abu kadan kesata kuka, kaman ma a daura musu auren yau yakeji yahuta da wanan wutan son nata dake cinshi amman ya zaiyi nanda 7days ne tazama tashi halak malak, da kyar Aby yasamu tai shiru sanan yadagota tareda sharemata fuska duk yabi yadamu danshi ko inane ko agaban uban waye baida kunyan nunama yarshi so, cikeda lallashi dakuma damuwa yace “me haka kike kuka so kike kitadamin hankali? Eh” girgizamai kai tayi hakan yasa yace “to menene? Bakida lpy ne?” girgiza mai kai kawai tayi dan batason ta tadamai da hankali zai sake magana Ahmad dayakasa hakura yadan matsi kusadashi cikeda girmamawa yace “ahhh Aby please can I have a moment with her” gyadamai kai Abba yayi yana kara kallon fuskarta cikeda damuwa yace “kuje falona watakila tai shiru, please tafada maka meke damunta” gyadama Aby kai yayi ya kalli Widad din dake share fuska yace “muje” juyawa tayi ahankali sukai ciki yayinda iyayen su suka bisu da kallo cikeda so, instead of yaje falon Aby saiya kaita rooftop her fevorite place in the house, zaunar da ita yayi ahankali kafin ya zauna agabanta yana kallon yanda take share hawayen dasuka kasa daina tsayawa cikeda damuwa yace “why are you crying? I thought today suppose to be the most happiest day of our lives Widad we’ve come a long way, we are getting married in 7days” shiru yayi yana kallonta ganin takasa daina kukan, ahankali yace “are you missing your Mum?” dago jajayen idanunta tayi ta kalleshi duk duniyan nan banda Aby no one understands her like Ahmad, intai kuka yasan kukan me intai bakin ciki yasan name hakama intai murna, saisa take sonshi, ganin takasa bashi amsa sai kallonshi take wasu hawayen nasake fitowa yasa yadawo ta saitin inda take zaune ya zauna a gefenta tareda lankwashe kafa yay dan shiru sanan ya kalli sararin samaniya yana bin taurarin dake sama da kallo, cikin yar lallausan murya yakira sunanta. “Widad look up ????” yanda yay maganan yasa ta dago kanta ta kallai ganin sama yake mata pointing yasa ta kalli saman itama yace “kinga wanchan taurarin dayafi kowanne cikinsu haske” shiru tayi tana kallon tauraron dayake nunama ta, yace “let’s take your Mum to be that tauraron, trust me your Mum is up there tana kallonki, and believe me inna gayamiki abu daya datafi tsana aduniyan nan shine taga hawaye nafita daga precious eyes dinki, banda hakama ni she will be angry with me” da sauri ta kallai irin kallon tambayan nan, dan juyowa yayi ya kalleta shima yazubamata kyawawa fararen idanunshi yana kallon fuskarta cikin tsantsan begen so yace “I promise Mum tun kafin tarasu akan I will always make u happy, bazan taba barin yarta ta zubar da hawaye ba gashinan yau I couldn’t keep my promise sai kuka kike, am a bad person I couldn’t keep my word am a bad person” yafadi shima kaman zaiyi kukan yana kallon kwayar idanunta, ahankali ta girgizamai kai tace “you are not a bad person in fact you are the best human I’ve ever come across in this world” takai hannunta ta share hawayen tass tana kallonshi Kaman yanda shima ke kallonta kaman ya tsaga jikinshi yasata aciki yakeji kawai yahuta, tun yana University yanadan saurayi yake son Widad tun ranan da Abban shi yazo dashi gidan wajen Aby dan Aby da Abban shi na business tare sosai, lokacin Widad kaman 11yrs take tun lokacin yake sonta, kuma yana bala’in alfahari da ita dan yasan bata taba kallon wani namiji ba balle harta tsaya kula wasu samari dudda tanada mugun kyau da farin jini but shi kadai takeso, yazauna yayi zaman jiranta all this while dan alkawarinsu was sai tagama makaranta zai jiranta sanan sai suyi aure amman hakanan yan kwanakin nan yaji bazai iyaba saisa yadami Abba yazo yasami Aby akai maganan saka rana da biki, yau kuma daya ganta hakanan yakeji kaman ma bazai iya jira kwana bakwai dinan ba kaman a daura auren yanzun nan yakeji a ranshi jiyake kaman za’a kwace mai ita. “Ahmad” Widad takirashi ganin kaman yay nisa atunani, dan murmushi yayi yace “Widad” murmushi tayi tace “tunanin me kakeyi?” shiru yayi yana kallonta kaman bazai bata amsaba saikuma yace “tunanin ranan da am gonna make u mine, namiki ciki” “subhanallah” tafadi da sauri tareda tashi tsaye zata gudu dan kunya taji dan tunda suke tsawo shekaru 10 kenan yanzu baitaba mata maganan banza hakaba, karap taji yarike hannunta yatashi tsaye shima turo baki tayi batare data kalleshi ba tace “ka sakeni” batare dayasake taba yazo ta bayanta yace “kinsan in kika haifamin mace sunan Mum dinki zamu saka ko Widad” akunyace tajuyo ta runtse ido ita adole kunya take ta kalleshi tanaso ta fizge hannunta tace “ni naji to kasaken natafi kaga ana jiranmu ko” dan bakinta yake kallo yanda idanunta ke arufe tana mai shagwaba, ahankali yakai bakinshi saitin nata wani abu na pulling dinshi kaman zai mata kiss saikuma kawai ya rungumeta tsan tsam ahankali yace “I love you so much Widad, I love you” “Widad” Sabeeha ta kwalamata kira da aka turo takirasu a mugun tsorace tabude idanunta tareda fizge jikinta daga jikin Ahmad, Ahmad baitaba rungumeta ba sai yau bama tasan ya akayi hakan yafaru ba dan abin yafaru cikin few seconds ne, sakinta Ahmad yayi ya kalli Sabeeha da idanunta kyam akansu yace “baki iya sallama ba” juyawa tayi tareda watsamai harara tace “baka koyamin ba, dayake kana batama Aby y’a ai dole kace haka” ta juya tafice abinta, a mugun tsorace Widad ta juyo ta kallai zatai magana kuma takasa sai kuka tace “mesa ka rungume ni kaga zata fadima Aby ko” yana bala’in son yaga Widad ta rude bala’in bala’in kyau take, ganin murmushi yake yasa tafashe da kuka, ganin yanda take kuka tana bubbuga kafa akasa yasa yace “wlh in bakimin shiruba kamaki zanyi naita kissing inyaso su Aby sazosu ganmu ahaka kinga a daura auren mu ma yau ko dan ansan mun kosa” yay maganan bakodar atattare dashi shiru tayi takasa cigaba da kuka murmushi yayi yazaro handky ya mika mata yace “wipe those tears mutafi” karba tayi ta share tass sanan yakama hannunta yarike suka wuce suka sauka daga rooftop din.
[11/1, 11:46 PM] Re@l???? K@usy ????: ???? TWO DIFFERENT WORLD ????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Leave a Reply

Back to top button