DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

✍️ M SHAKUR
9️⃣
This novel is 500 Fanmily❤
How to Subscribe to TWO DIFFERENT WORLD
zaki turo 500 to account 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment to watsapp number na 07012181461, sainai adding naki a group din danake posting DUNIYA BIYU MABANBANTA
NIGERIA
Abuja
Washegarin ranan biki
Misalin 9 na safe yafito yana sanye da fararen kaya, farin t-shirt sai farin wandon shadda ajikinshi da farin slippers din kafarshi, yana tafiyan nan tashi dai dai yana kallon yanda ma’aikatan gidansu ke aiki ana kara gyara gidan da aka gama biki jiya aciki kaman ba’ayiba, dan gajeren tsaki yaja yawuce ya shiga flat dinsu, babu kowa a falo sai wasu mata guda biyu dake sanye da uniform suna aiki daya na goge Centre table dayan na jera abinci dining, gaidashi duk sukayi amman ko kallonsu ma baiba yawuce yahau stairs dorect dakin dayasan zai sami Mom dinshi yawuce, bude kofan yayi bayan yay knocking akan dadduma yaga Mom hakan yasa yamaida kofar kawai yarufe ya shigo ciki hawa kan gado yayi yay kwanciyarshi tareda lumshe ido kaman mai jin bacci yay shiru kana gani kasan yaje dogon tunani. “Dan Yaro” Mom ta kirashi tana linke hijabin jikinta bayan ta tashi daga kan dadduman, dago kanshi yayi ya kalleta yace “morning Mom” “morning katashi lpy, daman yanzu nake shirin naje naduboka, kaci abinci?” yatsine fuska yayi yana tashi yana zama batare daya amsataba, daukan dadduma tayi ta linkeshi shima sanan ta ijiye ta taho ta zauna gefenshi abakin gadon takai hannunta ta daura akan kunnenshi tashafa tace “Dan Yaro how do you feel? Yau zaka koma gidan amaryan ka” yatsine fuska yayi batare dayace komiba murmushi tayi tace “muje dinning kai breakfast” tai maganan tana tashi tashi yayi shima yabita suka sauka kasa dinning sukayi tahadamai shayi yasha ba laifi dan yau yatashi feeling strong, ta zubamai Irish da source fork yadauka yafaraci duk sukai shiru.
Ahankali take tattakala matattakalan benen, tun kafin ta sauko take kallonsu barinma Waleed, ko tari batayiba takarasa saukowa kamshin turarenta yasa Mom ta dago kanta ta kalleta, tai bala’in kyau tana sanye cikin wata dark brown atampa da milk color na English wax, tai kyau irin hajiyoyin matan nan, washe baki Mom tayi tareda ijiye spoon din datake cin abinci dashi tace “ina kwana Adda kin sauko” gyadamata kai Ammi tayi still looking at the Waleed, ahankali yadan dago kanshi ya kalleta hada ido sukayi saikuma ya dauke kai murya chan ciki yace “good morning Ammi” “morning” ta amsashi atakaice tawuce kan dogon kujera ta zauna tareda daukan remote ta chanza tashan zuwa African magic taga ko anfara series dinan the Johnson’s badan komi takeson shirin ba saidan bada dariya da Nigerian series din keyi.
Ajiye fork din Waleed yayi yadau tissue yana goge baki Mom tace “badai harka koshi ba Waleed ai bakaci komiba anan ga peppersoup ga yamballs you haven’t touched any” ashagwabe yace “nina koshi, thanks Mom” yay maganan yana tashi daga dinning yamaida kujeran yafito zai fita batare daya kalli Ammi data bishi da kallo ba, har yakai kofa zai bude Ammi ta kirashi. “Waleed” juyowa yayi ahankali ya kalleta suka hada ido saikuma ya dauke kai, tun yana yaro haka yake in yana fushi da Ammi bai iya kallonta saidai kosunhada ido ya dauke kai kawai kuma bazai taba cemata komiba itakuma dazaran yafara mata haka tasan fushi yake da ita, ganin ya tsaya yasa tace “zonan” zuwa yayi ahankali ya tsaya agabanta yana kallon tiles yace “gani Ammi” gefen ta ta nunamai tace “zauna anan” murmushi Mom dake binsu da kallo tasaki tacigaba da breakfast dinta tana girgiza kai ita ya yarta har mamaki take bata, tanason Waleed fa kaman ranta amman rigimanta yafi karfinta.
Binshi da kallo Ammi tayi daga sama har kasa babu alamun wasa tattare da ita fuskarnan ta daureshi tace “were you sick ne jiya?” juyowa yayi ya kalleta baki yabude zaiyi magana tace “karka sake kamin karya, I ask a question, where you sick yesterday? Maiya sameka jiya?” ta tambaye shi kai tsaye, shiru yayi kaman ba zaice komiba saikuma yace “zazzabi ne nai amai once but am fine now nasha magani” ji Ammi tayi ranta inyay dubu yabaci tace “and u don’t think it was important to let me know ko, inda bantambayeka bama yanzu da bazaka fadamin ba eh?” shiru yamata baice komiba tsawa tadakamai cikin fushi tace “am talking to you kamin shiru Waleed, why didn’t you tell me u were sick?” cikin fushi shima yace “wai Ammi for godsake when will you stop treating me like a child eh? Komine saina fadamiki? Yes I was sick yesterday, and I treated myself and I feel much better” yay maganan tareda tashi cikin fushi yay hanyar kofa, cikin fushi Ammi ta kwalamai kira. “Waleed, Waleed, Son, Son” ko juyowa Waleed baiyiba yabude kofa yafice abinshi, cikin fushi Ammi ta kalli Mom dake dinning tace “kina ganin abinda danki kemin ko?” ture plate Mom tayi tace “maiya miki? Ai gaskiya yafadi kinbi kin matsama yaro, kin hanashi sakewan rayuwa, kwaf kwaf kikebin lamuran yaron nan, ki maidashi ciki kamai kihuta haba, kin haba yaro sakewa, kina mai dashi kaman jariri, ki ciro nono ki dinga bashi mana karewanta” cikin fushi Ammi tace “ni kike gayawa haka?” itama cikin fushi dan dama tadade tana tike da Ammi tace “mene fadi? Ba gaskiya bace, kin kama kin aurar da yaro batare dakin shawarce shiba ko tambayan ra’ayinshi inda wasu yaran ne angayamiki zasu yarda ne, wlh dawasu ne da kinga tijara, ba dole yaro yadinga fushi dakeba” tai maganan tana ijiye tissue tai stairs da fushi, cikeda mamaki dakuma fada Ammi tadaga murya tace “nizaku hadewa kai kujuyawa baya, dani kuke fushi?” tai shiru saikuma tace “but I choose the best girl for him kema ai kinganta, I want jika, am so lonely I need jikoki dazaici sunan mahaifin Waleed, laifi nayi danna zabama Waleed mata shine kuka fushi dani daga ke har shi?” yanda tai maganan araunane yasa Mom taji wani tausayinta tasan yayarta sama da kowa and tasan Waleed is her weak point dazaran yaron nan yafara fushi da ita har ciwo kamata yake nan da nan BP ta zai tashi, dayake shi Waleed din danyan kai har yanzu bai sakeshi ba baitaba lurada shine weak point din mahaifiyar shiba hasalima kullum gani yake mamanshi is harsh dan Ammi is too strick dashi gata batada fara’a ko kadan Mom tafita fara’a nesa bakusa ba, saisa all abokanenshi sunfi sabawa da shakewa da mom kan Ammi. Ahankali Mom tajuyo ta kalleta tace “Adda baki gane abinda nake nufiba nasan kowani hukuncin kika yanke akan Waleed is for the best, but yayan yanzu bahaka suke ganiba, naga Ilham yarinya mai kyau, ga ilimi ga kunya, ko makaho ya ganta yasan kin zabo sanan kin dirzowa danki mata, but the question is does your son see it that way? No” ahankali Mom tace “ki sauke wanan harshness dinan kije ki lallabo yaron nan kinmai aure and he feels bai shiryama aure yanzu ba, just patch things up with him kinfini sanin yanda zaki hakan, Adda solve this problem once and for all please inba hakaba ke zaibama kunya inya fara wulakanta yar mutane” Mom na maganan tajuya tai sama abinta, bin bayanta da kallo Ammi tayi harta bacemata daga gani sanan takoma ahankali tazauna akan kujera tabuga uban tagumi takai kusan minti ashirin ahaka azaune saikuma ta mike kaman wacce aka tsikara tai waje.