DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

✍️ M SHAKUR
1️⃣4️⃣
This novel is 500 Fanmily❤
How to Subscribe to TWO DIFFERENT WORLD
zaki turo 500 to account 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment to watsapp number na 07012181461, sainai adding naki a group din danake posting DUNIYA BIYU MABANBANTA
FREE PAGE
NIGERIA ????????
Wani irin juyawa jirgin yayi kafin kace me jirgin yabace a hazo, kwashe yaran aka shigayi ana lodasu a mota yayinda wajen yacika security personnel da some marine forces dake wajen, wasu mutane guda uku ne sukayo wajen Waleed na tsaye inda yake suka shiga cikin ruwan kaman sune search force, sun duba ruwan basuga komiba saidai suka dawo tareda coffin din, Arham ne yakaraso inda Waleed yake tsaye bayan ya tabbatar da staff dinsu suntafi da yaran yace “meya faru just now blood? Jirgin sama right above our head? That’s strange, bantaba ganin hakaba sanan ya jefar da akwatin gawa a ruwa is that even okay no wa…. ” hannun da Waleed yadagamai yasa yay shiru ya kalli inda Waleed ke kallo da sauri, mutane biyun ne suka fito daga ruwan rikeda akwatin dayake abude suka ijiye bakin ruwan sanan suka fito da sauri Waleed yay wurin Arham biye dashi, tsayawa chak sukayi suna kallon akwatin da jini yabata sosai garuwa ciki, dayan dake cire kayan ruwan da yasaka ne kafin ya shiga cikin ruwan yace “I don’t understand, jirgi kawai yazo yajefo mana akwatin gawa lafiyan su kalau ko bazugani da kyau sun zaci nan bolane” da sauri dayan yace “ni nama zaci gawa aka yardan mana ashema akwatin ce kawai, to Allah dai ya kyauta amman wanan abu haka, we will report to the police ashigar da karan susan inda zasu jefar da waste dinsu jibi yanda suka daga ma bakinmu hankal…..” shiru yayi ganin Waleed ya tsugunna yanabin jikin akwatin da kallo yana shafa akwatin da hannu kaman maiso yagano wani abu, kafin idanunshi su sauka kan dan kunne kwaya daya dayake makale acikin hole din shan iskan nan da akayi kaman ramin yatokare dankunen dayakeda fadi dan dankunne yama ramin kadan abinda yanashi fita kenan da ruwa shima yay sweeping nashi away, ahankali Waleed yasa yatsanshi yaciro dankunen yamike tsaye yana kallo daya daga cikinsu yace “wow dan kunnen mai kyau halan yayimoshi yayi a ruwan, muje Bala mutafi da akwatin” daukan akwatin sukayi harzasu tafi da sauri Waleed yace “are you sure kunduba ruwan nan da kyau babu kowa ciki?” “yallabai babu inda bamu dubaba ai indai wanan rafin dakake ganine babu wani lungu da sako dabamu saniba cikinshi, bayau muka fara ceto rayukan mutane acikinshi ba” gyadamausu kai kawai yayi suka wuce suna zance, Waleed yajuya yana kallon ruwan da sauri Arham yace “don’t tell me u want to go in da kanka” juyowa Waleed yayi ya kalleshi yace “of course yes, ga dankunne nagani a box din” da sauri Arham yace “this is river Waleed, ruwa ne, the coffin can pick the ear ring anyway aruwan, kagama wuce mutafi dan wlh kana kara making attempt din shiga ruwan nan zan danna ma Ammi kira” wani mugun kallo Waleed yamai yace “toka kira munafuki” yana maganan yafada ruwan da sauri Arham yace “Waleed” gabanshi nafaduwa yana kallon ruwan da Waleed ya nitse ciki, arude Arham yace “Waleed wai me haka sai wani abu yasameka acikin ruwan nan eh? Come out please” kusan 10min Waleed yadauka cikin ruwan sanan yafito ahankali, Arham yace “kagani kaima bakaga komin ba, kafi wayance iya aikinsu ne kawai kaje ka jika kayanka a banza” ballamai harara Waleed yayi yay gaba abinshi Waleed ya bishi da sauri yanadan dariya yace “wlh kacika rigiman banza, kawai daga ganin dan kunne shikenan” Waleed baice mai komiba har sukaje children section din, zai shiga ciki saikuma ya kalli Arham yace “lemme go and get Khadija and change” gyadamai kai Arham yayi Waleed yawuce.
Knocking yayi tareda bude dakin yashiga, daidai lokacin Ilham tafito daga bayi tana sanye da hadadden jeans din daya kawomata as gift jiya da crop top din da hakanan yadauko let’s just say he’s use to seeing ladies yan gayu dress in them so practically he wants to see his wife dress like that, tana ganinshi ta taho da gudu zata fada jikinshi ta rungumeshi yakoma baya yace “am wet baki gani” binshi tayi da kallo cikeda mamaki zatamai tambaya yawuce bayi, fitowa yayi daure da towel yazo ya chanza kaya, tajowa wajenshi tayi da sauri saikuma tarike waist tamai wani irin juyi tace “bakace nayi kyauba, nayi kyau?” dan murmushi yayi kawai yakarasa bakin gado ya zauna bayan ya chanza kayan yace “is nice” wani irin blushing tayi ta taho da gudu ta zauna kan laps dinshi sanan ta manna mai kiss a lips dinshi tace “thank you” gyadamata kai yayi kawai sukia shiru, ganin yamata shiru yasa tace “Dr jirgin na landing awajen nanne dazu naji karan jirgi kaman akaina” ahankali yace “it just came and yakuma juya” gyadamai kai tayi tana kallon yanda yake maganan yace “get dress let’s go out” cikeda wani irin murna ta dagashi wardrobe taje da sauri taciro gyale mai kyau dazai shiga da jeans din sanan takoma gaban mirror ta yaryada uban kwalliya tasa jan baki sanan ta yafa gyalen awuya tajuyo ta kallai yana danna waya tace “na shirya” dagokai yayi ya kalleta dauke kai yayi yace “change into something native” wani iri taji taso sufita ahaka ko Arham yaga shape dinta da kyau saikuma ta share tai gaban wardrobe din dakin wata pink atampa taciro da aka mata riga da skirt ta shirya tsaf ciki kayan sun mugun kamata suranta yafito sosai, tayafa gyalen daya shiga da kayan tasaka flat shoe sanan tazo gabanshi tace “Baby let’s go” dagokai yayi ya kalleta sai kawai yamike tsaye yamaida wayan aljihu yay gaba, bude mata kofa yayi tafito sanan shima yafito yamaida kofan yafita, ahankali suke tafiya har zuwa children section atare suka shiga wajen, da Arham tafara hada ido da sauri ta dauke kai kujera yabata tazauna yace “am coming” gaishe da ita staff dinshi suka shigayi tana ansansu ayangance shikuma yawuce inda Arham yake yace “am taking her out blood she has been indoors tunda mukazo” batare da Arham yakalleshi ba yace “saikun dawo” juyawa Waleed yayi yaje wajen ta suka fice inda bodyguard dinshi ke tukasu, cikin Bauchi suka shiga shi bai wani surutu da ita amman kome takeso tana fadi zai siyamata daga bayama supermarket yakaita yasami waje ya zauna tadauki duk abinda takeso sai dadi takeji sanan suka dawo mota, da magrib sukaje wani eatry bayan ya tsaya sunyi salla a masallaci, sosai ranan taji dadi tasamu sunyi pics sosai dashi komi yasai mata saitai snapping asamu na nunama friends a status sai wajajen 10 nadare suka dawo, baje tsaraban ta tayi a kasan dakinsu tana dubawa tana snapping shikuma yatabe fuska ya shiga bathroom abinshi wanka yayi yazo ya shirya cikin pj yakoma kan gado yabude system dinshi yana aiki, harya gama yay bacci yabarta tana daddanna waya ana saka status ana amsa comment din kawaye.
Ahankali motar data kwaso mutane kusan goma sha hudu ta God is good take tafiya sabida yanda motar ke over heating, passengers din cikin motar sai tsaki suke suna korafi daga Abuja da suke, yanzun nan suka baro Abuja Benin zasu amman shine tun yanzu sun tsaya yakai sau uku wanan wani irin abune, daidai sun shiga MURTALA MUHAMMADU BRIDGE dake nan hanyar lokoja gaban motan yafara hayaki hakan yasa dole direban yayi paki tareda tsaki yafito, bude kofa passengers sukayi dan sufito sudansha iska indamai fitsari yaje yayi, wata matace dake rikeda yarinyar da at least zatakai 7yrs ne tace “Mummy I want to ease myself” kallon Bridge din matan tayi duk titine ga maza kuma itama fitsarin takeji agaban su zasuyi tunanin hakan yasa takama hannun yarta tarike tareda rataya Jakarta akafada suka sauka daga Bridge din zuwa kasa, sauka sukayi suna tafiya, tanacikin tafiya taji ana tafiya da sauri matar ta juyo ganin wata yar matashiya yasa da sauri matashiyar tace “me to I want to piss madam, sorry if I scare you” juyawa matar tayi tace “no problem” sauka sosai sukayi suna dandarawa har zuwa gaban ruwan da ake cewa anan River Niger da river Benue suka hade, cirema yarta wando tayi tace “tsugunna kiyi, bari indan matsa ta chan is like na pupu dey worry me sef, since ba yanzu motar nan zatai cooling down ba gwara nai kayana our journey still fa, if u finish just stand here I dey come” gyadamata kai yarinya tayi itakuma Maman ta shiga cikin ciyayi sabida yadan kareta, yayinda itama dayan budurwa tashiga cikin ciyayi kowa yashiga biyan bukatun sa. Wani irin ihu da yarinyar ta kwala ba matan kadaiba har mutanen dake chan wajen mota saida yay calling attention nasu. “Mummmmmmyyyyy!” azabure uwar ta tashi ko kashin bata wanke ba tafito tanajan pant dinta sama same with dayar budurwan, da sauri Maman tai wajen yarta dake tsaye tana kallonta tace “wat is it Engozi?” daidai dayan budurwan itama tazo tace “wats the matter why are you shouting beautiful girl?” duk suka tsaya kan yarinyar suna tambayarta ganin yanda take shaking, ahankali tadaga hannunta tamusu pointing ???? rafin duk suka juya suka kalli inda take pointing atare maman da budurwan suka hada baki suka kwala wani irin ihu. “ahhh hhhhhhhhhh hhhhhhhhhh!” within 1min suka hada mutane wajen ciki harda direban su dan ihun yay yawa sun zaci macijine ma ya sarezu, yanda yan tafiye tafiye sukaga direbobi na sauka kasa ana ihu yasa aka shiga parking mota ana sassakkowa dan anzaci hatsari ne kafin kace me mutane sunfi dari dayan kai awajen, matsar da mataye biyun akayi dake rangada uban ihu, daya daga cikin mazan da duk suka tsaya suna kallo yace “are you sure this one is alive” daya daga cikin mutanen wajen ne yace “acirota please wanchan bishiyan daya rike mata riga ne da yanzu ruwan yakara sweeping nata away” wani ne yace “waya iya ruwa dan Allah anan?” daidai lokacin wasu rundunan mutanen sun iso wajen daya daga cikinsu yace “na iya na iya” da sauri matan wajen sukahau cewa “oga pray o, this river they chop people wey no be from here” murmushi kawai mutamin yamata yace “this na my work in my state” kayanshi yatube agabansu yarage dagashi sai boxer yamikama wani dasuke tare dayake nan kaman kaninshi kawai yay iyo cikin ruwan, mutane akahau salati masu kiran jesus nakira masu ciro waya na video nayi, cikin hukuncin ubangiji mutumin yakai inda take sanan yafito da kanshi hamdala akahau yi, karasawa yayi wajen ichen daya rike riganta sanan ya damke rigan kafin yazare daga jikin icen, yakarasa wajen yarike ta gangan ajikinshi yashiga iyo da ita yana zuwa baki bakin rafin maza kusan shida suka saka hannu suka karbeta aka cirota ana ihu mutane fam awajen wasu na cewa she don die, this one don die, wasu na cewa na Mamy water, kwantar da ita akai akasa aka danne cikinta amman batai aman ruwa ba, babu wani abu da ba’a mataba, wani direba ne da yanadaga cikin wayanda ke kanta yace “please waye likita anan ko nurse koda na gargajiya ne? Yakamata asan ko tana raye kota mace gashi kanta a fashe yake gabaki daya ta baya please in akwai Dr yazo” yay maganan yana ihu sabida aji hakan yasa aka shiga passing information din har zuwa kan titi inda tulin mutane suke tsaye dan basu samu wurin shigowa ba sabida acike, ciki ikon Allah aka samu wata mota da Dr keciki da sauri aka sauko dashi akai making mishi way har zuwa kan wacce aka tsinta a ruwan tsugunnawa yayi akanta gabanshi na faduwa yace “kai anya wanan bil adama ce?” yay maganan shikadai saikuma yace “ta zubar da any ruwa” atare duks samarin sukace “mum mata komi amman bata fito da ruwaba” soyake ya daga dogon gashinta dat is lying akasa dayaga yakai har cinya ta amman harga Allah tsoro yake baison abinda zai hanashi bacci, tunda yake a Nigeria baitaba ganin mace mai gashi hakaba, hannunta yakama yarike danyay feeling pulse dinta, almost 3min yana saurara amman baiji komiba yana shirin zare hannunshi yaji pulse dinta but very slow and weak a dimauce yace “sh…..she’s alive” wani irin kabbarta wajen yadauka. “Allahu Akbar” kiristocin sukahau cewa. “thank you jesus” tashi yayi yace “amman a kaita any nearby hospital this girl or whatever she is need to be saves quick inba hakaba za’a iya loosing nata, machine za’a sata dazai zuko ruwan” da sauri wani yace “wayasan any nearby asibiti?” shiru duk akayi duk asibitin da za’a fadi nacikin garine saikuma wani tsoho yace “ku kaita WARBAI ORPHANAGE HOME AND HOME OF THE DISABLED ko tsintuwa fa akayi gwamnati ta halatta mana kai abinda aka tsinta awajen, akwai asibiti da kwararrun likitoci a gidan, kana zuwa za’a karbeta, banda haka asibitin ne kadai zaku kaita ko sisi baza’a chajeku ba sanan kubarta awajen baruwan ku sune zasu dauka daga wajen, in nemo iyayenta ne inma menene duk su zasuyi, kuma ma ai babu wani nisa yana nan hanyar fita daga Abuja zakuga dankareren gini wane University ga sunan baro baro ajiki ga sojoji” addu’a akahauma tsohon maza suka dauketa wani bawan Allah dazaiyi Abuja yay volunteer motarshi mutane uku suka bishi sabida zamanin nan ba’a yarda da kowa tafiya kusan minti hamsin yakaisu gaban WARBAI ORPHANAGE HOME AND HOME OF THE DISABLES, sojoji suka taresu saida aka duba motan tsaf bayan sun nuna abinda suka tsinta sanan sukai ciki har asibitin aka kaita soja biyedasu.