DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

????????DUNIYA BIYU MABANBANTA???? ????
✍️ M SHAKUR
1️⃣5️⃣
Ahankali yatura kofan ICU kaman wanda bayaso yatura, wasu fararen kafa yagani farare tass wane kafar jaririya, tafin kafan so so pinkish kaman andiga mishi pink tiri ajiki da dogayen fararen yatsunta dakenan amike tsaye, ahankali yadaga kafanshi ya shiga dakin yanabin tundaga kafan zuwa wani blue jikakken hadadden doguwan riga dake jikinta da ruwan kayan ke diddiga akasa in drops, bakin silk gashinta daya fara tundaga kan cinyarta yake kallo har zuwa fuskarta da gashin yarufe gabaki daya ya mammanne awuyanta, faduwa gabanshi yayi shima dum! Hakan yasa ya tsaya chak dan dazaran yay motsi na bayanshi daman sun riga sun tsorata in shima ya tsorata ai mutuwa kawai yarinyar zatayi dan bazasu iya bata taimakon daya kamata ba, addu’o’i ya karanto a zuciyan shi daidai Dr Kemi da tuntuni suna wajen kofan dakin basu shigoba itama ta shigo dakin ta tsaya kusada shi tace “kaga abinda nagayama ko Dr Warbai, this gurl is not a human, look at her hair saikace bishiyan gashi” juyowa yayi ya kalli Dr Kemi irin kallon nan na in bazakiyi shiruba to kifita hakan yasa taja bakinta ta tsuke, karasawa gaban gadon yayi ya tsaya chak saikuma yadago kanshi ya kalli nurse din dake bakin kofar dakin yace “kawomin rubber band” da sauri nurse din tajuya ko minti daya bai dauketa ba tadawo rikeda robali guda biyu ta tashigo ta mikamai, karba yayi sanan yamika ma Dr Kemi yace “karba kwashe mata wanan gashin ki daure” wani irin matsawa baya da gudu Dr Kemi tayi ta rungume jikinta tace “Oga Waleed, haba now, please me no go touch this girl abeg, no vex Doctor” wani irin tsaki Waleed yaja idan har yace abin nan baikaishi wuyaba yay karya shiru yamata yajuya yay ta maza, hannunshi yasa na haggu yadagota zaune ahankali tareda saka mata filo abaya yatareta hakan yasa tai kaman ta zauna dakanta sanan yasa duka hannayenshi biyu ya tattare gashin nata ya kama da robalin da kyar, har ijiyan zuciya yake dan bai iyaba ya maida ita ya kwantar sai a lokacin idanunshi suka saukar kan fuskarta, dauke idanunshi yayi da sauri kaman wanda baiso ya kalleta sanan yasake juyowa ya kalli Dr Kemi cikin fushi yace “you have two options Dr, either you change this girl wet cloth to hospital cloth or you pack your things and leave my hospital har abada you are fired” da sauri Dr Kemi ta zuba kafafunta akasa tace “Doctor!” cikin fushi yace “what sort of unprofessional attitude are you displaying today? Da ace nasan this part of you tuntuni da bazan taba dauko ki harna baki aiki ina biyanki salary every month ba, for God sake yarinya daga cikin ruwa aka daukota ko kunya bakuji ba kunma kasa ciremata wanan jikakken kayan ajiki so kuke sanyi yakai har bone marrow dinta? Where is the hope, yarda da amincewa da al’umma suka daura akan wanan gidan marayun where is it? Where is that trust that the people and all this hopeless people bestow on us? Kunsan yanda yarinyar nan zataji lokacin data farka taganta alive bayan tariga ta dauka tata takare she is dead already, just look at this helpless child dakukai abandoning nata da sunan aljanna ne koma mayya ce whatever u guys named her ku kukasani, inkuka taimake ta, dame yarage ku ko angayamuku kuka taimaki aljani mutuwa ake? Listen ko aljanna ne, ko mayya ce koma wata halittan ce daban da bamusaniba all we know now is she needs help and Warbai orphanage and home of disables hospital is gonna offer that help to her, now my friend stand up change this girl or leave my hospital immediately” yafadi aziciye yana nuna mata tareda dakamata tsawa batare daya damu datama girmeshi ba, tashi tayi da sauri tace “zanyi, wlh zanyi? I Dr Kemi Ayobami will do it Sir, I am sorry Dr Warbai for my unprofessional code of conduct, or lemme say malpractice” matsawa baya yayi ya kalli Nurse din, da sauri ta shiga itama kafin yabata nata, dauke kai yayi yana kallon agogo har suka gama chanza mata kayan bai kallesu ba sanan suka cireta daga gadon da aka gungurota dazu akai suka maidata asalin gadon ICU nurse din tafitar da gadon sanan Dr Kemi tace “all set Dr kazo” karasowa ciki Waleed yayi ya tsaya akan Widad din dayaki kallon fuskarta yace “kunna the machine” wasu machina Dr Kemi ta kunna ta mikomai wasu igiyoyin dat are connected to the machines da bakinsu allura ne, yakarba tareda bude buturon gaban rigan Widad ya makala mata ta wajajen kirji guda uku, biyu kuma a goshinta ta both side, sanan ya kalli Computer wajen dan yaga heart beat rate dinta, daukekai yayi sanan yay placing two hands dinshi kan cikinta ya danna tareda wani irin matse flat cikin amman ko motsi batayiba ganin taki motsi balle sa ran zata amayar da ruwan yasa Dr Kemi tace “Dr I think you should go for CPR” dan jimm yayi kaman mai tunani saikuma yazo ta kanta ya tsaya yakalli fuskarta, ajiyan zuciya yasauke sanan ahankali yakai hannunshi yabude dan karamin bakinta, sosai gabanshi ke faduwa amman yasake irin dakewan nan na maza yakai kanshi ahankali saitin fuskarta, kasa jure kallonta yayi ya runtse idanunshi gam sanan yadaura lips dinshi kirjinshi na bugawa sosai kan nata, kaman an sashi dole ya hura mata iskan bakinshi cikin bakinta sosai sanan ya dago ya kalli Dr Kemi, matse cikinta Dr Kemi tayi amman ba ruwa, sake maida bakin nashi yayi ya hura iska wanan karan fin nada sanan yadago matse cikin Dr Kemi tayi cikin ikon Allah sai gashi tafara amayar da ruwa idanunta a kulle ya tsaya akanta yana kallonta saida tagama sanan ta cigaba da baccin, kallon Nurse din wajen yayi yace “get the scan room ready, I want to run magnetic resonance imaging (MRI) da computerised temograpy (CT) scan, duka biyun zan mata I want to be sure inga in hydrocephalus case (water in the brain) ne koba hakaba, inma akwai any other thing this two scan can detect ” fita Nurse din tayi bayan yagama mata bayani, shikuma yadau wata yar karaman touch mai kama da byro ya bude idanunta ya haska yaga har lokacin idanun ajuye suke, sakin idanun yayi suka koma suka kulle yay dan huci ya kashe torch din ya ijiye daidai nurse din ta shigo tace “all set Dr” gadon ya nuna musu yace “ku gungurata” gungurata sukayi bayan an ciccire mata abinda ya makale dazu yana biyeda su abaya, scanning din yamata kana ganin yanda yake kasan likita ne shi kwararre yanayi yana rubutu a wata yar karaman jutter yanama Dr Kemi bayani yace “akwai ruwa a brain din but we are lucky is not much, the water is not even the problem the problem is the injury she sustain, banda this outer one dakika gani akwai na ciki dan har jini yadan zuba but kadan aciki, but if she is still a lucky person I might be able to get it all out, idan kuma bahaka ba zan iya fito da wanda zan iya sauran with time dakuma medication zai koreshi zai tafi sabida inhar yana wurin this girl might likely behave abnormal inta farka dan dameji ne babba a brain din” girgixa kai Dr Kemi tace “ko ya akayi yarinya karama taji irin wanan ciwon akai haka yanzu gashi sai an mata aski ko”? Dan shiru yayi yana kallon computer saikuma yace “no only wajen daya tsage akan zanbi nama horizontal layi small aski haka, sabida nasamu nai mata stitches” gyadamai kai Dr Kemi tayi, ya kalli nurse yace “get the theater ready the earlier the better for her” fita nurse din tayi taje ta shirya komi, sukai theater da ita.