DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

Agogon hannunshi ya kalla 8 tayi na safe harda yan mintoci, masu shara da watering plant sai gaidashi suke yana amsawa atakaice dan baida son yawan magana ko dogon zance da ma’aikatanshi inbadai takama ba, karasawa clinic din yayi ya shiga da sauri nurses biyu dake wajen suka karaso inda yake. “good morning Dr” “morning” ya amsa atakaice yana tafiya, daya daga cikinsu dake rike da nursing chat sheet ne a hannunta tace “Dr the patient a ICU yanzun nan nadawo daga daukan vitals dinta everything seems normal” gyadakai yayi yana tafiya, sanan tace “jinin daka samata yakare, nacire waiting for you ka shigo tukunna” tai maganan daidai suna karasowa gaban ICU din, ahankali yace “good job Ramlat” murmushi nurse din tayi, dayan nurse din tace “Dr baby Mustafa, that sickle cell from pediatric ward da aka tsinta” gyadamata kai yayi alamun yagane wanne Mustapha take magana tacigaba da magana tace “we lost him last night” chak ya tsaya yajuyo ya kalleta, saikuma yace “wani irin we lost him? Ba Dr Kemi ke handling case dinshi ba amatsayin ta na pediatrician?” gyadamai kai tayi tace “Sir yaron yaji sauki sosai, toys din daka sayomai harya fara amfani dasu yana wasa playing sosai, ko jiya operation din da kayi net nasan bai baka daman dubashi ba, jiya kawai middle of the night temperature shi yay rising saikuma yafara convulsing, Dr Kemi did all she could amman we eventually lost him, actually Dr Kemi ma just left yanzun nan tana tafiya kana shigowa” shiru yayi saikuma ahankali yasaki handle din kofar ICU yajuya direct pediatric ward yaje single room section ya shiga nurses din biyedashi, ahankali yake kallon wani dan karamin jariri da duka duka bazai wuce 5month ba an lullube shi da farin zani dakin an gyara tsaf, dakin hadadden gaske, toys ta saman gadon da aka kwantar dashi dake juyawa wanda zai dinga sa yaron murna yana daukemai hankali, karasawa gaban gadon yayi yaja plastic chair ahankali ya zauna yay shiru yana kallon gawan yaron batare daya budeta ba, sanan yajuyo ya kalli nurses din biyu yace “kuje boys section, akiramin Baba Mani” gyadamai kai sukayi suka fita tareda rufo mai kofan, maida kanshi yayi ya kalli gawan kafin ahankali yasa hannu yabude fuskan yaron tahanyar yaye lullubin ya kallai, yaron baida wani kiba sosai fari ne kaman yaran fulani ga gashi akanshi sak irin gashin agwai yay wani irin haske yadan soma chanza kala dan tun around biyun dare ya rasu, hawaye ne yaji sun taho mai da sauri ya sharesu sanan yatashi yakai lips dinshi ya sumbaci yaron a goshi yana kallon fuskarshi kaman zaimai magana yamai gwarancin yara, ahankali yay murmushi yace “I remember ranan da aka kawo ka gidan marayun nan 5month ago” yay dan shiru yace “wasu manoma guda uku suka kawomin kai, suka cemin sunje gona zasu shuka iri sukaga abu a kwali ga kukan jariri suna budewa aka ganka ba kaya a jikinka jini duk yabata ka daga gani daga haifoka aka yardakai, aka kawomin kai gidan nan, I collected you and held you in my arms ina kallon fuskarka ina wondering wace mahaifiya ce zata haifo wanan kyakkyawan halittan ta yardashi awulakance haka, I whispered to your eyes Mustapha don’t cry again domin kuwan Allah yakawo ka idan bazan taba bari daidai da sauro daya ya cijeka ba, mahaifiyarka ta wulakanta ka amman Allah daya hallito ka yace bazaka wulakanta ba yakawo ka inda za’a baka kulawa, allura dakai, abaka duk wata aba dakake so” yay dan shiru ya share hawaye again sanan yace “na aika aka kira Mama Iyami nabata kai nace amai wanka asamai kaya akawomin shi clinic naduba Mustapha, nabaka Mustapha sunan prophet manzon mu da Allah ya aiko mana dashi, after series of tests nagano sikla ne kai, ban karaya ba nace I will do everything in my power naga karayu amman dayake Allah shine ubangijin mu yace baxaka rayuba harka kai matsayin danike tunani ba yau karasu Mustapha, Allah ubangiji ya jikanka, Allah ya gafarta maka, I so much wish dabaka rasu ba but Allah yafini sonka, till we meet again Mustapha” yay maganan ahankali yana kara sumbatar goshin shi daidai lokacin an bude kofan dakin, tashi yayi ahankali batare daya juyoba yasa hannu ya share hawayen shi tass sanan yajuyo ya kalli Baba Mani wani dan tsoho ne daya manyanta cikin shigan arziki ya shigo, hannu Baba Mani yamikamai yace “ina kwana likita, Allah ya gafarta mai kaji, Allah yasa yahuta” Baba Mami yamai gaisuwa dan yasan inhar akai rasuwa a gidan marayun nan yana mugun taba Waleed bakadan ba dudda yana daurewa baya nunawa, dan murmushi Waleed yayi yace “Baba Mani a dauke shi aje amai wanka amai sitira, in angama komi a kirani muyi jana’iza sai akaishi” gyadamai kai Baba Mani yayi yace “shikenan likita kayakuri, tafi ka cigaba da aikin ka, ladanka naga ubangiji ne abinda kake mana mu marasa karfi da wayan nan marayun ubangiji Allah ne kadai zai iya biyan ka, katafi” gyadamai kai yayi yajuya yafita daga dakin nurses din suka bishi, ICU yayi ahankali yabude kofar idanunshi suka sauka kan fararen kafar nan nata tafin kafan so pinkish suna facing kofa, ajiyan zuciya ya sauke ya shiga ciki yakarasa gaban gadon ya tsaya tareda folding hannunshi akirji yana kallon fuskarta da idanunta kenan a lumshe, dauke idanunshi yayi daga kanta yadau torchlight mai kama da byro yadan duko yabude idanunta tareda haskawa yaga idanun sun gyaru dan bakin sun sauko ba kaman jiyaba da ba’a ganin bakin,, sakin idanun yayi yakai yatsunshi biyu ahankali yadaura kan wuyanta, wani irin firgita tayi cikin bacci da saida shima ya firgitan ya janye hannunshi da sauri yakoma baya, ajiyan zuciya ta sauke tacigaba da baccin ta tayi kaman ba itane ta firgita yanzun nan ba, vitals dinta yaduba yaga komi nata is stable sanan ya kalli nurse yace “by 1 zan dawo na dubata” fita yayi daga dakin ya zaga through all wards din yaduba all patients dinshi dat are on admission sanan ya sallami wanda sukaji sauki sosai aka maidasu hostels dinsu, wuraren 10 yagama komi yafito sabida kiran da Baba Mani yamai, alwala yayi yaje akama Mustapha salla suka wuce suka kaishi shibai bisu ba sabida zai koma hospital.
[11/1, 11:47 PM] Re@l???? K@usy ????: ???? TWO DIFFERENT WORLD ????
_*DUNIYA BIYU MABANBANTA*_
✍️ M SHAKUR
1️⃣ 7️⃣
FREE PAGE
Hospital din ya shiga yawuce consulting room dinshi ya zauna, wata nurse ce ta shigo cikeda girmamawa ta gaidashi tace “Sir nafara aiko maka marasa lafiyan for consultation?” dan Jim yayi yana kallon wayanshi sanan yace “in 10mins time lemme make call” wayarshi yadauka yay dialing number Ilham amman har lokacin akashe hakan yasa yaja dan gajeren tsaki yay dialing number Arham, ringing biyu Arham da fitowansu daga wanka kenan tareda Ilham yadaga wayan yana kallon Ilham yana mata signal da cewan Waleed ne yace “Hey X-man ya akayi ne, katashi lpy?” anatse Waleed yace “lpy lau, how are you and how is everything going on around there?” murmushi yayi yace “gamunan duka muna sport yard ne nama fitone dan noise din yaran is too much, alot is going on, above all is super fun” dan murmushi Waleed yayi yace “to Alhamdulillah, I’ve been calling Ilham wayanta akashe, please blood take her to the airport inaso tadawo Abuja cause I don’t think I can come back, har yanzu yarinyar nan bata farka ba banda haka I have alot to do a asibitin nan, please kasa ta a jirgi tazo” wani irin bacin rai Arham yaji ya diran mishi amman yadanne da sauri yace “haba Waleed mesa kake hakane?” dan shiru Waleed yayi dan baigane ina zancen Arham din yayiba yace “what do you mean?” cikin dan fushi Arham yace “what I mean is banga dalilin da dankai bazaka dawoba kacema matarka da already tasaba da yaran nan tadawo ba, karka zama miji mai takura, kaga yanda Ilham ke kulada yaran nan kuwa, kasan bamu taho da any female staff ba, so now anything da yara matan ke bukata wajenta suke zuwa, and she’s so happy doing the work, trust me halan ma aikin ya mantar da ita bata kunna wayanta ba, please blood ko for the sake of those children dakeson matarka kayakuri kabarta kawai nanda 4days ne mun dawo yanzu kwanan mu 3 awajen fa, mekace?” dan shiru Waleed yayi kaman mai tunanin maganan Arham din saikuma yace “alright, shikenan to” wani irin hamdala Arham yay a zuciyanshi yace “idan nakoma ciki zan fada mata kana nemanta ta kunna wayanta, bye bari nakoma ciki” ahankali Waleed yace “alright bye, saina kira anjima” katse wayan yayi ya ijiye daidai lokacin nurse din tasake dawowa tabude kofa tace “Sir are you done sufara zuwa?” gyadamata kai yayi tawuce tafita tafara sendo yaransu, yawanci yan matan gidan marayun ne ciwon mara ne most complain dinsu sai masu toilet infection, kasan cewan baya wasa dasu babu wata sabo a tsakanin su yasa kowacce tana zuwa kai tsaye take gayamai matsalanta yana rubuta musu maganin sanan yana kudiran aniyan anjima da yamma da kanshi zaije yay inspecting bayin hostel din matan dan baigane infection din dasuke dama dashiba, one daidai yatashi dan yagaji yatafi mosque sallan azahar yayi sanan yadawo yawuce hospital din yana kallon agogon hannunshi karfe daya harda kusan rabi, direct ICU yayi, ahankali yabude kofan ya shiga har lokacin tana nan yanda yabarta tun safe, samin kanshi yayi da daukan plastic chair yazauna agaban gadon tareda folding hannunshi a kirji batare dayamata komiba yana kallonta kaman irin yanzun ne yasami courage din kallonta tunda yaganta jiya batare da gabanshi yafadi ba, tundaga kan tulin gashinta dayake a daure da lobari yake kallo har zuwa kan fuskarta kafin ya sauka kan hannayenta dayaga akwai yan zanen jan lalli ajiki, kaman ance yakoma baya dan hakanan saiyaga kaman idanunshi sunga wani abu, komar da idanunshi baya yayi yafara kallonta daya kan cikinta xuea fuskarta ya saukar da idanunshi kan kunnenta na dama, chak ya tsayar da idanunshi kan dankunen ta dake makale a idanunshi na dama hakanan yaji ajikinshi yataba ganin this exact dan kunnen, kaman jira mind dinshi yace haka kawai kanshi yay refreshing yatuna shine exact dan kunen dayagani da coffin a yankari, mikewa tsaye yayi da sauri yamika hannunshi yakai kan kunen nata yadaura hannunshi kan dan kunnen yadan daga jikin kunnenta ya kalla, wani irin bin dan kunnen da kallo yayi ganin har yanzu yakasa gasgata cewan dan kunnen ne yasa yakai hannunshi tabayan kunnen yabude hook din ahankali yabudu sanan yamaida hannunshi tagaban kunen zai zare dan kunen mistakenly hannunshi ya sauka kan fatar jikinta yana cire dankunnen wani irin firgita tasake yi da saida yasa yasaki dan kunnen akasa yakoma baya da sauri ya tsaya chak asandare yana kallonta, ware fararen idanunta tayi tarr tabude su duka biyun da har yanzu idanun sun karkace kaman harara garke tana kallon cilin din dakin, wani irin ajiyan zuciya ne ta kufce mai mai kara dayasa tajuyo da kanta ahankali kaman wata robot ta dauramai dara daran fararen idanunta wane madara sukai ido da ido da ita, wani irin kallonshi take kaman yanda shima yake kallonta gabanshi nafaduwa sosai, kasa jure kallon datakemai yayi hakan yasa ya runtse idanunshi da sauri yana karanto addu’o’i aranshi, an tsinci yara manya da kanana da dama agidan marayun nan wasu ma har amasai aka tsince su amman baitaba jin tsoronsu kojin wani abuba sai akan yarinyar nan shi yana rasa takamaimam miyakeji, ko tsoron dasu Dr Kemi suka haddasamai natane a zuciyanshi oho all he knows is yana shakkan ta.
“aaaahhsshh, aashh, auuuccchh, a hhhhh…..” yaji wata irin siriruwan murya, sassanya maidan gardi dake ratsa zukata na furta kalaman nan irin kalaman nan da ake furtawa idan kana jin zafi ko wani abu namaka zafi, ahankali yashiga bude idanunshi kaman wani mara gaskiya kafin yabude su tarr, zaune yaganta kan gadon tadaura hannunta akan saman kanta tana shafa inda ya aske mata a keya yamata stitches tana bata fuska tana making those sounds alamun zafi hawaye yacika idanunta gam, ahankali yake daga kafa yafara tafiya yana binta da kallo harya zagayo ta inda kafafuwanta suke ya tsaya awajen sanan yakama karfen gadon da duka hannayenshi guda biyu ya tsaya chak yana kallonta kaman ba zaiyi magana ba saikuma yace “sannu zafi yakemiki?” ko kallonshi batayiba sai cigaba da tatttaba wajen datayi daidai hawaye ya zararo zirr daga idon haggunta takai bayan hannunta tashare idanunta, tasake maida hannunta wajen tana tattabawa, ganin yanda take tabawan yay yawa zata iya warware dinkin dayay jiyan nan yasa yazagayo ta bangaren datake hannunshi yakai ahankali yakama hannunta dake kan wajen dinkin da sauri, dago idanunta dasuke akarkace tayi ta kallai, sakon hannun nata yayi da sauri yace “kul kidena tabawa, hannunki zai iya yuwa da germs ko bacteria akai bai kamata kina kai hannun kina taba fresh stitches dashi ba, so kidena” zaro ido tayi kaman irin wacce tadan haukacen nan saikuma tadan duko da kanta tana leka bakinshi kaman irin tanaso taga yay magana kuma, ganin yay shiru yana kallonta kaman yanda take kallonshi yasa ahankali takai yatsanta zata daura kan lips dinshi da sauri yakoma baya, komawa baya itama tayi da sauri saikuma tadaga hannayenta tana kallo, shiru yayi yana kallonta ganin da gaske ne lallai wanan blood yay affecting brain nata, ajiyan zuciya yasauke yana tunanin what exactly ma yakamata yamata yanzu, kujeran plastic yajawo yazauna yace “kalleni kina jina inaso nadam miki tambayoyi duk wani abu dakike ji yanzu ki gayamin” yay maganan yana kallonta still ganin har yanzu ba shi take kallo ba hannunta take kallo, ahankali yace “meke miki ciwo yanzu?” kaman ma batasan Allah yayo mutum awajen ba, wani irin kallon hannunta take tana kallon yan zane zanen lallen hannunta dasuka fara fading, jim yayi yana kallonta ganin kaman ma batasan magana yakeba yasa yakai hannunshi kusada kafarta ya bubbuga katifan yace “ke kallen dawo da hankalin ki nan” tsayar da kallon hannunta take ta kalli hannunshi da sauri daya buga akan katifa kaman irin Abun ya mugun jan hankalinta dinan, hannunta tasada sauri takai kusada tashi hannun itama ta bubbuga tana kallon nashi kaman taga wani irin film, safe gaban goshin shi yayi irin na yadamu dinan, ganin mouth conversion bazai musu aikiba dan bamata gane maiyake cewa yasanya yatashi daga kan kujeran kawai da zumin yafita sai yakira mata nurses azo a mata brush amata wanka ashiryata inyaso bayan sun gama sai akirashi yazo yay mata proper check up, tunanin hakan yasa yajuya ahankali yay wurin kofa wani irin wawan kuka yaji tasaki cikin yar muryanta dayaji har gangan jikinshi ta ratsa tashiga kiciniyar saukowa daga gadon, da sauri yajuyo ya tsaya chak yana kallonta, bare baki tayi tana kuka tana nunashi da hannu tana shirin saukowa yarinyar da tun dazu tai kaman bamatasan yana wajenba shine yanzu danya juya zai fita take wani dan iskan kuka hawaye sun wanke mata ido kaman sune abu mafi saukin fitowa ajikinta, ganin takasa saukowa kaman ma kafarta daya tarike ne dan takasa motsi dashi yasa da sauri yadawo dakin, komawa tayi ta zauna tajuyo tana kallonshi ahankali yabi kafar haggun nata da kallo sanan yamika hannunshi yazaro handglove cikin kwalin shi dake jikin windon dakin ya zura sanan yace “muga kafar” yakai hannunshi ahankali kan kafar yadaura duka hannunshi kai, mugun firgita tayi kaman irin firgita nan nacikin mafarki da sauri yasaki kafan yakoma baya yana kallon fuskarta yama kasa magana, dago kanta itama tayi ta kallai tana turo baki kaman mai shirin yin kuka kaman ba ita bace ta firgita yanzun nan ba, shiru yayi jim yama kasa cemata komi kawai saiya kara jawo kujera ya zauna ya rungume hannayenshi akirji, ganin har lokacin kallonshi take yasa yace “kalla baki magana ne ke kuma ce”? Yay maganan kaman yanda akema kurma magana yana hadawa da yatsa, yanda yay da yatsa tamai itama batare datai magana ba, ijiyan zuciya ya sauke ganin da gaske bata gane maganan shi ne, dagokai yayi ya kalleta ido cikin ido yace “what is your name”? Da sauri tanuna mai kanta cikin yar muryanta tace “name”? Abun ya mugun bashi mamaki ganin tagane turenci rass harda nuna kanta alamun da gaske tagane sunanta ya tambaya, samun kanshi yayi da murmushi dan he call this nasara dan tunda yafara magana da ita sai yanzu yaji tace wani abu, gyadamata kai yayi yace “yes, your name, tell me what is your name” kaman yanda taga ya sakin mata murmushi itama tasakin mai murmushin daya lobar da dimples dinta duka biyun tana leka fuskarshi tace “my name is” tai shiru kaman maison tuno wani abu kaman irin da gaske tanason ta tuno sunanta dinan, saikuma tace “my name issss……name” tai maganan tana lumshe mai idanu, shiru yayi kawai yana kallonta ganin ita karan kanta batasan wacece itaba yasa yace “listen to me, as from today, your name is……” yay shiru yana kallon yanda take kallon bakinshi kaman takosa yafadi mata sunan, dan ijiyan zuciya ya sauke yace “your name is Saheeba” da mugun sauri ta nuna kanta tace “ana Saheeba?” ta tambaye shi, wani irin mugun mamaki ne ya kasheshi jin tamai larabci ahankali ya gyadamata kai yace “anti Saheeba” sanan yace “Saheeba I want you to make my work easy for me, allow me to examine your leg, eye and head, my name is Dr Waleed Warbai, your Dr” yay maganan yana tashi tsaye daga kan kujera, binshi tayi da kallo kaman mai koyon magana tace “a Doctor, injection” tai maganan tana kallon alluran dake ijiye kan table din dakin, kallon alluran yayi kafin yasami kanshi dayin murmushi yace “no injection I promise, now lemme see the leg” yay maganan yana mikamata hannu alamun yabashi kafar, ahankali tadan matsomai da kafar, matsowa yayi shima yakai hannunshi ahankali yadaura kan kafar, firgita tayi sosai da saida yasa yarike kafan gam, ajiyan zuciya ta sauke yace “relax am not gonna hurt you, kidena firgita Inna tabaki” duba kafan yayi ta hanyar mamkatsawa take yagano buge kafan tai dawani abu, probably acikin ruwan nema halan ta buge, sanan yadau torchlight yazo tagaban ta Ahankali yakai hannunshi zai taduba idanunta, firgita tyi takai hannunta da sauri tarike hannun nashi tana kallonshi kaman yanda shima yake kallonta kirjinsu na bugawa atare.[11/1, 11:47 PM] Re@l???? K@usy ????: ???? TWO DIFFERENT WORLD ????