DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

???????? DUNIYA BIYU MABANBANTA???? ????
✍️ M SHAKUR
1️⃣6️⃣
sorry guys my screen broke yesterday, I couldn’t press or even answer call, na gyaro will give you more updates anjima
Da asuba ya farka wuraren karfe biyar na yamma, dawata shegen yunwa yafara cikin shi har wani hunger contraction yake having, sai yanzu yake tuna rabonshi da abinci tun breakfast din dayayi jiya at yankari kafin ma sufito hiking, shi mutun ne dabai yawancin abinci baima damu da abinci ba amman tunda yaji yunwar nan yunwan takai ne cikin shi so empty, tashi yayi ahankali ya sauka daga kan gadon yay bathroom brush yayi yadauro alwala yafito, cire pyjamas dinshi yayi ya shirya cikin wasu riga da wando nasoft yadi yafito, masallaci yaje yay sallan asubahi sanan yadawo, wayarshi yadauka ya lallubo number Mom, dailing number yayi ringing daya Mom dinshi ta dauka tace “su Dan Yaro mutan yankari yau antuna dani” yatsine fuska yayi kaman zaiyi kuka yace “Mom am hungry please ki aikomin da abinci” da sauri Mom tace “kana Yankarin ne zan aikoma da abinci Dan Yaro”? Girgiza kai yayi yace “nadawo jiya ina orphanage, ki aikomin da abinci am damn hungry bazan iya magana ba yanzu, please Mom don’t tell Ammi nadawo kinji” dan jimm Mom tayi kanajin muryanshi kasan yunwan yakeji dan da kyar yakema maganan hakan yasa tace “shikenan, bari namaka simple abu na aiko maka dashi in bama su Abdul ko direba yakawo ma?” da sauri yace “direba su Abdul da bakinsu bai shiru suje su tonani wajen Ammi” dan dariya tayi tace “shikenan matsoraci, sannu kaji nan da 30min abinci zai isoka in sha Allah” “thanks Mom” yafadi ahankali yana fadawa gado soyake yaje yaduba patient din nan but yunwa bazai barshi ba, security yakira ya sanar dasu wani zai kawomai breakfast abari ya shigo suka amsa mai da to cikeda girmamawa, ijiye wayan yayi yadan lumshe ido, ko 1hr cikakke ba’a dauka ba yaji ana kwankwasamai office hakan yasa yamike da kyar yafita kofa yabude ahankali cikeda girmamawa direban Mom dake rikeda wani hadadden basket yace “Barka da safiya yallabai” murmushi yamai yace “Adamu yau baka bata ba” dariya direban Mom Adamu yayi yace “yallabai ai yanzu na gane office din naka sosai ban bata, gidan marayun ne masha Allah da kwai girma Allah dai ya faranta ma kaman yanda kake faranta ma yaran nan marasa shi” murmushi yayi yasa hannu ya karbi basket din yazaro kudi masu yawa ya mikamai, karba Adamu yayi ya shigama Waleed godiya, batare da yadamu ba dan to him is nothing much yace “ka gaidamin da Mom, sai anjima” ya maida kofan yarufe yay ciki zama yayi kasa yana ciro komi na basket din katon flask ne dake cikeda coffee murmushi yayi ya tsiyaya coffee da kamshin shi ke tashi dan harya cika dakin da kamshi a cup, sanan yabude flax yadebi soyayyan Irish da plantain saiya debo pepper soup din fish yazuba agefe yafara ci, abinci ma rahama ne sosai wlh, duk sanda Allah yabaka ka godema dan yunwa bala’i ce, yaci abincin sosai dudda bawani cin azo agani bane but ya koshi, yay Hamdala sanan yature yatashi yakoma kan gado yakarasa shan coffee dinshi, saida ya shanye tass sanan yawuce bathroom wanka yayi yafito daure da towel a waist dinshi gashin kirjinshi sun kwanta gwanin ban sha’awa, ganin wayanshi na ruri yasa yakarasa wajen wayan ya dauka, ganin Mom ne yasa yay murmushi ya dauka yakarasa gaban dressing mirror yasa wayan a speaker ya ijiye yadau cream yabude zai fara shafawa, daga tachan bangaren Mom tace “oya start explaining nasan ai kagama cin abincin yanzu, maiya dawo dakai Abuja bayan duka duka kwanan ku biyu yanzu da tafiya Yankarin? Wani emergency ne yadawo dakai? Bayan nasan 7 days excursion kukeyi every year” dan ajiyan zuciya yasauke yace “Mom now ina miki karyane wai”? “no bakamin karya but ai I need to know abinda yadawo dakai kaida nasan baka wasa da wanan excursion din naku, yanzu dai ina matar naka kuna orphanage dinne tare?” girgiza mata kai yayi yace “a’a na barta achan” cikin daga murya Mom tace “kabarta achan Dan Yaro! Wai lafiyan ka kalau kuwa”? Ahankali yana shafa mai yace “Mom! Arham na wajen fa” dan shiru Mom tayi kaman mai tunani tace “dudda hakan bai kamata kabar yarinya achan ita kadai ba duka duka kwanan ku nawa da auren eh? Abinda zaka mata Arham zai mata ne? Kokuma angayama zata iya tunkaran Arham akan kome takeso ne kaman yanda zata tunkareka kai tsaye ta gayamaka, bama wanan ba maiya kawoka Abuja”? Dan shiru yayi kaman ba zaiyi magana ba saikuma yabata labarin komi, ahankali ta nisa tace “okay okay nagane, yanzu dai inhar kaga case din zai karasa ka kwana yauma toka kira Arham yakaita Airport tadawo nan kajini”? Murya chan kasa yace “tom” cikeda gamsuwa tace “bari na barka ka shirya kaje kaduba patient dinka, sai nakira anjima zan aiko maka da lunch” murmushi yayi yace “you are the best Mom” hararanshi tayi kaman yana wurin ta katse wayanta abinta, shiryawa yay tsaf cikin wata sky blue long sleeve shirt da dark blue wando, neck tie yadauka yasaka sanan yadauko agogonshi rolex ya saka, feshe kanshi yayi da turare sanan yazauna yasaka cover shoe yamike tsaye, wani drawer yabude yadauko wani clean ironed lab coat yarike a hannu yadau wayanshi yachusa a aljihu yabude kofa yafito yana takun nan dai dai duk wanda zai ganshi saiya kara juyowa ya kallai danyay mugun kyau sai baza uban kamshi yake.
Agogon hannunshi ya kalla 8 tayi na safe harda yan mintoci, masu shara da watering plant sai gaidashi suke yana amsawa atakaice dan baida son yawan magana ko dogon zance da ma’aikatanshi inbadai takama ba, karasawa clinic din yayi ya shiga da sauri nurses biyu dake wajen suka karaso inda yake. “good morning Dr” “morning” ya amsa atakaice yana tafiya, daya daga cikinsu dake rike da nursing chat sheet ne a hannunta tace “Dr the patient a ICU yanzun nan nadawo daga daukan vitals dinta everything seems normal” gyadakai yayi yana tafiya, sanan tace “jinin daka samata yakare, nacire waiting for you ka shigo tukunna” tai maganan daidai suna karasowa gaban ICU din, ahankali yace “good job Ramlat” murmushi nurse din tayi, dayan nurse din tace “Dr baby Mustafa, that sickle cell from pediatric ward da aka tsinta” gyadamata kai yayi alamun yagane wanne Mustapha take magana tacigaba da magana tace “we lost him last night” chak ya tsaya yajuyo ya kalleta, saikuma yace “wani irin we lost him? Ba Dr Kemi ke handling case dinshi ba amatsayin ta na pediatrician?” gyadamai kai tayi tace “Sir yaron yaji sauki sosai, toys din daka sayomai harya fara amfani dasu yana wasa playing sosai, ko jiya operation din da kayi net nasan bai baka daman dubashi ba, jiya kawai middle of the night temperature shi yay rising saikuma yafara convulsing, Dr Kemi did all she could amman we eventually lost him, actually Dr Kemi ma just left yanzun nan tana tafiya kana shigowa” shiru yayi saikuma ahankali yasaki handle din kofar ICU yajuya direct pediatric ward yaje single room section ya shiga nurses din biyedashi, ahankali yake kallon wani dan karamin jariri da duka duka bazai wuce 5month ba an lullube shi da farin zani dakin an gyara tsaf, dakin hadadden gaske, toys ta saman gadon da aka kwantar dashi dake juyawa wanda zai dinga sa yaron murna yana daukemai hankali, karasawa gaban gadon yayi yaja plastic chair ahankali ya zauna yay shiru yana kallon gawan yaron batare daya budeta ba, sanan yajuyo ya kalli nurses din biyu yace “kuje boys section, akiramin Baba Mani” gyadamai kai sukayi suka fita tareda rufo mai kofan, maida kanshi yayi ya kalli gawan kafin ahankali yasa hannu yabude fuskan yaron tahanyar yaye lullubin ya kallai, yaron baida wani kiba sosai fari ne kaman yaran fulani ga gashi akanshi sak irin gashin agwai yay wani irin haske yadan soma chanza kala dan tun around biyun dare ya rasu, hawaye ne yaji sun taho mai da sauri ya sharesu sanan yatashi yakai lips dinshi ya sumbaci yaron a goshi yana kallon fuskarshi kaman zaimai magana yamai gwarancin yara, ahankali yay murmushi yace “I remember ranan da aka kawo ka gidan marayun nan 5month ago” yay dan shiru yace “wasu manoma guda uku suka kawomin kai, suka cemin sunje gona zasu shuka iri sukaga abu a kwali ga kukan jariri suna budewa aka ganka ba kaya a jikinka jini duk yabata ka daga gani daga haifoka aka yardakai, aka kawomin kai gidan nan, I collected you and held you in my arms ina kallon fuskarka ina wondering wace mahaifiya ce zata haifo wanan kyakkyawan halittan ta yardashi awulakance haka, I whispered to your eyes Mustapha don’t cry again domin kuwan Allah yakawo ka idan bazan taba bari daidai da sauro daya ya cijeka ba, mahaifiyarka ta wulakanta ka amman Allah daya hallito ka yace bazaka wulakanta ba yakawo ka inda za’a baka kulawa, allura dakai, abaka duk wata aba dakake so” yay dan shiru ya share hawaye again sanan yace “na aika aka kira Mama Iyami nabata kai nace amai wanka asamai kaya akawomin shi clinic naduba Mustapha, nabaka Mustapha sunan prophet manzon mu da Allah ya aiko mana dashi, after series of tests nagano sikla ne kai, ban karaya ba nace I will do everything in my power naga karayu amman dayake Allah shine ubangijin mu yace baxaka rayuba harka kai matsayin danike tunani ba yau karasu Mustapha, Allah ubangiji ya jikanka, Allah ya gafarta maka, I so much wish dabaka rasu ba but Allah yafini sonka, till we meet again Mustapha” yay maganan ahankali yana kara sumbatar goshin shi daidai lokacin an bude kofan dakin, tashi yayi ahankali batare daya juyoba yasa hannu ya share hawayen shi tass sanan yajuyo ya kalli Baba Mani wani dan tsoho ne daya manyanta cikin shigan arziki ya shigo, hannu Baba Mani yamikamai yace “ina kwana likita, Allah ya gafarta mai kaji, Allah yasa yahuta” Baba Mami yamai gaisuwa dan yasan inhar akai rasuwa a gidan marayun nan yana mugun taba Waleed bakadan ba dudda yana daurewa baya nunawa, dan murmushi Waleed yayi yace “Baba Mani a dauke shi aje amai wanka amai sitira, in angama komi a kirani muyi jana’iza sai akaishi” gyadamai kai Baba Mani yayi yace “shikenan likita kayakuri, tafi ka cigaba da aikin ka, ladanka naga ubangiji ne abinda kake mana mu marasa karfi da wayan nan marayun ubangiji Allah ne kadai zai iya biyan ka, katafi” gyadamai kai yayi yajuya yafita daga dakin nurses din suka bishi, ICU yayi ahankali yabude kofar idanunshi suka sauka kan fararen kafar nan nata tafin kafan so pinkish suna facing kofa, ajiyan zuciya ya sauke ya shiga ciki yakarasa gaban gadon ya tsaya tareda folding hannunshi akirji yana kallon fuskarta da idanunta kenan a lumshe, dauke idanunshi yayi daga kanta yadau torchlight mai kama da byro yadan duko yabude idanunta tareda haskawa yaga idanun sun gyaru dan bakin sun sauko ba kaman jiyaba da ba’a ganin bakin,, sakin idanun yayi yakai yatsunshi biyu ahankali yadaura kan wuyanta, wani irin firgita tayi cikin bacci da saida shima ya firgitan ya janye hannunshi da sauri yakoma baya, ajiyan zuciya ta sauke tacigaba da baccin ta tayi kaman ba itane ta firgita yanzun nan ba, vitals dinta yaduba yaga komi nata is stable sanan ya kalli nurse yace “by 1 zan dawo na dubata” fita yayi daga dakin ya zaga through all wards din yaduba all patients dinshi dat are on admission sanan ya sallami wanda sukaji sauki sosai aka maidasu hostels dinsu, wuraren 10 yagama komi yafito sabida kiran da Baba Mani yamai, alwala yayi yaje akama Mustapha salla suka wuce suka kaishi shibai bisu ba sabida zai koma hospital.
[11/1, 11:47 PM] Re@l???? K@usy ????: ???? TWO DIFFERENT WORLD ????