DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

        ✍️ M SHAKUR 





                    1️⃣8️⃣

FREE PAGE
Tasowa tayi ahankali taleka fuskarshi tana kallon soft gemunshi da sajenshi har lokacin tana rikeda yatsunshi ta matso da fuskarta daidai saitin fuskarshi takai dayan hannunta ahankali tadaura kan soft gemunshi takama tana zaro ido kabarda hannunta yayi da sauri yakoma baya yana kwalama nurse kira. “Nurse! Nurse, Ramlat” ya kwalama nurse kira da sauri nurse ta taho dakin, cikeda girmamawa tace “gani Dr” anatse ya nuna mata Widad yace “ki kira wata nurse kuzo brush her teeth sanan anata wanka a chanza mata kayan nan be careful kar ruwa yaje kanta in anyway” gyadamai kai tayi tace “to sir” juyawa yayi zai fita Widad takwara wani uban ihu da saida yasa yajuyo da sauri kokarin saukowa take daga gado kota damke shi amman kafanta yahanata sabida ciwon dayike mata, sosai yaji tabashi tausayi saikuma yadawo yace “listen babu abinda zata miki I will be back soon okay” sanan ya kalli nurse din yace “make sure an bata abinci taci, go to the orphanage kitche……” saikuma yay shiru bai karasa maganan ba yace “just tafida ita bayin kimata all abubuwan danace, zan aiko da abinci dazaki bata da drugs kuma, zan fita yanzu zanje wani hospital acikin gadi nataho mata da glasses dazai gyara eye balls dinan nata in tana kallon ka” gyadamai kai nurse din tayi tace “saika dawo Sir” tsugunnawa yayi yadauki dan kunen ta daya cire dazu tai ihun dayasa yasaki dan kunen akasa, juyawa yayi yafita yana jiyota tana rangada shegen ihu da kuka, fita yayi daga asibitin yana dannama Mom dinshi kira ringing daya ta dauka yace “Mom ki aikomin da mota yanzu please” kaman zata tambayeshi saikuma tace “to bari na aiko direba” dan tare take da mai gidan ta, wucewa yayi ya shiga office dinshi basket din abincin rana da Mom ta aiko mai dashi yasa aka karba aka ijiyemai a office yadauka yafito, wani staff dinshi yakira yabashi basket din yace “kai this basket ICU kabama nurse din dake wurin” gyadamai kai staff din yayi yajuya yatafi shikuma yashiga cikin office, wanka yayi ya shirya cikin wasu fararen yadi yafeshe turare yay shegen kyau zama yayi abakin gado yabude wayanshi yay dialing number Ilham but har lokacin akashe tabe baki yayi yamike tsaye jin dayayi ana knocking kofar office dinshi, fitowa yayi direban Mom ne yace “barka da fitowa yallabai” gyadamai kai yayi direban ya mikamai key mota yace “Hajiya tace nakawoma mota gatanan nai parking dinta awaje” karban key yayi da murmushi yace “nagode” murmushi shima direban yayi yace “bari ni nakoma” da sauri Waleed yace “no muje na rage maka hanya ai fita zanyi nima” gyadamai kai Direban yayi ba karamin dadin hakan yajiba, fitowa Waleed yay daga office din yamaida kofan yarufe sanan yay wurin motan shiga sukayi ciki yaja motan sukabar gidan marayun, cikin gari suka shigo akan wata babban Junction ya sauke shi yazaro kudade masu yawa yamikamai yace “gashinan sai kahau abin hawa ni zan dauki wanan hanyar ne” sauka yayi yace “nagode, nagode Allah ikara taimakawa” murmushi kawai Waleed yamai yadauki wata titi daban, agaban wata babban super market yayi parking ya shiga siyayyan abubuwa yayi tundaga kan kayan abinci su buhun shinkafa, semi, wake jarkan manja da man gyada dasu madara da ovaltine sanan yakoma wajen supplement yasai irin supplements dinan na 30+ matan dasuka wuce shekaru talatin above yakamata suna sha, yawuce yabiya kudi ma’aikatan wajen sukamai packaging kayan sanan suka fitomai dashi, bude boot yayi suka zubamai kayan suka rufe yakoma cikin mota abinci yatayar yawuce yafita daga premises din, wata hanyar ya dauka kafin yay parking agaban wani dan madaidaicin gida mai kyau, kashe motar yayi yafito ya tsaya yana addu’an Allah ya jefo wasu yaran ko almajirai bai gama tunanin ba saiga yaran layin sun keto dagudu daga gani dana kwallo suke, dayake sun sanshi sosai kodan duk randa zaizo saiya musu kyautane yasa suka kwaso da gudu kafin ma yakirasu. “Yaya Waleed, Yaya Waleed, ina wuni, ina wuni, ina wuni” haka duk suka shiga gaidashi ajejjere harya rasa nawane zai fara amsawa murmushi kawai ya sakan musu da sauri kafinma yay magana sukace “me za’a shigan maka dashi cikin gidan Ya Waleed?” remote din motan ya danna hakan yasa boot din motar ya bude, kafinma yay magana suka shiga sunkutan kayan suna cikin gidansu Arham dashi saida suka gama shiga dashi tatas sanan suka dawo wajenshi sukace “munkai Yaya Waleed” kudi yaciro daga aljihunshi yakirga 20k yabasu karba sukayi suna ihu sunamai godiya murmushi kawai yayi yawuce ya shige cikin gidan daidai Maman su Arham nafitowa daga dakin tana tafi da hannu cikeda mamaki, ganin Arham yasa takama habanta tace “ai tunda naga kaya niki niki nasan sai Waleed, waikai Waleed baka gajiya da kashemana kudi dagakai har mahaifiyarka baku gajiya, ai yakamata yanzu duk kubar abubuwan nan tunda kunbama Arham aiki ana biyanshi, eh Waleed” ta karashe maganan da mugun mamaki, murmushi kawai Waleed yayi adan kunyace ya tsugunna yace “ina yini Mama, ya karin karfin jiki” dan dariyan farin ciki tayi takai hannu ta dagoshi a rayuwa tanason Waleed, so dashi kanshi Waleed baisan iyakan son datakemai ba, bala’in sonshi take sabida yama danta komi a rayuwa sanan yaso danta tsakani ga Allah, sanan ya fifita shi sama da kowa nashi aduniyan nan, shafa kanshi tayi tace “Waleed ai jiki kam Alhamdulillah, wayan nan magungunan daka bawa Arham yakawo min tunda nasha yanda kasan tsafi shikenan, muje ciki kaji nacika da surutu kahuta” tai maganan tana janshi ciki, ciki suka shiga, zama yayi akan kujera itama tazauna kujeran dake kallonshi tana washe baki bala’in dadi takeji tace “sannu dazuwa kaji Waleed ubangiji Allah yamaka albarka, Allah kuma yabarka da matarka lafiya” ahankali yace “Ameen Mama nagode” “madallah, madallah, yanzu me za’a kawo maka kaci? Dambu mukai da ranan nan bama adade da sauke ta ba, akawo maka da soyayyan naman talo talo” gyada mata kai yayi yace “Mama kin yanka tala talon kine” “uhmm” ta sauke ajiyan zuciya tana tabe baki tace “ai tunda dan uwanka yatasa yan tala talolina agaba waishi ihunsu na hanashi bacci zai yankasu nace a’a karya sake yatabamin kayana nasan wani abu zai samesu, kasan Arham da shegen bakin hali, ingayama shine fa jiya suka fara zazzabi fa nako gille kayana, nida Salma saici muke, ai bangayamaka ba dayake shekaran jiya tazo ko Arham ma ban gayamishi ba yar wajen kanwata Salma tazo daga kauye, kawai na karbeta koya kagani Waleed, kaga abokin ka bawani zama yakeba kullum ni kadai awanan tangamemen gida daka siyamin Waleed wlh nagaji bansaba rayuwa ni kadaiba, ko kanwar tawama dan mijinta yaki yardane da sonayi su dawo nan kawai tunda gidan gawuri koba komi ai nasami masu debemin kewa” gyadamata kai yayi yace “hakane Mama” tabe baki tayi saikuma ta nisa ta kwalama Salma kira. “Salameme, Salameme, ke Ummu Salama” amsawa yarinyar tayi daga kitchen tace “na’am gani nan zuwa Mama” maida kanta tayi ta kalli Waleed tace “danan bari yarinyar nan tazo kaganta” ki 2min ba’a dauka ba wata doguwan yarinya da tamafi Widad tsayi tana sanye da doguwan rigan atampa ja yarinyar kyakkyawa gata Black beauty, karasowa gaban Mama tayi da sauri tace “Mama gani” baki Mama ta kama tace “nifa dadi na dake haka kike abu kaman makauniya Salma, bakiga yayanki bane Yaya Waleed” tamata pointing Waleed dake zaune a kujeran data juyama baya, juyowa tayi ahankali ta kalli Waleed, jitayi kunya yakamata batasan lokacin data kara duka hannayenta biyuba tarufe fuskarta cikeda kunyan yaran kauyen nan tana washe baki tace “ina kwana” da sauri Mama tace “kwana kuma Salma, oh ni Bilkisu wanga yarinyar wanga yarinya dai to, Allah nagode maka” dan murmushi Waleed yayi yanabin yarinyar dakeda kunyan bala’i da kallo, Mama tace “tashi kije ki zuboma yayanki abinci kihado komi a tray kaman yanda nakoyamiki jiya ki kawomai” tashi tayi tawuce kitchen Mama tabita da kallo tana girgiza kai sanan ta kalli Waleed tace “Waleed kaga Salman ko ya kaganta, yar kanwata ce a kauye suke, ta taba aure sau daya amman ko sati hudu ba’ayi da bakin ba mijin yarasu maciji ya sareshi a gona, ingayamaka shikenan yarasu, yabarta da cikin sati biyu, cikin shima watanshi biyu jikinta yafice da kanshi, na daukota ne musamman sabida nahada aurenta dana dan uwanka” wani irin mahaukacin dariya ne Waleed yaji yazomai da kyar yarike dariyan yadan zaro ido yana kallon Mama, zata sake magana daidai lokacin Salma ta shigo.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Leave a Reply

Back to top button