DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

Shigowa tayi rikeda tray mai kyau da flask ke kai da plate da serving spoon da cup dakuma juice da ruwa, tun kafin takaraso gaban falon Mama kebinta da kallo sabida taga kotai shirme ganin takawo komi daidai kaman yanda ta koyanata yasa ta sauke ijiyan zuciya, karasowa gaban Waleed yayi daya saukar da kanshi kasa dariya na neman kwasheshi shiba yarinyar kebashi dariya ba Arham kebashi dariya danhar yafara hango bura’uban da Arham zeyi idan Mama tagabatar mai da maganan, harta ijiye ta juya takoma ciki baima saniba sai maganan Mama yaji tace “ya kaganta fisabilillahi Waleed batayi ba”? Gyadama Mama kai yayi yakai kololuwa wajen damke dariyan shi amman saida yar murmushi ta subuce mai yace “tayi Mama” washe baki Mama tayi tace “Allah sarki Waleed wlh kai dan Albarka ne, yaro maijin maganan iyayenshi, jibi fa kai Ammi ka tacemin tana gabatar maka da zancen auren kai na’am inama ace haka dan uwan naka Arham yake, amman ina Arham baida wanan kawaicin” dan shiru tayi tana kallonshi sosai take farin cikin ganinshi ko Allah yasan tanajin Waleed har ranta sosai, ajiyan zuciya ta sauke tace “Waleed daman inaso nakawo maka karan dan uwanka” shidai kanshi nakasa baice komiba tace “kasan menene dan Albarka abokin ka baya kyautamin, tunda yay tafiyan nan bai kirani ba sai jiya, kasan bani iya fito da sunanshi awayan nan daka siyamin, amman ai shi yanada number ta, saida nafita na shiga nan gidan makotan nawa na nemo danta Aliyu inma karike maka zance har jiran Aliyun nayi yadawo daga gantalinshi dan kawai na ganshi na bashi wayan nace yanemo min Arham shinefa yaciro number yakira nasamu nai magana dashi, wai ina mishi korafin bayi wani kirani shine yahau cewa waini nacika fada abu kadan fada kome yayi fada, wai naje naga yanda akema ba’a maka fada kome zakayi agidan ku” ta karashe maganan ahankali alamun kalman yamata ciwo, bata cika kawomai karan Arham ba amman tunda yaga wanan karan takawo mai karan abun yay mata ciwone, ahankali yadago kanshi ya kalleta yace “Mama kiyakuri, ba lallai yanda kikadau zancen haka yake nufiba, kinsan aiki yake sosai achan ko hayaniyan yara zai iyasa yaji baya hayyacinshi, kimai uzuri aiba haka yakeba….” da sauri tace “wlh haka yake, kai bazaka gane Arham bane, nasan abokin kane ka tsani kaji laifinshi wanan halinka ne tun kana yaro amman saina fada saidai ku hadakai kuita fushi dani, kaga wanan Arham din dakake gani” tai maganan tana karkada kafafu tace “Waleed bawai banda godiyan Allah ba, kokuma inafa takura ba wlh Waleed bancin kudin Arham, nasan inada komi kamin komi Waleed amman wani zubin kowace uwa zataso ko biyar ne danta yadauka yabata yace ungo Mama asamana albarka, Waleed kaine chefanena duk wata, kaine motata kudin man da ake xubamin ciki, kaine magunguna na sanan kaine mai bani kudin kashewa tun kana dan kankanin ka kakemin wanan hidiman har gobe, bawai korafi nakema ba kokuma naga gazawar ka a’a yakamata ayanzu Arham kemin irin abubuwan nan sabida yagama makaranta yanada aikin yi, amman bayi komi, haryakai ga nace Arham ban kaza saida yace ai Waleed yayi miki kaza kokuma kinada kudi Waleed yabaki, kaga ai badadi” hakanan Waleed yaji baiji dadin abinda Arham yayi ba anatse yace “kiyakuri Mama zai gyara in sha Allah” tabe baki tayi tace “Allah yasa ci abincin ka na tsareka da surutu dan Albarka” spoon yadauka ahankali yashiga cin dambun yaci sosai dan yakusan cinye plate din sanan yature, sosai sukasha hira da Mama dudda kusan rabinta karan Arham take kawomai, sai wuraren la’asar yabar gidan, wani eye clinic yaje kai tsaye yafadi irin glasses din dayake so a keramai akamai yabiya kudi ya shiga mota yakoma orphanage.
[11/1, 11:47 PM] Re@l???? K@usy ????: ???? TWO DIFFERENT WORLD ????
✍️ M SHAKUR
1️⃣9️⃣ & 2️⃣0️⃣
FREE PAGE
Tsayawa yayi yay sallan magrib sanan yawuce clinic, yana shiga daidai Dr Kemi data shigo aiki da yamman nan dan night take tace “good evening Dr Warbai” gyada mata yayi tace “naduba patient ta ICU ai shi lost memory completely babu abinda tasani yanzu, zan chanza mata daki na maida ita normal ward tunda babu wani huge issue muna fitowa zamu wuceda ita idanunta suka sauka acikin pediatric ward kaga kuka kuwa” tadanyi shiru da mugun mamaki tace “she almost turned this hospital up side down, hakan yasa dan asami lpy babu kuma kyau tana kuka tana bare baki kodan aikin dake kanta yasa kawai na kaita pediatric ward din, Dr kaga murna kuwa” tadanyi dariya tace “tamafi yara wasa da kayan cikin ward din the thing is damn funny go see for yourself” sanan Dr Kemi tace “I think using medical lens zaiyi correcting those eye balls dinta dasuka karkace” ahankali Waleed yace “I’ve already got 1” yajuya yay pediatric ward din, ahankali yabude kofan dakin ya tsaya chak abakin kofa gadaje uku ne adakin, dakin cike yake da kayan wasa, kowani gado nada nashi kayan wasan asama dake juyawa kaman fa ka, tana zaune kan gadon tsakiyan ukun, tajuyama kofa baya, an saka mata wani pink gown na hospital mai kyau, kanan nata adaure yanda ya daure natashi saikuma gadan inda yama aski yay dinki, wani irin kallon kayan wasan take takai dan yatsanta tana tabawa take wasu yare da baima gane takamaiman metake cewa, dudda baya ganin fuskarta but he could see and feel how happy she was, dan murmushi yasaki yana kallonta still danbama tasan da zuwan mutum ba. Daidai takai hannunta zata kama toy din jirgin saman ta tsaya chak kaman ance ta tsaya sanan tajuyo ahankali ta hanyar waiga kanta ido da ido dasukayi da Waleed yasa da sauri ta juyo da duka jikinta ta fuskance shi da kyau, ta washe fararen hakoranta tareda wani irin daga hannu ta shiga tafi tana dan diddirke azaunsn ita adole murna take yadawo, murmushi yayi yasan one thing dashi ko staff dinshi basa ganin murmushin shi kaman yaran gidan marayun shi, haka yake sonsu ne is a natural thing in him, daga kafanshi yayi ya shigo dakin yasa hannu ya janyo kofan yana tafiya ahankali yana dumfaro ta, kasa daurewa tayi dan kaman duk taku dayan dayayi kara samata farin ciki yake yasa tama dena tafin tafara yarfe hannu bakinta na babar babar tanason tai magana amman maganan yaki fita karasowa gaban gadon yayi yace “someone is happy to see me” kyalkyacewa da dariya tayi irin na yaran nan bai Ankara ba yana kokarin ciro glasses din daya kawo mata kawai yaji ta rungume shi daga zaunen tsam tsam kanta nakan cikinshi, sakin glass din hannunshi yayi da sauri glasses din yafada kan gado da ace hannunshi na saitin kasan da sai glass din yafashe, sunkai kusan 3min ahaka tana rungume dashi tana dariya sanan yadan tureta ta hanyar kwace kanshi yadan koma baya yace “sit Saheeba” komawa tayi ta zauna hakan yasa yadan matso kusada gadon, glasses din yadauka cikin harshen turenci yace “this will help with your sight, zoki sa nagani” fuskarshi takawo mai da sauri ahankali ya zura mata glass din sanan ya kalleta ba karamin kyau glass din yamata ba sanan ya maida idanunta daidai, inta tana sanye da glasses din ka kalleta zaka ga kaman idanun are normal inta cirene zakaga idanun sun karkace. “are you hungry?” yamata tambayan yana dauke kanshi daga kallonta sabida wani irin faduwa gaba yake inhar tana kallonshi suna having eyes contact, hamma tayi ganin bata rufe bakiba yasa yakai hannunshi yarufe mata yadan kalli idonta yace “always do dis okay” gyadamai kai tayi tana kwanciya ahankali tamika hannunta takama hannunshi, sake dagokai yayi ya kalleta amman saiyaga ta lumshe ido kafin kace me bacci yay awon gaba da ita yana tsaye akanta tana rikeda hannunshi, bude kofan ward din akayi aka shigo hakan yasa ya waiga yana daura hannunshi kan nata yana kokarin zare hannunshi daga rikon datamai, Dr Kemi ce ta shigo tana kallon yanda tarike hannun Waleed, ahankali Waleed yazare hannunshi sanan yakama hannunta ya ijiye kusada ita ahankali yaja bargo ya lullube ta yace “just look at her tagaji sosai which is abinda bai kamata ba, ko kadan ba’ason wanda keda brain damage yay stressing kanshi out” ahankali Dr Kemi tace “to Dr Warbai ba dole ba, I came in this evening I met this gurl crying, kukanta ko’ina shi akaeji awanan clinic din gatada shegen zakin murya, to ninefa namata yan dabaru tai shiru, da nakawo ta nan kuma saitai kaman ba ita tagama kuka ba she was so happy” dan ajiyan zuciya ya sauke yamaida kanshi ya kalleta yace “ko kadan bai kamata tana kuka da ihu hakaba, daman I was waiting for ta farka naga yanda take, normally someone dakeda brain damage that is caused by fluid in the brain yakamata the amount of sleep dayake having each day yay doubling lokacin datake staying up, her brain needs to relax, batason pressure damuwa da koma wani kalan abune, akwai wasu magunguna we don’t have them in our clinic but yanzu ina fita zan aika akawo, zata dinga shansu zata dinga bacci kaman wacce ke coma, this girl needs sleep from now till few months, the more tana bacci tana relaxing the more jinin na tsinkewa yana draining kanshi with the help of magungunan” gyadamai kai Dr Kemi tayi sanan tace “Dr what about broadcasting din tsintuwarta, naga haka kakeyi ma duk wanda aka tsinta aka kawo idan ankawoshi da any rashin lafiya kowani abu zakai treating nashi dazaran ya warke u send his picture da labarin yanda ya iso gidan marayun ka to government, sukama government zasu yada labaran akafafan yada labari, idan yanada family they come for him idan kuma ba’a samu family shiba yacigaba da zama damu” shiru yayi yana kallon fuskar Widad, she is the first person da tunda yabude gidan marayun nan aka kawota yaji baison yay wanan, hakanan jikinshi ke bashi yarinyar is in danger, serious danger, banda haka yaga bruises na alamun an damke mutum a hannayenta, this injury kanta he also belive ba faduwa bane ko accident this is an intentional Well planned incident, he just wanna take his time yasamu yarinyar ta sami lafiya, first now is fluid din kanta ya tsotse inhar ya tsotse zata dena wanan abnormal behavior, daga nan he concentrate on gaining her memory back, akwai wani workshop daya tabayi a ???????? Cuba kan memory lost, but dole sai fluid din kanta ya tsane sanan zai iya daurata kan medication na memory lost, yanaso harsaitaji sauki tafadi mai she is in danger ko she is not before yay announcing tsintuwarta, for now her safety and her wellbeing first. “Dr Warbai” dago idanu Waleed yayi ya kalleta tace “tunanin me kakeyi ne?” dan yatsine fuska yayi yace “alot! Anyway I will see about abinda kika fadi, bari tadanji sauki tukunna, bari naje na aika magungunan da allurai zaki mata some this night” gyadamai kai tayi yawuce yafita daga dakin, rubuta sunan all abinda yake bukata yake sanan yabama wani ma’aikacin shi da kudi yaje yasayo yakaima Dr Kemi shikuma yawuce office dinshi.