DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

Tadade rungume dashi shima yay mugun kewanta inyaga Ammi ko Mom shagwaban shi tashi take, dagoshi tayi ta mannamai kiss a goshi sanan tace “sannu da zuwa Son, ya hanya? Hope bakagaji ba ko?” gyadamata kai yayi yana yatsine fuska yace “I miss you Ammi” murmushi tayi kaman ta hadiyeshi take tasake shi tace “ina zuwa” sanan takalli Ilham dake tsaye tana kallonsu tace “daughter na” guwiwa Ilham takai kasa zata tsugunna ta gaidata da sauri Ammi ta dagata ta rungumeta tace “sannu dazuwa diyar kirki, my son is looking masha Allah, Allah yamiki albarka kinji” akunyace ta gyadama Ammi kai, sakinta Ammi tayi tace “wuce kishiga ciki, nasa an gyara muku daki a upstairs yau awajena zaku kwana jeki wanka kufito aci abinci” gyadama Ammi kai tayi tawuce, sai alokacin ma Ammi ta lurada Arham dake tsaye kanshi akasa, dan murmushi tasaki ba yabo ba fallasa tace “Arham mutanen yankari” dago kanshi yayi fuskarnan cikeda murmushi saiyadan rage tsawo yace “Ammi ina yini, mun sameku lpy” “lpy lau Arham” Ammi ta amsa tace “shigo mana” tai maganan tana juyawa takama hannun Waleed dayabi ya langabe mata kaman wani dan jariri sukai ciki Arham biyeda su abaya, hakanan yaji wani iri, Ammi ta rungume kowa harda musu peck amman shi ko kanshi bata shafaba kaman ba bataji dadin ganinshi ba, shine abokin danta tun yana yaro amman haryau bata wani sakemai ingaka murmushi da fara’an Ammi toda danta Waleed ne, bude kofa Ammi tayi suka shige ciki itada Waleed Arham biyedasu, ahankali Ammi tace “to go and freshen up saika sakko aci abinci” kaman zaiyi kuka yace “wlh ni yunwa nikeji Ammi I will do dat after eating, blood ai kaima yanzu zakaci ko”? Dan murmushi Arham yayi sanan ya gyadakai, Ammi tace “to ai saiku taso kattin banza ko Khadija bazaku iya jiraba” dining din sukayi taja kujera Waleed yazauna Arham ma yazauna Ammi tace “Arham feel free zuba abinci kaci wanan abokin naka shirme zaitayi” kaman Waleed zaiyi kuka yace “nine mai shirme Ammi to bazan ciba ma” ya yunkura zai tashi da sauri Ammi tarike shi, zaunar dashi back tayi tana dariya.
Tai maza tadau serving ta shiga zubamai rice datamai dawani ubansun vegetable soup da ita da kanta tamaishi yaji kayan ciki, ta debo da hadadden nama takai bakinshi tace “yauwa bude bakin Dan Yaron Mom” bude bakinshi yayi ahankali Ammi takai spoon din bakinshi shima yakawo bakinshi yana shirin ya karba ta kauda spoon din takai bakinta zataci wani irin malalacin ihun shagwaba yasaki. “aaaammmm Am…” kyalkyacewa da dariya Ammi tayi tai maza takai spoon din bakinshi daman wasa takemai tace “ihakuri, oya amshi” saida yadan mata kumbure kumbure sanna yabude bakin tasakamai ciki, ko motsi Arham bayayi bayau yasaba ganin ana bama Waleed abinci abaki ba dan inhar Mom ko Ammi na gida to Waleed bayataba saka hannu a abinci yace shida kanshi zaici, dudda yasaba dagani amman baya taba daina kallonsu in sunayin har karshen ranshi jiyake inama ace shine, yaso ace Mamanshi is educated kaman Ammi, Mama na sonshi shima amman ba kaman yanda Ammi keson Waleed ba kaman zata hidiyeshi ba, ahankali Ilham ke saukowa daga stairs tana sanye da wata doguwar rigan atampa super, free gown ne babu komi jikinshi, tundaga stairs take kallo yanda Arham ke kallonsu Ammi, dauke kai tayi kar alura shi take kallo takaraso dinning din tana murmushi tana kallon Ammi data waigo tace “zo daughter zauna kici abincin ki” tai maganan tana kai abinci bakin Waleed, kujera taja tazauna sanan tadau plate ahankali ta shiga zubama Arham masa dudda batasan koshi zaici ba tazuba mai miya da uban namomi ta turamai gabanshi tace “bismillah Yaya Arham” dan juyowa Ammi tayi ta kallesu sanan tadauke kai tacigaba dabama Waleed abinci itama Ilham ta debi masa duk akai shiru ana cin abinci dariyan Waleed da Ammi kawai kakeji sai wasa suke sunacin abincin gwanin ban sha’awa dan shima Waleed bayan yagamaci zubama Ammi tayi yashiga bata kasacin wani abincin kirki Arham yayi yature abincin yadau tissue yana goge bakinshi, sanan yamatsar da kujeran baya yamike tsaye da sauri Waleed ya kallai yace “badai harka koshiba kaidake son masa” dan yatsine fuska yayi yace “nagaji ne blood inaso naci but taki shiga nasan innaje gida na huta zan iyacin abincin” da sauri Ammi tace “ina za’ai haka, bari nakira a deba maka a kula kaje gida saikaci ka gaidamin da Maman ka please, jiya ta aikomin da kwamdon tumatir da buhun albasa daga gona, haba ita bata gajiya, kace nace tadena daurama kanta dawainiya please kaji, niya kamata nabata ba itaba kaji” gyadamata kai yayi kanshi akasa maganan karshe ta mugun mai ciwo wanan kasancewan har ina wai ita yakamata tabata wato ga Mamanshi fatararriya matsiyaciya ko, sukuma masu kudi, hmmm wata rana dagake har danki saina saku kuka wlh, saina muku abinda kudinku bazai taba gyara abinba, tsayar da maganan zucin yayi daidai yar aikin Ammi takawo wani hadadden kula da masa da miya keciki tabashi, karba yayi yace “thank you Ammi” sanan yajuya, tashi Waleed zaiyi Ammi tace “kanacin abinci baka gama bane zakawani tashi” kaman zaiyi kuka yace “nifa Ammi nakoshi, kuma I want to see blood off” “to ai saikaje su mai blood” Ammi tai maganan da zuciyanta daya dariya Waleed yayi yawuce yabi bayan Arham dahar yajuya da sauri yay kofa itakuma Ilham tai kaman ba satan kallon Arham din dataga ko bye baimata ba, yarage dinning din daga ita sai Ammi.
Concentrating Ammi tayi tana cin abinci saikuma chan tadan dago daidai itama Ilham ta dago hada ido sukayi da Ammi, Ammi tai murmushi sanan ta mayarda hankalinta kan abinci cikin seriousness dinan nata da halinta na bawasa tace “Khadija kinyi kyau, you look so fresh Masha Allah, am expecting good news kwanan nan fa daga wurinki” kasa dagokai Ilham tayi tama kasakai abincin baki tana wasada spoon din ahannunta, Ammi ta cigaba. “nasan ku yaran zamani bakusan dazaran kunyi aure ayi aciki a haihu kunfison sai anci soyayya, bakuson ace daga shigowa kunyi tuntube dashi, wasunkuma ma har planning suke, please daughter banda planning take note, I need an heir, inason magaji, inason naji good news daga gareki kwanan nan kinji” gyadama Ammi kai Ilham tayi akunyace tace “in sha Allah Ammi zakiji kwanan nan” murmushi Ammi tayi cikeda gamsuwa tace “sai magana tabiyu, bazaki yi aikiba, am sorry about that I know bazaki so hakan ba, banson kina dauke da jikana a jikinki kije kinama wasu aiki, this magana is between me and you bazakiyi aikiba but every month zan dinga biyanki salary is that okay with you?” gyadama Ammi kai tayi ahankali tace eh, juyowa Ammi tayi ta fuskance ta da kyau tace “sai magana ta karshe ki kulamin da yarona da kyau, Alhamdulillah kinga Waleed yanzu kinyi zama dashi kinsan yanda yake, Waleed is a very sweet calm boy, baida hayaniya ko kadan kuma baidau duniya da zafiba, nasan abinda na haifa nasan, nasan waye shi, nasan Waleed zai kuladake da kyau dan haka kema ki kulada shi da kyau, kome yamiki ki kirani ki fadamin bawai kihau yima d’ana fadaba, ni kadai nakeda wanan ikon na dagama yarona murya da sunan fada duk duniyan nan, ba’a haifi wanda zai ma innocent yarona ihu aka ba koyaci mutuncin shi saidai in ban raye, inko daraina sai inda karfina yakare so ki kula kinji” gyadama Ammi kai tayi gabanta nafaduwa daman tun kafin ayi auren mahaifiyarta ta riga tafadi mata Ammi nada zafi gata kuma da zaki but inhar kanason kaji zakinta kaso danta, akan danta zata iya komi, muryan Ammi ne yadawo da ita daga dogon tunanin dataje kwalama yar aikinta kira tayi. “Huwaile, Huwaile” dagudu yar aikin tazo tarage tsawo agabanta tace “gani Hajiya yakuri banjiki da wuri ba ina baya ina aikin dakika sanine” tabe baki Ammi tayi tace “wuce kije fridge kidauko min magungunan dana bakiyau ki samin a fridge nace miki na matar d’ana ne” da sauri yarinyar ta tashi taje fridge, wasu goruka guda uku ta dauko a basket mai kyau takawo ta ijiye gaban Ammi, daukan gora daya tayi ta jijjiga tareda budewa tamikama Ilham tace “gashi kisha” karba tayi cikeda girmamawa ta kwankwada zata ijiye Ammi tace “shanye duka” kwalkwalewa tayi ta ijiye tana lashe baki dan maganin da dadi, Ammi tace “wanan maganin dakika gani yana wanke ciki tass da mahaifa, inma yarinya tai planning ne kan kartadauki ciki tass saiya wankosu su fito ta fitsari, sanan ya wanke mahaifa koda ya cushe zata wanke tsaf ta yanda once yay releasing zai tafi mahaifarki direct, inhar mace tasha maganin nan akayi batai ciki ba to tanada wata natural condition ne dake hanata haihuwan” faduwa gaban Ilham yahauyi wanan son yara da Ammi kedashi haka na lafiya ne, mika mata sauran gorunan Ammi tayi tace “wayan nan tsumi ne kishanye su” karba tayi tasake gyadamata kai daidai Waleed ya shigo tashi Ammi tayi tace “zonan yallabai” dariya yayi yabita stairs tahau yana biyeda ita abaya, Ammi tace “bakabani labarin excursion dinba, how was it” labari ya shiga bata sunayin sama Ilham tabisu da kallo har suka bace mata wanan wata irin matace, wayarta tadauka data ijiye agefenta tabude da sauri daidai sako na shigo mata, ganin Arham ne yasa tabude dagudu.