DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

“you are mine, ban yarda wani yatabaki ba, karki yarda ki kwanta da yaron nan, is a warning ⚠”
Murmushi tayi tamai reply da.
” to sarkin kishi, babu wanda zai taba maka ni yallabai, I miss you, sainaji inama bamu dawoba, please kazo da daddare nadan ganka”
Maido mata da reply yayi da.
“I don’t wanna come, bazan zoba, cus I hate that old witch, she don’t like me is obvious babu dai yanda zatai danine sabida tasan danta bazai iya rayuba bani ba, I will see you tommorow”
Wani iri taji kaman tai kuka, hakan yasa tai reply dinshi da.
“promise”?
Dawo mata da reply shima yayi da
“I promise Lawyer”
Da sauri ta turamai da.
“but tayaya bayan gobe kuna orphanage kuna aiki”?
Sake aiko matada sakon yayi yace.
“just trust your Arham, ki kawai tabbatar ya maidake gida dasafe kafin yatafi orphanage, you will see me, cus if I didn’t have you I might die, I can’t go a day without that yummy pus”
Wani malalacin murmushi tayi tace.
“I trust you my dirty nigga, gat to go bye
Tai maza ta tura sakon tareda deleting messages din duka ganin Waleed na saukowa daga stairs daure da alwala zashi masallaci, karasowa yay dinning din ya tsaya daga dan nesada ita yace “har yanzu baki gamacin abincin ba?” murmushi tayi ta kalli plate din gabanta sanan ta kalli fuskarshi saitai shiru kawai ta tsaya tana kallonshi barinma ruwan daya jika pink lips dinshi, bazata iya karyaba tanason Waleed soma mahaukacin so, kodan baimata yanda takeso ne yasa takejin Arham dake yimata yanda takeso oho, sanan tana tausayin Arham sosai saisa take sonshi ko menene oho ita tama rasa, all she knows is takasa tsanan Waleed, and duk in zata kalleshi saitaji wutar sonshi nakara ruruwa aranta to kodai kyanshi da kudinshi ke dibanta ne? Or is it possible kaso MAZA BIYU KUMA ABOKANAN JUNA? Ta tambayi kanta. “Tunanin5 me kike”? Waleed yamata tambayan yana karasowa gabanta a dinning din ya rungume hannayenshi akirji. “wai ni?” ta tambayi kanta tana kallonshi, daga mata gira yayi alamun yes you, murmushi tasake mai tace “kawai tunanin gidan mu nike inaso naje zaka barni?” yana kallonta eyes to eyes ya girgixa mata kai, sanan yace “matar Waleed bata zuwa ganin gida sai bayan ta shekara da aure, I am a well cultured man you know” yasake daga mata gira, samun kanta tayi da kasacemai kala saima wata shegiyar kasala da sha’awan shi dataji ya diran mata all of a sudden, he was so close to her yana mata magana ciki ciki sanan yana wani kashe mata sexy idanun nan nashi yana daga mata gira, ganin ta shagala da kallonshi yasa yajuya kawai yafice daga dakin yace “tashi kije kiyi salla, ankira magrib”.
Sai wuraren 9 bayan anyi isha’i yamayi magana da wasu naroka yan anguwanni haka dasukazo neman taimako ya sallame su sanan ya shigo cikin gidan, maida kofar falo yayi yarufe yana kallon Ammi data zauna kan kujera tana aiki da laptop dinta duba sales din da aka mata a campanonin ta take, is a normal thing kullum around that time zata saka fararen glasses sanan ta zauna tana aikin sai wajen 11 na dare sanan zata gama taje ta kwanta, zama kusada ita yayi ahankali yace “sannu da aiki Ammi” kanshi ta shafa tace “kadawo son” gyada mata kai yayi ya jingina da kujera yana zaro wayanshi daga aljihu yarike wayan yana kallo saikuma ya shiga daddanna wayan yanemo number Dr Kemi yay dialing, ringing daya kaman wayan na hannunta ne daman ta dauka.
“Hello Dr Warbai, good evening” kafin ma yay magana yaji karan kuka sosai a background din wayan, ahankali yace “who is crying?” “your patient” tabashi amsa da sauri, tashi yayi yazauna dukya damu, ahankali yace “what about medication dinta danace a dinga bata dakesata bacci” cikeda damuwa tace “Sir wlh na bata tun bayan ta farka da magrib dinan but taki bacci, daidai da ruwa takisha, inta ganmu ma ihu take, taki yarda damu kwata kwata jikinta ma yadau zafi, tun dazu ina kanta sai yanzu nafito daman nazo nakira kane saigashi kiranka ya shigo kaman kaji ajikinta tana kuka” shiru yayi yana rasa mezaiyi saikuma ya kalli Ammi dake aikinta hankali kwance gabanshi nafaduwa yasan yanzu yana fadimata orphanage zashi saita balbaleshi da bala’i, katse wayan yayi yamaida wayan aljihu ya ijiye yay shiru gabaki daya jin karan kukanta yasa yakasa natsuwa mikewa yayi zumbur kaman an dagashi yazuri key motar Ammi dake Centre table da sauri Ammi ta kallai tace “ina zaka?” “orphanage Ammi, emergency case gareni, I have to go” shiru Ammi tayi tana kallonshi kaman zaiyi kuka yace “please Ammi dazaran nagama zan dawo” yanda yayi yasa tace “saika dawo” da sauri yafita daga gidan, motar Ammi ya shiga yay horn gateman yabudemai gate yawuce yafita ya shiga titi yaba sharara gudu, wani super market yawuce akan hanya hakanan saiya sami kanshi dayin reverse back yadawo parking yayi agaban super market din ya shiga, yau kusan 3days kenan bata sakashi a ido ba, wata Teddy babba yasaya, saikuma yasai su snacks da chocolate da ice-cream yabiya kudi yafito ya shiga motar yaja, ko minti 15 baidauka ahanya yakai orphanage din, parking motarshi yayi agaban clinic din yafito lokacin 10 harda kusan minti 15 but yana iyajin ihunta daga wajen, daukan Teddy din yayi da sauri yama manta da sauran abubuwan saya sayo tsabagen yanda kukanta ke rudeshi ya shige cikin, ward din datake ciki yayi agaban dakin datake yaga Dr Kemi da nurses dukansu tsaye sunyi charko charko, babu wanda kukanta the bai dagawa hankali ba, Dr Kemi na ganinshi ta sauke ajiyan zuciya tace “thank God you are here, bari naje nahuta ba’a taba kawo mana patient data taba bamu wuyaba irin wanan yarinyar” wucewa suma nurses din sukayi suka tafi bayan sun gaidashi, ahankali yake daga kafanshi haryakai gaban dakin, kukanta dake tsuma zuciya nakara tashi yana kururuwa, daura hannunshi yayi kan door handle din kafin ya murda yatura kofan ahankali yana kallon dakin, tana zaune akasa kusada kofan ta tankwashe kafa kanta sauke tana rusa uban kuka dakowani gaba na jikinta ke amsawa, bama tadago kaiba balle tasan waye yashigo ba, maida kofan yayi yarufe ahankali, sanan yadago kafanshi yazo har gabanta, ijiye mata Teddy yayi akasa agabanta sanan ya zaga ta gefenta ya tsugunna ahankali yana kallon yanda tsabagen bala’in kuka kandaya kulle mata ta wargajeshi yama rufe mata fuska da baya, cikin wata irin karaman tattausan murya yace “Sabeeha” har kasan kwakwalwanta taji kiran sunanta dayayi dawani irin sauri ta dago kanta takai hannayenta ta gyara gashin gaban fuskarta ta hanyar waresu kyakkyawar fuskarta ya bayyana ta kallai suka hada ido, wani irin fashewa da kuka tayi saikuma tasa hannayenta biyu ta tureshi tana ihu da kuka. “ahhhhh ammmm” saikuma tajuya da sauri ganin Teddy daya ijiye mata awurin yasa tai grabbing nashi da sauri ta daga ta shiga kwadamai tana mugun kuka jikinta na rawa ranta ya bala’in baci, saida ta kwalamai Teddy iya son ranta sanan ta jefar dashi akasa ta tattaka tana kuka saikuma ta dauka ta mike tsaye tana tafiya tana dingishi tai wajen gadonta tahau ahankali ta kwanta ta rungume Teddy tana sauke ijiyan zuciya.
[11/1, 11:47 PM] Re@l???? K@usy ????: ???? TWO DIFFERENT WORLD ????
???????? DUNIYA BIYU MABANBANTA???? ????