DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

        ✍️ M SHAKUR 





                    2️⃣3️⃣

FREE PAGE
Yadade atsugunne yanda ta barshi, zai iya cewa tunda Allah ya halltoshi duniya da dai wayanshi aka bai taba ganin mutumin daya daga hannu da sunan zai dakeshi ba aduniyan nan ballema har ya dakan sai akan yarinyar nan, bude idanunshi da tuntuni suke alumshe yayi yadan juya ya kalleta, sai ajiyan zuciya take irin na wanda yay kuka dinan ta kankame Teddy tana jikinta har bari bari yake, ahankali ya furta zuciya! Mikewa tsaye yayi ahankali yafara tafiya batare daya waigo ya kalleta ba yay kofa, hannunshi yadaura zai bude kofan yaji tawani irin fasheda kuka da sauri yajuyo, ganin yayi ta tashi daga kan gadon tana kokarin saukowa daga gadon, saukowa tayi tana kuka ta taho har gabanshi tana dingishi, rungume hannayenshi yayi yanabin gashinta dake lilo da kallo yace “you just finshi beating me, why are you crying again? Ba bakison ganina ba?” yay maganan gabaki dayanta cikin harshen turenci, cigaba da kukan tayi batare data cemai kalaba, sosai yaje yanason yay training nata yabata tarbiya mai kyau, ahankali yace “you don’t beat your elder koma mesuka miki, is wrong, now say sorry” dago jajayen kumburarrun rinannun idanunta tayi ta kallai kaman yanda shima ya tsare mata ido, ahankali cikin dishashiyar muryanta dabata fita sosai tace “so…rry” yanda tafadi sorry was so cute da saida yasashi murmushi, handky aljihunshi yaciro yazo har gabanta ya tsaya sanan ahankali yadaura left hand dinshi kanta sanan yakai right hand dinshi dake rike da hanky din kan fuskarta wani irin wawan ajiyan zuciya ta sauke da saida yasa ya kalli fuskarta kafin ahankali yashiga goge mata hawayen dayay chaba chaba a fuskarta, sanan ya share mata hancin daya baci da majina, sanan yawuce cikin dakin zuwa gaban gadonta, pink bathroom slippers din da aka bata na sawanta yadauko ya ijiye agabanta yace “put on the slippers” sakawa tayi da sauri tana kallonshi shikuma ya tsaya yana kallon cute yatsun kafarta fararen da zai iya cewa baitaba ganin yatsun kafan mace kai kyau hakaba kodan baya kallon yatsun ne oho, dago kanshi yayi ya kalleta yace “let’s go” yay maganan yana bude kofa yafito yajuyo ya kalleta, da sauri itama tafito tana kara rungume Teddy dinta ta tsaya kusadashi, hannunshi yasa yajawo kofar yarufe sanan yafara tafiya ahankali sabida ita, kallonsu nurses din suka tsaya sunayi da mamaki yarinyar daketa uban kuka, tana ganinsu tadaga Teddy ta sama tai gaban counter dinsu da gudu zata rafka musu da sauri Waleed ya daka mata tsawa. “Saheeba” tsayawa chak tayi bata rafka musu ba tajuyo kaman zatai kuka ta kallai, daure fuska yayi tamau yace “come here” tahowa tayi ahankali sukuma nurses din na dariya kasa kasa, hannunta yakama yarike sanan yay wajen kofar fita daga clinic din da ita, security yabude musu kofan suka fito, tunda aka kawota bata taba fitowa ga wuta ko ina a premises din kaman ba dare ba, ga hadaddun flowers ga few cars dake pake a filin, tsalle tahau yi tana kara kankame Teddy ta kana ganinta kasan she’s very very happy, tai wajen flowers tana tattabawa saikuma ta daura Teddy ta akan flower tana tsalle, murmushi yayi yawuce ta yace “lets go” daga Teddy ta tayi ta dauka tabishi da sauri tana dingishi har zuwa inda yay parking motarshi, bude mata gidan gaba yayi yace “seat” shiga tayi ta zauna ahankali sanan yazaga mazaunin direba tana binshi da kallo kaman zai gudu saida yabude motan ya shigo sanan ta sauke ajiyan zuciya ta shiga tattaba motan tana yan surutai kaman yanda yara keyi in sukaga kayan barna, wajen radio mota ta shiga tattabawa da sauri yace “stop” denawa tayi ta hade hannayen takai dukansu baki tana kallonshi da kwala kwalan idanunta, dan ajiyan zuciya yayi yahanata wanan takoma wanan, ahankali yamika hannunshi baya yadauko jakan desert da snacks din daya siyo mata ya daura kan jikinshi ice cream yaciro yabude yasaka spoon yamika mata yace “ice cream” tsayawa tayi tana kallon ice cream din dabai wani narkeba da kallo dan da kankaramshi aka bashi, kwanto da kanta tayi tana leka ice cream din kaman wata matsoraciya spoon din yazaro ya lakato ice cream din yakai bakinshi yasha ya lumshe ido yace “is sweet, ice cream” karban duka ice cream din tayi daga hannunshi zata sha saikuma ta dago takai hannunta ta fizge spoon dinta shiga shan ice cream din kaman zata hada da roban cikin 2min ta shanye tass tamikamai spoon da roban ice cream din, murmushi yayi yaciro muffin daga ledan yabata kaiwa baki tayi taci taci ye tasake mikamai hannu alamun yakara mata saida tacinye duka guda biyar din dayasa yo sanan yabata ruwan sanyi ba sosai ba tasha tai gyatsa da karfi dayasa yatabe fuska yana kallonta yace “yanyanyaa, don’t do that again” gyadamai kai tayi hankalinta yakoma kan yan littatafai data gani kan saman motan, da sauri tamika hannu zata dauka kafin ta dauka ya dauke yace “stop is not mine na Ammi ne” ahankali tana kallon fuskarshi tace “Am….mi?” gyadamata kai yayi yace “yes Ammi Saheeba” saita shiru ta tsaya kallonshi, murya chan kasa yace “now listen kinsan me yasa nakawo kinsan nabaki kayan dadi”? Yay maganan da turenci dan turenci kadai ya lura tanaji inya mata hausa bata ganewa, turencin ma yawanci bata cikamai reply ba, badaita wani maganan kirki dan baitabajin tamai full sentence da turenci ba, ahankali yace “you see am a very busy person, I work in this orphanage, and I am a Dr, bakoda yaushe zaki dinga ganina ba, kinsan menene banso inhar kinayi zanyi fushi dake?” da sauri ta girgiza mai kai yace “banso kina kuka, kobaki ganni ba karki kara kuka do you know why? Because am going to make you a promise now” yay dan shiru yana kallonta ganin gabaki daya ta natsu shi take kallo yace “duk ranan duniya zaki ganni in sha Allah, zanzo naduba ki dan nine Dr ki, but ba lallai ki ganni dawuri ba sabida ina aiki dayawa, bawai dan baki ganni ba kiyita kuka, no banso kina kuka sabida in kina kuka bazaki warke ba, kidena kuka, be a good girl kome kikeso za’amiki, kidinga shan maganin ki in anbaki kinji” gyadamai kai tayi yay murmushi yace “muje nabaki wasu magani saikiyi bacci saikuma gobe u will see me okay, zan sayo miki ribbon and other hair stuff kidinga kama gashin nan” gyadamai kai tayi yabude kofa yafito yazaga yabude mata side dinta tafito ahankali rikeda Teddy dinta yamaida kofan yarufe sanan yamaida ita dakinta, wasu magani yabata sanan yasa ta kwanta, kwanciya tayi rikeda Teddy tana kallonshi shima yana kallonta kaman wayanda fuskokinsu ke magana da juna harta fara lumlumshe ido, saida bacci ya Kwasheta sanan yatashi bargo yaja yarufa mata sanan yatofa mata addu’an bacci yajuya yafita daga dakin, Dr Kemi yama sallama yawuce yatafi, koda ya isa gida wuraren 12, kulle kofa yay yay upstairs, Ilham yasamu tai bacci abinta bayi yashiga yay wanka yafito saida yay sha’fa’i da wuturi sanan yazo ya kwanta sai bacci.


Da asuba yatashi as usual yatafi masallaci, itama yana fita ta shiga bayi dan maganan Arham ne aranta dayace mata ta tabbatar yakaita gida, salla tayi bayan tafito sanan tai kwalliya cikin doguwan riga baki mai kyau.
Wuraren 7 tafito jin muryan Ammi akasa, ahankali take sauka daga stairs daidai Waleed shima ya shigo gidan, a stairs suka hadu, murya chan ciki tace “good morning baby” “morning” ya amsata yay gaba saikuma ya tsaya yace “kinyi arranging kayan ki ko am dropping you off at home kafin na wuce aiki” gyadamai kai tayi tace “to yallabai bari na gaida Ammi nadawo nayi” gyadamata kai yayi yawuce itakuma ta sauka, a kitchen tasami Ammi dayan aikinta suna breakfast, har kasa ta tsugunna ta gaitada, dda murmushi Ammi tace “Khadija harkin tashi, to barkanmu da asuba Mike tsaye kidena tsugunnawa kina gaidani dan Allah” tashi tayi ahankali tace “Ammi bari nai breakfast din kije kihuta” da sauri Ammi tace “kul, matar d’ana bata wahala, wuce kikoma wajen mijinki ki taimakamai ya shirya aiki, saiku sauko kuyi breakfast kan kuwuce, wuce wuce” Ammi tai maganan tana cigaba da aikinta wucewa tayi tafice tanajin dadi inhar haka Ammi take ai tafita masifan ta ko ajikinta, duk masifar matarnan jibi yanda takeji da ita, sama ta koma Waleed na bayi hada kayanta tayi tsaf sanan tai kwanciyan ta kan gado tadau wayanta ta shiga message ta turama Arham sako.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Leave a Reply

Back to top button