DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

???????? DUNIYA BIYU MABANBANTA???? ????
✍️ M SHAKUR
2️⃣4️⃣
FREE PAGE
Saida yayi yanda yakeso da ita akan gadon Waleed yabata zanin da fluid sai wuraren 11 yadagata shima sabida kiranshi awaya dayaji anata yi kuma yasan ba kowa bane illa Waleed, sauka yayi daga kan gadon yace “lemme shower Lawyer nasan Waleed ke kirana” gyadamai kai tayi tana daga kwancen tana kara sauke ijiyan zuciya, wanka yayi a hadadden bayin Waleed yanabin ko’ina da kallo komi kar kar sanan yafito daure da towel dinshi, kayanshi yadauka ya mayar yana kallonta ganin ko motsi bata iyawa, gira daya yadaga mata yace “ya akayi you need more”? Lashe lips dinta tayi tadan tashi zaune ta jingina da bango tace “kawai nagaji ne yaushe zakai resigning daga gidan marayun nan eh? I will find a job for you I promise, kuma zan dinga baka salary, nawa Waleed ke biyana every month as salary”? Batare daya kalleta ba yana kokarin saka links din kayanshi yace “500k” “wow 500k” dagokanshi yayi ya kalleta yace “is too small ko, kowani watan duniya gwamnati nabama gidan marayun tallafin kudi, dudda nasan Waleed baya jiransu da kudin kampanin babanshi dakuma gadonshi yake running komi, yakamata idan gwamnati takawo tallafin saiya dinga bani kaso mai kyau koda 2min ne duk wata” da sauri tace “let’s be Frank, 500k is a very good amount trust me Waleed kawai kyautansu yakema wani aikine zaka samu da zasuna biyanka 500k duk wata ko as an engineer dakake adai Nigeria nan babu saidai in a abroad” shiru yayi yana kallonta sai kawai ya kada kai yace “you will not understand, am his partner, I run the place kaman yanda shima yakeyi namafishi aiki tunda dai shi kike supporting is fine” da sauri yace “wlh bashi nike supporting ba” “bye” yamata yana bude kofa yafita daga dakin ya sauka kasa yabude kofa yafito daidai direba na bude gate wani irin wawan faduwa gabanshi yayi amman yadake yacigaba da tafiya yakasa dagokai ya kalli motar da shigo, hayaniya da surutun mata dayaji yasa yadago kanshi, wasu manyan matane guda biyu da kananun yara a hannunshi mataye suna bala’in kama da Ilham kaman yayyinta binshi sukai da kallo baice musu kala ba yabude mota ya shiga sukuma sukai ciki.
Suna bude kofa suka shiga falon suke kwala mata kira. “Ilham, Ilham” da sauri Ilham tashiga saukowa daga stairs da hijabi ajikinta har kasa ciki tana daure da zani tana washe baki. “oyoyo Anty Hassu da Anty Husai” takarasa tadau yaransu da gudu tace “ke Aiman da Ameera ba magana kuna wani shan alawa” batare da Anty Hussaina dasuke cema Hasai tazauna ba babu alamun wasa akan fuskarta tace “waye wanan daya fito daga flat dinki yanzun nan? Naga ba Waleed mijinki bane wayeshi” ijiye yaran tayi tadago ta kallesu ganin duksun tsareta da idanu yasa tace “Arham nefa Anty, best friend din Waleed, ya aikoshi nabashi wani kati ne dazai kaima chan orphanage, inama bacci nima yay knocking banmaji ba saida Waleed yakirani wai ya turo nabada sako nafito nabude kofa, shine fa nabashi yatafi” atare sukace ayyo kafin Anty Hussaina tace “amman baida mutunci ya kare mana kallo tsaf sanan ya zubar kaman yaga kashi bako gaisuwa, kinga kawo mana ruwa musha, ya honeymoon a Yankari” hanyar kitchen tayi gabanta nafaduwa.
Nafaduwa har lokacin ganin tawuce da kyar, drinks takawo musu da ruwa sanan tai sama tace “bari na watsa ruwa sai nazo namuku girki” sama tayi tana zuwa dakin Waleed ta shiga direct ta yaye zanin gadonshi tasaka wani sabo ta shiga bayinshi ta jefa zanin a washing machine ta feshe dakin da turare sanan tafita ta shiga dakinta wanka tayi ta shirya cikin wasu kananun kaya sanan tafito ta shiga kitchen ta daura musu girki suna hira.
Wuraren 12 ya shigo orphanage din yayi parking motarshi daidai Waleed nafitowa daga office dinshi tareda Iyami, mai kula da girl section da yara ke kira da Mama Iyami, bude motar Arham yayi yafito Waleed ya daukekai kaman baiganshi ba dan ranshi yadan baci tayaya za’ayi yafita batare dayasanar dashiba bayan sunada uban aiki aka saidai kawai ya nemishi yarasa daga cemai dayayi bari yaje office dinshi yana Mama abu yadawo, shikenan saiya fice, girl section suka wuce shida Iyami, gate dinsu tabude yana biyeda ita abaya yara mata ne manya da kanana wasu na wasa wasu na wanki different activities all the girls looks happy and so undisturbed, stiars sukayi shida Mama Iyami sukai sama suka shiga room one, bunk bunk din gadaje yagani dasuka sami matsala tace “to kaga wayanda nagayamaka da sai an gyara yanzu haka nahana ai amfani dasu harsai an gyara” gyada mata kai yayi yace “zan aiko azo a fita dasu za’a saka sababbi yanzu dai kima Shafa’atu magana kome tace saiki fadi mini” gyadamai kai tayi suka fito suna sauka kasa har gate tarakashi yawuce yafita sanan takoma ciki, office dinshi yakoma yana shiga Arham nabude kofa ya shigo, dan juyowa yayi ya kalleshi saikuma yakoma kan kujera shi ya zauna batare daya nunamai wani abuba yace “ya akayi Mr P.A” yanda yake maganana shi adole fushi yake yasa Arham yay dariya yace “common baka iya fushi ba baima maka kyau shatwababben yaron Ammi, am sorry wlh Mama takira ni guess what?” ahankali Waleed yace “what?” dan dariya Arham yayi sanna ya nuna kanshi yace “waini Mama ke cema na auri wanan yarinyar yar kauyen nan niyama sunanta? Mtswwwww wlh nama manta, but just imagine wai nine zan aureta” tsareshi da ido Waleed yayi yace “to me aciki danka aureta I did see anything” dukan table din Arham yayi yace “na farko bazawara ce tafa taba aure a kauyen su, that aside gata yar kauye, kauyen ma kauyen kayayau, how can someone like me get married to yar kauye haba now” girgiza mai kai Waleed yayi yace “bahaka bane u are getting it all wrong Arham, yarinyar nan yar uwarka ce, idan ma aureta still kanka kataimaka, ko anje an dawo she will still be called your cousin, and kanacewa yar kauye ne, once you brush dat girl kanata kulawa ko shekara baza a dauka ba zata kile tadawo kaman kowa, your Mom likes her she spoke to me about it, kodakai bakaso do it for the sake of your Mom kaman yanda nima nayi” “bura’uba Allah ya kyauta, am not like you Waleed bazan taba iya auren abinda banso ba, ni inaso na auri mace yar gayu yarinya mai ilimi da aji kaman Ilham dinka” yay maganan yana kallon kwayan idon Waleed kaman yanda Waleed ke kallonshi Waleed yace “kaikuma abinda kakeso kenan?” gyadamai kai Arham yayi, dan tabe baki Waleed yayi saikawai ya girgixa kai yace “kawai kai addu’a Allah ya zaba maka mata tagari , but gaskiya you are due for marriage ka isa aure but ka kiyi” dan dariya Arham yayi yace “dudda banyi ba but trust me nafi wani mai auren ma morewa, I dey dive and scatter pussy” tsareshi da idanu Waleed yayi yace “I thought we’ve spoke about this thing tun muna school kacemin bazaka kara all this pre marital sex ba, ka komane kuma yanzu blood”? Waleed ya tambayai ahankali kuma ranshi adan bace idan akwai abinda ya tsana shine yaga Arham na aikin zunubi da suna school a kasan waje lokacin yabi wasu bad friends yan department dinshi dasuka sa yafara bin mata sosai, lokacin ne shida Waleed sukai having their first ever serious fight ganin Waleed yay fushi dashi sosai yasa yamai alkawari bazai jarayiba kuma yarabu da abokanen da yan matan yazo ya natsu kaman bashiba saikuma yau dayakeji yanamai magana haka, ganin yanda Waleed yay nisa yana tunani yasa ahankali Arham yatashi yazo ta wajen kujeranshi yace “hey tunanin me kake?” yadanyi dariya yace “wasafa kawai namaka, I was just joking bada gaske nakeba, ya za’ayi nakoma ma aikata zina bayan nasan haramun ne trust me ko lokacin danayi friends suka sani, yanzu ma kawai nafadi ne naga reaction dinka, but kasan wani abu”? Yay maganan yana kallon fuskar Waleed kaman zaiyi kuka yace “I use to wish inama nine nai auren nan da akama na auri Ilham sabida ko ni har yanzu banga wata mace datamin ba, Mama kuma fisabilillahi haka ake nomoma ma mutum mata, just take u now for example Ammi tanemoma mace daidai kai your standard ni kawai ta kama takawomin wata bazawara yar kauye” yaja tsaki kafin yadaura hannunshi akan forehead dinshi, hannunshi Waleed yakama yarike yace “Hey listen, aure lokaci ne don’t pressure yourself, idan lokaci yayi zakayi, idan bakason yarinyar is fine talk to Mom kamata explaining politely sanan kadinga kyautata mata kama faranta mata hakan zaisa you will prosper and excel in this life, iyayenmu dakake gani are the gateway to our success abinda yakamata shine mu gyara zamanmu dasu” Waleed yashiga mai wa’azi yanamai fada batare daya nunamai cewan Mama takawo mai karanshi ba sun dade ahaka saida aka kira salla sanan suka wuce suka fita salla.