DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

Dawowa Salima tayi ta tsaya akanta, karasa soke daurin tayi Ilham tamike ta kalli Salima ganin ta daddaure fuska yasa tawani fada jikinta tareda rungumota tace “dalla na face miki sorry please karki damu anjima zan baki labarin Dr kinji ni yanzu kiyakuri dan Allah” yanda duk takaiga fushi saida tai murmushi tace “shikenan” tace “kinga yanda kikai kyau kuwa kaman bakeba Ilham” murmushi tayi tace “yi sauri muje naga Dr dina” hannunta Salima takama sanan tabude kofan suka fita sau daya tasaci kallonshi ta sunnar da kanta kasa ganin bashi kadai bane, shi hankalinshi ma nakan wayan hannunshi yana danne danne yay wani irin kyau da saida taji gabanta yafadi hakanan taji wani kishi yataso mata yanzu duka matan dasuka cika gidan nan su ganshi ahaka, da kyar ta iya ta danne kishin suka cigaba da sauka daga stairs ahankali, Hasim ne da Abdul suka tashi suna murmushi “wow, Amaryan Ya Waleed” karasa sauko da ita Salima tayi tana musu murmushi sanan takaita harkan kujeran da Waleed ke zaune two sitter ta xaunar da ita a gefenshi tace “Dr ga amaryan ka nan nakawo maka yanzu kwa barni nahuta” maganan dayaji yasa yadan dagokai ya kallesu sanan yadauke kai, juyawa Salima tayi tai waving su Hasim tace “bari naje waje” da sauri Abdul yace “bari muma mubiyoki mubama love birds some space” dan dagokai Waleed yayi ya watsa musu harara suka kyalkyace da dariya suka fice abinsu falon yarage dagashi sai Ilham dake zaune kusada shi dukansu sunyi shiru.

Almost 5min suna zaune basucema junansu komiba sanin zasu iya kwana ahaka bai cemata kalaba dan tasan magana wuya takemai yasa ahankali tamika hannunta dayasha lalle ta daura kan hannunshi daya ijiye kan laps dinshi ta kama hannun gam, atare suka dagokai suka kalli juna, tasake matse hannunshi dat feels so soft kaman hannun mace smiling, ahankali tace “Dr is our wedding are u not excited? I feel so happy because am getting married to love of my life, I love you so much Dr Waleed Warbai” tai maganan hawaye na gangarowa daga cikin idanunta, dauke kai yayi da sauri he don’t really know abinda ma zai cemata, ko 1 single feeling baidashi akanta, ganin baice mata komi ba yasa cikeda son janshi zance tace “waye best friend din naka cikin wayan nan da kazo dasu?” ahankali yace “bayanan, this are my siblings” murmushi tayi tareda lumshe ido tana bala’in son jin yana magana, maganan shi dadi sosai wlh, voice dinshi bala’in dadi, murmushi tayi tace “yana ina shi? Maisa baizo tareda kaiba?” dan dagokai yayi ya kalleta suka hada ido sanan yace “I left him in the office you will see him later” gyadamai kai tayi cikeda sonshi tace “kayi kyau sosai” dauke kai yayi yace “thanks” yadanyi shiru saikuma yace “you look beautiful as well” wani irin cikakken murmushi tasaki cikeda jin dadi sosai tace “nagode Dr” sukai shiru, agogon hannunshi ya kalla sanan yadago kai ya kalleta hada ido suka sakeyi dan idanunta na kanshi har lokacin, hannunshi yatura cikin aljihu yaciro duka rapan kudin daya taho dasu ya ijiye mata akan cinya yace “use it for anything you need, will see you later” gyadamai kai tayi ya mike tsaye tashi itama tsaye tayi itama batai wata wataba tafada jikinshi ta rungume shi tsam tsam murya chan kasa tace “thank you Dr, sai anjiman kaji” sanan tasake shi da sauri yajuya yafita daga dakin batare daya kalleta ba yafita daga gidan.
[11/1, 11:42 PM] Re@l???? K@usy ????: ???? TWO DIFFERENT WORLD ????

                 ✍️ M SHAKUR 





                    3️⃣

FREE PAGE
Wuraren 4 yafito daga office dinshi ko kallon office din Waleed baiyiba yasauko yay wajen hadaddiyar motarshi ya shige yaja motar yadau hanyar barin gidan marayun, agaban wani gida dan madaidaici mai kyan gaske yay parking ya sauko, shiga gidan yayi yabude gate din sanan yakoma mota yaja motar zuwa cikin gida, parking yayi sanan yafito yaje yamaida gate din ya kulle yana bin tsakar gidan da kallo dayasha flowers ga interlock akasa dudda gidan baida wani girma sosai but yanada kyau, karasawa yayi ya shiga flat babba kwara daya da shi kadaine atsakar gidan, bude kofa yayi ya shiga falon da babu kowa ciki sai TV dake aiki gawasu hadaddun setin kujeru dasuka zagaye falon suka karama falon haske da kyawu, wucewa yayi ya shiga wata yar corridor da dakuna uku ke ciki, ahankali yake tafiya har yakai gaban dakin dashine last room din corridor yabude kofar dakin ya shiga, dakine mai kyau sai kamshi yake, ga Royal bed aciki sai kujera daya 3sitter komi na dakin fari harda curtains din dakin, wani babban frame na hotonshi ne ajikin bango, rage kayan jikinshi yayi yawuce yashiga bathroom din dake cikin dakin, wanka yayo yafito ya shirya cikin wata yar 3quater da farin singlet yazauna kan gado, wayarshi dayaga tana dan kawo wuta yasa yagane anyomai message, mika hannunshi yayi yadauki wayar ya danna, sako yagani daga Waleed.
“Where are you My P.A?????” yay emojin dariya agaba alamun tsokana yake, tsaki Arham yayi ya cillar da wayan yay kwanciyar shi akan gadon tareda lumshe idanu yana sauke ajiyan zuciya.

“Arham” muryan wata yar dattijuwa ta kwalamai kira, “Arham” aka sake kiran sunan nashi ana bude kofar dakin gabaki daya, bude idanunshi yayi dasuka dan chanza launi dan bacci yasomaji, wata mata ce da a kalla zatafi fifty ta shigo dakin tana sanye da doguwan rigan atampa dayasha stone work hannunta rike da charbi, tsayawa tayi chak ajikin kofa tana kallonshi cikeda mamaki ganinma bacci yasoma yi shida keda biki saikuma tace “ka shigo gidan kafi karfin ka shigo ka gaidani ko Arham” murmushi yayi na rashin gaskiya yana kokarin tashi ya zauna yace “yakuri Umma, danaga baki falo nasan kina ciki kina salla saisa nayo dakin straight dannai wanka, inayin wankan kuma shine na kwanta” gyadamai kai tayi alamun ta gamsu da bayanin shi tace “yana ganka adaki kaida yakamata kana tareda Waleed yanzu, banma dade da dawowa daga gidan nasuba munata yan aikace akace achan” shiru yayi baice mata komiba, hakanan ranta yabata wani abu ganin yasauke kai yasa tace “kai ba magana nake maka ba” juyowa yayi ya kalleta cikeda takaici yace “bazani bikin ba yaje yay bikin shi shikadai su Abdul samai komi” yanda yay maganan yasa Umma ta shigo dakin da kyau tayo kanshi tace “me kake cewa ne haka? Wai Arham maisa kai gabaki dayanka bahaggon mutum ne eh? Kadaisan Waleed bazai taba iya komi batare dakaiba ko? Kakuma fi kowa sanin cewa duk duniyan nan Waleed baida aboki saikai ko? Kana cewa su Abdul, wani irin su Abdul abinda zai fadamaka comfortably bazai taba gayama su Abdul kannenku ba, Arham abokin ka kokuma ma nace dan uwanka dakuka taso tare yau bikinshi shine zaka juyamai baya eh?” daure fuska yayi tamau baice komiba, ganin da gaske fushi Arham yake yasa ta zauna ahankali gefenshi, hannunta tadaura akanshi ta shafa kan ahankali cikeda lallashi kafin ahankali tace “maiya hadaku Arham? Kuda komu iyayenku bamu isa muji tsakanin kuba shine yau kakeso ajiku, maiya hadaku tell me” shiru yayi kaman bazaiyi magana ba saikuma yace “Umma Waleed is rude, very rude, yana controlling dina anyhow, yau ya shigo office so moody shine…..” harya gama bama Umma labarin kallonshi take saikuma tai murmushi tareda sauke ajiyan zuciya tace “Arham nasha gayama ka chanza halin nan nak…….” cikin fushi yace “dama nasan side dinshi zaki dauka saisa banso na gayamiki bama, nasan u will always support Waleed sabida sunada kud…..” wani mugun kallo da Umma tamai yasa yakasa karasa maganan yasaukar da kanshi kasa yana wasa da yatsu, ahankali tace “Arham harga Allah am not happy da wanan dabi’un naka, abu kadan kadauke shi da zafi, Arham do I need to explain yanda yaron nan yake sonka? Saina fadamaka? Kaida bakinka kasha fadan Umma Waleed nasona, Waleed na sona, Arham akwai abinda Waleed baima aduniyan nan ba? He saw u on the street kana 7yrs old kana tallan ayaba, yaron nan kullum saiya fito yabika kuje ku saida ayaban tare kudawo, tun iyaye basu saniba har suka sani, Arham yaron nan Allah ya jikan mahaifinshi, Allah yakai haske kabarinshi saida yasa mahaifinshi by fire by force yasaka a school din dayake the biggest school a Abuja then, Turkish, adaukeku a mota adawo daku a mota, Arham kadawo dan gayu, kuka gama yasa kuka tafi same University a kasan waje ka karanta business administration shikuma medicine, baitaba aboki ba cus yasha fadamin Umma Arham is my everything, Arham is my blood, Arham is my this and dat, yaron nan kome zai saya kome za’a sayamai agida in ba’a sayo nashi da nakaba bazai karbaba, yaron nan bought this house for me, yasaimin car, handling everything that has to do with me, every end of the month saiyayo min har gobe dudda na nunamai yanzu kana aiki kanada kudin yimin komi but yaron nan yaki, yabaka job a inda yake shima, he carry u along a komi, in yananan he want to see u awurin with him, he did everything for us and look I will forever be grateful to Waleed har karshen rayuwa ta, dabadan Waleed ba da Allah kadai yasan inda muke yanzu maybe muna kwana a kasan gada, ankoremu agidan haya” tai dan shiru tana sauke ajiyan zuciya sanan ta nisa tace “menene aibun fadimaka dayayi cewa lokacin office lokacin aiki ne bana firan abota ba eh? Kowa dake da any dangantaka da Waleed yasan the way his world revolve around gidan marayun nan, kafi kowa sanin irin soyayyan dake tsakanin shi da mahaifin shi, bayan rasuwan shi yabude gidan marayun da sunan mahaifin shi, gabaki daya soyayyan dayakema mahaifin shi yay transferring nashi to gidan marayun ne, Arham idan Waleed wants to do good I think u should be the number person dazai bashi support, banda haka just take a look shima yadamu yana ganina agidan yazo wajena ya tambayan kadawo nace bansani ba, yamaka text kakimai reply, Arham karage zuciyan nan dan Allah karage, yanzu tashi kaje ka shirya katafi he needs u komi na hannunka kaji?” gyadamata kai yayi ahankali, dan murmushi tayi tace “right from day one Waleed has been a rude person but ahaka ai ka kawomin shi Umma ga abokina remember? Ka girmeshi yakamata ace kayi amfani da hankalinka and understand him better than anyone, babba babba ne yarona” dariya yadanyi hakan yasa tace “ko kaifa I sauri ina jiran ka a falo” gyadamata kai yayi tawuce tafita shikuma yatashi ahankali zaiyi wajen wardrobe dinshi wayarshi tadanyi kara juyowa yayi yadawo wajen yadauki wayan yabude sakon da sauri ganin Waleed ne.
“okay okay, I get it, you want me to say those words right? Sorry blood I know I was rude dazun nan but hey! Don’t put too much pressure on me I might break, Ammi ne tamin fada dazu da safen nan but I am sorry for taking it out on you, please kazo su Hasim are driving me nut am about to loose it
Dan murmushi yayi ya ijiye wayan batare dayamai reply ba yadauko wata bugaggiyar farar shadda ya saka dan akwai kayan dinner dazusu saka anjima da night ya feshe kanshi da turare, sanan yadau makullan motan shi yafito, tuk kafin ya iso Umma ta kafe kofar corridor da ido fitowa yayi hakan yasa ta murmusa tace “abokin ango da kanshi, agama nashi dakafana zanje wajen Ammin Waleed dama ita ke goyamaka baya wlh kokai aure kona bama wanan bazawaran datazo takanas tafadamin tana sonka dan kaji” dariya yayi yace “habadai Big boy irina zaki sadaka dashi Umma” dariya dukansu sukayi tace “dalla bacemin daga gani nisai kuma gobe in Allah yakaimu zan koma gidan” “alright bye Umma” “bye” tamai waving hand yana fita daga dakin, motan shi ya shige ya zauna ya kunna motar sanan yafito ya bude gate yana tunanin yakamata yadauko mai gadi fa fa fitar da motar yayi waje yadawo ya kulle Gate din sanan yadau hanyar gidansu, dayake Umma tariga tafadamai ta bayan layi shima ya zagaya yay parking akofar gidan sanan ya kashe motan yafito yana tafiya dai dai yabude Gate ya shiga gidan, tundaga tsakar gidan wajen yakejin hayaniyan su Hasim girgiza kai kawai yayi yabude kofan ya shiga falon duk waigowa sukayi suna kallonshi, harara ya watsa musu hakan yasa suka fashe da dariya Hasim yace “ga best man din ango nan ya shigo, iyye see the glow” da hannu ya nunamai kunnenshi hakan yasa da sauri Hasim yace “tuba nake Ya Arham” barin falon yayi yadauki hanyar bedroom dinshi ahankali yabude kofa dakin nashi daga Mom har Waleed din datakai spoon bakinshi danya karbi abinci juyowa sukayi suka kalli kofan, ganin Arham ne yasa Mom tasaki wani murmushi, dauke kai yayi daga kallon Waleed din dayadan murmusa kadan ganinshi sanan ya karasa gaban mom yadan rage tsawo cikeda ladabi yace “ina yini Mom” cikin wani irin jin dadi Mom tace “lpy lau Son, barka da zuwa, Allah yamaka albarka kaji, ina yawan fadama abokin ka ai duk duniya bazai taba samun aboki mai amana irinka ba ga girmama nagaba dashi, uwa uba ga kunya, kai Allah dai yabarku tare, kadinga hakuri da halin Waleed, dabi’un Waleed sai du’a’i jinshi yake kaman dan shekara biyu kagafa yanzu abincin nan wlh inda ban bashiba da bayici, ai nagode ma Allah yanzu zaiyi aure nahuta daman Adda tace ninenan nabata shi” tai maganan tana tallo keyanshi, yi yayi kaman zaiyi kuka saikuma yatashi ashagwabe yayi hanyar kofa da sauri Mum tace “ina zaka?” ahankali cikin yanayin maganan shi kaman na wanda yagaji yace “ni ruwa zan dauko” yana fadin haka yawuce yafita, ajiyan zuciya Mom ta dauka sanan ta maida hankalinta kan Arham dahar lokacin bai tashi daga gabanta ba tace “Arham nasanka yarone mai hankali da sanin yakamata ga abokin kanan kacigaba da sashi a hanyar kwarai, kacigaba da hakuri dashi, ka girmeshi, Waleed is still a child kawai girman jiki dayake da shine yasa a kemai kallo kaman wani babba but har yanzu baikai 30ba kaima kasani, Arham always watch his back kaji dan Allah, kafishi wayau always guide him for us kaga shi kadai garemu, Allah muku albarka dukanku, bari kaga nakoma cikin gida in yazo ga abincin shinan kasashi yaci kasan matsalan shi na Ulcer pls, Ulcer shi yatashi batamai da kyau” gyadama Mom kai yayi ta tashi tawuce tafita, tashi yayi ahankali yana kallon hadadden bowl din da pepper soup din fish keciki ga plate na white rice da spoon komi anjera kan tray, girgiza kai kawai yayi yanabin ko ina nadakin da kallo kafin ahankali yadaga kafarshi yay gaban mirror dakin yana tafiya ahankali, tsayawa yayi yana kallon turarukan wajen, hannunshi yamika ahankali yadauko wani da shi kadai ne baisaniba cikin turarukan wajen mai suna “Men of Chastity” ya shiga jujjuya turaren yana kallo kaman mai wani tunani, bude kan turaren yayi yafesa kadan ahannun subhanallah saida ya lumshe ido tsabagen dadin kamshin, bude kofa da akayi yasa yajuyo da sauri rikeda turaren a hannu, Waleed ne ya shigo rikeda bottle water a hannunshi maidan sanyi, binshi yayi da kallo kafin idanunshi su sauka kan turaren da Ammi tabashi jiya as gift, dan murmushi yayi ya shigo dakin yace “wanan turaren kake kallo, Ammi tabani shi jiya da daddare gift, gama kwalin shi nan kasa dazun nan nabude shi” yamai pointing wani hadadden kwali dakenan kusada kafarshi ja akasa a ijiye, tsugunnawa Arham yayi yadau kwalin yadaura kan mirror sanan yabude kwalin ahankali, kwalin kadai abin kallo ne, har zai rufe kwalin idanunshi suka sauka kan receipt din turaren dake cikin kwalin idanunshi suka sauka kan kudin turaren 2.8m, da sauri yace “wanan turaren ne 2.8 million X-man?” batare daya kalleshi ba Waleed ya sauke goran ruwan dake bakinshi yace “eh kaima kaga bai tsada bako?” yafada yana daukan plate din rice trying to see in zai iyaci da kanshi dan bai koshi ba, sosai Arham ke binshi da kallo yama kasa magana he just wish inama ace shine dandan Ammi shikuma Waleed dandan Umman shi, Waleed dan gatane da baitaba ganin irinshi ba tarairayan shi ake kaman egg, bai dauki kudi anything ba sabida yanada su in excess ma, kaman ance yajuyo yajuyo gani yayi har lokacin Arham kallon turaren yake yamayi nisa a tunani dan murmushi yayi yamaida kanshi kan abincin yace “take it blood” maganan shi yadawo da Arham daga duniyan tunani yace “take wat?” cikin halin ko in kula yace “the pef” da sauri Arham yace “are u crazy? Ammi tabaka gift ne zaka wani ce nadauka” murmushi yayi yana chakalan abincin yace “ai itama tasan everything two ake saimin me and u maybe ta manta ne tasayo just one this time around, anyway take it will order akawo min wani” wani irin murmushi Arham yayi yataho wajen da sauri yadan bugi kafadar shi yace “thank you ango, angon Ilham”
dagokai yayi ya kallai tareda ballamai harara hakan yasa Arham yace “to me dalla, common chill, dan gatan Ammi I know yanda Ammi ke sonka dinan will choose the best girl for u, a princess kaman yanda kake a Prince to this family yar gata irinka” tabe baki yayi yatashi yace “nidai mutafi mosque” tashi Arham din yayi suka wuce suka tafi masallaci sallan magrib.
[11/1, 11:44 PM] Re@l???? K@usy ????: ???? TWO DIFFERENT WORLD ????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Leave a Reply

Back to top button