DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

Koda Mama tafito har motar Ammi direba yajata sunyi gaba, awani irin hankali Mama takarasa motarsu, baya tabude ta shiga direba ma baya cikin motar da alamu masallaci yaje, fashewa da kuka tayi sosai, intace dukan da Arham yama Waleed bai mata ciwo ga wlh tai karya, ta bala’in jin ciwon dukan nan kaman me, Waleed d’a ne wlh, dan halas d’a na kwarai, tasan harga Allah tanaso aramamai amman da Waleed yafarka yayma Ammin shi maganganun nan saida ranta ya sosu, bala’in sosuwa ma, Waleed d’ane da kowace uwa zatai alfahari dashi aduniyan nan, taji kunyan abinda danta yamai wlh taji kunya, tasan Ammi tagaya mata maganganu amman ko kadan bataji zafinsu ba dan tasan ciwon dakake ji in wani yakama maka d’a yadaka ba gaira ba dalili, Arham bakin halinshi da bakin zuciyanshi tamai yawa, kuka tayi mai suna kuka amotar nan hakanan ma taji bazata iya komawa cikin asibitin tahada ido da Waleed ba, tana zaune direban ta ya shigo yace “Hajiya yakuri ina masallaci ne mutafi?” gyadamai kai tayi tace “eh mutafi”, tada motar direban yayi suka fita daga gidan marayun.
Direban Ammi nakaiwa gidan bamata jira yabude mataba tabude tafito, ahankali take tafiya dan bamata gani sosai, kanta wani irin bugawa yake kaman ana dukanshi da gatari, falo tabude ta shiga, yar aikinta da gudu tafito tana mata sannu da zuwa ko iya amsata bata iya tayiba tawuce stairs tai sama ahankali tabude dakinta ta shiga, yarda jakanta tayi anan tsakiyar dakin tawuce kan gadonta da kyar ta zauna tamika hannunta ta shiga tattaba saman kan side drawer dinta wani goran magani ta dauka da sauri, sanan ta bude taciro wasu kwayoyin magani na masu hawan jini guda biyu ta jefa abaki ta hadiye sanan tadauko bottle water ta kurbi ruwa kadan tasha, kanta na bala’in ciwo, tadafe kan da duka hannayenta ba’awani dauki lokaci ba bacci yay awon gabada ita.
Wuraren karfe biyun dare cikinta yawani irin murda mata da sauri tabude idanunta rass ta tashi zaune tznabin dakin da kallo, fuskarta ta taba taji tahada wani uban zufa kaman wacce tai dambe dudda uban AC dake dakin, tashi tayi ahankali ta dauki wayarta ta lalubo number Waleed tana yatsine fuska sabida ciwon maran datakeji, dailing number shi tayi amman bai shigaba, hartai bacci taga bai dawo ba gashi number ta bayi shiga hakan yasa tamike tsaye ahankali da kyar tana daga kafarta tabude kofa tafito daga dakinta, dakin Waleed tabude taga baya ciki hakan yasa tai stairs tafara tafiya ahankali zata sauko, wani irin ciwo dataji ya tokare mata mara yasa ta kurma wani mahaukacin ihu. “Mai gadiiiiii” zama tayi awurin tana wani irin nishi kafin tasake kwalama mai gadi kira, akaro na uku ne yaji yafito daga dakinshi yana share idanunshi dake cikeda bacci, ganin daga flat ake kiranshi yasa yay flat din yabude kofa ya shige hango Ilham daga ita sai doguwan rigan bacci yasa yay wurinta da sauri yace “Hajiya sannu haihuwan ce bari nakira miki dakta awaya” zai ciro wayarshi tace “kabarshi bayi shiga, kiramin duk wanda zaka iya kira azo a kaini asibiti azaba nikeji mai gadi” takurma wani uban ihu da saida ya firgita yace “Hajiya salati zakiyi, salati ake” juyawa yayi ganin bamatasan inda kanta yakeba ihunta kawai take, saida ciwon yadan sarara sanan ta nemi number Arham amman harya gama ringing bai dagaba, sau biyar takirashi amman shiru, dialing number Ammi tayi shima bayi shiga, ganin haka yasa tai dailing number Mummy ta, ringing daya Mummy ta tadauka fashewa da kuka tayi tace “Mummy mutuwa zanyi, Waleed bai dawo gidaba number shi bayi shiga, ina kiran number Maman shi itama bata shiga, dagani sai mai gadi agidan, kuma bai iya tuki ba balle yakaini asibiti, Mummy mutuwa zanyi” tafashe da kuka sosa daya ruda mahaifiyarta, anatse tace “kinga ba’a kuka in ana nakusa, be strong kinji yar albarka, ga Babanku nan yanzu zai kawoni wurinki just stay where u are kinji am coming” ta katse wayan, daidai mai gadi na shigowa yace “Hajiya wlh duk basa bude gate kinsan anguwan manya ne nan” ko jinshi batayi tahau ihu tana kuka sosai mai gadi yama rasa maizai mata sai dialing number Waleed yake amman bata shiga.
Wani ruwane yafashe mata dayasa tahau ihu. “mai gadi zan mutu kataimaka min wayyo Allah na kataimaka min dan Allah, daidai lokacin akai knocking kofar gidansu, da gudu mai gadi yafita yana zuwa yabude gate iyayen Ilham dinne mamanta da Babanta} da mota, Mmummy ce ta shigo tai ciki tafito da ita aka sata a motar Baba sanan takoma ciki taje ta nemo akwatin haihuwan ta adaki sanan tawuce takai motar ta shiga baban su yaja motar sai hospital.
Bakaramin wahala tasha ba sai wuraren karfe 8nasafe ta haihu, ta haifo danta namiji katoto mai bala’in kamada Arham kaman yay kaki ya tofar.
[11/1, 11:48 PM] Re@l???? K@usy ????: ???? TWO DIFFERENT WORLD ????
✍️ M SHAKUR
3️⃣1️⃣
Shirya yaron akayi aka fito da fitoda shi aka kawoma Mummy shi, ahankali Mummy ta karbe shi tana murmushi tace “miji nasamu ko kishiya”? Dariya nurse din tayi tace “miji ne Hajiya” karbanshi Mummy tayi tana kallonshi yaron kato dashi Masha Allah.
Daidai mijinta yakaraso tace “Alhaji kaga mijina masha Allah dawa yay kama”? Dan dariya Alhaji yayi yace “ai kamanshi daban da uwar da baban, hala sai nan gaba zai dauki kamanni, sake gwada namban mijinta dana mahaifiyar shi kiji ko zasu samu yakamata” number Waleed tafara dialing amman bai shiga har lokacin hakan yasa tai dialing number Ammi, lucky wayar ta shiga, wayar na gab da katsewa Ammi ta dauka, kafin ma Ammi tai magana Mummy tace “kawata lpy kuwa? Tun jiya da daddare muke kiranki dagake har Waleed baya shiga wlh hankalina yatashi” dan murmushi Ammi tayi tace “Waleed ne yadan sami hatsari wlh yana asibiti agidan marayun shi har karyewa yayi akafada, ban fadima Ilham bane kinsan mai ciki ba’a daga musu hankali haka, nikuma ina dawowa gida magani nasha na kwanta sabida hawan jinina yatashi, Mom ce awurin shi amman yanzu nai wanka shiryawa ma nike nakaimusu breakfast” da sauri Mummy tace “innalillahi wa innailaihi raji’un, ashe abinda yafaru kenan Ilham takira takira mijinta bayi shiga daga karshe saidai takira mu mukazo gamunan a asibiti wlh tasami karuwa yanzun nan amman tun cikin dare mukazo, anmiki miji fa, baki ganshi ba dan lukuti dashi” Mummy tafada cikeda farin ciki sabida tasan yanda Aminiyarta keson jika, Ammi mutuwan zaune tayi tama kasa magana, hakan yasa Mummy ta kyalkyace da dariya ta kalli mijinta tace “Alhaji tayi mutuwar zaune fa” sukahau dariya sanan tace “ki shirya saiki biyo kiga jikanki kafin ki kaima su Waleed abinci, Allah yabashi lpy, anjima dazaran an sallameta zamuje mu gaidashi”
Ammi kasa yarda da abinda aka gayamata tayi hannunta har wani irin rawa yake tai dialing number Mom dake zaune dakin tana kallon Waleed da tun jiya daya lumshe ido yaki budesu bacci mai nauyi ya kwasheshi yanzu muka yatashi dan tasan yana jinta sarai wlh, kaman bazata dauki wayan Ammi ba saikuma ta dauka takai wayar kunnenta, wani irin zabura tayi tace “Ilham ta haihu?” rass Waleed yabude idanunshi jin ance Ilham ta haihu, katse wayan Mom tayi tana murmushi sanan ta kalli Waleed dake kallonta ta tabe baki tace “mara kunya aika bude ido dakaji matarka ta haihu, suna asibiti ta haihu ansami namiji” ahankali yadan saki wata yar kyakkyawan murmushi sanan ya yunkura zai tashi, kafadarshi kawai da akai dauri kehanashi motsi yanda yakeso, da taimakon Mom ya iya tashi, Mom tace “me kakeso?” ahankali yace “office dina zani, I want to shower na chanza kaya naje nagansu” taimaka mai Mom tayi yamike tsaye ahankali suka fito waje, nurses sai gaidashi suke gyadamusu kai kawai yake, haryakai kofa yatuna alkawarin dayama Widad, Mom ya kalla yace “am coming Mom” sanan yay hanyar dakin datake, hannunshi yasa yabude kofar ahankali yashiga yana kallonta ganin tana bacci, ahankali yakarasa gaban gadon ya tsaya akanta yana kallon fuskarta kaman yatasheta dan taganshi saikuma yafasa yajuya kawai yafito tareda kullo mata dakin sanan yafito yay office dinshi shida Mom suka shiga ciki, dakin shi ya shiga yay bayi, brush yayi sanan yay wanka da ruwan zafi, jikinshi ciwo yakemai bana wasaba bai taba fada a rayuwanshi ba ko saisa Arham yay galaba akanshi oho, fitowa yayi yadauko wani jean yasaka da kyar sanan yadauko wata riga sai saka yakasa sawa, kwalama Mom kira yayi hakan yasa ta shigo, wani scissors yanuna mata, saida suka yanke hannun rigan daman sabida hannunshi yay balance sanan tasamai rigan ta shinfidamai dadduma yay sallolin da ake binshi sanan suka fito, Mom kejan motar suka dauki hanyar asibitin da Ilham take, parking sukayi suka fito sanan suka fara tafiya har zuwa dakin datake akwance.