DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

Bude kofan Mom tayi ta shiga, Ilham na kwance kan gado, fuskarta ya kumbura suntum tsabagen kuka, sai Mummy dake zaune kan kujera rikeda jaririn da aka shirya yay kyau, Mummy na ganinshi tace “subhallahi, innalillahi wa innailaihi raji’un, Waleed wanan wani irin hatsari ne kaga yanda jini yataru a idanunka kuwa, jibi wuyanka da fuskarka sannu Waleed” kanshi akasa duk take maganganun nan ahankali yace “ina kwana Mummy” “ina kwana Waleed, ya karfin jiki? Allah yabaka lpy kaji, Allah yasa kaffara ne sannu” gyada matakai yayi suka shiga gaisawa da Mom sunama juna barka, karasawa gaban gadon yayi yana kallon Ilham data tsareshi da ido itama tana kallonshi tana mamakin abinda yasame shi haka, dan murmushi yamata ya shafa goshinta da hannunshi saida ta lumshe ido tabude su ahankali ta kalleshi, murya chan kasa yace “thanks for giving me a baby khadija, Allah yamiki albarka” gyadamai kai tayi tareda mika hannunta takama lafiyayyen hannunshi tarike gam, cikin muryanta da baya fita sosai tace “what happen to you Babyna”? Baki yabude zaiyi magana Mom ta taho rikeda jaririn tace “wato agaban mu ake nuna mana sonkai ko kana nuna kafi damuwa da matarka kan yaronka dayazo duniya yauko” murmushi Mummy tayi ranta fess ganin Waleed naji da yarta. Mom tamikamai yaron tace “ga danka nan dauki abinka kaga yanda yay kama da abokin ka kuwa kaman yay kaki ya tofar” wani irin mummunan faduwa gaban Ilham yayi saikuma ta daure ta lumshe idanunta da sauri kaman wacce bacci ya sace, ahankali Waleed yasa hannunshi ya karbi yaron yana kallon fuskarshi sanan yazauna abakin gadon yana rikeda shi yana kallon fuskar jaririn dake bacci yana murmushi, ko Allah yasan cewan yanason Arham, so na domin Allah, Allah ya azurtashi da d’a amman sai yaron bai biyoshi ba bai biyo mahaifiyar shi ba saiya dauko kamannin amininshi hakan yasa yaji bazaima iya sakama yaron sunan mahaifinshi ba, dan da yace in namiji yahaifa zai sakamai sunan mahaifinshi but wanan da yaron ke kama da Arham dole Arham zai bama yaron kodan Arham yagane shibai rikeshi da komiba sanan har gobe har jibi shi dan uwanshi ne no matter what.
Bakinshi ya daura kan goshin yaron ya sumbaci yaron yana murmushi sanan yama yaron huduba ya karbi dabinon dasuka sayo da zasuzo yatauna yabama yaron yabashi ruwan zamzam, yadago kanshi ya kalli Mom yace “Mom sunan d’ana Arham Waleed Warbai” shiru Mom tayi tana kallon Waleed din for few seconds itama Ilham saida tabude ido gabanta nafaduwa ko Waleed yagane ne saisa yabama yaron sunan Arham sosai ta birkice saikuma cikeda siyasa tace “d’ana yawani kama yayi kama da abokin ka saikuma kawani bashi sunan shi” karban yaron Mom tayi tace “Allah ya rayaka Arham, daidai nan aka bude kofa Ammi ce ta shigo yar aikinta abayanta da direba rikeda basket din abinci, tace “ku yakuri ai danaji ya’ta ta haihu kitchen na koma da kaina namata abincin da maijego yakamata taci, sassanunku now ina Dr da nurses din dasuka karbi haihuwan jikana kuga” tawuce tafita waje tana kwalama nurses da Dr kira, duk wanda yazo bashi bandir din yan dari biyar guda take zukuga yanda aka cika Mummy sai murmushi take, saida ta rabar da kudin tass sanan ta shigo dakin ta kalli Mummy Ilham tace “bakin ciki kikemin ne aminiyata bazaki tashi akan kujera na zauna na dauki jikana ba”? Kwashewa da dariya akayi, Mummy ta tashi daga kujeran tace “maida wukan dadin abin nidai kafin nayi wanan jikan naki nayi wasu balle amin yanga” zama Ammi tayi tace “yanga yanzu kika fara gani” all this maganganun ko Waleed dake zaune bata kalla ba, saisa ma bataje gadon ta duba Ilham ba sabida yana wurin, ahankali Mom ta taho rikeda Arham junior sanan tamikama Ammi shi ahankali tace “ga Arham Waleed Warbai, Arham karami” Mom tai maganan tana kallon fuskarta kaman yanda itama Ammi tadago tana kallon fuskar Mom kafin ahankali tadaura fuskarta kan yaron, shiru tayi ganin yaron kaman Arham yay kaki, dudda yaron jariri ne but kamannin was so obvious da kana gani zaka gane da Arham yake kama, gabaki daya Ammi jitayi duk wanan farin cikin da murnan nan da rawan jikin datake yi na zatazo taga jikanta yakoma ciki, abinda ma yafi bata abin shine sunan dataji Waleed yasamai, kuma tai alkawari bazata sake shiga rayuwan shiba kaman yanda yafadi, so yasaka sunan abokinshi ma danshi danyaci mata mutunci itakuma bazata cemai komiba ya kyauta, murmushi kawai tayi tace “Allah rayaka Ar…..an jikalle” tafadi ahankali danta kasa kiran sunan Arham din, bude kofa akayi Baban Ilham ya shigo ciki yana ganin Waleed yace “assha, sannu son wanan daurin asibiti ai saikafi shekara baka warkewa tashi muje nakaika wajen wani mai dauri yana maka zaka warke cikin sati tashi muje” yay maganan yana kallon Waleed tashi yayi ahankali yabita gaban Ammi da kanta kekan jaririn, suka wuce suka fita, a mota baban Ilham ya daukeshi sai janshi yake da hira amman baya wani iya amsawa da kyau dan nauyin mutumin yakeji, agaban wani gida yaga sunyi parkin, fitowa sukayi baban Ilham yace “muje” shiga sukayi har wani dankareren falo inda wani mutumi ke zaune, Baban Ilham yace “Barka da rana malam, ga dana nan ya karye akafada munzo agyaramai” tashi baban yayi yazo yadaura hannunshi kan wajen saida Waleed ya yatsine fuska sabida zafi, Baban yace “ba karaya bace kashi ce ta goce ina gyarawa yanzu shikenan” da sauri Baban Ilham yace “kagani ko babu abinda asibiti suka iya indai kan dauri ne, yace Baba ayi mun gode” kwalama wasu maza kira Baba yayi, Waleed yaga wasu karfafan maza su kusan shidda sun shigo, hannu Baba yasa ya warware daurin sanan aka rike Waleed din, addu’a Baba yayi yatofa kan kafadar sanan yakai hannunshi kan wajen yafar kokarin saita kashin sosai Waleed yaso yadaure dayaga azaban ba nan bane yafara kokarin kwace kanshi amman ko motsi baya iyayi, da azaba yay azaba kuka yafara kaman zai mutu Baban Ilham sai sannu yakemai kusan awa daya aka dauka a hannun sanan baban ya gyara tsaf aka sakeshi da sauri yasa hannu yana share hawayen Baban Ilham sai sannu yakemai, magani Baba ya shafamai akafadar yace “ka warke baka bukatan wani dauri kuma angama” kudi Baban Ilham yaciro mai yawa yabiya mai sanan suka tafi.
Duk suna zaune adakin Dr ta shigo ta duba Ilham sanan tabasu sallama tawuce tafita, ahankali Mummy tace “aminiya natafi da ita gida tai jego ne?” ada Ammi tai alkawari bazata je jegon gidaba amman sai kawai taji gwara sun tafi, gyama Mummy kai tayi tace “eh kuwuce kuma a kulamin da matan d’a da jika da kyau, suna arba’in zanzo na kwashi abuna wlh” duk akai dariya Mummy tace “nina nafi kowa sanin bala’in ki ai bazanyi wasa ba yallabiya” tai maganan tana kallon kofa ganin anbude Baba ne da Waleed da idanunshi sukai jajir da sauri Mom tai wajen Waleed din tace “sannu Dan Yaro an gyara” gyadamata kai yayi, Baba yace “bama karaya bace ashe gocewar kashi ne yanzu an gyara an shafamai magani, Allah yabashi lpy” ahankali Mom tace “angode Alhaji” Mummy tace “Allah baka lpy” itadai Ammi tai kaman bataji su ba, Mummy ne tace “Alhaji an sallamemu mutafi dasu gida, agida zatai jego” da sauri Baba yace “to bari nakai kayan mota” daukan kaya yashiga yi Waleed yaje zai tayashi da sauri Baba yace “kaga jeka zauna kaida hannu ba lafiya ne zakadau abu jeka huta” yay maganan yana fita, ganin haka yasa Mom ta shiga tayashi suka kwashe komi sukakai mota, sanan Waleed yadau hijab yabama Ilham tasaka ahankali yace “test me all that you need zan aiko miki dashi” murmushi tayi ya gyadamai kai ganin yana wani ji da ita kodan ta haifamai d’a ne, kofa yabude mata tafita suka jera atare tana tafiya ahankali har motar Baba ta shiga ta zauna sanan ya matsa ganin Ammi tazo baby ta shiga ta bama Mummy sanan suka rufe musu motar suka tafi Ammi tajuya tai motar ta ta shige direba yajata banda Waleed daya tsaya chak awajen, ahankali Mom tace “mutafi” daga kafa yayi yawuce ya shiga motar ta suka tafi, gida sukaje yana fitowa flat dinshi yaje kwanciya kawai yayi, yaciro wayarshi number Arham yakira amman harta gama ringing bai dauka ba, 3 miss calls yamai ganin bai dauka ba yasa yamai message.