DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

“Hey blood, I called no answer I guess you are still angry with me, I called nafada maka Khadija ta haihu, an sami baby boy, yaron yay kama dakai sosai blood, and do you know what’s even} great? Yaci sunanka, sunanshi Arham Waleed Warbai, blood you mean alot to me, u make my life colourful, I am sorry idan maganan dana maka jiya kajita somehow I was just trying to know what you’ve been up to lately, and I am also sorry akan abinda Ammi na tamaka please forgive us, take care, anjima zan shigo

Yaturamai sakon tareda lumshe ido bacci na saceshi kafin baccin yay nasaran daukeshi.
[11/1, 11:48 PM] Re@l???? K@usy ????: ???? TWO DIFFERENT WORLD ????

????????DUNIYA BIYU MABANBANTA???? ????

        ✍️ M SHAKUR 





          3️⃣2️⃣ & 3️⃣3️⃣

END OF FREE PAGE
Wuraren karfe biyun rana ya farka, sosai yaji karfin jikinshi kawai gajiya yakeji bawani abuba, tashi yayi dagakan gadon yaje gaban madubi ya tsaya ya kalli kwayar idanunshi na dama ganin har yanzu akwai jini aciki yasa yabar gaban madubin yana tunanin inya fita anjima zai tsaya a pharmacy yasai maganin dazai saka jinin idanun ya washe, bathroom ya shiga, wanka yayi yasake yin brush sanan yafito, wardrobe dinshi yaje yadauko wasu native, farin yadi ne mai taushi da akamai jumper yasaka sanan yadau turare yafeshe kanshi dashi, dadduma yahau yay sallan azahar sanan ya zira takalmi bayan yadauki wallet dinshi yafito, side din Ammi yayi gabanshi nafaduwa, ahankali yabude kofar ya shiga hada ido yayi da Ammi dake zaune kan dogon kujera hannunta rikeda remote ko taji zai shigo ajikinta ne oho dayasa take kallon kofar oho, suna hada ido ta ijiye remote din ta tashi daga kan kujeran da sauri ya shigo dakin yamaida kofan yarufe yace “Ammi, Ammi please wait” sama Ammi tayi da sauri yabita kafin yakai harta shige dakinta tarufe da key dan bamata son ya shigo, tsayawa jikin kofar yayi yay shiru, yakai kusan 5min ahaka sanan yace “Ammi please listen to me, kiyakuri kinji please Ammi na” yay maganan ahankali yana knocking kofarta yakai kusan 10min ahaka awurn ganin bamata da niyyan bude kofan yasa yawuce ya sauka kasa, dinning yaje yazauna sabida shegen yunwa yakeji, warmer yabubbude, tuwon shinkafa yagani da vegetable soup, zubawa yayi baima wani iyaci da yawaba yasha ruwa yamike tsaye key motar Ammi dake kan centre table yadauka yawuce yafita, motar ta ya shiga ya zauna sanan yaciro wayarshi ganin har lokacin Arham baimai reply din message dinshi ba yasa yatada motar direba yabude mai yawuce yafita daga gidan.

Agaban gidansu Arham yay parking motarshi yabude yafito yatura gate ya shiga gidan, babu kowa a tsakar gidan, sallama yayi yabude kofa ya shiga falon Mama ce ta amsa mai ahankali, saikuma tasaki murmushi tace “Waleed kaida bakaji sauki bane ba kafito? Ya karfin jikin? Maman ka takirani ta sanar dani abin farin cikin daya samemu ubangiji Allah ya raya, ya dayyaba, ya sunan yaron ne”? Murmushi yayi yace “sunanshi Arham Mama” wani iri Mama taji jikinta yay sanyi, sanyin ma karara hakan yasa tama kasa magana, lurada yanayin ta yasa Waleed yace “Mama ina Arham yana nan”? Cikin dan fushi tace “ohon mai rabona dasa Arham a idanuna kwana uku kenan yau” mikewa da sauri Waleed yayi yay corridor falon shiga yayi direct yay gaban dakin Arham, knocking kofar yayi yakirashi. “blood” jin shiru yasa yatura kofar ahankali ya shiga cikin dakin, dakin babu haske sai uban duhu, ahankali yamika hannunshi ya kunna switch hakan yasa dakin yya haske, Arham ya hango kwance kan gado bai lulluba ba dagashi sai gajeren wando fuskarshi ta kumbura suntum tsabagen dukan dayaci, jikinshi duk tabon ciwo dawani irin sauri Waleed yay gadon yace “subhallahi blood who did this to you eh? Waya maka haka”? Yay maganan yana dago Arham zaune, tashi zaune Arham yayi yana wani irin kallon Waleed din da sauri Waleed ya sauka yay bayinshi, ruwan zafi ya dauko yajefa towel ciki yazo yazauna akan gadon cikeda tausayi ya matso towel din kaman zaiyi kuka yakai kan fuskarshi yana dannamai yace “blood am so sorry, am ashamed of abinda Ammi na tasa aka maka, look what they did to you, this people are heartless, sorry blood” yay maganan yana gaggasamai, ijiye ruwan akasa Waleed yayi bayan yagama yasauka daga kan gadon yanabin dakin dayay kacha kacha da kallo yace “kasha any medication, kaci abinci?” dudduba dakin yayi ganin baiga maganin anything ba yasa yadau ruwan yakai bayi yafito sanan yadawo kan gadon, hannunshi yadaura kan kafadar Arham yana kallonshi kaman yanda Arham din ke kallonshi, ahankali yace “talk to me blood meke maka ciwo eh? Sanan wani abinci zakaci let me go out and get it for you, kafada min please ina da ina ke maka ciwo mow”? Wani irin kallo Arham kemai kafin ahankali yakai hannunshi ya kabar da hannun Waleed daga kan kafadarshi yace “wato halinka Waleed naban mamaki” ahankali Waleed na kallonshi yace “halina blood kaman ya”? Dan murmushi Arham yayi yakai hannunshi ya share fuskarshi dahar lokacin lema leman ruwan da Waleed u gasamai jiki kekai yace “kaida uwarka kunsan polisawa sunzo sun kamani sunmin bugun mahangurba shine yanzu zakaso kana wani rawan jiki kana bani kulawa kaman bakasan hakan yafaru ba” sassauta murya Waleed yayi ahankali yace “blood listen to me, I have no reasons to lie to you koda chan banmaka karyaba yanzu ne zan maka karya, believe me bansan Ammi tasa amaka abu makamancin hakaba, a lokacin danasani saida nasa aka janye aka sakeka, blood you are my only friend danai basing life dina dashi in this world, bazan taba hurting nakaba no matter what, besides you are morethan a friend to me, you are my blood Arham” tabe baki Arham yayi sanan ya nunashi da yatsa yace “ku masu kudin nan feels zaku iya duk yanda kukaga dama aduk lokacin dakuka so, zaku iya duk yanda kuka so aduk lokacin dakukaga dama, listen to me Waleed wlh zan gwadama aduniyan nan dudda uban kudinga, kadaiga mahaifinka nada kampany akasan waje dake gina boat dawasu kampanoni, mahaifiyarka nada kampany da business da dama ko, amman wlh zan nuna maka duk wayan nan kudin da dukiyan dakuka tara bazai taimakeka da komiba saika gane kurinka Waleed” shiru Waleed yayi yana kallon idanun Arham, all he could see was hatred, tsantsan tsana kawai yake gani a kwayar idanun Arham, wani iri yaji yanaji kaman zaiyi kuka saikuma yahana kanshi, ahankali yana kallon Arham din yace “Arham all wanan fadan da maganganun is it akan kawai natambayeka ina kake kai kudin ka? But why do I feel kaman there’s more to this case, blood na kalli idanunka abu daya kawai nake gani shine tsantsan tsana ta, blood mena maka? Menataba maka? What have I done to you please kafadi mini watakila bansani ba please tell me kaji my friend” da sauri Arham yanuna kanshi yace “friend? Nine friend dinka Waleed? I can never be a friend to rich kids sabida all they know is sumaka ihu, suyi controlling naka, suyi matching naka and step your your neck aduk lokacin dasukaga dama, Waleed zaka iya tuna how many times kakemin ihu kakemin tsawa in your office kanamin fada”? Wani irin hawaye ne Waleed yaji sun gangaromai shaaarr, hannu Arham yanunamai yace “ba kuka nace kamin ba tambayanka nayi, kasan how many times kakemin ihu aka a office”? Girgiza mai kai Waleed yayi ahankali kafin yafuzar da iska yasa hannu ya share idanunshi tass sanan yanisa yace “I never meant all those shout, badan cin mutunci kowani abubane yasa nayi hakaba, Blood kasanni sama da kowa, and you know how passionate I am towards my work at the orphanage, idan yazo takan orphanage dina ne banson wasa kawai strictly work saisa I do all those to you sabida kai aikin da yakamata kayi, but tunda har ahaka kadauki abun ka fassara am sorry for that too I didn’t do it because am rich or whatever I do it cus I feel is my own way of motivating my staff to do more, to perform better, idan akazo kan human resources management akwai two ways of motivating a staff, akwai positive motivation and negative motivation, I guess mine was the negative one but kayakuri” ya karashe maganan ahankali muryanshi tayi sanyi sosai, tabe baki Arham yayi yace “orphanage orphanage orphanage, staff, staff, staff, Mr, Dr. Waleed Warbai the chief CEO of Warbai orphanage home and home of the disables how does the name sound”? Yatambayi Waleed dake kallonshi cikin yanayi na isgilanci sanan yaydan murmushi yace “I will make you a promise yau dinan akuma gabanka, Waleed kome kaci sai Arham yaci! Waleed kome kasaka sai Arham yasaka! Waleed kome kahau sai Arham yahau! Waleed kowani matsayi ka taka sai Arham yataka shima! Sai last thing dazan fada maka is over between us” da sauri Waleed ya kallai, gyadamai kai Arham yayi yace “yes is over tsakanina dakai Dr Waleed Warbai, we should go our separate ways, yanzun haka danake maka magana my resignation letter na gidan marayun ka duk lokacin dakaje za’a baka, ka kama gabanka nakama gabana, daidai da silebiyar dinka karka sake bama Mahaifiyata, Arham bai sanka ba bai san dazaman kaba kaima do me a favour ka kwatanta hakan, is over we are not friends we are not friends, please katashi kafitar min daga daki kabar min gida and yau yakasance rana ta karshe dazaka kara zuwa gidanmu” kasa koda motsi Waleed yayi daga inda yake, hannu Arham yadaga yanuna mai kofar dakinshi yace “out, I said out” yadaka mai tsawa irin na cin mutuncin nan yace “indai kai ba maye bane katashi kafitar min daga daki mara zuciya kawai dolo” sosai Waleed ke kallonshi kafin ahankali yasauka daga kan gadon idanunshi sunyi ja mugun ja yabude kofa ahankali Mama yagani gaban kofan, murmushin dole ya kakalo yace “sai anjima Mama” baima jira amsanta ba yawuce yafita da sauri yya wajen gate yafita yabar gidan ya shiga motarshi yaja dawani irin gudu sanan yabar anguwan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Leave a Reply

Back to top button