DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

Bin bayan Waleed Mama tayi da kallo taji gabaki dayan maganan su sabida ita kanta tadamu tun ranan batada Arham a idoba sabida fushin datake yi dashi yasa taki zuwa tadubashi, hakan yasa Waleed na shiga dakin tabiyo bayanshi.
Tura kofan dakin tayi ta shiga, hada ido tayi da Arham da yana ganinta ya saukar da kanshi kasa, ahankali dawata irin murya dake rawa sosai Mama tace “Arham Waleed kama wanan cin mutuncin, Arham anya nina haifeka kuwa? Anya nonon nan nawa kasha”? Takama nonon ta tanunamai, saikuma tafashe da kuka sosai dan her heart is so heavy tace “wlh wlh da’ace a asibiti na haifeka Arham da na rantse maka da Allah dayau dinnan sainace bakaine danda nahaifa ba, anchanza mini kai a asibiti, amman agida na haifeka dagani sai unguwar zoma” tafashe da kuka sosai, sanan ta share idanunta tass da bakin zaninta tace “wlh albasa batai halin ruwa ba, babu ta inda ka gado malam mahaifinka, baban ka malami ne, wayan nan manya manyan malaman da ayau a Abuja dasu akeji duk ubanka ya koyarda su Arham, Arham ubanka malami ne, kakanka malami ne, amman kaiko Arham shaidanin yaro ne” tafadi haka tsabagen yanda zuciyarta ke tafarfasa, cikin ihu da fada da kunan rai tace “Arham wai shinko katuna waye Waleed koko kamanta ne?” tamai tambayan tana kallonshi sanan tace “Arham kanajin tsoron Allah kuwa? Arham kana kokarin ka tabbatar da cewan mutane kadau mutum daga rana ka maidashi inuwa shi saiya maida kai rana, Arham kai butulu ne eh? Yanzu inda ace zaka tashi kaje sip dinan naka zan rantse da Allah nakuma kara idan akwai kayanka daka saya da kudinka basu wuce kala biyu, Arham gabaki dayan sitiranka Waleed kisiya maka, Arham yaron nan nasonka har kuka naji yana maka kanamai ihu kana cewa ba kuka kace yamaka ba, matarshi ta haihu yarada ma danshi sunanka Arham duk baka ganin abubuwan nan? Da ace Waleed bai tsamoka daga talauci dahar yau ayaba kake saidawa, Arham Arham Arham” Mama tama rasa maizata cemai saikuma tafashe da kuka tace “kaga yanda idanun yaron nan suka taru da jini dukan dakamai? Amman bai rikeka ba ya tattako yazo wajenka, bari kaji bazan taba bari ka wulakanta mai sonka ba wlh, bazan taba bari ka wulakanta wanda ya chanza mana nidakai rayuwa ba, Arham bazan taba bari ka wulakanta Waleed ba domin ka wulakanta yaron nan kadauka nika wulakanta aduniyan nan, dan haka dau wayar ka ka kirashi agabana kasa handsfree dan naji, kabashi hakuri sanan kafadimai duk abubuwan daka fadamishi wasa kake kanajina “! Mama ta dakamai tsawa, dago idanunshi Arham yayi ya kalli Mama yace “Mama kiyakuri amman wlh ni bazan kirashi ba, kuma kidena cewa ya taimake mu babu abinda Waleed yamana Allah ne yataimake mu kuma shine yamana komi wlh, daman shi Allah haka yake abinshi inya tashi taimaka maka saiya nemo wani ya taimaka maka ya hanyar shi, tunda ai shi Allah bazai sakko kasa yamika maka kudi da hannunshi ba yace gashi Arham saidai yay amfani dawani, dan haka wlh Mama ni Allah ne yamin komi babu wani mahaluki daya isa yataimaken, Shidin banzan shi, kudin shi na banza meyake dashi, shi idan ma yaga asalin masu kudi guduwa zaiyi yaboye wlh irinsu Otedola, Zuckerberg da sauransu, shidin me shidin banzan shi, dan ubanshi nada kampani a kasan waje yake mana kapapa yana daga mana kafada wlh bazan kirashi ba” yay maganan ranshi duk abace, rungume hannu Mama tai aciki tana kallon Arham kaman tasami TV, ahankali Mama tace “Arham Annabi yace a kullum mudinga kallon nakasa damu bana sama damu ba hakan zaisa mungode ma Allah da kyau, Arham batun yau nake karantan wani abu tattare dakaiba amman yau Allah ya bayyanamjn abin gabaki dayanta Hassada kakema Waleed” da sauri Arham yana daga murya yace “shi awa zan tsaya inamai hassada Mama? Ubanme yakeda shi? Allah ya kyauta kafin na ganshi naga masu kudi dubu ni mama kima dena min maganan wani Waleed banson jinta, dashi da wanan matsiyaciyar uwarnan nas….” bai karasa maganan ba Mama taxuba ma bakinshi mari, sanan tacire slippas din kafarta tahau dukanshi ta ko’ina tace “Arham kaci uwaka, bani na haifeka ba, wanan bakin halin naka da bakar zuciya uwarka da ubanka basu dashi, wayanda suka taimake ka kake zagi eh, kai wani irin butulu ne, Arham ni kake so kabama kunya aduniyan nan” dudda dukanshi take bakinshi kin mutuwa yayi yace “ki kasheni Mama, dama batun yau nasan kinfison Waleed kan danda kika haifa ba, Waleed nada kudi, yasai miki gida da mota, gaki da generator ga solar, ga kayan abinci ga kudin kashe wa ba dole ba, Mama ki kasheni sabida Waleed, badai danni banda kudiba banda gidan marayu ba saisa bakisona nima ba zakiga abinda zai faru Mama kicigaba da dukana har saina daina numfashi, badai kowa dukana yake akan Waleed dan gata ba, ajebota kucigaba nikuma namuku alkawarin sainaima Waleed abinda dukanku bazaku iya taimakon shiba wlh, wlh kuwan, kiyita dukan” yakara mika mata kanshi dantaji dadin duka, dukanshi Mama tayi har saida Sadiya taji ta shigo da gudu taja Mama baya dake haki kaman zata mutu tace “sadiya kibarni na kashe yaron nan nahuta dan ba da’na bane, Sadiya kibarni, Arham nason yacimin mutunci, Sadiya Arham nason ya kunyatani aduniya, dawani idanu yakeson na kalli mutanen nan dasuka mana komi a rayuwa eh” tafashe da kuka, rungumeta sadiya tayi itama tahau kuka tace “Mama yakuri kidena kuka dan Allah” cikin wani irin fushi Arham ya tashi ya finciki key motarshi yafita daga dakin ya barsu awajen idanunshi sunyi jajir.
Waleed rasa inda zashima yaji dadi aranshi yayi kirjinshi sai wani irin mugun tafarfasa yake, baisan ya akayi ba yadaiga yazo gidan marayun shi, parking motarshi yayi yafito sai gaisheshi ake yama kasa amsasu da sauri da sauri yake tafiya har zuwa cikin asibitin shi, direct ward din da Widad ke kwance yake, bude kofar ahankali Ya shiga maida kofar yayi yarufe yana kallonta ganin bacci take, direct yawuce gadon da sauri zama yayi kan plastic chair gaban gadon kawai yakifa kanshi kan gadon kukan dake cinshi tun adakin Arham ya shiga sakinshi awajen ahankali yana sheshek, maganganun Arham gets to him sosai, sun shigeshi was he that bad kaman yanda Arham ya suffanta shi? Was he?.
Kaman amafarki taji kaman ana kuka ahankali wanda sautinshi ke kaiwa har kokon kirjinta, bude idanunta tayi kaman wacce ta firgita ta kalli ko’ina kafin ta kalli gefenta, kan mutum tagani kife kan gadon, gashin kan nawani irin shining sunyi sili sili tsabagen gyara dasuka ji, dudda bataga fuskarshi ba amman tagane mutumin nanne bargon jikinta tayaye da sauri taja jikinta ahankali ta tashi tazauna tana kallonshi tai raurau da ido, ahankali tadaga hannunta ahankali tadaura akanshi, jin soft hannu dake dauke da dan danshi danshin zufa akan sumanshi yasa yadago kanshi ya kalleta da jajayen idanunshi da hawaye yacikasu sosai, wani irin kallonshi take hankalinta yatashi sosai ganin yana kuka ahankali yakai hannunta kan fuskarshi sharemai hawayen tayi da sauri tana girgizamai kai, jiyayi zuciyarsshi tawani irin tsinke baisan lokacin daya tashi daga kan kujeran yazauna abakin gadon ya rungume cikinta tsam ba, fuskarshi nakan cikinta yasaki kuka ahankali cikin harshen turenci yace “Saheeba baki sanni ba, dudda duka yanzu 10month kikayi da sanina, dan zaman dakikayi tareda ni please ki gayamin am I a bad person? I know I makes different decisions, but kowani decision zan dauka abune dazai kawo cigaba dakuma raya wanan gidan marayun, you know ana yawan cewa breakup masoya ne kawai irin couples haka ke breakup ba’asan cewa akwai friendship breakup ba and the shit hurts badly” yasaki kuka sosai akan cikinta dayasa tahau girgiza mai kai tana bubbuga kanshi alamun yay shiru tana kokarin magana takasa but kana ganinta kasan ta mugun damu, ahankali yace “I am so saddd, I don’t know who to talk to, banma san mesa nazo wajenki ba bayan bazama kingane menake cewaba, but crying ajikinshi anyway makes me feel better, am sorry natashe ki kinji” yay maganan yana dagowa daga jikinta tareda tashi daga kan gadon yana juyawa da sauri batare dayabari sun hada idoba, hannunshi yaji anrike gam hakan yasa ya tsaya chak, dirkowa tayi dagakan gadon tana rikeda hannunshi ta zagayo tagaban shi ahankali ta tsaya tana kallonshi, gani yayi itama idanunta sunyi ja, ahankali tabude bakinta tana kallonshi takai almost 20sec tana kokarin iya maganan dazatayi sanan cikin yar siriruwan muryanta tace “you aren’t a bad person” tai maganan tana kara kai hannunta yakama dayan hannunshi tarike gam, sanan ta kallai tace “you are a goodman” tai murmushi dayasa hawayen idanunta suka zubo, saikuma ta washemai baki tace “and I love you” tasakin mai wani heart melting murmushi dayasa all her dimples suka lotsa, wani irin ajiyan zuciya yasauke yasan bamatasan metake cewaba, sanan this is not the first time ake cemai I love you besides Ilham tasha fadimai kalman nan countless time but yau da Saheeba tafadi saida heart dinshi yakusan skipping out, like he felt the words har cikin diddigan kashin jikinshi sosai yay nisa yana tunani yaji an fizge hannunshi, firgigit ya farka yaga ita ke janshi, zaunar dashi tayi akan gado ga mamakin shi daiyaga tasa hannayenta akan kafadarshi ta turashi ya kwanta tana murmushi, samun kanshi yayi da kwanciya yana wani iri kallon yanda takemai murmushi kaman yau yafara ganinta, stethoscope din dayake dauka kullum dake kan bed drawer dinta inya shigo dubata ta dauka ta makala a kunnenta tsaf tana murmushi sanan tazo bakin gadon tana ware Big lulu eyes dinta ta daura hannu kan lips dinta tana kallonshi alamun yamata shiru sanan takai bakin stethoscope din ta daura kan saman kirjinshi ta saman riga lumshe ido yayi da sauri yana sauke wata nauyayyan ijiyan zuciya jin hannunta kan jikinshi, ita kawai she is doing it jokingly ne but jin beat din kirjinshi acikin kunnuwan ta yasa tawani irin kwalalo ido a tsorace ta fizgo daga kunnenta ya yar, dan dariya yayi yatashi yazauna ahankali itama dariya tayi saikuma ta makemai kafada ta taho dagudu tawani fada jikinshi ta daure hannayenta tabayanshi tana murmushi, wani irin natsuwa ne yaji ya shige shi, lumshe ido yayi tareda manna hancin shi cikin gashinta, murya chan kasan makoshi yace “I love you Saheeba”.