DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

Ahankali Nura shima yazo ya tsaya bayan Waleed yace “nayi imani da Allah sanan na yarda cewa ubangida bazai taba iya aikata wanan mummunan halin ba da abu akasa, na wuce 18yrs ko ayance inada yancin kaina inada ikon nace bazan bikuba kuma baku da yanda zakuyi dani so I stand with ubangida na dayamin komi” yay maganan yana dafa kafadar Waleed takowa shamsiyan dayakeso tazo ahankali tace “Allah zai sakama Teacher, na zauna gidan marayun nan ko bangaren mata baka taba shigowa kai kadai ba saida izinin Mama Iyami, sanan saita sanar damu cewa Dakta zai shigo mu gyara sanan zasu shigo tare yay kome yazoyi yagama duk tana tsaye tareda shi, Hassana, Rukayya, Farida, Hauwee, Bushira, Laila, Adama, Kabira, Razika kuji tsoron Allah, flat dinmu daya, daidai dasau daya bantaba ganin yanayinku ya chanza ba balle har adanganta shi da anmuku fyade, inkun gaji da gidan saiku tafi amman basaikun ma bawan Allah nan shairi b….. ” “shut up there” babban cikinsu ya daka mata tsawa daidai lokacin antaho dasu Widad da kowa nacikin asibitin harda su nurses da Dr, mutumin yace “listen inhar kawuce ko kakai 18yrs you have the right to choose, ko kubimu akaiku safer orphanage kokuma kuyi gate kufita kuyi duk duniyan dakuka ga daman, as for this young folks dabasu kai matakin kansu ba they’re all coming with us, now move to the car” yay maganan yana nuna musu marcopolo da aka bubbude, ahankali ake tafiya yara na shiga manya na shiga staff ma na shiga, mutumin ya juya ya kalli wayanda suka kawo daga asibiti yace “ku shiga mota, Dr kukai patient dinku mota” da sauri Dr yace “what’s happening here” tsaki mutumin yaja ya kalli wanda ke kusadashi yace “sa yan asibiti cikin motan” kama yan asibitin ya shigayi yana kaisu mota Widad na tsaye tana zaro ido tana kallon kowa dan bata taba ganin mutane da yawa hakaba, kuka tasaki ahankali, mutumin nadawowa yazo zai kama hannunta wani irin wawan ihu ta kwara da saida Waleed yajishi har cikin kirjinshi mutanen wajen suka taushe kunnuwansu dan Widad akwai murya, tsaki mutumin yaja yace “are you stupid zaki fasamin dodon kunne ne let’s go” makemai kafada tayi tana kuka sosai tana komawa baya tana kalle kalle, cikin fushi Mama Iyami tace “itama bazata biku ba ai tawuce 18yrz wanan so akyaleta” wani irin kallonta officials din sukayi ta daure fuska tawuce tai wurin Widad data makale abango tana kuka sosai, anatse Mama Iyami tace “ke baturiya ishuru nan ga oga chan je wajenshi tunda kema bakiso kibisu ki tsaya abayanshi, tai maganan tana mata pointing Waleed” bin hannun Mama Iyami tayi da kallo tana kuka, Waleed datagani zaune kanshi akasa yasa dawani irin gudu tai wajenshi tana zuwa batai wata wataba tafada kan jikinshi tasaki kuka tana nunamai officials din da hannu, tunda ya zauna akasa dazu yakasa dago kanshi sai akanta, yanayin idanunshi data gani yasa ta sauka daga jikinshi da sauri tana leka fuskarshi, saikuma takara fashewa da kuka duwatsun wajen ta kwasa dan yanayin shi data gani tasa tagane wayanda sukai harassing nata ne sukai mai shima, da sauri ta mike zata wurga musu dutse chak taji an kama hannunta da sauri tajuyo, da Waleed suka hada ido girgixa mata kai yayi hakan yasa ta zubar da duwatsun tasake fashewa da kuka tana wani irin kallonshi.
Loda yan gidan marayun akayi suka cika marcopolo fam, wayanda suka tsaya da Waleed are just mutane 8, Baba Mani, Mama Iyami, Nura, Shamsiya, sai staff dinshi guda biyu sai Widad, shi Dr Ayo bacin rai yasa ya shige motarshi yabar gidan marayun, cikeda rashin mutunci baban su yazo gaban Waleed yace “all set you have lessthan a minute kabar gidan nan kaida fadawan ka, and mind you Mr Waleed you are advised not to leave the country or the state dan zamu iya nemanka at anytime” ganin ko motsi yakasa har lokacin Baba Mani da Nura suka kama hannunshi suka mikar dashi ahankali, da kyar Waleed ya iya standing on his feet Widad sai kallonshi take tana kuka gani take kaman anmishi wani abune ko mugayen nan sunmai duka ne, ahankali ya kalli Nura yace “je office dina ka daukomin car keys, da keys din wani mota a garage dazaku dauka” gyadamai kai yayi da gudu yatafi hawaye na zuban mai bashi akama shairi ba but he wanna cry for Waleed, dan dariya mutumin yayi yana kallon Waleed yace “ahaka kaman bazaka iya abinda akace kayi ba, da farko da aka kawomana case din ni kaina na musa halinka ne not u till lokacin da aka kawo evidence nagani” dan murmushi da za’a kira murmushin ciwo Waleed ya sakinmai, ahankali yace “I have just 1 request please, badanni ba ku kaisu good orphanage da za’a lurada su da kyau dan most of kananun yaran nan have medical condition” tabe baki mutumin yayi yace “you don’t have to worry about that, sabon orphanage fill zamu kaisu, infact sune first set of yara da zasu fara shiga orphanage din, jiya jiyan nan akai commissioning orphanage din, sunan gidan marayun ARHAM DAN MALAMAI ORPHANAGE HOME AND HOME OF THE DISABLES wanda wani matashin arziki yabude mai suna ARHAM ABDALLAH!!! ba Waleed kadaiba hatta su Nura da zuwanshi kenan wajen dasu Baba Mani saida sukaji wani iri, murmushi Waleed yayi yace “inhar Arham ne mai gidan marayun then I can relax hankalina ya kwanta dan nasan waye Arham yaran nan zasu samu kulawa daya dace” “Allah ka sakama Waleed, Arham bamu yafe makaba! Cewan Mama Iyami da baya iya shiru, murmushi Waleed yasake yi da clearly za’a kira data dariya ya karbi key mota daya daga hannun Nura sanan yace “je garaj ka dauko mota ka kwashi dukanku zan tura maka address din inda zaku tawaya” da sauri Nura yatafi ya dauko mota ya yadawo sienna ce motar dayake ya iya tuki dan Waleed na yawan basu mota, ahankali yakalli su Baba Mani da Mama Iyami data jona Widad suna kuka sosai da wani irin tausayi Waleed din taji yana bata yace “ku shiga mota kutafi zan biyoku” Baba Mani ne yafara shiga gaba itakuma Iyami ta shiga baya Shafa ma haka, ahankali yajuya ya kalli Widad dake kuka sosai yawani irin daure dan baiso tasashi kuka yace “enter d car Saheeba” makemai kafada tayi tana kallonshi tana kuka, lumshe ido yayi da karfi sanna ahankali yace “please get in karki sani surutu” ganin yanda yake yasa Shafa tafito hannun Widad dake tutturje mata takama ta shigar da ita mota tana kwala uban ihu tana kallon Waleed suka zazzauna, sanan staff din suka shiga seat din tsakiyan motan, ahankali Waleed yarufe musu kofan yace “kutafi” Nura yaja motar sukabar wajen sanan batare daya kalli security ba yadaga kafanshi ahankali yafara tafiya yaje har inda motarshi yake pake ya shiga, “oya oya you are wasting our time ” cewan official din, ahankali yadaukey motar yasaka ya kunna motar ahankali yaja motar yana kallon marcopolo da yaranshi ke ciki suna kallonshi kananun namai bye bye, da sauri ya dauke kai, gate yayi yafito yanaso yama security magana kan ya sallamesu amman yakasa dan kuka zaiyi yawuce kawai yay hanyar gida baima gadi da kyau dan duhu duhu yake gani.
Ikon Allah ne kawai ya kaishi gida lafiya, parking yayi yafito daga motar yay flat din Ammi da sauri zuciyarshi namai nauyi tana wani irin rawa da hayaki, bude kofar falon yayi ya shiga baima tsaya maida kofan ya kulle ba yay stairs da sauri ganin Ammi bata falo, ahankali yabude kofar dakin Ammi ya shiga, Ammi na zaune kan doguwan kujeran dakin tana duba wata takarda tana sanye da shiga irin ta alfarma, jin an shigo dakinta ba sallama yasa ta dago kanta, hada ido sukayi da Waleed, ganin yanayin idanunshi yasa ta tsareshi da ido, baki Waleed ya bude cikeda zuciyanshi datamai wani irin nannauyan nauyi cikin irin sigan nan da yaro keyi idan zaikawoma mahaifiyar shi kara idan an cuceshi awaje yace “Am…….m….” kasa maganan yayi tsabagen yanda zuciyanshi ya kumbura kawai yataho dagudu yawani irin fada jikinshi Ammi yadaura kanshi kan kirjinshi yafashe da kukan da bata tabajin Waleed yay irinshi ba, cikin kuka sosai yace “Ammi mutuwa zanyi, Ammi daman haka akeji in aka maka shairi and bakada wata hanya dazaka nuna shairi aka maka ba gaske bane? Ammi na dan Allah nataba raping any yarinya tunda kika haifeni? Ammi tayaya zanyi raping mata ba daya ba, ba biyu ba, har guda takwas, Ammi sunce I rape 8girls” yawani irin fashe da kuka Ammi could feel yanda jikinshi ke bari tanajin yanda zuciyanshi ke bugu, cikin kuka sosai yace “Ammi please don’t let them take my orphanage from me, this is what I dedicated my life to, Ammi inason gidan marayu na with every part of my life, Ammi kinga king…..” yakasa magana sai kuka, kasa jurewa Ammi tayi dudda tana fushi dashi sosai, dagoshi tayi daga jikinta takai hannunta kan fuskarshi ta sharemai fuskan shi tace” Waleed menene? Calm down kamin magana da kyau, suwa suka maka shairin rape”? Hannun Ammi dakekan fuskarshi ya rike gam yace “Ammi please tell me the truth am I a bad person, kinga kin sanni sama da kowa, menama Arham? Ammi what have I done to Arham? Menamai? Arham yabude gidan marayun shi yasa an rufemin nawa, sanan ya kwashemin yaran gidan marayuna duka, yasa akamin shairi da kazafi, Ammi my heart is bleeding” kasa jure yanda Waleed ke kuka Ammi tayi duk juriyanta saitahau kuka dan her heart was shrinking dudda bataji labarin nashi in details ba but she clearly understands abinda Waleed keso yafada mata, cikin wani irin muryan so da tsantsan tausayi tace “Waleed Arham ne yay hurting naka to this extend”?
[11/1, 11:48 PM] Re@l???? K@usy ????: ???????? DUNIYA BIYU MABANBANTA???? ????