DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

???? TWO DIFFERENT WORLD????

       ✍️ M SHAKUR

This novel na kudi ne, idan kika karanta baki biya ba banyafe ba????????‍♀️

This novel is 500 Fanmily❤
How to Subscribe to TWO DIFFERENT WORLD
zaki turo 500 to account 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment to watsapp number na 07012181461, sainai adding naki a group din danake posting DUNIYA BIYU MABANBANTA

       3️⃣7️⃣


         Gyadama Ammi kai yayi yana wani irin kuka, yace "Ammi wai nai raping mata guda takwas, Ammi nataba ma any mace fyade eh Ammi?" girgiza mai kai Ammi tayi tanajan majina trying tahana kanta kuka ta girgixa mai kai takai hannayenta kan fuskarshi tana sharemai hawayen sanan tai cupping face nashi tace "Waleed nina haifeka nakuma raineka I know who is my son, nasan what you can do and wat u cannot do, Waleed nasan cewa bazaka taba yima yara mata fyade ba, bazaka tababa, Arham ne yamaka shairin nan kuma yama kanshi, zakaran da Allah ya nufa da chara ko ana ha maza ha mata saitayi, kadena zubar mai da hawaye come here Waleed dina" Ammi takama kanshi ta daura akan kirjinta tana bubbuga bayanshi tana wani irin kuka mara sauti hawaye, tamafi Waleed jin ciwon abinda ya samai, but yanzu he should calm down first yay shiru tukunna kafin taji full labarin abinda yafaru, takai almost 20min lallashin shi take, jinshi shiru yana sauke ijiyan zuciya ahankali yasa tagane bacci yayi ahankali taja cinyarta ta tashi tsaye tana rikeda kanshi a kirjinta kaman dan jariri sanan ta kwantar da kanshi ahankali kan kujeran tana kallonshi idanunshi sun kumbura sosai sabida kuka fuskarshi yay ja, same da lips dinshi dayay jajir sabida tsabagen kuka, tashi tayi ahankali tadauko bargon saman gadonta tadawo ta lullube shi da bargon sanan tadau wayarta tabude kofar dakinta tafita daga dakin kirjinta na tafarfasa, sauka tayi kasa tazauna kan dogon kujeran ta shiga contact dinta number Mama Iyami ta nemo tai dialing number, ringing daya Mama Iyami ta dauka, Mama Iyami zata fara surutunta Ammi ta tsareta tace "please Mama Iyami, abinda nakeso kawai shine ki sanar dani maiya faru banson surutu kaina ciwo yake sosai, ina jinki" ahankali Mama Iyami ta shiga mata bayanin duka abubuwan dasuka faru har zuwa kan address din da Waleed yatura musu cewa yanzu hakama suna gidan, shiru Ammi tayi duk tana jinta sanan ta sauke ijiyan zuciya tace "ok nagode zansa akawo muku kayan abinci sabida kudinga girki" "to Hajiya mun gode Allah saka da Alkhairi, sanan Allah ya fitar da Waleed ya wanke shi daga wanan shairin" katse wayan Ammi tayi ranta na boiling takira Mom, tana daukan wayan tace "kizo gida yanzun nan" katse wayan tayi direct takira number vice president din Nigeria Osijoban.

Ringing daya, biyu ya dauka yace “Hello Hajiya” “don’t call me Hajiya Osijoban” Ammi tafada da fushi sosai dan zuciyarta tafarfasa yake sosai tace “after all that I’ve done for you, banji kyashin baka all kudaden dakake bukata ba for you campaign, because my late husband kafin yarasu consider you his close one nima haka na dauka shine da ranka da lafiyan ka har alakama d’ana shairi sanan a kulle mai gidan marayu kayi shiru, no no no am disappointed and heart broken Osijoban” Ammi tafada kaman zatai kuka, cikin wani irin calm voice vice president yace “listen to me Hajiya, wlh ina shirin kiranki kenan kiranki ya shigo wayana, as am talking to you now yanzun nan case dinan ya shigo office dina, Ministry of Women suke incharge of orphanage sunada wanan ikon su kulle duk wani gidan marayu dake harka mara kyau, danaga gidan marayun d’ana ne Waleed raina saida yabaci, namasa acema Minister inason ganinta yau yau dinan bama gobe ba, and I will promise you one thing, kibani lokaci kalilan sabida dole ayi bincike bazan iya kawai nace baza’ayi binciken ba, amman kibani nan da 30days namiki alkawarin zan budemai gidan marayun shi, da ace nasan kan case din kafin su yanke hukuncin nan dana hana amman sai yanzu nake sani, I will do everything in my power nabude mai gidan marayun nan for now ki kulada shi kinji Hajiya, take care okay, sai gobe” ahankali Ammi tacire wayan daga kunnenta ta katse sanan ta ijiye tanaso takira Maman Arham amman saitaga enough sunma kansu but wlh tayi alkawarin zatai maganin Arham, tana cikin tunanin Mom tabude kofa 5a shigo tana rikeda hadaddiyan jaka tayi kyau sosai tana ganin idanun Ammi tagane da wani abu da sauri ta ijiye jakanta kan centre table takaraso kan kujeran da Ammi ke zaune da sauri ta zauna takai hannunta kan wuyan Ammi tace “Adda bakida lafiya ne eh? Maisa idanunki sukai ja haka kaman kinyi kuka”? Ajiyan zuciya Ammi ta sauke tace “idan da zanga Arham yanzu zan iya shakeshi sainaga yana gab da shurawa zan sakeshi, an rufema Waleed gidan marayunshi! Da sauri Mom tace “what” gyadamata kai Ammi tayi tana cijan lips tace “not just that yahada ma d’ana shairi kala kala, ciki harda yay raping yan mata guda 8, can you believe yaran sun fito sunyi confessing wai Waleed yay raping dinsu da gaske agaban kowa harda kuka” ahankali Mom tace “innalillahi wa innailaihi raji’un” ahankali Ammi tana wani irin kallon Mom tace “ance Waleed na saida yara, yana trafficking yaran gidan marayun and maltreatment, Waleed told me an kwashe yaran an maida su gidan marayun Arham shima wai yabude gidan marayunshi” kasa magana Mom tayi wanan lokacin sai

Kallon Ammi take jikinta yay morethan sanyi, cikin wani irin yanayi Ammi tace “ban taba son abotan shi da yaron nan ba daidai da sau daya, kullum sani kike nadinga ma Arham dariya tunda d’ana nason shi amman ban iyawa, kaman Allah ya nunamin nan gaba zai yaudari d’ana ne, Arham ya yaudari Waleed bakadan ba, he uses my child weakness against him, he cheated my son, ya yaudari yarona” tai maganan tana girgiza kai, ahankali Mom tamika hannunta takama hannun Ammi tace “Ammi listen to me, nasan halinki sosai, I know yanzu haka zuciyanki na kitsa miki abubuwa da dama, I want you to calm down Ammi, ba’a rama mugunta da mugunta, ba’a rama cuta da cuta, nasan yanzu haka duk inda Arham yake yana tunanin bama hakaba yana expecting zuwanmu for revenge ko rashin mutunci, Ammi kinajina please wanan karan ki sauraran, tunda dai Allah ya nuna mana wayeshi, sanan Allah yabude mana ido harda da Waleed munsan waye Arham din mubarshi da Allah, kome yama Waleed yama kanshi, ni to me da Waleed ma yahakura da gidan marayun dudda passion dinshi ne yana ma mahaifinshi ne but kawai yakoma normal hospital yafara aikinshi still lada zaikai ga Abba, yabar Arham da halinshi, yana kanshi yaci amanar kanshi, ya manta dashi da abinda yamai and move on, ga yaron shi chan, jibi suna yakamata yaje yagansu kiyakuri Adda na” shiru Ammi tayi tana kallon Mom ko kadan batason ta hakura tanason ta gwadama Arham ba’a taba mata yaro a zauna lpy amman kuma tana tunanin maganganun Mom, wani irin ajiyan zuciya ta sauke ya jingina da kujera ta lumshe ido takasa daina tunanin abinda Arham yama Waleed, takasa daina tunanin yanzu Waleed baida gidan marayu yanzu Arham ne mai gidan marayu da yaran gidan marayunshi. Ajiyan zuciyan takara saukewa hakan yasa ahankali Mon ta rungumeta tace “ya isa Adda I know what you are going through is okay, kiyakuri Allah natare da masu hakuri duk wanda ya cuceka kanshi ya cuta Adda so kibarshi da halinshi” haka Mkm ta dinga bama Ammi baki harta saukko sosai, suna zaune nan akasa sukaji anbude kofar dakinta daga sama da sauri Ammi da Mom suka daga kansu, Waleed ne yafito idanunshi sun kumbura suntum da sauri Ammi tai hanyar stairs din tace “Son katashi” tai maganan tana mika hannunta tarikeshi ahankali tace “katashi Waleed” gyadamata kai Waleed yayi yana kallon Mom dayagani biyeda Ammi tana kallonshi murmushi ya sakin mata yace “Mom kinzo” gyadamata kai tayi ahankali tace “nazo Dan Yaro na” ahankali yake saukowa daga stairs din tareda Ammi, murya chan kasa yace “Mom yunwa nakeji” Ammi jitayi kuka yazo mata tuntuni fushi take dashi tasan baya wani cin abinci yan kwanakin nan tunda yafadi da bakinshi cewa yunwa yakeji dat means yaji yunwa sosai dan Waleed bayacin abinci sosai, muryan Ammi na rawa sosai tace “sh…..shiga kitchen ki dafamai abin…..abin….d….yakes…..” kasa karasa maganan tayi saikuma tafashe dawani irin kuka Ammi tayi da sauri tasaki hannun Waleed zata koma sama dan batason yaga tana kuka rike mata hannu yayi gam ahankali yace “Ammi” fadawa jikinshi tayi tasaki kuka tace “Waleed I am sorry, nima I abandon you jibi yanda kakejin yunwa eh, you have been going through alot Waleed wlh ban kula dakai yanda yakamata ba inda nayi da non of this would have happen to you” girgizama Ammi kai yayi yadagota share mata fuska yayi yace “shiiii Ammi don’t cry, idan kina kuka I will break down Ammi, you are my strength, please kidena kuka if anything happen to you bazan yafema kaina ba, stop crying kinji Ammi na” gyadamai kai tayi tana kara share fuskarta, ahankali tace “Arham hurt you Waleed” hannun Ammi yarike yace “Ammi kidena maganan Arham, abinda yamin hurt me deep but such is life nayi imani da kaddara mai kyau da mara kyau, please ku manta da komi kima dena kiramin sunan shi, I want to forget everything and move on Ammi, kinji” gyadama Waleed kai tayi, Waleed yakama hannunta sukai dinning, Mom kuma ta share gajeren hawayen daya zubo mata tai kitchen, spaghetti kawai ta dafa musu hadadden gaske, sosai Waleed yaci yanuna ma Ammi babu abinda ke damunshi duddan karsu damu itada Mom, saida yaci ya koshi sanan yatashi yace “bari naje nai wanka” murmushi Ammi tayi tace “ka shirya gabaki daya kawai sai muje muga Ilham da Baby mukai musu kayan suna ko” gyadamata kai yayi kawai yawuce yafita, duk suka bishi da kallo.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Leave a Reply

Back to top button