DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

Wuraren 8 nasafe yake bude idanunshi ahankali, akan kyakkyawan fuskarta yasauke ido baccin ta take fuskarta na facing nashi akasa har lokacin tana lullube da bargo tai wani fayau, lumshe ido yayi yana kokarin hana kanshi tunanin jiya sanan yatashi zaune ahankali ya kalli agogon dakin ganin 8 nazafe yasa da sauri yay jumping yatashi yay bathroom brush yayi da sababbin brush da toothpaste dake bayin sanan yadauro alwala yana kallon kayanshi dayagani har yanzu ajike dan babu wani iskan kirki, tunani ya shiga yi yanda zaiyi da sauri laundry yafado mai arai, dakin yakoma yakira reception ta landlines kan aturomai lubdry services, sanan ya ijiye ya koma bayi ya kwaso duka kayan harda pj shi daya bata tasaka jiya sanan yafito daidai ana knocking budewa yayi yabasu yace “ayi drying a kawomai yanzu” karba sukayi suka tafi ko minti 30 basu bataba suka kawomai karba yayi sanan yamaida kofar yarufe, riga da wandonshi ya saka sanan yay salla ya idar yana azkar ya jingina da bango yana kallonta kaman yau yafara ganinta, he just wish inama halaliyar shice dayaje ya kwanta akan gadon nan and have her to his content, yana cikin yan tunane tunanen tabude fararen idanunta kaman wayanda aka wanke su da madara ta daura akanshi kaman dachan idanunta biyu, ganin kyakkyawan fuskar Waleed zaune jikin bango yana kallonta yasa tasakin mai wani cute smile she is so fund of him, tana bala’in sonshi, ganin tana shirin tashi zaune yasa da sauri yadauke kanshi dan baison yaga anything dazai tadamai da hankali, bakinshi na dan rawa yace “g……go to the bathroom and shower kizo kiyi salla” yay shiru yana mugunjin nauyin yacemata tai wankan tsarki dan yasan gabanshi yataba gabanta but yanzu ma zai iya koyamata ne yakaita gidan Mom, Mom takoya mata, yansan then idan yakaita gidan tahadu da yaran Mom dan Mom nada mace daya dake ss3 yanzu kuma yadawo gida hutu dan boarding school take zata iya magana zai mata kawa da Asma’u, Ma’un Mom, jin karan kofa yasa yagane tabude bayin shiga bayi tayi dan fitsari takeji sosai, tashi yayi da sauri ya shiga tattare kayanta dayacire ya yarda mata akasa sanan yadau jakan yabude yaciro mata wani gown da pant mai kyau sanan yay wajen kofar bathroom din dan yasan zata iya tafito daga bayi tahau kuka in bataga shi ba, dan knocking kofar yayi yace “Saheeba am coming wanna go get you some things outside” yajuya da sauri yafita daga dakin, kasa yasauka yay waje wajen motarshi yasan Ammi takulirashi sama da sau dari, shiga motar yayi yazauna yadau wayarshi 28miss calls yagani all daga Ammi, dan ajiyan zuciya ya sauke sanan ya shiga number Mom yay dialing, ringing daya Mom ta dauka tace “Dan Yaro haba kaiko yanzun nan Adda takirani akan kafita tsakar dare batasan inda kaje ba tana kira kuma baka dauka” dan murmushi yayi yace “wayan na mota ne, I will call her now, Mom are you at home”? “eh ina gida, da zama muzo gidanku ne nida Asma’u sunyi hutun makaranta daganan saimuje gidan suna” dan yatsine fuska yayi shiyama manta yaune suna, anatse yace “Mom karku fita please kijirani yanzun nan zanzo” yana maganan ya katse wayan yakira Ammi, ringing daya ta dauka kafin tai magana yace “Ammi am fine, gidan danakai su Mama Iyami Arham yaje tsakar dare suka kirani shine natafi” Ammi zata fara magana yace “nan bada jimawa bama zanzo bye Ammi, love you” yay maganan tareda katse wayan, tada motar yayi yafita cikin gari ya shiga ya nemo mata wani hijab dark blue yadi uku da aka dinka sanan yadawo yay cikin hotel din.

Kofar dakin yabude hada ido yayi da ita tana zaune kan gado tadauki wani littafi tana kallo, tana ganinshi ta washe baki sanan ta tashi da gudu tai kanshi zata rungume shi, hannunshi yadaura kan kafadarta ya tsayar da ita yace “wait Pretty, come and wear this hijab lemme see you” yay maganan yana warware hijabin hannunshi yasaka mata, wani irin bala’in kyau hijabin yamata da saida ta tsaya yay shiru yana kallonta saikuma yaciro wayanshi daga aljihu yace “smile lemme snap u” murmushi tamai daya mugun lobar da dimple dinta ya dauketa hoto tai wani irin kyau, sanan yamaida wayan aljihu, silipas ya tsugunna ya ijiye mata kafarta ta zura tana dafamai kafada sanan yatashi ya kwashe kayansu tass da ba yawa ajakan boutique din kayan daya siyo mata sanan suka tafi, a reception ya tsaya yana rikeda hannunta kafin ta gudu wani wajen yay clearing all bill dinsu sanan suka fito, gaban motarshi yabude ya sata ciki yamaida kofar yarufe sanan yakoma mazaunin direba ya shiga tareda wurha kayansu baya yaja motar yamusu playing soft music a motar, juyarda kai tayi sai kallon hanya take tana kallon motoci kaman bata taba gani ba, shi abinma har mamaki yabashi yanda taketa kallon motoci da gari sai kuma yatuna all this while yaune rana na farko datake ganin cikin gari, ahaka har suka shigo anguwan su Mom, horn yayi agaban gidan aka budemai gate yaja motar cikin gidan yay parking ya kashe yafito.

Zagayowa yayi yabude mata motar tafito ahankali tana kokarin rikemai hannu ta daure fuska yace “don’t touch me” turomai baki tayi kaman zatai kuka yadauke kai da sauri ganin nema take tasa ya daburce tana wani turomai small pink lips dinta da har yanzu ganin yanda ya tsotsesu jiya yake. Gaba yayi da sauri yace “let’s go” ahankali take biyoshi tana turo baki, kofa yabude ya shiga falon yajuyo yana kallonta har lokacin turomai baki take ta shigo dakin kaman zata burgeshi dan murmushi yayi yanajin wani shegen sonta a ranshi yabiye mata kwarkwancewa zaiyi kaman ita, kawai yasa hannu yamaida kofan yarufe ya shigo falon daidai Asma’u tafito daga dakin Ya Abdul asama data kaima coffee tana sanye da wata doguwan rigan atampa yellow itama batada kiba siriruwa ce kaman Widad saidai Wudad tafita tsaye dan ita doguwar mace ce , tana hango Waleed tawani irin kwala ihu. “Ya Waleed!” dagokai Waleed yayi ya kalli sama, dawani irin gudu Asma’u ta shiga saukowa daga stairs dan arayuwanta tanason Waleed yafiji da ita a family su gabaki daya. “oyoyo Ya Waleed” tana zuwa gabanshi tawani daka tsalle ta rungume shi tana murna sosai kaman anmata kyauta, Widad da tun lokacin datai ihu take binta da kallo ta tsaya chak tana kallon yanda ta rungume Waleed tana murna, ranta ne yabaci tazo gaban Waleed din hannu tasa ta fizgo bayan riganta da sauri Asma’u ta sauko daga jikin Waleed tana waigowa dan taga waye ya fizgota, da sauri Widad ta shiga gaban Waleed takama waist dinta tarike tana turoma Asma’u baki tana zaro mata idanu, mutuwan tsaye Waleed yayi yana kallon Widad din yama kasamagana, sai Asma’u data bita da kallo ne kaman zata cinyeta tana kallon Widad still tace “Ya Waleed wacece wanan kyakkyawan yarinyar? Sorry matan? Ko itane matan da Mom tacemin ka aura kasan har yau bantaba ganinta ba duk innazo hutu bansamu naje gidanka saidai wajen Ammi na, itane Ya matarka Ya Waleed”? Ganin yanda Widad tai tsayin daka a gabanshi har lokacin rikeda kugu tana hararan Asma’u yasa da sauri yaja hannunta yazaunar da ita akan kujera yace “sit down, she’s my sister, her name is Asma’u but we call her Moxi, she is your friend kinji” makemai kafada tayi tana kallonshi idanunta sun ciccika da hawaye sosai kaman anbude pampoo, wani iri yaji saikuma yaji badadi yajuyo ya kalli Asma’u dake tsaye kansu yace “common kin isheni da tambaya aku, go call Mom kice mata nazo” gyadamai kai tayi tajuya da sauri ta tafi shikuma yajuya yamaida hankalinshi kan Widad dahar hawayen sun zubo da sauri yakai hannunshi kan idanunta yashare mata hawayen cikeda damuwa yace “don’t cry please, she is just my sis, don’t cry okay come here” yajawo kanta yasa a kirjinshi ahankali tasaki kuka harda tarin kuka abin ya mugun bashi mamaki sai duk yaji ba dadi, yashiga jijjigata, murya chan kasa ta yanda dagashi sai ita zasu dinga ji cikin harshen turencin wanda daman dashi kadai yake mata magana danshi kadai yaga tana fahimta yace “stop crying Pretty, I love you so much and you are the only one in my heart, I will never do anything that will hurt you, now clean your tears banso mutane suga kina kuka” yadagota daga jikinshi yasa hannu yagoge mata fuskar idanunta har sunyi jajir, daidai lokacin Mom tafito daga daki itada Asma’u dake bata labarin kyakkyawan yarinyar data gani tareda Ya Waleed, saukowa Mom tayi tazauna akan kujera tana kallon Widad tace “Dan Yaro harka iso” gyadamata kai yayi yace “good morning Mom” sanan ya kalli Widad yace “greet my Mom” ahankali tadago kanta murya chan kasa tace “good morning Mom” murmushi Mom tasaki tace “morning yarinya, yaya sunan ki”? Ahankali Waleed yace “batajin hausa, Mom please sata dakanki tabi Asma’u suje sama” sanan ya kalli Moxi yace “ki kaita dakinki, help her out tai wanka kibata kayanki zasu mata tasaka sai kizo kihada mata breakfast, mostly fruits tafisha sai yogurt batacin all this heavy food for now, Mom talk to her” yay maganan ahankali, tasowa Mom tayi tazo har wajensu ganin Waleed yadamu da ita tasan yarinyar must be very special, anatse takai hannunta ta shafa kan Widad cikin turenci tace “kibi Asma’u takaiki kije kiyi wanka kinji” juyawa tayi da sauri ta kalli Waleed gyadamata kai yayi ahankali sanan ta tashi, da sauri Asma’u tamika mata hannu tana murmushi tace “ke baki sona niko wlh bakiga yanda nake sonki ba, muje dakina kiga dakina kiga, inada abubuwa da yawa, kinga Ammi na tamin sababbin dinki jiya ta aikomin dasu nabaki daya cikinsu kisaka kema?” gyadamata kai Widad tayi dan tagane metace sabida da turenci tai maganan sukai sama binsu Waleed yayi da kallo harsaida suka bace sanan yajuyo ya kalli Mom da tuntuni kallonshi take, kafin ma yay magana tace “who is she?”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Leave a Reply

Back to top button