DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

Ahankali yace “I want it so simple banson any event ko taro, kawai daurin aure kadai nakeso”
Anatse Uncle yace “is fine, bayan haka saikuyi signing marriage certificate”
Gyadakai Waleed yayi cikeda gamsuwa.
Uncle yace “will talk to you later son, bye I love you”
Ahankali Waleed yace “I love you second Dad”
Murmushi Uncle yayi ya katse wayan, Waleed yawani fada gado tareda daura wayan akan kirjinshi zuciyanshi tai fari kal, dan yasan tunda uncle yay na’am to kaman ya auri Widad ne yagama, tashi yayi yacire kaya ya shiga bathroom yayi wanka, fitowa yayi ya shirya cikin wani 3-quarter yasaka farin singlet ya feshe kanshi da turare sanan yazura silipas yafito yay flat din Ammi.
Babu kowa a falo sai TV dake aiki hakan yasa yay sama, bude kofar dakin Ammi yayi cikeda farin ciki yana kallon Ammi dake kallonshi tana zaune kan kujera rikeda system, murmushi yayi yamaida kofan yarufe yakaraso inda take zaune, hannu yasa yadauke system din ya ijiye akan gado yace “Ammi system dinan baisan nan cinyanki wurina bane” murmushi Ammi tayi ganin yana cikin nishadi ya zauna kusada ita tareda rungumeta ta side yace “oyoyo Ammi na good morning” “morning Son, yau sunan danka, kako kirasu” girgiza mata kai yayi yace “no sai anjima da yamma” gyadamai kai tayi tana kallonshi kaman maison karanto abu a fuskarshi, dauke kai yayi da sauri yatashi yadauko system dinta yadaura kan cinya shi yace “aikin me kikeyi Ammi natayaki” hannu Ammi tasa ta karbe system din ta ijiye gefenta tace “talk to me Waleed, there’s something strange about you today? Why this sudden happiness kaida kake cikin kunci, menene ke faruwa dakai eh Waleed dina?” shiru yayi yana kallon fuskarta ba abin yafada mata bane tahau mai bala’i gwara Uncle yafadi mata saitamai bala’in inzata iya, kuma once uncle yace sai danshi yay auren sai yayi. “Son” Ammi takirashi ahankali tace “menene?” dan jim yayi saikuma yace “aure nakeson nakara Ammi zaki yarda”? Wani irin kallo Ammi tamai irin kallon mehaka kake cewa kaman wani mara hankali, dauke kai yayi yamaida kanshi kan TV dakin yace “daman nasan bazaki taba yarda ba, bazaki taba barina ba, saisa nakira Babana nafadamai” wani irin kallo Ammi tamai tace “Waleed in the middle of crisis, kana cikin matsalolin nan an kwace ma gidan marayu shine all you could think of shine kara aure, are you even okay” cikin wata irin cool voice yace “Ammi aure nakeson nakara, please” yay dan shiru sanan yace “Ammi I don’t wanna go into details dake but please Ammi aure nakeson nakara ki barni, at least my first marriage namiki abinda kikeso yanzu ki barni na auri wacce nakeso kinji” cikin dan kakkausan murya Ammi tace “Waleed do you even realise you are just 28 ko 29yrz bakakai ba dahar zaka ijiye mata biyu, angayamaka kanada karfin ijiye mata biyune” cikin yanayin dan fushi yace “Ammi nifa namiji ne shine kuma banda karfin managing two wives, Ammi I love her kinji, kina hanani wlh zan iya mutuwa” wani irin kallo tamai irin na yaronan lafiyanka kalau kuwa, hannunshi yamika ahankali yakama hannunta sanan ya shiga bata labarin komi na Widad har zuwa abinda yasameta jiya da daddare, sosai jikin Ammi yay sanyi, Waleed yace “Ammi what if kece kika haifeta, can you imaging me in this life datake ai zakizo ataimaken ko, Ammi that girl needs care, banda haka ina sonta Ammi so sosai, please Ammi inhar kinasona dagaske ki yarda kika yarda ni kinmin komi dan girman Allah Ammi” yay maganan yana rokonta, ganin seriousness din dake idanunshi da tsantsan sonta, dakuma tausayin yarinyar dataji tanaji yasa ta sauke ijiyan zuciya, ahankali tace “Waleed inhar bantayaka son abinda ka kawo kace kana soba menayi, kawai kaga ukuba da dama ne ciki harda Arham, karyazo Arham yaturo yarinyar tama wani abu, but tunda kana sonta shikenan zan kira Mom takawo yarinyar nan itada Ma’u duk saisu zauna anan inyaso saita dinga zuwa islamiyyan su Ma’u, Wata daya za’a saka shima sainai magana da Baffan ka kome yace haka za’ayi” wani irin fadawa jikin Ammi yayi sanan ya manna mata kiss a goshi yace “I love you Ammi thank you” ahankali Ammi tace “but da sharadi” da sauri ya gyara zama, Ammi tace “banson kana zaman gida, zakaje kadinga min managing company na for now harsai an maidamaka da gidan marayun ka, sanan zaka koma chan gidanka, kaje ka gyara inda zaka gyara amaryanka, inhar Amaryanka na nan bazaka dinga zuwamin gida anyhow ba, kaida ka kara ganinta dagayau sai in ankaita gidanka” da sauri yace “na yarda Ammi” dan acewanshi ganinta inhar tazo gidan Ammi abu mai sauki ne, murmushi Ammi tayi tace “kasami lokaci kaje kasami Ilham kafadi mata sanan kamata kayan fitar kishiya, kazama mai adalci” dan shiru yayi yana tunani sanan yace “Ammi is a simple wedding, banson any taro, zan mata kayanta na ijiye mata inta dawo daga wanka I will te her Ammi” shiru Ammi tayi tace “tadaiji daga bakinka, ina zuwa bari naduba yan aikina nasasu min aiki” tai maganan tana tashi daga kan kujera tafita daga dakin, wani irin tsalle yayi kaman dan yaro yafada gadon Ammi, he never knew haka akeji idan zaka auri love of your life, all this excitement baijisu ba dazai auri Ilham ba sai yanzu, da Ammi ta yarda kaman an bashi kyautan kujeran makka.
Washe garin ranan Mom da Asma’u da Widad sukazo Waleed baya gida dan tun safe Ammi takadashi company ta, sosai Ammi tadinga kallo Widad da saida Mom tasata ta gaida Ammi ta gaidata sanan takoma wajen Asma’u dake zubamata uban surutu kaman gidan radio, sun dade zaune afalon sanan Ammi ta tashi tai sama Mom tabita, dakin Ammi suka shiga Mom biyeda ita, zama Ammi tayi kan gadon Mom ma tazauna tace “kinga yarinyar ko? Batada matsala Adda, komi sai wanda ka koyamata zatayi and nalura she is very sharp, yau Asma’u na koya mata karatun Al’qur’ani tacigaba dayi da kyau, wlh dadin muryanta saida yasa nafito daga dakina da asuban nan na shigo dakinsu, kinga abubuwan data iya kuwa, magana ne kawai bata waniyi saida Asma’u, but she is good Adda” ajiyan zuciya Ammi ta sauke tace “indai Waleed na sonta shikenan, yarinyar namin yanayi da….” Ammi tai shiru bata karasa maganan ba da sauri Mom tace “dawa take miki yanayi?” dan yatsine fuska Ammi tayi tace “never mind kawai raina ke kirfamin hakan, but basa yanayi, zan baki kwangilan akwatin ta kinji afara shirye shirye, kima mai gyaran jikin nan magana” gyadamata kai Mom tayi tace “angama Adda” sosai suka dade sai plan suke, sai wuraren magrib ta tafi sukuma Ammi tabasu hadadden daki.
Wasa Wasa lokaci ke tafiya, time to time Waleed ke zuwa yaduba Ilham da little Arham dudda har yanzu bai gayamata cewan zaiyi aureba, yayinda rabonshi da Widad tun ranan dayabar gidan Mom, babu yan dabarun dabaiyiba akan zai ganta amman Ammi tahana, Widad sai gyara takesha, yanzu tana dan hira sosai, ta mugun sabawa da Asma’u, akwai randa Asma’u taje gida tadawo batajeda Widad ba sabida shegen ciwon maran datake yi dahar saida Ammi tasa aka kawo mata maganin ciwon mara tasha, Asma’u nafita tadinga rusa uban kuka Ammi nata kallonta, kaman ranan tafara ganin yarinyar, charisma din yarinyar na nuna kaman yar baBban gidace sanan tanada shagwaba, da kyar ta samu ta lallasheta ajikin Ammi tai bacci.