DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

         ✍️ M SHAKUR 


                     6️⃣

_*This novel is for free. Wanda mu Kungiyan FREE HAUSA NOVELS WATO BANZA *ASSOCIATIONS* muka dauki nauyin kawo maku.

Page 6

MOHAMMED V INTERNATIONAL AIRPORT, MORROCO.

Karfe shida na safe daidai jirgin British Airways ya sauka a airport din Mohammed VI, sai kataniyar saukowa passinger suke daga cikin jirgin kana ganinsu kasan they’re all stressed out sun gaji iya gajiya, saida kusan kowa yagama saukowa daga cikin jirgin sanan ahankali wata yar doguwan matashiya tasawo kanta tawajejen kofan zata fito tana goye da jakar makaranta abayanta tarike igiyoyin gefen jakan gam da hannunta, farace sol yarinyar tana sanye da wata bakar doguwan riga mara kwalliya ko daya ajiki jallabiya, sai gyalen ta datai rolling aka sai abin yay kaman hijabi dudda hakan bai hana bakin suman gaban goshinta bayyana ba sun mugun kwanta sunyi lublub kaman na yar jaririyan da aka haifo yau, tanada manyan idanuwa fararen fat da brown kwaiduwan ido dan ko kadan nata ba bakake bane brown nesu light brown, giran ta full da gashi baki mai shining kaman ta sakamai relaxer, gawani siririn dogon hanci daya ratsa tsakiyan fuskanta ya bala’in karamata kyau, lips dinta pink yirr yan fele fele kananu kaman na yaron da aka haifa yanzu yanzun nan. Sake rike igiyan jakan datake goyedashi tayi gam, ahankali ta lumshe ido iskan garinsu yawani kada mata fuska tasaki murmushi daya lotsar da dimples dinta na both sides, dama da haggu sun lume chan ciki sosai kaman rijiya tai wani irin kyau da ba’a iya misaltawa sanan tabude idanun ahankali kafin tadaga yar kafarta tafara saukowa daga kan matattakalan jirgin tana kallon ko’ina ganin bataga yan gidansu ba daidai da mutum dayaba yasa taji wasu hawaye sun taho mata masu dumi, ahankali takai hannunta kan fuskarta zata share hawayen kaman daga sama taji an kwalamata kira. “Widad! Widad!” wani irin juyawa tayi da saurinta, wata mata tagani ita kadai tadan manyan ta sosai dan akalla zatafi 70 yar tsohuwa ce tana sanye da doguwan riga itama da hijabi daya tsaya mata aciki tana tahowa da dan sandanta a hannu, wani irin tsalle yarinyan tayi hawayen suka karasa zubowa cikeda murna cikin harshen larabci tsohuwan tace “ahlan wa sahlan wa marhababik Widad” cikin wani irin muryan kuka yarinyar da tsohuwar takira da Widad tace “Assalamu Alaykum Amah” holding shoulders nata taohuwan tayi sanan tai kissing left cheek nata sanan tamata ana dama tana murmushi cikin tsantsan farin ciki da tsantsan so takara mata another peck a forehead tace “waallaykumus salam Widad, kaif? (how are you)” juyawa tayi tana kallon ko’ina na filin Airport din kaman mai neman wani abu tace “Alhamdulillah Amah” ganin yanda take kalle kalle yasa tsohuwar tai murmushi sosai batare datace mata komiba tabarta tacigaba da kalle kallenta, tana cikin kalle kallen kaman mai neman wani abu taji anrike mata hannu gam wani irin ajiyan zuciya ta sauke ta tsayar da kanta chak kafin ahankali lebbbenta suka furta “Ab…..Aby” dawani irin sauri ta juyo kaman amafarki, wani magidanci ne tsaye a bayanta yana rikeda hannunta yana sanye da jallabiya fari fat, kafanshi sanye da skos na maza, sai kanshi daure da rawanin larabawa sai farin gilas a idanunshi da daga gani kasan na kara karfin ganin idanune, kana ganinshi kaga tsantsan balaraben morroco kyakkyawa ajin farko, wani irin fashewa da kuka tayi haka Allah yayi ta tanada saurin kuka, very emotional mutum ce ita, sanan duk duniya batada wanda takeso kaman babanta saisa kodaga nesa takanji a jikinta yana kusada ita, fashewa da kuka sosai tayi tace “Abyyyy” anatse magidanci yasakin mata wani kyakkyawan murmushi yakai fararen hannunshi yadaura kan fuskarta ya share hawayen datake tass kafin yarungumeta ahankali yana bubbuga bayanta anatse irin na manya dinan cikin muryanshi na dattawa yace “marhababik, marhababik” sunkai kusan 5min tana jikinshi har lokacin tana sheshekan kuka sanan yadago ta, hannayenshi yasa akan fuskarshi yay cupping face dinta cikin tsantsan so yace “kidayra? (how are you)” ahankali tace “Alhamdulillah Aby” gyadamata kai yayi yace “masha Allah” yanuna mata mutanen dake tareda shi alamun ta gaidasu, ita sai a lokacin nema ta lurada su dazu mahaifinta kawai idanuwanta suka gane mata, yangidansu ne dan gidansu family house ne babban gaske, wata balarabiya dake kusada mahaifinta ta gaida ta hanyar cewa “Assalamu Alaykum Um” sanan ta kalli sauran tacemusu “Assalamu Alaykum” amsata sukayi ko wanne da murmushi kan fuskarshi banda matar dake kusada mahaifinta dako amsata batayiba, cikin harshen larabci mahaifin nata yace “mutafi gida” kasancewan ansan koshi waye agarin saisama aka bari suka shigo har filin jirgin yasa suna zuwa akaimata clearing komi suka shiga wasu manya manyan jeep farare sukai gida, itadai tana cikin na mahaifinta kusada shi sai matar data kirada Amah gefen ta, mahaifinta kuma na gaba da direba, sukabar airport din.

Agaban wani babban tangamemen gida sukai parking, irin gidan nan da aka ginashi na usulin culture larabawa, an zagaye gaban gidan da flowers iri iri daban daban kalolinsu kaman kazo ka kwasa ka gudu, tun kafin tafito daga cikin mota takejin sautin ganga na mandiri ana bugawa ana wake, murmushi tayi ta kalli mahaifinta cikeda so duk lokacin dazata dawo daga school sai Aby yahada mata walima na kayatarwa daban mamaki dan tarbanta kadai, bude kofa tayi tafito sanan tamikama kakanta hannu tafito daga motan Aby yafito yana kallonsu, kowa ya sassauko daga cikin motar akai cikin gidan, babban compound ne da girman tsakar gidan zaiyi girman primary school ana raye raye ana wake ana, ana rawa, ganin Widad din da iyayen ta sun shigo yasa mawakin yataho gabansu da yan amshin shi suna buga mandiri suna rera wake yace “kaifa Anti? Wa kaifa ji’iti? Marbabiki Ya Widad binti Othman Benjalloun” wani irin murmushi tayi ta washe fararen hakoranta tana kallonsu tana kara rike igiyan jakan makarantan ta abubuwa like this nabata peace sosai yanasa tana tunawa da mahaifiyar ta, ahankali mahaifinta ya kalli fuskarta murmushin dayagani kwance kan fuskar yasa yaji hankalin shi ya kwanta sosai, flowers ya karba a hannun daya daga cikin ma’aikatan gidan sanan yazo ta gabanta yabude flower ya sanya mata flower a wuyanta cikin harshen turenci dakeda Arabic intonation yace “wercome bark homer Widad” rungume mahaifinta tayi tana murmushi sosai tama kasa magana, ganin abun nasu bamai karewa bane yasa Amah cikin harshen larabci tace “to mayyar mahaifinta tadawo fa yanzu mun shigesu, saki ubanki muje daki kiyi wanka kizo ki chanza kayan nan kizo kici abinci ki kwanta kiyi bacci” Amah tai maganan tanajan hannunta, binta tayi tajuyo tama mahaifinta waving hannu sukai cikin gida, dan murmushi mahaifinta yayi yajuyo ya kalli matarshi datai kini kini darai cikin harshen larabci yace “kawomin shayi dakina” yay maganan tareda wucewa yashiga wani wakacecen falo irin traditional falon larabawan nan namasu kudin gaske, babu kujeru adakin sai wasu irin filulluka hadaddu set set da ake kishigada akansu gawani wargajejen hadadden carpet daya zagaye ko’ina a falon sai uban laushi kaman da fatar jarirai akayi sai shisha pot asalin pot din na larabawa, dan daidaikun asalin gidan rikakkun balarabe ne zakaje da bazaka ga shisha pot a dakunan su ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Leave a Reply

Back to top button