LabaraiMata Da Miji

Wannan Sune Mata Da Miji da Suka Kashe Wata Mata Suka Yanka Kanta Suka Sayar Naira Dubu 70

Wasu mata da miji mazaunan Abeokuta, Kehinde Oladimeji mai shekaru 43 da matar sa Adejumoke Raji mai shekaru 35, waɗanda aka kama da sassan jikin ɗan adam sun bayyana yadda su ka tafka wannan mummunan aika-aikar. Jaridar Daily Trust ta ruwaito

Mata da mijin da ke rayuwa a No 72 MKO Abiola Way, Leme, ƙaramar hukumar Abeokuta South ta jihar Ogun, an tasa ƙeyar gaban ‘yan jarida ranar Litinin.

Mijin ya bayyana yadda matar da halaka ƙawarta

Da ya ke magana da manema labarai, mijin ya bayyana cewa matarsa ta halaka ƙawarta, ta yi gunduwa-gunduwa da gangar jikin sannan ta siyar da kan ga wani ɗan kasuwa mai suna Oluomo, mazaunin Ibadan a  jihar Oyo akan kuɗi N70,000.

Oladimeji ya ce:

Akwai wata ranar da matata ta gayyato ƙawarta zuwa gidanmu. Ta zo ranar Talata sannan ta koma a ranar. Amma a rana ta biyu da ta dawo, ranar Alhamis ce. Matata ta dafa mata indomie da ƙwai wanda ta cinye. Daga baya ta shiga banɗaki inda tayi wanka.

Da naga dare ya nayi, sai na tambayi matata lokacin da ƙawarta za ta tafi, amma sai matata ta ce yarinyar ta gaji ta ce tana son hutawa. Sai na koma na zauna a bayan gida, lokacin da na dawo ɗakin, na fahimci cewa matata ta halaka ƙawarta sannan tayi gunduwa-gunduwa da jikinta.

Haka kuma, ina da wani aboki a Ibadan wanda aka fi sani da Omo Baale. Ya faɗa min cewa yana son kan mutum. Matata taji hirar mu inda ta tambayeni nawa zai biya, na  gaya mata a shirye ya ke da ya biya  N70,000. Ban san cewa matata har ta gama yanke shawara ba.

Matar ta ƙaryata zargin da ake mata

Sai dai matar ta ƙaryata kisan budurwar inda ta ce “bani da masaniya akan lamarin” sannan ta kalli mijin ta ce masa “ka dai na yi min sharri”

Sai dai, ta tabbatar da cewa abokin mijinta, wani mai suna Michael, ya ba su wani buhu wanda daga baya su ka fahimci cewa akwai sassan jikin mutum a cikin sa.

Hukumar ‘yan sanda ta tabbatar da aukuwar lamarin

Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya bayyana cewa an cafke mata da mijin da ake tuhumar ne bayan samun rahoto a ofishin hukumar ‘yan sanda na Kemta daga wani Chief Moshood Ogunwolu,  cewa wani fasto mai suna Adisa Olarewaju wanda ya ke haya a gida ɗaya da mata da mijin da ake zargin, ya faɗa masa cewa ya jiyo wani wari yana fitowa daga ɗakin waɗanda ake zargin.

Mr Oyeyemi ya bayyana cewa bayan an shigar da koken, jami’an hukumar sun garzaya gidan sannan “bayan bincikar ɗakin, an samu wata roba ɗauke da sassan jikin ɗan adam sannan aka cafke waɗanda ake zargin”

Daga Labarunhausa

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button