LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

“ADAMSY ka kwantar da hankalinka. Gata can nasamu kanta ta farfad’o… Ai dajin hakan dukkansu sukayi d’akin da take batare da sun tsaya sunji qarashan abinda Dr Aryan zaice musu ba.
Tana kwance akan qaramin gadan na d’akin. Hawaye ne yake zuba mata dan tuno da abinda ya faru da tayi.
Tana ganin shigowarsu tawani rumtse idanta.
Ganin hakan yasa ADAMS zuwa ya durqusa a gabanta da kama hannunta yace.. “Nayi kuskure matata. Nayi miki lefi my luv. Saidai bazan qara aikata miki hakan ba.
Bud’e idanta tayi da saukewa akansa tace.. “Ka rigada kayimin komai ADAMS. Ka b’ata tunani na tuntuni da qaunarka. Ba yanda zanyi in cire hakan daga zuciyata. Yanzu kazo ka Auri qawata aminiyata wacce tasanni ciki da bai. Hakan bai isheka ba kabini da abinda ban tab’a tunani ba. Marina fa kayi ADAMS. Marin daban tab’a jin irinsa ba arayuwata. Wallahi saika sakeki dan bazan iya zaman kishi da TAUDHAT ba. Saboda ina MASIFAR SANKA DA KISHINKA. Inda ace wata ce ba TAUDHAT ba na tabbatar bazanji ciwo azuciyata kamar haka ba…
Dafe kansa Adams yayi da hannu d’aya. Yayinda d’ayan yake riqe da hannayenta. Idansa ne ya kad’a yayi jajar saboda b’acin rai. Bai tab’a tunanin akwai ranar da NUFAISAT zatace mai wallahi saiya saketa ba.
A hankali ya maida kallansa gareta yana mece mata. “Wallahi NUFAISAT saidai ki mutu da Aurena akanki. Dan kalmar saki bata cikin agenda ta!
Har abada nidake zamu rayu rayuwar da bata qarewa. Dan har agidan aljanna ina rokwan Allah dayasa ki zama matata..
Na aikata miki hakan da zuciyar d’aya ne NUFAISAT..
Wallahi ban iya yi miki qarya. Na rantse miki da Allah na Auri TAUDHAT ne dan kawai na faranta ranki. Ganin danayi kinfi kowa saninta. Kinfi kowa amincewa da ita. Kinfi kowa jin dad’in zama da ita. Shiyasa na aureta dan aganina zakifi kowa farin ciki da hakan..
“Kadena danganta wannan had’in naka da matsayin zan samu farin ciki acikinsa. ADAMS akwai abubuwa da dama da ban sani ba agame da TAUDHAT. Wallahi Zuciyata zafi take min tana tafasa da k’una idan natuna TAUDHAT itace kishiyata.
Bazan iya da TAUDHAT ba Adams. TAUDHAT tafi qarfina. Ina da tabbacin alkairin da kake hangowa agareta kuma agareni bazaka tab’a samunsa ba.
Danta b’ata tunanina lokacin dana san wasu abubuwa akanta..
Dan Allah mijina ka sawwaqe min dan ayanxu nafi buqatar qaunarka ta kasheni agidanmu dana zauna zaman kishi da TAUDHAT….

Miqewa ADAMS yayi da sakin hannunta. Yace “bazan sakeki ba NUFAISAT.
kuma idan har ayanzu ma ina amsa sunana na mijinki’ ina umartarki daki tashi namai dake gidana yanzu yanzu. Wannan shine qarshen maganata dake anan. Ya qarashe furucin da miqa mata d’ankwalinta..
Kuka NUFAISAT tafashe dashi wiwi tana cewa. “Wayyo Allah kakawomin d’auki cikin wannan matsalar data kusantoni. Allah Kaine kace nayima mijina biyayya akan komai banda sab’anka. Narok’eka Allah daka sanyayamin Zuciyata na iya bin duk abinda yacemin acikin wannan halin da nake ciki dan bana San na sab’a maka.
Tana gama fad’in hakan tatashi da karb’ar d’ankalin nata tayafa akanta gami da tashi tana me tafiya cikin yali yali. Ganin hakan yasa TAUDHAT nufanta amunafunce danta riqeta alamar temako…. Aiko azafafe NUFAISAT ta wurga mata wani mugun kallo daja da baya tace. “Karki kuskura ki tab’ani…
Jan numfashi Yusuf yayi da bugan kafad’an Adams da yake kallansu. Aiko cikin sauri Adams ya gane me Yusuf yake nufi
Dan haka saurin matsawa ga NUFAISAT yayi cikin kulawa ya tarota jikinsa. Zata mishi masifa saidai suna had’a ido tafasa. A haka ya kaita har motar tashi gidan gaba. TAUDHAT tashiga baya. Shi kuma ya zauna wajen mazaunin direba. yana niyar tada motar ne d’aya daga cikin masu tsaransa yace.. “Oga daka bari nakaisu gidan. D’aga mishi hannu Adams yayi alamar aa. Sannan yaja motar yana gayama Yusuf ya jirasa yanxu.
Girgiza kai Yusuf yayi cikin damuwa dan har ga Allah baiji dad’in abin daya faru ba. Ji yake kamar basu kyautama NUFAISAT ba. Haka yana ji kamar abin da sukayi shine ya dace. Tunanin dayafi tsaya mai arai dai shine basu kyauta ma NUFAISAT ba kawai.. Haka yayi shashin da suka Kwantar da Hajjiya kakarsu. Anan yaga Nazifa qanwarsa taxo da abinci. Dan haka yaci kad’an bawai dan har alokacin yana tare da yunwar tasa ba. Kawai dai yaci ne dan karta mishi illah…

Su Adams ko babu me magana acikinsu. Ahaka suka iso gida yace duk susamesa a babban falan nasu…
Qarfin hali kawai NUFAISAT tayi taje falan bayan tawanke fuskarta a part d’inta
Adams sasu yayi a tsakiya ya kalli NUFAISAT data d’aure yace da ita… “Ki tausasa zuciyarki matata. Dan bazan iya rayuwa babuke ba. Ina San kiyi hakuri na d’auki lefina na Auran TAUDHAT da nayi. Na kuma yarda nayi miki lefi. Dan Allah ki yafemin ki zauna da lafiya a d’akinki dan samun farin cikina. Sannan kiriqe girmanki ki saki ranki ki rungumi y’ar uwarki Ku zauna lafiya dan kinfi kowa sanin bana san fitina da tashin hankali
Shuru NUFAISAT tamai bata da alamar cewa komai. Ganin hakan yasa ya maida hankalinsa gun TAUDHAT yaci gaba da cewa.. TAUDHAT na aureki ne dan samun d’orewar farin cikin matata. Saidai kinga yanda al’amuran suka sauya. Ina San matata ina San rayuwa da ita. Dan Allah ki zauna da ita lafiya ki riketa kamar yanda kuke da. Dan nasan zata dawo tayi miki kallan dada take miki danna samu sukuni acikin gidana… Kima NUFAISAT biyayya TAUDHAT ki bita idan kina San samun farin cikina agidan nan
Jan numfashi TAUDHAT tayi ranta yayi masifar b’aci. fad’i take aranta Wallahi saita gyarama NUFAISAT zama acikin gidan. Dan bazata d’auki rainin hankali agabanta mijinta ya dinga nuna mata yafi San uwargidansa akanta ba… Tsaida tunanin nata tayi da kallansa ta sakar mai murmushi da cewa. “Ba komai mijinmu insha Allah zanyi abinda kace min.
Da sauri NUFAISAT takalleta ranta cike da tsanarta taja mugun tsaki da cewa. “Nidai bazan shiga harkarta ba. Amma katabbatar idan tashigo harkata zan yaga mata rashin mutuncin da bata tab’a ji da ganinsa ba Wallahi.
Kallanta Adams yayi da mamaki dan shi ko’a mafarki idan akacemai NUFAISAT zata nuna tsana ga TAUDHAT haka wallahi bazai yarda ba. Bare a zahiri. Girgiza kai yayi dace mata. “Watoh bakiji abinda na gaya miki ba kenan. Zaman gaba zakiyi da ita kenan…
Sanda ta gallamai harara kana tace “Allah ya bamu zaman lafiya… Tana fad’in hakan tatashi da saurin shigewa part d’inta

Da kallo ya bita kawai. Ganin hakan yasa TAUDHAT tashi itama tabar mishi falan tana kisa abubu aranta.

"Mata mata saidai abarku. Ya fad'i hakan abayyane tare da tashi ya koma dining ya fara cin breakfast d'in da NUFAISAT d'in tayi musu d'azu dan suci. Sanda ya gama yaje ya ibi jinin TAUDHAT kamar yanda sukayi shida ita a daran nasu na jiya sannan ya ficce daga gidan zuwa offishinsa.

Yusuf bai tafi ba. dan nan ya tarar dashi yako bashi labarin yanda yayi dasu. Yusuf ya kallesa yace. “Gaskiya Adams sai yanzu naga rashin dacewar Auranka da TAUDHAT.
Murmushi ADAMS yayi da gyara zamansa kan kujerar offishin nasa yace da Yusuf d’in.. “Koma dai miye yanxu ya wucce Yusuf kawai fuskantar gaba zamuyi. Nidai bazan iya rayuwa babu NUFAISAT ba. Haka kuma bazan iya sakin TAUDHAT ba saboda wani dalili nawa.
Dan haka Dan Allah ka tayani da addu’a kan Allah ya shiga tsakaninsu ya daidai tamin kansu.
Jan numfashi Yusuf yayi dace mai toh kawai…

Kakar Yusuf tasamu sauqi tashin datayi. Danji tayi kamar tafi kowa lafiya aduniya. Dama hakan Adams yake fata. Nan Yusuf yasata agaba kan tagayamai me yake sata shiga damuwa haka. Murmushi tamai da cewa Aurenka nake San gani Yusuf.
Jin hakan yasa Yusuf dariya dace mata zanyi kwanan nan. Adams shima dariyar yayi da basu sallama
Kana yabi takan bincikensa akan jinin TAUDHAT… Aiko baida matsalar komai. Ma’ana baya tare da cuta…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button