LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

 "Me kake san cewa. Kana nufin idan sunci abincin ni zambi duniya su suzauna saboda nice naci abincin..

“Ina nufin kome zaki musu bazai kamasu ba. Idan kuma kika matsa komai dawowa kanki zaiyi.
“Ban yarda ba. Dan ina ji ajikina nice dacin galaba akansu.
“Haba TAUDHAT. Ya kamata ki gane qaunar ki nake har cikin zuciyata. Wane malami ne yake gayama miki gaskiya tsagwaranta imba niba. Wallahi abin dana gaya miki idan har baki bishi ahankaliba haukacewa zakiyi..
“Haukacewa. Haukacewafa kace. Waini d’in kake cema zan haukace.
To canja tunaninka. Dan ba wani asirin dazan yima wani ko wata dazai dawo kaina har nayi hauka.
“Ba mamaki qila akan MUSLEEMA da yaranta qarshenki yake san zuwa TAUDHAT….
Saboda haka kiyi duk abinda kike sanyi kiyi na barki lafiya. Amma kafin nan kikawomin y’ata da hannunki dan Wallahi yanda banyi auran nan ba ko sama da qasa zata had’e saina karb’i yata agun mijinki Adams. Danko gawarki nagani saiya bani y’ata b’cos kinfi kowa sanin yanda nake qaunarta. Shiyasa nake qara jaddada miki daki kawomin y’ata tun da wuri….
“Da Allah dakata Isma’in. Kama dena batu akan Haneepha. Dan Haneepha y’ace ga ADAMS. Kaima kasan muslinci ya bashi ita…
“Wato TAUDHAT baki sanni bane.
“Zan sanka tunda ina darai da lafiya.. Tana faɗin hakan takashe wayarta da mamakin yanda asirin da tama mamanta ya qarye..
Ahankali ta d’auki abincin tanufi shashinsu MUSLEEMA.
Lokacin NUFAISAT na tare dasu. Tana nunama MUSLEEMA yanda ake dressing d’in kayan yara.

Da nutsuwa TAUDHAT ta’ajiye musu abincin agefe ta harari inda NUFAISAT d’in take tace da Yawo. “Gashi abinci nakawo muku kuci kuji irin nawa girkin..
Da murmushi yawo tace.. “Toh angode Allah ya saka..
Har takai ƙofar fitta tajuyo da qara kallan YAWO tace.. “Kuci fa.
“Insha Allah zamuci yanxu kuwa. YAWO taqara bata amsa da kulawa
Sanda NUFAISAT tatabbtar tatafi Sannan tace da MUSLEEMA. “Kar kuci kuzubar a shara. Badan ina zarginta ba. Saidan hankalina bai kwanta da abincin ba..
Ba musu MUSLEEMA tajuye a baqar leda kana taje tasaka a sharar…????

ADAMS ko daya tashi daga office gidansu ya nufa. Kasancewar jiya baisamu yaje ba.
Anan yake qara gayama Dadynsa ya kwantar da hankalinsa yayaba da hankalinsu YAWO. Alamu sun nuna mutanan arziqi ne.
Sanda ADAMS ya tabbatar Dadyn nasa ya gamsu sannan yaje gun Amminsa itama ya kwashe labarin komai ya gaya mata.
Da jin daɗin temakwan da yayi musu Ammin nasa ta kallesa da cewa.. “Gayamin sunansu.
“Ita dai yarinyar sunanta MUSLEEMAT sai kakarta YAWO. Sai yaran MUSLEEMAN Khalit da Khalil & Rahma..
Shuru Ammin tayi cikin tunani. Can taqara cewa. “Kuma kace fulani ne ko.
“Murmushi yayi da bata amsa… “Eh fulani ne. Saima kinga yaran ita MUSLEEMAT d’in suna kama dani sosai. Wallahi saikace nine ubansu.
Bara naje gida dare yayi kuma gashi ina jin yunwa.
Jan numfashi Ammin tayi da cewa.. “Kona zubo maka abinci ne.
“aa barshi. Karki had’ani fad’a da ita????
Murmushi tayi da cewa.. “Wacece acikinsu.
Tashi yayi da sakar mata kiss ahannu yace. “NUFAISAT..
“Wato har tayi nesa yanxu a girki dazaka k’i cin nawa ko.????
“aa wasa nake miki Ammina. Kingama na zauna zubomin naci kawai????.
Murmushi tayi da cewa. “Nagodema Allah data kware yanxu. Allah ya qara had’e kanku maza jeka bana san kana yawo da yunwa.
Murmushin shima yayi mata da sallama ya fitta daga falan nata suka d’auki hanyar gida..

Suna isowa shashin su MUSLEEMAT yayi.
Nan yaga MUSLEEMAN da Rahma suna kallo. Da alama YAWO da su Khalit sunyi bacci.
Ahankali takemai sannu da zuwa da gayamai YAWO dasu Khalit sunyi bacci.
Dajin dad’in yanda tasake da gidan nasa yayi mata sallama daniyar ficcewa daga falan..
Ai cikin sauri tatuna tana san yimai godiya dan haka cikin sanyin murya tace… “Nagode da cika maganarka da kayi d’azu da safe YAYANA.

Juyowa yayi da kallanta ya d’aga mata gira alamar me take nufi.. Ganin hakan sai tacigaba da cewa.. Ina nufin wajen sakasu amakaranta dakayi.
Murmushi yayi da harararta yace… “Idan kika qaramin godiya akan wani abu dazan miki ko nayima yarana saina sab’a miki.
Cikin shagwab’a tace.. “Afuwa YAYANA. Wallahi na tuba bazan sake ba.
“Idan kika sake fah.
Shuru tamai.
Sai yaci gaba da cewa.. Ke da kanki nakesan kigayamin wane hukunci ne yadace dake.
Jan numfashi tayi da cewa “Saika dena kulani.
“Shikenan. Yanxu saikin sake ki gani a kwaryarki. Gud9t
Yana faɗin hakan ya ficce daga falan…
Wallahi Yayana ina MASEEFAR SONKA tafad’i hakan aranta tare da tashi takulle musu kofa…

Ya samu NUFAISAT kamar yanda yasaba ganinta cikin tsafta. Bayan sunyima junansu wlcm part na TAUDHAT ya nufa. Ba lefi yaga tasake ba kamar yanda yabarta da safe ba.
Anan yasakarma Haneepha kiss ya koma shashinsa yayi wanka dama NUFAISAT tashirya masa komai na abinda zaici.
Dan haka yana yin sallah yahau cin abincinsa.
Anan NUFAISAT take gayamai gobe zataje kasuwa da MUSLEEMA..

TAUDHAT har kwanciyar bacci taji shuru su MUSLEEMA na tare da lafiya.
Dan bala’i haka takasa nutsuwa qarfe goma sha d’aya da rabi taje ta bugama su MUSLEEMA kofa.
Nan taga MUSLEEMA ce ma tabud’e mata kofar dan har alokacin basuyi bacci ba ita da rahama.. A rikicewa take tambayar MUSLEEMA waiko sunci abincin data basu d’azu.
Nan ko MUSLEEMA ta bata tabbacin sunci har suna Santi..
Da mamaki ta dawo d’akinta tana tunanin ita dai tunda take da bokan nata bai tab’a bata abu tayi taga sab’anin abinda yace mata ba.
Nan alokacin takira malaminta tace bataga komai daya faru dasu MUSLEEMAT ba. Kodai zancenshi haka yake.
Murmushi yayi dace mata TAUDHAT kinqi gane gaskiya nagaya miki. Dan duk inda zaki saidai kawai suci kud’inki.
Shuru tayi bayan ta kashe wayar. Tunani tashiga kodai taqara komawa wajen bokan natane.
Sai wata zuciyar tace mata tadai d’an jinkirta taga gudun ruwan lamarin

Washe gari haka MUSLEEMA taqara taya NUFAISAT had’a breakfast..
bayan ADAMS ya fitta NUFAISAT saurin gama shirya d’akinta tayi. Saita tasa MUSLEEMAT agaba sukaje kasuwa inda tazab’an mata kayan make-up dasu kayan gyara jiki irin na mata kala kala masu kyau. kana suka nufi wajen atamfofi fashion masu kyau tasai mata kusan kala talatin tare da su les material. Daga nan wajen telanta suka wucce ya gwada MUSLEEMA tace mai tana san kayan dukka su kammala nan da sati d’aya. Pls ya rabama yaransa aikin dan suyi sauri.
Nan ya tabbatar mata insha Allah zai kawo mata kayan bazai qara ko kwana d’aya ba.
Nanko NUFAISAT tabasa kud’in d’inkinsa cif bata rage masa komai ba suka dawo gida.

Godiya ba irin Wanda MUSLEEMA batama NUFAISAT ba. Ganin akwalla kud’in data kashe mata yau zaikai dubu d’ari biyu. Duk da cewa dama kana kallan NUFAISAT kasan taci tatada kai amma abin a jinjina mata ne wannan siyayyar datai mata ai..
Haka yawo ma tadinga gode mata.
Sanda NUFAISAT tanuna musu b’acin ranta kana suka hak’ura suka dena yimata godiyar..

Alokacin NUFAISAT d’in tafara koyama MUSLEEMA yanda ake make-up na zamani.
Aiko dake kwakwalwar MUSLEEMAN abud’e take nan tafara gane komai..

Zuciyar TAUDHAT ko tayanke mata shawara kan taqara komawa wajen bokan nata. Dan hausawa nacewa kanufi cimma burinka da zafi zafi yafi kabishi da sanyi sanyi .. Still yau d’inma haka taficcewarta batare data gayama Adams ba..
Saidai koda taje gun bokan shima bata tabbaci yayi kan tayi hak’uri Kawai da lamarin. Idan kuma tana ganin bazata iya hak’urin da lamarin ba. Toh ta lura da lokacin da MUSLEEMA take al’ada. Tasan duk yanda zatayi takawo masa tsumman da take amfani dashi alokacin kota kawo masa wani dai abu dayake da jinin al’adar tata..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button