LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Ba qaramin tsoro bane ya kamasu.. Dan ogansu yace musu kada su kuskura su kasheshi.
Sudai mai dukan daba zai moru ba. Shiyasan abinda zai cema wanda yasa shi aikin…

Aiko Ahankali suka fara tab’ashi suna cewa.. “Mun kashe shi fah. Yanxu me zamucema oga..
D’aya daga cikinsu yace.. “Ga shawara.. Me zai hana mukaisa Rugar malam jauro.. Kasan rugace wacce ba kowa bane yake da sani akanta. Saboda tayi cikin daji da yawa.
Me zama a wannan ruga sai Wanda ya taki abubuwa da dama. Dan bakowane mutum bane yake iya rayuwa awajen. Kasancewarta muguwar riga….
Cikin sauri wani cikinsu shima ya amshe da cewa.. “Kaga shike nan asirinmu ya rufu agun oga.. Dan idan mukace mai munyi yanda yace muyi zamu zauna lafiya dashi.
Idan ko mukace mun kasheshi saiya d’auki ran d’aya daga cikinmu..
Kaga rugar Malam Jauro bame zuwa bare asan da zaman gawarsa awajen.
Idan ko muka yar dashi anan kaga dole atsince shi kuma labari yajema oga..
Shuru sukayi suna nazari
Can wanda ya harbi Sunusi yace. “Wannan shawarar tayi. Kunga sai musa Sunusi shi kad’ai a buhun barkonan kamar yanda ogan yace. Sai muce mai gabaki d’ayansu ne mukasasu a buhun bamu san ya akayi aka rasa ADAMS d’in ba.

Kowa cikinsu yayarda da wannan shawarar…. Dan haka suka kinkimi ADAMS suka sashi cikin motarshi. Sannan suka saka Sunusi abuhu irin babban nan wanda yake d’auke da barkono aciki. suka kullesa. uku daga cikinsu suka shiga motar ADAMS d’in d’aya yajata.. Sannan sauran suka shiga cikin dajin inda suka ajiye motarsu dan kar’a ankare dasu.
Sannan suka kusa cikin wani daji me nisan tsiya. Dan sai tafiya suke kamar basa tafiya.. Akalla sunkai kusan biyu na dare kana suka iso rugar.. Saidai basu bari sun qarasa cikinta ba dan sunsan illar dake cikinta..
Ad’an nesa da rugar cikin dajin suka yada Adams…
Suka juya abinsu da barin wajen…

Washe gari da misalin qarfe takwas suka samu fitowa daga rugar…
Nan suka d’auki hanyar garin Kaduna. Sanda sukayi awa uku kana suka samu kansa a garin Kadunan. Sannan sukaje unguwar su Dadyn ADAMS suka bar Sunusi cikin motar da key na motar Adams d’in sannan suka bar unguwar.
Amman sanda suka zaro wata kwarab’abbiyar waya suka kira num na Dadyn Adams kamar yanda Ogansu ya basu suka gayamai ga Adams nan da direbansa cikin unguwarsu da alama yana cikin wani hali… (Kuji fa masu karatu)
Suna gaya mai hakan suka kashe wayar da cillar da ita awajen sukayi tafiyarsu..

Lokacin da Dady ya d’auki wayar tasu yana zaune ne shida Hajjiya Rukayyat da Ammi. Suna magana akan rashin jin Adams d’in daba suyi ba awaya. Gashi basu da number na Yusuf kona Ibrahim d’in.. Aiko da sauri Dady ya tashi jin abinda suka ce mai yana me cewa “Subhanallah.. Nan su Ammi suka buqaci suji meya faru. Da sauri ya gaya musu ya fito waje yana cilla ido yaga ta’inda zaiga motar Adams d’in
Aiko ya d’anyi nisa da tafiya cikin layin nasu saiya hango motar..
Da sauri ya qarasa gareta yana duba amman baiga kowa aciki ba sai wayoyin ADAMS dana Sunusi..
Yana bud’e Boot na motar sai yaga qatan buhu fari kallo d’aya zaka mai kasan na barkono ne.
Yayi duba iya duba wajen wai kozaiga Adams alayin amma baiga kome kamarsa ba.
Hankalin Dady ya tashi matuqa dan haka nan ya shiga kiran wayar da suka kirasa da ita nan yaji akashe.. Saiya kira wani amininsa babban d’an sanda yana gayamai yaxo yanxu unguwarsu ankawo mai motar d’ansa Adams kuma baya ciki da alama wani abu nasan faruwa.

Ai dajin hakan yacema Dadyn gashi nan zuwa..

Haka yazo da yaran aikinsa suka hau caje motar basuga komai ba. Sai kwarab’abbiyar wayar da suka yar nesa da motar.
Ogan nasu yace abud’e mai buhun barko nan nan.
Aiko dan yaransa suka bud’e mai saiko ganin sunusi sukayi cikin barkono..
Nan suka fitto dashi anan suka gane yazama gawa dan ga shedar harbi nan akansa bai b’uya ba..

Hankalin Dady yayi matuqar tashi nan ya yanke jiki ya fad’i sumamme..

NUFAISAT da Ammi da sukaji labari nan suma haka suka zube sumammu.
Masu qarfin halin Hajjiya Rukayyat ce da TAUDHAT..

Nanfa zance ya baza gari an nemi ADAMS ba’a agansa ba..
Hankalin y’an uwa da abokan arziqi ya tashi matuqa..
Dan b’atan mutum yafi mutuwarsa Shiga tashin hankali. Saboda idan mutuwa yayi ba shakka damuwar ta dabance.
Idanko b’ata yayi kullum tunani mutane zasu shiga yi koyana wane hali koya mutu koyana raye oho
Wannan yasa hankalin kowa yayi mayuqar tashi.
Nan aka fara sanarwa a gidajen radio da gidan talabijin yanar gizo wajen nemansa.
Anan Yusuf yasan Adams ya b’ata…
Dan haka ba shiri ya baro garin gwambe dan shima ya rasa nutsuwarsa ganin baiji Adams d’in ba.
Dama Ibrahim bawai agarin gwanben yake ba. aa Aure ne kawai mamansa takeyi agarin dan tarabu da mahaifinsa. Hakan yasa shi yake gun Mahaifinsa anan cikin garin Kadunan.
Dan haka tare da Yusuf suka dawo Kaduna suna masu san jin ba’asin yanda akayi Adams ya b’ace.

Babufa ADAMS babu labarinsa sam cikin garin Kaduna.
Dan har y’an sanda da masu farin kaya kaf sunyi iya binkikensu basuji labarin Adams ba..

Dare da rana safe da yamma malamai addu’a suke akan Allah ya bayyana Adams..
Dan a binciken istaharan duk malamin da yayi ya nuna ADAMS yana RAYE saidai yana cikin wani mawiyacin hali
Jin hakan da Dady yayi shiyasa jininsa qara hawa a asibiti..
NUFAISAT ko ba ita tasamu kanta ba sanda tayi sati a asibitin tadawo hayyacinta..
Saidai tasaka salloli agaba dare da rana akan Allah ya fitto mata da mijinta ya karesa aduk inda yake.
Haka TAUDHAT duk ta karad’e malamanta da bokayenta sun bata tabbacin Adams yana raye saidai baza suce ga inda yake ba.
Gaskiya itama hankalinta ya tashi sosai.

Ganin hakan yasa masu tsaran lafiyar Adams d’in suka fito sukace su suna zargin Ibrahim shine ya b’atar da ADAMS kuma ba mamaki shine ya kashe Sunusi.
Jami’an tsoro sunsasu agaba kan sufad’i dalilinsu na fad’in hakan..
Nan suka gaya musu shine yasa wasu suka kaima ADAMS d’in hari a shekarun baya.
Kuma yaxo ya buqaci dasu kulle dashi dan shi rayuwar ADAMS d’in yake buqata..

Ai dajin wannan batu nan take ogan y’an sanda yasa yaransa suje su nemamman Ibrahim aduk inda yake..
Sunci sa’a tare da Yusuf suka dawo daga gwamben dan haka basusha wahalar ram dashi ba..
Dafarko yayi musu gaddama akan baisan komai akan labarin ba.
Kuma qarya masu tsaran lafiyar Adams suka masa na wai shine yasa wasu suka kai mai hari..
Sam jami’an tsoran basu wani yarda da Ibrahim d’in ba
Dan haka nan suka hau gana masa azaba cikiko harda guntule mishi y’an yatsu guda biyu..
Ai yana jin azaba ya gaya musu shine yasa aka kai mai hari shekarun bayan. Kuma da gaske shine yasa yanxu a kashesa akuma kashe Sunusi dan karya tona musu asiri..
Jami’an basuji mamakinsa ba dan sun saba ganin abin mamakin irin hakan
Dan haka sai suka buqaci suji dalilinsa nayima Adams d’in hakan…
Ba wata kwakkwaran magana dan cemusu yayi…. Tun suna skull ADAMS yake samun nasarori arayuwa amman shi baya samu.
Haka shi LEEKITAN ZUCHIYA ne hakama Adams d’in shima LEEKITAN ZUCHIYA ne.. Saidai sunan Adams yafi fitowa duniya tasanshi fiye dashi..
Haka tafanni kasuwancin da yakeyi nan ma ya qara fito da sunansa ko’ina aka sanshi…
Wannan dalilin shiyasa yaji hassadar Adams d’in takamasa. Saiya bara bin bokaye kansu dak’ushe tauraran Adams su d’aukaka nashi.. Saidai abin bai yuhu ba. Sakancewar shi me ibada ne. Shine kawai ya yanke shawarar yasa akasheshi. Nanma way’anda yasa sumai hakan baisan dalilinsu na kasa kasheshin ba har akaro na biyu..
Shine yanxu yayi amfani da wannan damar dayaji Adams d’in yace bazaibi jirgiba ba motarsa zaibi. To shine yacema yaran aikin nasa duk iya wiya kadda subar ADAMS darai awannan karan….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button