LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Suko su Dady da Ammi da Adams da Salim hira suka b’arke da ita sosai duk akan halin NUFAISAT ne Wanda suke ganin da wiya yasamu mace me hankalinta.
Sanda goma tayi Adams yama Dadynsa sallama sukafito daga falan shida Amminsa
Sunyi mamakin ganin yanda lokaci d’aya sukaga canjawar NUFAISAT. Danga damuwa muraran akan fuskarta har wani gumi take.
Ahankali Ammi tazauba dab da ita tare da dafata tace. “Y’ata meya sameki kike cikin damuwa haka. Shuru NUFAISAT tayi mata. Ganin hakan yasa Ammi murmushi tacigaba da cewa. Wato Rukayyat ce tajefaki cikin wannan halin ko. Ahankali NUFAISAT ta gyad’a mata kai tare da rushewa da kuka..
Ammi bata tambayeta miye ba. Amman tayi kokarin rarrashinta har tasamu tayi shuru. Sannan tayi mata nasiha akan taguje sakama zuciyarta zancikan da zasu dameta gudun kar wata ranah tasamu babbar matsala da ita. Kuma duk abinda zataji akan sharhin da za’a mata kan matsalarta taji tsoran Allah wajen yanke hukuncin daya dace da ita.
Godiya sosai NUFAISAT tama Ammiin sannan Ammin tabada turare suka mata sallama da barin gidan

Shuru haka suke tafiya amotar bame magana acikinsu har suka iso gida.
Wajen baccinsu ne anan Adams ya kasa jurewa ya rungumeta yana tambayarta me momy Rukayyat tagaya mata Wanda yasata shiga cikin wani hali haka.
To dama bawai tagama kukan nata bane agidansu dan haka saita qara b’arkewa da kuka wiwi
Cikin rikicewa yahau lallashita yana cewa tunda batasan cewa komai to tabar kukan haka ya ishesa.
Bata dena ba. Sanda ya had’e bakinsa da nata yahau aika mata da wani shu’umin kiss da wasu sakwanni kana tadena kukan tahau manne masa dajin dad’in yanda yake aika mata da sakwannin
Can da suka samu nutsuwa saita fara cewa. “Dan Allah mijina kamin aikin gafara kai kad’ai nake so. Nake ji. Nake qauna. Nake fatan kasancewa dakai har agidan Aljanna. karka wulaqantani kamar yanda momy Rukayyat tace zakamin. Tace min zaka wulaqantani dazaran kasamu d’a daga wata mace badaga gareni ba. Sannan zaka korani gidamu da farar takadda na saki saboda lokacin zakaga bani da amfani agareka. Idan hakan ta kasance agareni mijina hauka zanyi. Wallahi mijina harkacewa zanyi. Dan Allah kamin aikin gafara karka bari zuciyarka taraya maka hakan ko’a mafarki ne bare a zahiri. Wallahi sanka nake irin dayawa d’in nan.
Murmushi yayi da qara maqaleta jikinsa yana me shafa kanta cikin soo da qaunarta. Yasani Hajjiya Rukayyat ta tsoratata da yawa. Gashi ita bata iya shiga damuwa da tsoro ba. Gaskiya Allah ya sakama matarsa dan tacutarmai da ita cikin lokaci qanqani.
Da sanyin murya yake cemata… “Ki kwantar da hankalinki matata. Bana d’aya daga cikin waƴannan mazajen da suke aikata hakan ga Uwargijayensu. Wallahi NUFAISAT idan aka cire mahaifana bani da wani sauran abin so arayuwata kamarki. Hatta haihuwan bata shigeni ba kamar yanda qaunarki tashigeni.
Dan Allah kibar ZUCIYATA tasamu nutsuwa wallahi bazan tab’a wulaqantaki cikin hankalina ba. Dan bana tunanin zan qaunaci wata mace kamar yanda na qaunaceki. Saidai kinsan d’an Adam agizine koda hakan tafaru dani agaba karki zargeni kimin uziri dan Allah…
Zatayi magana ya hanata maganar saboda aika mata da yayi da wani sakwan na soyayya…

NUFAISAT tana qaunar qaunar mijinta irin sosai d’innan
Shiyasa tsoro yake kama zuciyarta idan aka kawo mata batun rabuwa dashi.
Haka Adams ya raya mata wannan daran da bata farin cikin da ita kanta sanda tayi mamaki
Danji tayi kamar aranar yafara Love da ita❤

Itako TAUDHAT tana zuwa gida tacire kayan jikinta dan itama kanta turaran na bokan nata ya isheta. Dan bashi da dad’i da gaske kamar yanda Adams yace
Wanka taqarayi dayin sallah kana tamiqe agadanta tare da fad’awa tunanin gata a qirjin ADAMCY….. Nanko take ta lumshe ido tare da rungume filo cikin San kasancewa a yanayin.
Bata d’auki lokaci tana tunanin ba wani Alhajinta ya kirata akan yana San kwana da ita. Aiko tana jin hakan tadiro daga gadan nata da zarar jakarta da key na motarta tacema mahaifiyar tata bazata dawoba sai gobe. Bata jira cewar mahaifiyar tata ba taficce abinta.
Haka uwar tabita da kallo tana me addu’ar Allah ya shiryar mata y’ar tata ya kuma cire mata tsoranta dan tasamu damar yanke mata akan abinda takeyi kamar yanda kowace uwa tagari takema y’arta.

Rahma Nalele ce Y’an hannuna ????????????????
[6/21, 12:22 AM] ®????◾◼▪official Auntyn Luv.: ☆´-☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾☆• ❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH* *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ☆´-☆´- ☆“˜•☆• ¸☆“☆ª☆_☾☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story
April.. 2018

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh’md Rufa’i Nalele..☆

© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM????
☆We the best ☆

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&tn=H-R

” بسم الله الرحمن الرحيم

☆page 10☆

Washe gari da cikakken farin ciki Adams ya yabar gidan nasa. Kasancewar yabar matar tashi da farin ciki.
Da misalin qarfe biyu ne na ranah Adams da abokinsa Yusuf suke tare cikin ofishin Adams d’in. Abincin da NUFAISAT ta’aikuma da Adams d’in suke ci
Sai Adams yake ma Yusuf bayani akan Auran da yake San qarawa. Yusuf ya qara tsaida kallansa akansa da murmushi Yace.. “Toh yanxu ta ina zaka fara. Bayan nasan NUFAISAT ita kad’aice madubin dubawarka. Bayan ita ba wata wacce kake da ita afannin so. Yanxu ta ina zaka fara kenan
Shafa kansa Adams yayi da murmushi Yace. “Da wai na yanke shawaran Auran TAUDHAT. Kasan cewar itace tasan NUFAISAT fiye da kowa. Ba wani abu dazata mata wanda zai zama na Allah wadai. Sannan ita kanta NUFAISAT nasan hankalinta zaifi kwanciya da TAUDHAT d’in. B’cos tana Santa sosai na tabbatar zan iya samun zaman lafiya agidana tunda sunsan kansu.
Shuru Yusuf yayi cikin nazari yana tuna yanda TAUDHAT da NUFAISAT suke. Tabbas Auran TAUDHAT shine abinda ya dace da Adams. Kasancewar TAUDHAT tafi kowa sanin NUFAISAT. Kuma zasu iya samun zaman lafiya me d’orewa. Saboda suna San junansu. Kuma sun taso ne tun yarinta.
Kallan Adams Yusuf yayi da cewa. “Gaskiya kam ka Auri TAUDHAT. Saboda na tabbatar bazata cutar da NUFAISAT ba. Saboda kaga yanda suke qaunar junansu. Sun taso tun yarinta. Kuma kowa yasan halin kowa. Sunsan abinda in sukama junansu zai b’ata musu rai. Haka sunsan abinda idan sukama junasu zai faranta ransu.
Ka aureta kawai.
Murmushi Adams yayi da cewa. “Nima abinda na duba nagani kenan..
“Gaskiya kayi tunani me kyau Amman wani hanzari ba gudu ba. Shin ita TAUDHAT d’in tana sanka kuma zata amince da hakan kuwa.
Jan numfashi Adams yayi da cewa. “Hmm ai nadad’e ina hango qaunata cikin kwayar idanta.
cikin dariyar Yusuf yace. “Lalle kace zata fad’o hannu. “Sosai ma kuwa. Adams ya bashi amsa cikin sauri. Girgiza kai kawai Yusuf yayi dacigaba dacin abincinsa dan yafi kowa sanin irin farin jinin da Adams yake dashi agun jama’a. Maza nasu San daban haka mata nasu San daban
Yusuf abokin Adams ne tunna k’uruciya. Yawancin halaiyar Adams Yusuf yana dasu. Hakan yasa Adams yafi yarda da Yusuf fiye da kowa a cikin abokanayansa. Haka shima Yusuf d’in ya yarda da Adams fiye da kowa
Yusuf yana kyau hankali da nutsuwa san soyayya. su biyu ne iyayansu suka haifa shi da qanwarsa Nazifa. Iyayansu sun rasu sun suna qanana. Hakan yasa suka tashi a qarqashin kulawar kakarsu Hajjiya Delu.
Saidai iyayan nasu sun tafi sun bar musu dukiya me tarin yawa.. Dake Yusuf d’in kasuwanci ya karanta sai kawai ya karb’i dukiyar tasu gun qanin babansu yahau juya musu ita. Sosai Adams yake qara bashi haske akan kasuwancin. Duk da shi karanta yayi Amman Adams ya fishi wayewa akai.
A yanxu dai Nazifa qanwar Yusuf d’in tana secondary skull. A islamiya kuma takusa yin sauka. Yusuf yana ji da ita sosai. Yana Santa sosai. Hakan yasa yaqi yin aure da wuri saboda yana San yasami mace tagari wacce zata kulan mishi da qanwar tasa tasota ta qaunaceta dan Allah
Wannan dalilin yasa yaketa gwada mata da nuna musu yana matuqar ji da qanwarsa dazaran yaga kin fara nuna masa wani hali akanta na yanda yake nuna miki kulawarsa akanta. Toh nan take zai rabu dake. Har yanxu a haka yake. Wannan shine labarin Yusuf a takaice.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button