LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Wannan shine sirrin zama da kishiya. Kinga baki nuna mata baqin hali ba. Baki cutar da ita ba. Baki danne mata hakkinta. Baki aikata mata wani mugun abu. Ke kawai mijinki shine agabanki ba kishi da ita. Toki saiki gayamin ta inda zata fiki kwanciyar hankali acikin gidan…
Magana ta qarshe dazan gaya miki NUFAISAT itace. Bana San wasa da sallah. Lokacin sallah nayi kitashi kije kiyi. Dan duk macen da take yin sallah akan lokaci wallahi tafi qarfin kishiyarta tako ta ina..
Sannan duk sallar da zakiyi idanga rokwan Allah ya cire miki kishin abokiyar zamanki. Sannan ya fifita qaunarki acikin zuciyar mijinki
Yasoki ya qaunaceki fiye da kowace y’a mace afad’in duniya dama gidan lahira.

Amatsayina na uwarki mahaifiyarki ban yarje miki ki sararama TAUDHAT wajen kishi akan abinda Adams yake so ba
Na baki dama kije ki kwace mijinki agun TAUDHAT ki nuna mata ko babu haihuwa bazaki tab’a wulaƙanta agun mijiki ba.
Ki nuna mata ita da banza duk d’aya kika d’aukesu
Ki nuna mata ita bata kai kiyi kishi da ita ba
Ki nuna mata Adams naku ne ku biyu amman kece abar qaunarsa…

Toh saiki tambayeni. Tayaya zaki nuna mata dukkanin way’an nan abubuwan.
Ta hanya d’aya ce itace HAKURI da nazari wajen yanke hukunci
Na sanki da San fad’an gaskiya atake idan aka miki abu. Saidai kisani Yanzu dole ki koyi yanda ake danne abu. Koda kin ganshi gashi gaskiya ne kuma ke aka cuta saiki share nunu sam abinda aka mikin bai dameki ba.
Dan idan kikayi hak’uri ga wanda yake sab’a miki wallahi wata rana shida kansa zai zauna yayi tunani da nazari akan ya dace yadena miki abinda yake miki…
Ki iya kirsa da kisisina da basarwa akan komai da zakiyi agidanki. Ammafa me kyau banda mara kyau.
Sannan kisa aranki raguwar mace itake kuka da buri da fad’ace fad’ace idan anyi mata kishiya.
Kedai kisa aranki abokiyar zamanki ba abar tsoranki bace.
Ki riqe Allah duk abinda zakiyi kiyi damunsa
Wannan itace nasihata agareki. Kuma itace gaskiyar dazan gaya miki. Kuma daga yau bazan qara zama dake irin wannan dan kinrasa yanda zakiyi da kishiyarki ba….
Mommy na kawowa nancikin zancenta taja numfashi da d’auke kallanta daga kan NUFAISAT d’in taciga da cewa. Naji kince text message kika masa wajen wajen gaya mai zaki nan gidan. Kuma bai turo miki amsa ba kawai kikayo gaban kanki kika tawo ko….
D’aga mata kai NUFAISAT tayi jiki asanyaye.
Ganin hakan yasata murmushi taci gaba da cewa.. Kishi da tsanar TAUDHAT yana neman ya canjamin ke NUFAISAT a lokaci d’aya
Hmm ba komai. Idan kikayi abinda nace miki zanga aikinsa ajikinki. Idan kuma naga akasarin hakan. Zaki ban mamaki dan zan d’auka da gaske TAUDHAT tafi qarfinki. Ta gaske tsoranta kikeji. Da gaske takwace miki farin cikinki
Wallahi NUFAISAT idan naga hakan atare dake da baqin cikinki zan mutu…
Da sauri NUFAISAT ta kalleta.
Aiko mommy d’in ta gyad’a mata kai alamun tabbatarwa. Kana taci gaba da cewa. Ki tashi kije gidanki ki gyara kanki da ingantattun magungunan mata da kayan marmari. Ki wadata kanki da qamshi da kuma d’akunan ki. Kici gaba da koyan girki agun y’ar uwarki. Kisa aranki kina da Allah baki da damuwa da albarkacin manzan Allah. NUFAISAT tashi ki tafi gidanki Allah ya miki albarka ya d’oraki akan mijinki da abokiyar zaman naki. Zan bama Y’ar uwarki Zainab magungunan gyaran jiki anjima saita kawo miki gobe..
Tashi NUFAISAT tayi hawaye na zubo mata tayimusu sallama da ficcewa daga gidan.
Da kallan tausayi mommyn tabita dashi kana ta kalli Zainab dake kuka tace “miye naki na kuka kuma.
“Momy ina kukan rashin adalcin da TAUDHAT tama NUFAISAT ne. Sannan tausayin NUFAISAT d’in ya kamani. Sannan godiya nake ga Allah daya bamu iyaye kamarku….
Murmushi mommy tayi da tashi tana nad’e sallaya dace mata. “Naji futan Dadynku bara na kirasa nagaya masa zani unguwa. Kinga kanki tashi daga office nagama had’a mata komai da komai. Sai kawai ki biyo ki karb’a idan Allah ya kaimu gobe kya bata kamar yanda nace mata..
Toh Zainab tace mata tare da share hawayenta ta d’auki jakarta da key na motarta tanufi wajen aikinta.

Lokacin da sakwan NUFAISAT ya iske ADAMS shida TAUDHAT suna kan dining yana cin breakfast d’in da tayi mai.
Na tafi gidanmu ba wani jimawa zanyi ba.
Wannan shine sakwan data tura mai.
Murmushi ADAMS yayi dajin takaicinta. Kana ya ture wayar gefe yana me sanyin sauri ya gama yaje ya sameta. Dan baya San kiranta TAUDHAT ta ankare da wani abu
Saidai kanya ida gamawa yaji tashin motarta.
Sanda ya rintse idansa dan takaici.
TAUDHAT ko duk ta fahimci NUFAISAT ce ta fitta tsaresa tayi da ido tana me tambayarsa ko wani abu ne ya shigar mai ido.
Bud’e idan yayi da sakar mata murmushin yaqe batare dayace mata qala ba.
Sanda ya gama ne ya sakar mata kiss a kumatu da d’aukar jakarsa ya ficce daga falan. Ai tana jin fitansa da masu tsaran nasa tafad’a tunanin me NUFAISAT tafutayi da sassafe haka. Ganin takasa ba kanta amsa sai kawai ta saka wani layinta cikin wata qaramar wayarta takira wani malaminta akan ya duba mata ina kishiyarta taje yanxu da safen nan. Murmushi ya mata da cewa su TAUDHAT yau an tuna damu. Yaushe kikayi Auran da har kike magana akan kishiyarki baki bamu labari ba
Da murmushin yaqe tabashi labarin yanda akayi tasamu Adams d’in kana ta qara mishi da cewa ita dai yanxu ya gano mata me NUFAISAT tafuta yi
Sanda yayi mata kirari kafin yace zai duba mata takwantar da hankalinta. Saidai koya duba bazai gaya mata sakamako ba sai indai tazo garesa.
Waro ido TAUDHAT tayi da cewa “Ina matar aure me zan maka idan nazo. Murmushi yayi da bata amsa… “Lalle TAUDHAT. Mata nawa ne suke da Aure amman suke cigaba da abinda sukeyi.
Gaskiya bazaki samu nasara akan kowane abu daga gareni ba har sai idan zaki dinga zuwa ina d’anaki. Dan yanxu kika gama bani labarin yanda kike sakarma da boka jikinki.
“Kaga da Allah dakata. Me zakace akan boka. Naga ai duk aikinku d’aya ne dashi. Kawai shi yana amsa sunansa na boka ne kai kuma d’an iskan malami.
Sheqe mata da dariya yayi da cewa. “Ya San ranki mutuniyata. Kawai malama idan zakixo kizo kawai. Idan bazakizo ba kisha zamanki
“Zanzo amma gaskiya sai nakai kwana bakwai d’ina kafin nan na lashe amarci na. Dan bazan Bari kalashi tanadin da nayima mijina nan kusa ba. Dan haka ka adana binkikenka akan udirin nawa idan nazo ka gaya min komai… Tana fad’in hakan bata jirayi cewarsa ba ta kashe wayartata danya bata haushi. Gashi bokan nata baya da waya bare takirasa taji ina NUFAISAT d’in taje…
Kwantawa tayi tana tuna yanda Adams yake da dad’in mu’amala.
Komai nashi daban yake. Dole mace taso shi dan yana da abubuwan da za’a soshi dansu.
Duk yawan bud’e idanta afannin karuwanci da iskanci taga Adams oganta ne ta wannan fannin. Saboda yasan kan mace fiye da tunaninta. Wannan kad’ai ya isa yasa NUFAISAT hauka akansa. Dan itama taji abinda NUFAISAT d’in take ji akansa.
Nan tunaninta ya fara juyewa akan gaskiya itace tadace da Adams ba NUFAISAT ba.
Kuma dole NUFAISAT tabar mata Adams taje can tanemi wani mijin ta aura????. Dan bazatayi sake da duk wani abu da yake dashi ya mazana su biyu ne ita da NUFAISAT suke da mallakinsa ba.. Haka dai tadinga sak’a sharri aranta har taji lokacin da NUFAISAT d’in tadawo.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button