LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Yana gaya mata hakan taficce daga falan..

ADAMS ya rungumi NUFAISAT da sakar mata kiss da cewa.. “Naji ajikina kamar wani abun nasan faruwafa. Kinga bata tab’a rikice mana irin nayau ba..
Qara lafewa a jikinsa NUFAISAT tayi da cewa.. “Aini tun jiya gabana yake fad’uwan nan kamar za’ayi mutuwa..

Ai ADAMS na jin hakan ya d’ago da fuskarta zuwa ga kallansa cikin tsoro yace.. “Wa kike tunanin zai mace.. Hawayene ya zubo mata tace.. “Nima ban sani ba mijina. kawai dai nafijin fad’uwan gaban yana qara yawaita yanxu…..
Innalillahiwainna’ilaihirraji’un shine abinda ADAMS ya fad’i da qanqame NUFAISAT kamar ance mishi itace zata mutun….

???????????????????? yau ba dariya y’an hannuna.. Kawai dai Ina gaisuwa. Danni naga abinda nagani a page d’in gaba
LEEKITAN ZUCHIYA saura page guda ya rage muku masoyana????
[8/5, 10:18 PM] ®????◾◼▪official Auntyn Luv.: ☆´-☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾☆• ❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH* *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ☆´-☆´- ☆“˜•☆• ¸☆“☆ª☆_☾☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story
April.. 2018.. Viawattpad@rahamanalele

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh’md Rufa’i Nalele..☆

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&tn=H-R

” بسم الله الرحمن الرحيم
realhausafulaniwriters@gmail.com
☆page 28☆ qarshe????

Lumshe idanta NUFAISAT tayi cikin jin wani iri ajikinta haka…
Shima ADAMS d’in yaji hakan dan haka saiya zaunar da ita kan kujera cikin rikicewa yake qare mata kallo da cewa.. “Koma miye zai faru ina rokwan Allah daya barni da matana….
Murmushi NUFAISAT tayimai hawaye ya qara zubo mata da cewa.. “Na tsinci kaina dasan binka asibiti yau mijina. Dan Allah karkace aa. Ina san kawai naganni dakai ne. Saboda naji wani mafificin tsoro araina yanxu kamar idan katafi wani abu zai faru dani..
Kallo d’aya zakama ADAMS kagane ya qara rikicewa.. Dan haka tashi yayi da shiga bedroom nata ya d’auko mata gyalanta yayafa mata da cewa. “tashi muje matata.. Dan nima ayanxu yanda nake ji araina bazan iyama tafiya nabarki cikin wannan yanayin ba..
Kan tabashi amsa kiran YUSUF ya shigo wayarsa.. Cikin sauri ya d’auka inda Yusuf d’in yake cemai dan Allah ya tawo asibiti da sauri yanxu ya kawo Hajjiyansu yau kam jikin nata ba sauqi.. Dan har aman jini takeyi.. Amma Dr Ibrahim ya bata temakwan gaggawa har tasamu bacci. Amma duk da haka Shidai kawai yazo dan yafi gane aikinsa fiye dana Dr Ibrahim d’in..
Rintse idansa ADAMS yayi dacemai Gashi nan zuwa..

Haka suka fito masu tsaransa suka bud’e masu kofar mota suka ficce sam kotakan MUSLEEMA Adams baibi ba..
Dan haka MUSLEEMAN najin fitarsu tashiga wanka sama sama da d’aukar y’arta little NUFAISAT tayafa gyalanta tafito da cema direban gidan yabi mata bayansu Auntynta NUFAISAT
ina yasan inda suka nufa. Yace mata ba mamaki asibiti suka nufa. Tace mai to maza yakaita gunsa…

Dake ADAMS yana baya direbansa ne me tuqasu dan haka NUFAISAT na jikinsa tayi lef da ita kamar matacciya..
ADAMS yana jin wucin zafin da jikinta yakeyi.
Nan ya fahimci zazzab’i ne yake shiga jikin nata..
Ai ba shiri ya d’ago da fuskarta arikice yake cewa.. “NUFAISAT ke NUFAISAT wai meyake daminki ne.. Shuru tamai dana me lumshe ido da bud’ewa kad’an kad’an..
Iya rikicewa ADAMS fa ya rikice.. Dan haka cikin tsawa yake cema direban nasa ya qara gudu..
Sam NUFAISAT baki ya rufe dan bata cewa umm bare um um..

Suna isowa ya kwantar da ita kan d’aya daga cikin kujerun office d’in nasa. Yusuf Yace mai.. “Lafiya meya sameta. “Wallahi YUSUF yanxu fah kamar wasa zazzab’i ya kamata. Bara na kira Dr Aryan ya duba min ita. Nan ya kira Dr Aryan yahau duba masa ita…
Aiko Dr Aryan ya gane zazzafan zazzab’i ne ya shigeta nan take..
Dan haka suje su kwantar da ita kan gadan asibitin dan bata cikakken temakwan daya dace da ita..

Nan ADAMS ya d’auki NUFAISAT dan kaita d’akin dake da gado. Aiko yana kwantar da ita sai yaga kamar bata numfashi.. Arikice yakai kunnansa setin qirjinta dan yaji tana numfashin ko batayi..????

Ai dai jin ADAMS yaji bata numfashi. Dan haka cikin wani yanayi me tafe da tashin hankali yahau girgizata yana cewa.. “NUFAISAT ke NUFAISAT ke matata.. Dan Allah kitashi.. Dan Allah na roqeki daki tashi pls.. NUFAISAT NUFAISAT. Haba NUFAISAT..

Ina shuru NUFAISAT bata da alamar amsa ma ADAMS…
Dan haka saiya saketa yaja da baya hawaye na zubo masa tunaninsa tamace ya kalli Dr Aryan da YUSUF dake waje jikin window yana Kallan abubuwan da suke faruwa yace dasu… “NUFAISAT tatafi Tamutu ta barni. Zan iya rayuwa kuwa.. Yana fad’in hakan ya zube qasa sumamme agun…
Nan Yusuf ya shiga d’akin da matuqar rikicewa ya temakama Dr Aryan suka sashi kan wata kuje dake d’akin.. daqer da sid’in goshi Dr Aryan yasamu ADAMS ya farfad’o.. Lokacin ko a akan idan NUFAISAT ya farfad’o dan haka suna had’a ido tasakar mai murmushin yaqe da cewa.. “Na d’auki kwanaki uku mijina ina jin wani yanayi ajikina da fad’uwar gaba. Hak’ik’a MUSLEEMA ita taji abinda taji yau aranta mijina. Ina san rayuwa daku amma hakan bazai yuhuba. Saboda lokacina yayi. haka dole natafi na barku. Takai qarshen zancen nata da zubo da wani hawaye me d’umin gaske. Sannan tacigaba da cewa.. Nagode ma Allah dayasa kakeda MUSLEEMA mijina.. Ina san kariqeta amana ka….
ADAMS bai bariba ta qarasa zancenta ba!!! ya katseta wajen cewa.. “Waya gaya miki idan babu ke zan iya rayuwa.. Banyi zatan abinda nake gaya miki akullum zai kasance awannan ranar ba.
Nima gasu sunzo da fararan kaya suna san d’aukar rayuwata NUFAISAT.????
Dan haka Ina yima MUSLEEMA fatan alkairi a rayuwarata.. dan zatayi rashi biyu a lokaci d’aya..

MUSLEEMAN na jikin window tana jinsu tana kallan abunda yake faruwa dan tun sa’adda YUSUF ya shiga d’akin tafahimci ba mamaki kosu NUFAISAT d’in suna ciki. Danta duba office d’in ADAMS baya nan.
hakan yasata isowa wajen da tsayawa gurus jikin windown d’akin. Ganin NUFAISAT kwance ADAMS kwance…

Qara tsaida kallanta NUFAISAT tayi akansa.. Tace. “Zata zama abin tausayi mijina. Ina san MUSLEEMA tasamu Farin ciki me d’orewa. Takai qarshen zancen nata da maida kallanta zuwa ga MUSLEEMA wacce fuskarta tawanku da jiqewar hawaye. Sai Kawai NUFAISAT ta sakar mata murmushi da cewa La’ilaha’illallahu-muhammadarrasulullahi-sallallahu a laihiwasallam. Tana fad’in hakan ADAMS ya rintse idansa da Kallan Yusuf yace.. “Kagani tatafi ko. Kamar yanda tatafi haka kaima zaka tafi. Ina rokwanka da Allah daka Auri MUSLEEMA kabata kulawar data zarce wacce nake bata. Dan nima… Bai qarama YUSUF zancen ba????.. ya b’ige da cigaba da faɗin.. La’ilaha’illallah muhammadan rasululla sallallahu’alaihiwasallam.

“NUFAISAT tatafi.. ADAMS abokina wanda ya zama d’an uwa gareni abokin hira abokin wasa da dariya. Abokin kasuwanci na. Me gaskiya me amana me kirki. Wanda yasan abinda ya dace ya bita.. Yusuf ya fad’i hakan da zubewa qasa sumamme…

Aiko MUSLEEMA batasan sanda tayi wurgi da little NUFAISAT ba… Ta kwalla qarar da duk asitin sanda suka jita… Hankalin kowa yayo kanta..
ALLAH yaso wata ma’aikaciyar wajan na tsaye gefe ita ta cab’e little NUFAISAT d’in amatuqar tsorace dan jifan da MUSLEEMA tama little d’in bana wasa bane…

Da wani shegen gudu MUSLEEMA tafad’a d’akin tarasa kan wazatayi cikinsu.. ADAMS ko NUFAISAT.????????.
Ai kawai sai tayi kan NUFAISAT… Fad’i take.. “Aunty dan Allah kitashi.. Dan Allah Dan annabi Aunty kitashi.. Aunty kinyimin alqawarin bazaki tafi ki barni ba. Kinyimin alqawarin kina tare dani.. Na shiga uku ni MUSLEEMA. Tafad’i hakan da komawa kan ADAMS tana meci gaba da cewa. Ya ADAMS kaima katashi. Dan Allah Dan soyayyarka da manzan Allah katashi kacema Auntyna tatashi muci gaba da rayuwa.. Wallahi ina sanku ina qaunarku ina fatan qare kowace rayuwa daku..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button