LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Kuma ita Hajjiya Hadiza tace mata Hakan ne dan tasamu nata raban ajikin Hajjiya Rukayyat d’in
Dan tasan tunda taganta cikin wannan hali ba qaramin sakar mata bakin aljihu zatayi ba wajen san tabi bokayen da suke bi tasamo mata makarin aikin da TAUDHAT d’in tayi mata

Ataqaice dai Hajjiya Hadiza tasa aranta zata nema mata magani ammanfa saita d’auki biyar ko bakwai tana samun nata kafin ta nemo mata maganin

Suna isa gida ko Ammi takira NUFAISAT da TAUDHAT awaya ta gaya musu komai dan haka duk ran da suka tashi dawowa suxo gida kawai dan sunbar asibitin.. Toh sukace mata.
Salim ya kalleta da murmushi yace.. “Ammi dakin bari nasan ya Adams zai gaya musu..
Itama murmushin tayi da cewa. Gwara dai dana gaya musu dan ka sanshi da mantuwa..
Hajjiya Rukayyat na jinsu tayi shuru tana saqa hukuncin da zata d’auka akan TAUDHAT idan tatashi…

Dake shi Adams yana da matsala. Sam baya iya kwana baiji mace ba. Idan ko kikaga ya kwana bejiki ba. To qila kunyi fad’a ne ko yaga kina bacci me nauyi ko rashin lafiya. Toh shine zai barki amman bazai raba kansa dake ba wajen jin d’uminki.

Hakan yasa yaji NUFAISAT a wannan dare. Kasancewar ranar girkinta..
Abin yazo mishi awani saban salo..
Yadai sani yafi samun nutsuwa da kwanciyar hankali agun NUFAISAT. Dan nesa ba kusa ba tafi TAUDHAT gamsar dashi.
Amma sai gashi jiya yaji dad’in TAUDHAT dad’in dabai tab’a tunanin samu daga gareta ba.
Ga kuma NUFAISAT Sam sai yajita babu dad’in komai ko kad’an. Wai me yake faruwa ne..

Kamar zaima NUFAISAT magana washe gari lokacin da yake breakfast.. Sai kuma ya fasa..
Abinfa bai canja zani ba. Dan yauma hakan ne ya qara kasancewa dashi agun NUFAISAT d’in
Har Allah Allah yake washe gari tayi wato girkin TAUDHAT yajita ko zai dad’a jin abinda yaji daga gareta..

Haka ko akayi.. Yana shiga girkin TAUDHAT yaji komai zamzam..
Washe gari yana breakfast ne kawai amman hankalinsa na kan NUFAISAT.. Tunani yake wane irin canji ya samu agunta ne haka me d’aga hankali..
Shuru yayi da barin abin aransa har izuwa lokacin daya koma girkin NUFAISAT d’in..
Still abinda yaji awancan girkin nata shiya qara ji..
Dan haka da safe suna breakfast ya kalleta cikin so da qauna yace.. “Kiyi hakuri matata zan gaya miki wani abu Sam bana San kiyimin wani kallo na daban. dan zan gaya miki ne saboda bana San rashin fahimta ya shiga tsakanina dake. Dan sirri na naki ne. Kuma aganina idan nabar wannan batun da zan gaya miki araina ban miki adalci ba. Saboda zan nuna miki wasu hali wanda bamu saba dasu ba ni dake. Hakan yasa na yanke shawarar gaya miki dan karkiga canji ki zargeni..
Shuru NUFAISAT tayi gabanta na fad’uwa dan tunkan taji miye abun taji hankalinta ya tashi…
Ahankali ta kallesa da cewa.. “Babu hakan tsakanina dakai. Magana indai ta fahimtace kaima kasan ina fahimtarka.
Dan haka fad’i kawai babu wani abu..
Zan gaya miki Amman ki tabbatar bazaki canja min ba. Dan nasan zakima maganar wata fassara ta daban.
“Nace maka Karka damu. Nime sauraranka ce da fahimtarka aduk lokacin dakaso na saurareka kona fahimcekan..

Jan numfashi yayi da cewa.. “Wancan girkin na TAUDHAT daya wucce ba Wannan na shekaran jiya ba. Naji dad’in TAUDHAT fiye da kowace ranah arayuwata.. Nasan da cewa kece macen da kike iya sarrafani yanda nake jin dad’i kuma nake samun gamsuwa gamsuwar da take zama a Zuciyata nake kasa mantawa dake. Sosai na shiga mamakin meyasa naji canji kuma yanxu daga gareki.
Wato matata tunda naji TAUDHAT a wancan girkin nata na rantse miki girkin da kika shiga kafin Wannan jinki nayi wani iri. Sam na nemi Wannan jin dad’in da nake samu daga gareki na rasa. Jinki nayi babu dad’in komai ko kad’an..
Cikin tashin hankali ta qara kafeshi da ido tace… “Banfa gane me kake nufi ba. Ban fahimta ba. Wallahi kwakwalwata ta d’auke. Dan Allah me kike nufi. Wallahi ban gane ba’

“Yafa dace ki gane ki kuma fahimta. Wannan abu ne bana wasa ba. Yanda kikaji na gaya miki haka shine gaskiyar zancen. Ina San jinki kamar yanda nasaba jinki matata. Dan ALLAH ki temaken kisan yanda zakiyi ki dawo kamar da. Dan bana San abin yayi nisa. Saboda na saba dake. Ke kanki kinsani. Wannan bakwan abu ne ya shigo rayuwarmu.
Sam bana San na fuskanci wata matsala daga gareki..
Nasan kuma kin dad’e da fahimtar hakan…
Adams na kawowa nan azancensa ya tashi da d’aukar jakarsa har yakai kofar fitta daga falan ya juyo da kallansa gareta yaci gaba da cewa… Ki fara neman canjin daga yanxu. Dan idan na dawo girkin naki naji canjin..
Tashi tayi a hankali tazo gabansa jikinta a sanyaye cikin wata murya tace mai. “Zan iya fitta unguwa yau..
“Zaki iya fitta akone lokaci banda dare kuma aduk lokacin da kikaso indai akan matsalar ne..
Murmushi ta sakar mai da cewa. “Nagode.
Shima Murmushin ya mayar mata da rungumarta ya sakar mata kiss a kumatu da d’ayan gefan kumatun kana ya ficce daga falan.. Ko shashin TAUDHAT baiyi ba ya shige mota masu tsaran nashi suka jashi.
Sanda sukayi nisa a tafiyar ne sannan ya tuna da TAUDHAT d’in saiya kirata awaya kan tayi mai uzuri ammishi kiran gaggawa ne.
Sanda ta magantu dan ganin da tayi yau lahadi ne kuma har ya iya ganawa da masu neman temako gunsa. Ya kuma qara komawa ga qawarta NUFAISAT amman ita ya kasa tsayawa ganinta koda na minti biyu ne..
Hakuri ya bata da cewa tamai uziri hakan bazata qara faruwa ba..
Tayi mai uzirin sannan tabishi da kalamai..
Murmushi kawai yayi da kashe wayar..

Itako NUFAISAT dafe kanta tayi cikin damuwa tana tunanin meyaja mata haka..
Can dataga tunanin bazai bata shawara ba dan haka sai kawai takira asiya da larai kan su qarasa mata aikin ta zata fitta ne…..
Aiko nan suka mata aikin cikin gaggawa sun fahimci tamatsu dasan tafitan akan lokaci..
Haka kawai suke jin tausayinta. Dan ganin yanda TAUDHAT ta aure mata mijin nata. qawarta aminiyarta..
Sun rasa ya akayi hakan ta faru.
Sudai suna Santa da qaunarta dan macece ita agaresu me kulawa da kyautata musu. sam bata y’amatarsu…
Suna gama yimata ta kulle shashinta sai gidansu..

Cikin nutsuwa ta zayyane ma mommy nata komai
ba wani batun kunya taqara da cewa.. “Nifa ina tunanin TAUDHAT tayi wani abu ne fitanta ranar mommy. Dan aranar yace yaji canji agareta..
“Idan ma tayi wani mugun abin ne kanta tayima bake ba.. Dan yanzu zanje na nema miki qaiqayi koma kan masheqiya kisha da Lipton insha Allah komai zaizo miki da sauqi..
Da murmushi NUFAISAT ta sakarma mommy d’in kiss a hannu tace.. “Nagode mommy..
“Ba komai ki jirani gun Hajjiya shuwa zani na ganta dashi da yawa satin daya wucce..

Dake acikin layin nasu ne Hajjiya shuwan take hakan yasa mommy d’in batafi minti goma ba tadawo da wani koren ganye shar adake..
Nan ta had’a mata Lipton tasaka mata maganin tabata tasha. Sannan ta kulle mata sauran tace taje dashi gida tasha na kwana uku insha Allah komai zaizo mata da sauqi

Saidai koda Adams ya dawo girkin NUFAISAT abin bai canja zani ba…
Aiko NUFAISAT na gane hakan ta fashe da kuka..
Bata kira mommy natan tagaya mata ba. Sai ta duqufa kaima Allah kukanta..

Ahaka Sanda suka shafe kusan wata uku da kwanaki ba abinda ya canja
Dan Yanxu ko kad’an Adams ya dena daurewa yana amfani da NUFAISAT d’in
Sam ya dena kulata ta wannan harkar..
Dan idan ya kulata gabansa zafi yake mai kamar ya saka kansa a rami me zafin wuta
Dan haka saiya denayi da ita ya kama kansa ran girkinta..
Tun abin na damun NUFAISAT har yazo ya dena damunta. Amman ganin da tayi sunfara d’aukar watanni nan hankalinta ya tashi dan koba komai ai ita mutum ce. Tana buqatar kulawar mijin nata..
Duk da cewar ko kad’an bai canja mata ba akan komai. Amman yanda wani lokacin yake juya mata qeya wajen kwanciya ai dole yafi d’aga mata hankali. Gashi taqi qara zuwa ta gayama mommy d’in nata. Ko zainab taqi gayama.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button