LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL
TAUDHAT ko sun tsula tsiyarsu sosai ita da Alhajin nata. Dan bai barta ba sai kusan sha biyu na safiyar yau. Bata koma gida ba sanda tabiya supermarket tayi sayayyanta dan ba qaramin kud’i ta cajesa ba
A haka takoma gida da kaya niqi niqi. Naci dana sawa dadai sauransu
Ita dai mamah mahaifiyarta ido ne kawai nata akanta.
NUFAISAT ko Auntynta Zainab na tare da ita tana qara ganar da ita tafannin girki. Dan yanzuma da daddare wani kayataccen girki take had’ama megidan nata.
Bayan TAUDHAT ta huta wanka tayi tanufi gun bokan nata tazayyane masa abinda ya faru tsakaninta da Adams wajen jin qamshin turaran da yaji. Wai tajishi shuru bai nemeta ba. Anya turaran ya bigesa dakyau kuwa.
Dariya bokan ya sheqe mata dashi yana me cewa. “Ai ina tabbatar miki tunda ya sheqa saiya aureki. Kuma ga ranar Auran naku dashi nan. Ya shafi gefansa dawani abin shed’anancinsa. Aiko muraran saiga TAUDHAT da ADAMS cikin d’aki d’aya. Tana zaune kan gado shima yana gefanta. Da lillib’i akanta irinna amare.
Aiko ganin hakan yasa TAUDHAT fashewa da dariya tace. “Ina sanka boka. Dan aikinka nakyau. Yanxu yaushe zaizo gareni.
“Ai kisha kuruminki kawai cikin daran nan zaki gansa. Godiya tamai sosai bayan ya d’anata ta karkad’e jikinta ta koma gida da matuqar farin ciki yau Adams zaizo gareta.
Sai farin ciki NUFAISAT take ganin yanda yake nuna santinsa akan girkin nata. Tace. “Yau fa nakai awanni ina had’a komai. Ba mamaki shiyasa yau santinka yafi na jiya.
Murmushi ya mata cikin so da qauna yace. “Allah ya dad’a miki albarka matar aljannah. “Amiin mijina
Bayan yagama ne tana kan ciyarsa yake ce mata. “My luv kinsan wacce na yanke shawarar Aura. Girgizamai kai tayi kuma da sauri tace. “aa. Sannan bana San nasan kowacece tunda dai auranta zakayi ai dole nasanta.
“Nasan zakiyi farin ciki da ganinta. Saboda kina qaunarta kuma.. “Haba mijina. Dan Allah kabar batun haka. Dan zuciyata tafara rawa. Karka b’atamin farin cikina.
Murmushi yayi da kama fuskarta yace. “Har abada bazan tab’a b’ata miki farin cikinki ba matata. Kiyarda dani
Kwantar da kanta tayi akan kafad’arsa tace “naji ana kiran sallah in tashi maka daga kan cinya ko.
“Eh. Amman daga masallaci zan wucce wajen qanwar taki kina da sak’o gareta Wanda zan bata ne. “Aa Saidai kagaya mata ina gaisheta. Sannan ta kulammin dakai sosai. Idan tabari kadawo min gida rai ab’ace saina hukuntata.
“Insha Allah ko zan gaya mata.
Haka NUFAISAT tatashi daga jikinsa ya sakar mata kiss da rungumarta kana ya ficce daga falan. Tana jin fitarsa wajen get hawaye ya zubo mata. Ahankali tace “baka iya yimin qarya ba mijina. Sannan wannan gaskiyar da ciwo take. Zan iya jure komai arayuwata amman bazan iya jure ganinka da wata ba. Tana kaiwa qarshen zancen nata tarushe da kuka wiwi. Harda d’aga hannuwanta ta d’ora aka tana me cigaba da cewa.. Wayyo Allah mijina aure zaiyi. Mijina kishiya zaiyimin. Mijina yau ya tafi zance gun wata. Dan Allah zuciyata kimin adalci kidena jin wannan zafin da rad’ad’in nan ki sake kibarni na huta dan wata rana bama zance ba wallahi raba shinfid’a zanyi dashi……
Haka NUFAISAT ta dinga sambatu ita d’aya. Daga qarshe dai tayi toilet tayo alwala ta gabatar da sallar i’sha tare da kaima Allah kukanta akan ya cire mata damuwa da kishi akan Auran mijin nata
Da gaske Adams daga masallaci gidansu TAUDHAT ya nufa.
kunsan dama a kintse TAUDHAT d’in take. Tunda bokanta ya tabbatar mata da zuwan Adams gareta cikin daran
Dan haka tana ganin wayarsa tamiqe jikinta na rawa ta d’auka da cewa. “Ina maka fatan ALKAIRI mijin k’awa.
Da murmushi Yace “Tare dake. Ina ƙofar gidanku Allah yasa ina da raban ganin kyakkyawar fuskarki. “Mezai hanaka gani. Bayan nida qawata duk mallakinka ne. “Insha Allah kuwa. Zanso dai naganki yanxu kafin kicinye min lokaci na awaya.
“To kakashe mana. Daka juyo da fuskarka izuwa ƙofar gidamu daka ganni katabbbatar bazan cinye maka lokaci ba.
Murmushi yayi bayan ya juya ganinsa ga kofar gidan nasu nanko ya gantan a kofar gidan. Hakan yasa ya kashe wayan. Dayi mata nuni data shigo cikin motar. Ba musu tashiga gaban motar tana me kallansa da cigaba da cewa. Nasan dai ba abinda zai kawoka ƙofar gidamu adaidai wannan lokacin imba wani abu me mahimmanci ba. Allah dai yasa qawata tana lafiya. Danna farajin fad’uwar gaba.
“Ai dole kiji hakan. Dan kina San aure mata miji. Wato TAUDHAT Nazo miki da wata magana me mahimmanci.
“Kafin ka Sanar min da maganar ina San naji batun lafiyar qawata. Dan wallahi da gaske zuciyata tasaka tsayuwa waje d’aya. Sannan meyasaka cemin zan aure mata miji.
“Tana cikin k’oshin lafiya. Dan tacemin mah in gaya miki ki kula dani sosai. Dan idan nakoma mata gida rai b’ace saita hukuntaki.
“Masha Allah. Naji dad’in yanda take cikin koshin lafiya. Batun zan aure mata miji fah.
“Shine ya kawoni. Kuma ina San kima abin kyakkyawar fahimta.
NUFAISAT tafi saninki fiye da kowa arayuwarta. Sannan tana sanki fiye da kowa a qawayenta. Hakan yasa nazo da k’okwan barana akan kiyarje min na Aureki matsayin matata ta biyu dan nasan idan kece kika zamo kishiyarta bazaki tab’a bata matsala ba. Amma fa idan kin yarda dan babu dole aciki. Kawai farin cikin matata nake nema.
Jan numfashi TAUDHAT tayi kamar gaske tace. “Idan har dai NUFAISAT ta amince zan aure ka Adams. Saboda katara duk wani abu da y’a mace take fatan samu agun mijin auranta.
Ina sanka Adams. Amman dan qawata nake sanka. Inasan inciga da raya mata wannan San nata acikin zuciyarka. Dan bana sha’awar wata can tazo ta b’ata mata gininta….
“NUFAISAT bata San ke nayanke shawarar aura ba. Bare har aje batun amincewa. Taqi bani damar na gaya mata hakan. Hakan yasa ban takurata ba. Dan nasan idan taganki matsayin abokiyar zamanta zataso hakan kuma zatayi farin ciki sosai.
Murmushin mugunta TAUDHAT tayi dayimai wani kallo qasa qasa tace.. “Idan ko haka ne nayarda da Auran ka. Ko yanxu kace a d’aura wallahi nabaka goyan baya.
Murmushi yayi da cewa. “Ina San kiyimin iso wajen mama acikin daran nan
Haka ko tamai iso wajen mama.
Hankalin mama ya tashi sosai da buqatar da Adams yazo mata dashi.
Dan tanuna mai hakan bai dace ba sam. Bai dace ya Auri TAUDHAT ba kuma yana Auran NUFAISAT
Nutsuwa sosai Adams yayi yabata hujjojinsa nasan yin hakan kafin tayarda.
Sun yanke shawarar limamin unguwar shi zai bada Auran TAUDHAT d’in. Kasancewar basa da kowa masu ganin mutuncinsu
Adams yaji dad’i sosai. Dan haka acikin daran bai duba qurewar lokaci ba ya nufi gidansu.
TAUDHAT Adams na fitta ta rufe mahaifiyarta da masifa wai akan me zata nunama Adams bai dace ya aureta ba
Wannan wane irin baqin ciki take mata.
Ita dai mama shuru tayi mata hakan yasa ta qare mata rashin kunya ta nufi d’akinta da mafificin farin cikin burunta ya kusa cika
Adams ya tadda Dadynsa na qoqarin kwantawa. Anan ya zayyane masa komai kuma Dadyn yayi farin ciki da hakan. Yace Allah ya kaisu gobe ya qara nazari akan lamarin. Toh yace masa ya nufi gun Amminsa. Saidai ita Ammi yana gaya mata komai yaga jikinta yayi sanyi bata wani nuna farin cikinta ba.
Shidai ahaka ya lallab’a yabarta lafiya dan yasan idan ya d’auki lokaci agunta ba makawa saita kawo mishi dalilinta na rashin nuna farin cikin nata. Kuma ya saba bin abinda take so. Yanxu saita canja mishi ra’ayi. Kuma abinda bayaso kenan akan wannan lamarin. Dan yana ganin Auran TAUDHAT shine mafi ALKAIRI agaresa da kuma matarsa NUFAISAT.
Da farin ciki yakai gidansa lafiya lokacin qarfe goma sha d’aya na dare. Tun NUFAISAT nasaran dawowarsa hardai ta hakura bacci yayi awan gaba da ita