LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL
Shiko ganinta tana bacci hankali kwance sai kawai yayi wanka da gabatar da lafula kana yabi jikinta ya kwanta anan taji ajikinta yada dawo. Dan har ta bud’e ido Amman bata nuna mai ta farka ba.
Tunani kawai takeyi akan yanxu sai sha d’aya zai dinga dawowa. Hmm Allah ya sanyaya zuciyarta..
Wàshe gari bata nuna mai komai na dad’ewar da yayi jiya ba. Sam baiga wani alamu na b’acin agareta ba.
Hakan yasa yaji dad’i sosai harya tafi office da nutsuwa. Amman ta gayamai zata gida tagaida momynta
Ya amince mata dan yasan tana buqatar tattaunawa da mahaifiyartata akan lamarin Auran nasa dan tabata shawara. Kuma yana da tabbacin zata bata shawara tagari dan yafi kowa sanin halin momynsu nata wajen nutsuwa da hankali sanin ya kamata da hak’uri…
Aranar qanin Dadynsa dashi Dadyn kansa sukaje nemammai Auran TAUDHAT d’in. Dan Dadyn yayi tunani yaga dacewar hakan. Kuma wani iko na Allah ko kad’an abinciken dayasa amai akan TAUDHAT d’in ansamu kyakkyawar sheda akanta. Sam basuci karo da mummunar sheda akanta ba..
Wannan dalilin yasa suka kai sadaki awashe garin ranar. Sannan suka buqaci da asaka ranar d’aurin aure nan da sati d’aya☝????..
Murna wajen TAUDHAT ba’a magana
Sai bayan kwana biyu Adams ya gayama NUFAISAT Auran nasa nan da kwana biyar
Duk da taji fad’uwar gaba amma bata nuna masa ba. Ita yasa agaba sukaje manya manyan boutique suka had’o lefe na kerema sa’a. Dan Wannan tsarin Amminsa ne tace mai yaje da NUFAISAT susuyo komai. Duk abinda ta d’auka ta d’aukarma amaryar. Hakan yasa komai bibbiyu NUFAISAT take d’auka. Ba lefi sun samu akwatina shidda shidda ammafa manya manyan…????
Qanwar Hajjiya Rukayyat da qawayenta ne sukaje gidansu TAUDHAT sukakai lefan awashe gari.
Anan Hajjiya Rukayyat taja TAUDHAT gefe tana kitsa mata wasu kalamai kamar haka..
Kasan cewar bokanta ya bata tabbaci akan bazata samu nasara akan NUFAISAT ba. Saboda tana da qarfin imani. Zadai ta iya cin galaba akan TAUDHAT. Ya bata wani magani yace taba TAUDHAT d’in cikin wani abun ci. idan har taci bazata tab’a haihuwa da Adams ba. Idanko ta haihu da Adams toh wallahi cikin wani ne bana Adams ba
Wannan dalilin yasa Hajjiya Rukayyat ta dafama TAUDHAT kaza da maganin tabata yanxu amatsayin wai kyautarta na maganin mata. Har tana qarama TAUDHAT da qarya wai shi tabama NUFAISAT shiyasa Adams yake qaunarta kamar ransa. Aiko jin Hakan nan take TAUDHAT ta miqe agaban Hajjiya Rukayyat tacinye kazar nan harda sid’e flasks.
Dariyar mugunta Hajjiya Rukayyat tayi da jinjina kishi irin na TAUDHAT
Hmm tab’e baki tayi da cewa aranta.. tunda buqatata tabiya banda matsala dake..
Dan haka da farin ciki sosai Hajjiya Rukayyat tadawo gida tana bama Ammin Adams da Dady labarin karramawar da mama mahaifiyar TAUDHAT tayi musu. Sosai tanuna taji fad’in zuwanta gidan.
Jin hakan yasa Ammi da Dady jin dad’i sosai
Gobe ne d’aurin aure dan haka Adams yasa akazo aka canjama NUFAISAT wasu abubuwan d’aki
Duk da cewar shashin amaryama shiyayi mata komai Amman hakan baihana idan kashigo shashin NUFAISAT kaga nata yafi baka sha’awa da birgewa ba.
Ita amarya nata shashin komai Skye blur ne.
Yayinda komai na NUFAISAT ya kasance ash color n black
Gidan ya qara fitowa fiye da tunanin me tunani.
NUFAISAT ta kalli ADAMS da kulawa tace. “Gabe zaka zama ango Amman banji kana maganar yin wasu bidi’o’eh da shagalewa ba
Murmushi ya sakar mata da bata kiss a wiya yace. “Amaryama tabuqaci ayi hakan amman nace mata banda ra’ayi. Saboda bani San nuna miki d’okina.
Saidai yau sunyi walima da qawayenta har nayi mamakin yanda baki halacci wajen ba kamar yanda tace min
Murmushi NUFAISAT tayi da cewa. Ba’a gayyaceni ba. Hasalima bansanta ba. Aganina abu me wiya ne zaisa taganni wajen. Gaskiya naji haushin kawo maka wannan qarar tawa da tayi.
“Toh ai gani nayi Ku qawayene. Ai basai ta gayyaceki ba.
Zadai tazama y’ar uwata idan tashigo gobe. Dan bazan barta a matsayin qawa ba. Kaga mubar batun nan mubarma goben kawai haka kawai naji bana jin dad’i azuciyata.
Dake dama suna zaune ne akan kujerar falo saiya janyota jikinsa ya rungumeta dan ya hango bama baman kishi b’aro b’aro a tattare da ita.
Dan haka yau baija da nisa ba. Yashiga lallab’ata. Shi sai Yanxu ma ya tuna ai batasan TAUDHAT zai aura ba.
Washe gari asabar NUFAISAT da yayarta Zainab da sauran y’an uwanta harda momynsu dake wayayyiyar macece tazo gidan haka suka saka NUFAISAT agaba suka dinga mata nasiha dajan hankalinta akan ta qara hak’uri akan komai karta saka damuwa akan zuwan wannan amaryar tata.
Aiko da misalin qarfe gamo sha d’aya aka d’aura auran ADAMSY da TAUDHAT…
Kowa ya watse a gidan yazamana shuru daga NUFAISAT dake shashinta sai y’an aiki dake shashinsu sai amarya TAUDHAT dake nata shashin.
A haka Adams ya dawo shida masu tsaransa da abokanayansa biyu wato Yusuf da wani wai shi Suleiman
B’angaran NUFAISAT suka nufa nan suka ganta afalo cikin kyakkyawar shiga ta doguwar rigar less jah. Ya haskata sosai abinka da fara.
Tashi tayi tana musu barka da zuwa cikin yaqe…
Da wani hali suke gaisawa da ita suna masu kiranta da uwar gida ran gida. In bake ba gida. Murmushi kawai tayi musu da kama hannun mijinta tana mece musu dasu tashi aje rakiyar da ita zuwa d’akin amaryar…
Ta basu mamaki sosai haka taja mijin nata gaba Yusuf da Suleiman sukabi bayansu Adams na qara janta jikinsa yana kuma hango farin cikin dazai ganta aciki idan taga TAUDHAT ce amaryar tata…
Hmm???? masu karatu yake nan..
By Rahma Nalele Auntyn luv
[6/21, 9:11 PM] ®????◾◼▪official Auntyn Luv.: ☆´-
☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾☆• ❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH* *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆
☆´-☆´- ☆“˜•☆• ¸☆“☆ª☆_☾
☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story
April.. 2018
Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh’md Rufa’i Nalele..☆
© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM????
☆We the best ☆
” بسم الله الرحمن الرحيم
☆page 11☆
Sunsami TAUDHAT d’in akan gadanta kanta lullub’e da mayafi. NUFAISAT ta zauna kusa da ita da kama hannunta ba tare data bud’e mata fuska ba tace. “Aminci agareki ya y’ar uwata. Yau gaki agaidan mijina matsayin matarsa ta biyu. Ina rokwanki da Allah daki d’aure kiba mijina kulawar data dace. Wallahi ina San farin cikinsa. Allah ya bamu zaman lafiya da rayuwa me d’orewa.????
TAUDHAT batayi magana ba. Amman tad’an motsa alamun tajita.
Ganin hakan yasa NUFAISAT sakar mata hannu da tashi tama abokanayen nasa sallama ta ficce daga d’akin
Tana fitta Yusuf da Suleiman suka ma TAUDHAT nasiha kana itama suka ajiye mata kaza da madara kamar yanda suka ajiyama NUFAISAT suka fito suma daga d’akin
A can waje Yusuf ya dingama Adams tsiya akan yadai bi TAUDHAT a hankali danyaga har wani rawar kai yakeyi.
Adams yayi murmushi da cemai. Haba dai rawar kai. Sai kace wani saban shiga. Bana tunanin zatazo min da wani abu wanda NUFAISAT bata zomin dashi ba. Kudai kawai kujira gobe. Koma miye zaku gani akan fuskata dan kyakkyawan amarci baya b’oya..
Dariya suka sheqemai da ita kana suka shine motocinsu damai sallama megadi ya kulle gida.
Part d’in NUFAISAT Adams yayi. Amman yana murd’a kofar tata saiya jita a kulle. Ahankali yashiga bugawa yana kiran sunanta amma shuru wai malam yaci shirwa. Haka ya koma part d’in TAUDHAT lokacin tana toilet da alama alwala takeyi. Hakan yasa ya zauna jiranta yana tunanin meyasa NUFAISAT kulle mishi kofa ba tare da sun yima junansu sai da safe ba…. Fitowar TAUDHAT ne ya katse mai tunanin. Ya kalleta da murmushi yace. “Amarya kinsha qamshi. Dafatan kina tare da alwala mu gabatar da sallar godiya ga Allah daya bamu damar zama ma’aurata.
Da matuqar farin ciki tace.. “Dama banyi isha bane shine nayo alwalar.
“Toki gabatar kafin nan na shirya saimu gabatar da wannan.
Toh tace mai ya ficce ita kuma tacanja kaya zuwa wata doguwar riga ta bacci. Kana ta saka hijab ta gabatar da sallar i’sha’in.