LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Yana zuwa room nasan yayi wanka da qara d’auro wata alwalar ya canja kaya shima zuwa na bacci duk NUFAISAT ta tsaya mishi arai.
Dan haka kwanciya yayi agadansa yahau kiran number nata. Saidai ya kira yafi sau goma amman taqi d’aga wayar. Nanko take hankalinsa ya tashi ya nufi part d’inta yana bugawa da kiran sunanta. Bata bud’e kofar ba. Saidai yaga shigowar message d’inta cikin wayar tasa.
Hakan yasa ya dena buga kofar ya shiga duba abin data rubutomai kamar haka.
Haba mijina. Bayan ina tare dakai. Kawai bazan iya jure ganinka kazo yimin sallama zaka gun tawa bane. Hakan yasa na kulle kofata. Kuma idan na d’auki wayarka kuka zan fashe maka dashi wannan dalilin yasa naqi d’aga wayanka. Kaganni nan ina cikin koshin lafiya. Aci amarci lafiya da qanwata. Saidai Karka wahalar da ita. Dan bazan jure zuwa yin jinya da safe ba????.

Murmushi ADAMS yayi da mamakinta. Kai shiyama kasa gane wane irin kishine da ita. Yau tanuna gobe kuma kaga kamar bata da matsala da dashi. Da wani hali ya tura mata da… Allah ya barni dake matata. Wallahi zanyi maraicinki sosai cikin wannan dare. Kasancewar shine na biyu atarihin rayuwarmu da muka tab’a raba shinfid’a.
Yana tuna tura mata da hakan yabar ƙofar ɗakin nata.
Akan sallaya yaga TAUDHAT tana zaman jiransa yace da ita.. “Amin afuwa nabar amarya da jiran ango
“Batun afuwa babu tsakaninmu. Nasan dai akwai abinda ya riqemin kaine. “Kwarar kuwa yanxu tashi mu gabatar da sallar..
Haka tatashi suka gabatar da sallar
Yayi musu addu’a da tambayarta yanda take wankan tsarki tako gaya masa. Yaji dad’in haka. Sosai.
Haka yasa mata kaza a gaba da madara yace ta daure suci.
Ba wani kunya can tasake sukaci suka koshi. Kana labari ya canja.
Dan koda wasa Adams baiji aransa zai iya tsallakema TAUDHAT wannan dare batare da wani abu ya shiga tsakaninsu ba.
Ya jata jikinsa yana aika mata da wasu sakwanni. Yana me jin dad’in yanda doguwar rigarce kawai a jikinta.
ADAMS gwanine qajen iya sarrafa mace. Danko a wasan ni ya barki bazaki tab’a San yabar rayuwarki ba.
Yasan kan mace fiye da komai arayuwarsa. Yasan yanda zai sarrafaki kimanta duniyar da kike.
Sannan idan yagane inda kikafi mutuwa agun yakan iya b’ata lokaci wajan ganin ya qara b’ullo miki da wata hanyar da zatafi wacce kikafi sani wajen mutuwa akanta.
Lamarin yana tsuma TAUDHAT sosai fah.
Dake tayi shaye shayen maganin mata hakan yasa Adams yaji dad’inta sosai.
Saidai hankalinsa ya tashi sosai dayaga ƙofar bashi bane ya fara bud’eta.
A hankali ya tashi da zama gefan gadan ya sauke kallansa akanta bayan komai ya wakana. Yasani ya bata wahala sosai. Dan yasan ba kowace mace bace wacce zata iya dashi imba NUFAISAT ba. Saidai TAUDHAT tabashi mamaki. Bayan yanda kofa take bud’e harda wasu salo data kware wajan nuna masa su.

D’an tashi tayi a hankali ta jingina da bangwan jikin gadan nata ta kallesa kad’an ganin ita kawai yake kallo saita sadda kanta qasa tace dashi.. “Kamin rai Ya mijina. Nasan na b’oye maka shi. Abun ya faru ne wata ranah danaje bikin wata qawarmu. Lokacin da aka tashi daga bikin. Sai wasu samari suka buqaci dana shiga motarsu suragemin hanya. Har nayi musu musu amma saboda nacinsu da qaddarar da take kaina saina shiga motar tasu. Adams ban tashi tsintar kaina ba sai a wani gida cikin wani d’aki kan gadan wani. Yana d’aya daga cikin SAMARIN dake cikin motar da suka d’aukoni. Yana gefena lokacin dana samu kaina. Anan nagane yayi min b’arna yayi min illa ya rabani da mutuncina da kimata. Nayi kuka nayimai Allah ya isa amman da dariya yabini da ita. Daga wannan ranah nake cikin kunci amman na kasa gayama kowa. Duk da cewar naje asibity an tabbatar min da lafiyata qalau bana tare da wani ciwo. Amman hakan bai sani nasamu nutsuwa ba. Dan nasan zan fuskanci qalubale agidan aurena.
Wannan dalilin yasa nayi saurin amincewa da auranka dan nasan kai kad’ai ne wanda zaka iya rufamin asiri ka rayu dani cikin aminci batare da nuna min tsana ko tsangwama ba. Da TAUDHAT tazo nan azancenta sai kawai tarushe da kuka kamar gaske☹

Shuru Adams yayi dajin tausayinta. Hakan yasa ya rungumeta da lallashinta akan tayi shuru insha Allah bata da matsala dashi.
Amman zai ibi jininta gobe dan yaje asibiti ya tabbatar da lafiyarsa.
Ba qaramin jin dad’i TAUDHAT tayi ba.
Dan batayi tunanin shirin nata zaiyi tasiri agunsa nan take haka ba.

Shiko Adams har a zuciyarsa yayarda da abinda tace mai. Hakan yasa yacire duk wani mugun tunani akanta da wani mamakinta dayaji yanzun yasaka aransa zai rayu da ita dan ya tabbatar ba qaramin lada zai samu agun Allah ba.

Haka ya tsaftace kansa itama ta tsaftace kanta. Ta koma da kwantawa shikuma yahau yin nafula da qara godema Allah akan al’amuransa. Saidai yaji ya qara San NUFAISAT aransa dan koba komai shine dai ya bud’eta aleda. Sannan uwa uba tafi TAUDHAT dadin harka. Duk da cewar yaji dad’in TAUDHAT d’in. Amman gamsuwar tashi yafi jinta agun NUFAISAT. Gaskiyama babu had’i
Haka kafin ya bar kan sallayar sanda ya tura ma da NUFAISAT message akan takula sosai da kanta. Babu wata y’a mace daza tasha gabansa akanta. Wallahi yanxu ya qara tabbatar da hakan.
Yana tura mata ya tashi da tashin TAUDHAT yana ce mata tatashi suje bedroom nasa su kwanta bazai iya kwana a d’akinta ba. Dan bai saba da hakan ba
Ba musu tabishi d’akinsa suka kwanta yana me rungumarta saboda sabo da yayi da NUFAISAT…

NUFAISAT ko tunda tasama ƙofarta key. Tayi sallar i'sha fad'awa tayi a gadanta kawai tana tunani barkatai akan yau ba ita ba kwana da mijinta. Zaije ya kwana da wata ba ita ba. Ya dinga mata abinda yake mata. Ai bata ankara ba!!! Wani kuka me ciwo ya kufce mata. Nan tadinga yi tana sambatu.

Tana jin bugun kofarsa na farko bayan ya raka abokanayen nasa amman taqi bud’emai. Dan wani haushinsa ne yazo ya rufeta. Gani take baiyi mata adalci ba
Tana jinsa yabar wajen
Haka kiranta daya dingayi awayama tana kallan wayar tayi burus da ita. Daya dawo ne yana qara buga mata kofar saitaji sanyi azuciyarta tatabbatar ya damu da ita. Hakan yasa ta tura masa da text message har yake bata amsar nan ta d’azu
Ganin ya qara turo mata da wani text d’in kusan biyu na dare hakan yasata ganewa komai ya wakana tsakaninsa da amaryar..
Hawaye me zafi yashiga bin kuncinta
Lokacin tana kan sallaya dan takasa bacci kwata kwata. Hakan ne yasa ta yanke shawarar d’auro alwala tafara bada lafula tana rok’ar Allah. Sanda taji idanta na rufewa kana tabi gado ta kwanta.
Ko baccin awa biyu batayi ba taji ana kiran sallar asuba. Nanko ta duro da qara d’auro alwala tagabatar da sallar raka’atailinfijir kana tayi sallar asuba tana cikin lazimi bacci me qarfi yayi awan gaba da ita☹

Ba ita ta farka ba sai kusan goma da rabi… Aiko da sauri tatashi hankalinta ad’an tashe tana tuna abinda momynta ta gaya mata akan ta daure zuciyarta ta had’a musu breakfast qarfe takwas. Aiko cikin sauri sauri gudu gudu tahau had’a musu me sauqi. tia da soyayyan dankali da kwai had’i da fafesun kazar da auntynta Zainab tayi mata jiya tasa cikin furish dama dan tabasu tayi mata…
Sanda tayi wanka tasaka wasu fitunannun kaya riga da siket ne na atamfa d’inkin ya karb’e irin sosai d’innan. da feshe jikinta da turaranta sannan taje taleqa ta window taga Sam ADAMS bai fitta ba. Amman kamar ana kwankwasa mata kofa d’azu. Tayi ma tunanin ko shine ya fitta. Tab’e baki tayi da sake labulanta tana rayawa aranta qilama su Asiya ne
Haka ta nufi baban falo falan dazai sadata da shashin TAUDHAT haka dana Adams d’in to anan tajera komai na abinda tayi musu kan dining.. Sannan tayi shashin Adams d’in.. Bata ganshi ba. Sai taji gabanta ya fad’i tatsaya tana tunanin taje d’akin amaryar ne kota koma shashinta…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button