LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL
Abinda da yafaru ko da Adams da TAUDHAT shine.. Bayan yata sheta sallar asuba sai shi yayi masallaci. Bai dawo ba sai kusan qarfe bakwai da rabi kamar yanda ya saba dawowa.
Anan ya dinga buga kofar NUFAISAT da kiran wayarta amman shuru
Yana cikin hakan ne kiran wayar Yusuf ya shigo mai waya akan dan Allah yazo asibitinsa yanzu zaikai Hajjiyansu can ciwan zuciyarta ne da alama ya tashi dan gashi tana dafe da zuciyar wai tana mata zafi kuma tana numfashi sama sama.
Da sauri Adams yace toh ya kaita gashi nan zuwa.
Aiko da sauri ya koma shashinsa ya shirya ya ficce shida masu tsaransa basu dire ako ina ba sai’a asibitin nasu. Anan yaga harsu Yusuf d’in sunzo
Da sauri ya shiga nubata. Aiko ya samu nasarar gane me yasa hakan tafaru da ita. Wai damuwace..
Yusuf Yace “narasa me yake damun Hajjiya wallahi
Murmushi ADAMS yayi da cemai. “Yaci ace Yanxu ka gane miye matsalarta. Zata samu kanta nan da awa biyar. pls ka temakemu kagano damuwarta dan Allah.
Toh Yusuf yace mai.
Anan suka bar qanin babansu Yusuf da matarsa dan Yusuf d’in yace yunwa yakeji Adams yace toh yazo su koma gida susamu abinda zasuci.
Lokacin da suka dawo gidan ne NUFAISAT ta shiga wanga Lokacin sha d’aya saura. Shine sukayi shashin TAUDHAT inda tayi farin ciki da hakan amman bata nuna musu ba tace musu bara ta shiga ciki ta had’a musu abinda ya dace.
Anan Yusuf yake mata tsiya wai amarya da aiki anya basu takurata ba
Murmushi kawai tayi mai da nufar kitchen d’in nata
Adams yace wallahi na zak’u naga NUFAISAT. Kagafa har Yanxu banji motsinta ba kusan 11. Yusuf Yace “mu bata minti goma idan bamu jita ba sai’a b’alla kofar muga ko lafiya. “Aiko haka za’ayi. Adams ya bashi amsa da fad’in hakan cikin damuwa.. Wannan shine abinda ya faru
Har NUFAISAT ta nufi yin shashinta sai kuma ta kalli agogwan falan Adams d’in taga sha d’aya daidai. Dan haka sai kawai tayi qarfin halin murd’a kofar dazata sadata da falan amaryar tana meyin sallama
Aiko karab ta had’a ido da Adams da Yusuf
Murmushi ta sakar musu da qarasa shigowa falan tana me cewa.. “Amin afuwa tunda nake arayuwata ban tab’a makara irin nayau ba.
Tsaki Adams yaja da kallan Yusuf Yace.. “Kasan Allah na manta da wannan kofar da zata sadani da ita.
Yusuf yayi murmushi da cewa. “Nima nayi mamaki sosai danaga ta b’ullo tanan
NUFAISAT tazauna kusa da Adams tace kaddai kanata bulayin buga min waccar kofar.
“Yanxu ma muka yanke shawarar zuwa mu b’alle ƙofar taki muga ko kina cikin k’oshin lafiya..
“Ina lafiya lau. Yanxu dai bara na gaisa da amarya sai muje babban falo danna had’a muku komai na breakfast
Murmushi yayi da shafa gefan fuskarta yace. “Nayi missing d’inki matata. Dana jiki shuru wallahi duk bana cikin nutsuwata. “Yanxu dai ina kadawo normal
Kiss ya sakar mata a kumatu da fad’in. “Sosai mah.. Bara na kira miki amaryar dan tashiga kitchen ne had’a mana abinda zamuci.
“Toh na hutashat da ita dannayi komai.
Murmushi ya sakar mata da kwala ma TAUDHAT kira da AMARYA…
Da sauri TAUDHAT tafito daga kitchen tana niyar amsawa. Amman ganin NUFAISAT kusa da Adams saita tsaya cak tana me yarfe hannu da alamata wanke hannun tayi..
Da sauri NUFAISAT tatashi ta nufi TAUDHAT da mamaki take ce mata. “Har sab’anin da muka samu yakai kishigo cikin gidan nan kikasa fara shigowa shashina saina abokiyar zamana har kina tayata aiki.
Sosa qeya TAUDHAT tayi cikin wani hali dan taji wani iri tace da ita. “Aina d’auka ya gaya miki jiya cewar nice Amaryar taki…..
Cikin furgita NUFAISAT tace.. “What????. Da zaro ido… Ta juya da kallanta ga Adams sannan tadawo da kallanta gareta tacigaba da cewa… Me kike cewa. Kina nufin kicemin kece wacce ADAMS ya Aura matsayin matarsa ta biyu✌????..
D’aga mata kai TAUDHAT tayi da cewa.. “Eh ni ce ya Aura. Saboda yasan zakiyi farin ciki sosai da hakan….
“Farin ciki. Wane irin farin ciki. Kefa TAUDHAT ce. Aminiyata wacce na d’aukeki amatsayin y’ar uwata. Yau kece agabana kina gayamin wai mijina keya Aura saboda yasan zanyi farin ciki da hakan.
Haba TAUDHAT wannan wata irin amsa kike bani. Daga tambayarki saiki jefeni da muguwar kalma irin wannan. Tayaya kike tunanin ADAMS zai iya rainon zuciyarmu nida ke..
Dafa Y’ar uwa kike kirana. Aminiya qawa. Amma jiya ki rasa wanda zaki Aura sai mijina..
Shuru TAUDHAT tama NUFAISAT tana me kallan qasa. Ganin hakan yasa NUFAISAT tafe kanta dayake barazanar tarwatsewa ta kalli Yusuf arikice tana me cemai!!! Kana ganin abinda yake faruwa tsakanina da TAUDHAT Yusuf.. Waifa fad’amin take wai mijina ADAMS ta aura..
Ka tuna natashi da ita tun yarinta. Na rayu da ita har gidan aurena. Wai yau itace take amatsayin kishiyata YUSUF
Shuru Yusuf yayi cikin matuqar tashin hankali danshi wallahi sai yanzu ya gane kuskuran da suka tabka..
Sam alkairin Auran ya hango wallahi ko kad’an bai kawo cewa hakan zata faru ba. Sam ya manta kishi irin na mata..
Adams ya tashi cikin tashin hankali idansa akan NUFAISAT yace.. “Wai me yake shirin faruwa ne. Nayi hakan dan naga farin cikinki amman yanaga sab’anin hakan.
Cikin zubda hawaye NUFAISAT ta kallesa da wani b’acin ran da tunda yake da ita bai tab’a ganinta cikinsa ba tace dashi… “Dalla rufema mutane baki munafuki azzalimi wanda ya manta abinda ya dace ya duba wanda bai dace ba karasa wacce… Ai bata qarasa futucinta ba!!! ya wani d’auketa da marin daya daqarqare iya qarfinsa da shi. Dan kalmar munafuki azzalimin data ambatasa dasu ta shigesa sosai..
Da gaske sanda NUFAISAT taga wasu taurari suna mata yawo afuskar. Dan bata tab’a cin karo da wannan azafaffen marin ba.
Hakan yasata dafe wajen da sauri ta tsaya dan dawowa hayyacinta na sakwanni. Kana kuma tafara ja da baya da baya tana kallansu d’aya bayan d’aya cikin matuqar razana da sanyin murya tace. “Na shiga uku ni NUFAISAT.. Qarshen rayuwata tazo…. Tana fad’in hakan ta fad’i sumammiya..
Da sauri dukkansu su ukun sukayo kanta. TAUDHAT fad’i take.. “Na shiga ni TAUDHAT. Dan Allah NUFAISAT ki tashi kiraya zuciyar dake qaunarki. Idan ba ADAMS bazan iya rayuwa ba. Zuciyarsa na tare dake. Idan kika mutu binki zaiyi. Wallahi a daran jiya yaqara jefamin qaunarsa a zuciyata kuma ina da tabbacin idan nayi k’ok’arin bar miki shi saina fara haukacewa kafin nabar duniya..
Ba qaramin tashin hankali ADAMS ya shiga ba. Haka ma Yusuf dan ko kad’an ba motsi ajikin NUFAISAT..
By Rahma Nalele Aunty luv… Ina yinku y’an hannuna????????
[6/23, 3:14 PM] ®????◾◼▪official Auntyn Luv.: ☆´-
☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾☆• ❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH* *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆
☆´-☆´- ☆“˜•☆• ¸☆“☆ª☆_☾
☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story
April.. 2018
Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh’md Rufa’i Nalele..☆
© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM????
☆We the best ☆
” بسم الله الرحمن الرحيم
☆page 12☆
Da sauri ya d’auki wani ruwa dake cikin gora a gefansa ya fara yayyafa mata… Fad’i yake. “Ki tashi NUFAISAT dan Allah ki tashi. Nayi kuskure na kuma yarda da duk abinda zaki cemin.
Sam NUFAISAT bata da alamar motsawa. Ganin hakan yasa ya kinkimeta bai direta ako ina ba sai cikin motarsa. Haka Yusuf da TAUDHAT suka shiga motar ko sauraran masu tsaran baiyi ba ya fige motar ahargitse yabar gidan. Aiko masu taransa da sauri sukabi bayansa.
Kaf y’an asibitin basu tab’a ganin rikicewar ADAMSY ba sai yau. Dr Aryan ne yashiga duba NUFAISAT dan ko kad’an Adams baiyi tunanin dubata da kansa ba.
Dan duk hankalinsa a tashe yake. gani yake kamar ta mutu. Dan hakan bai tab’a faruwa da ita ba…
To idan tamutu yayi yaya da rayuwarsa. “Kai ina NUFAISAT ba zata mutu ba. Ya fad’i hakan a bayyane cikin tashin hankali
Da sanyin jiki Yusuf ya kama hannunsa da zaunar dashi yana me masa magana cikin sanyi da lallashi.. “Kanutsu ADAMS. Insha Allah NUFAISAT zata tashi kamar komai bai faru ba. Kuskure ne dai munyi shi arashin sani. Gyarashi kuma kaine da alhaqin hakan..
Shuru Adams yama Yusuf kawai