LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

NUFAISAT ko shigewarta part d’inta fad’awa tayi kan gado cikin kuka takira momynta tazayyane mata komai akan ba wata bace kishiyarta Ashe TAUDHAT aminiyarta ce????
Mommy tayi mamaki sosai dajin hakan.
Dan haka tace mata taxo gobe gida zata bata shawara akan yanda zata zauna da TAUDHAT d’in

Sosaifa mamakin Mommyn d’in NUFAISAT ya qaru bayan sun ajiye waya ita da NUFAISAT d’in
Dan ita sai yanzu tatuna jiya Marwanatu y’ar aikinta tagaya mata kamar maman TAUDHAT tana taro. Sai momyn take ce mata ba yanda za’ayi maman TAUDHAT tayi wani taro batare data gaya mata ba. Saboda ko babu komai ai akwai hakk’in makwaftaka da mutunci.. Qila dai ko qawayen TAUDHAT ne suke kawo mata ziyara.

Tuno hakan da mommy d’in tayi sai yasa ranta b’ata taga kamar abinda maman TAUDHAT d’in tayi mata kamar bai dace ba. Idan tayi duba da irin zaman amanar dake tsakaninsu. Hmm mutum kenan.

NUFAISAT ko bayan ta gayama mommy d’in tasu kira Zainab yayarta tayi itama ta gaya mata komai
Wannan karan taga tashin hankalin Zainab d’in. Dan ce mata tayi gobe itama zata gida su had’u acan.
Toh NUFAISAT tace mata da kashe wayan.
Sanda tayi sallah raka’a biyu taroki Allah daya sassauta mata lamarin sannan tasamu nutsuwa.
Kiran asiya tayi tace taje babban falo ta kwaso kayan breakfast d’in datayi d’azu taba masu so takai yakan kitchen dan Allah ta wankesu.
Cikin ladabi ta amsa mata da toh.

Sai wajen qarfe Tara da rabi na dare Adams ya dawo gidan. Saboda bai tashi da wuri a asibitin nasu. Sannan ya biya gun iyayansa ya gaishesu kamar yanda ya saba. Koda ya murd’a kofar NUFAISAT akulle yajita. Haka daya duba tacikin babban falan nasu ma tasaka key
Dan haka murmushi yayi kawai dajin rashin jin dad’i aransa dan wallahi ya dawo da muradin San ganinta da sakawa aransa sai sun daidaita shi da ita cikin daran nan. Dan bai saba fad’a da itaba. Jinsa kawai yake wani iri haka. Zama yayi afalan ya dinga kiranta bata d’auka ba. Haka yayi hakuri dayin part d’insa yayi wanka da canja kaya ya nufi part d’in TAUDHAT
Ba lefi shashin Nata yana tashin qamshi amman baiji kamshin ya ratsa ba kamar yanda yake jin na NUFAISAT
Anan falan ya tarar da ita tana kallo hankali kwance. Aiko tana ganinsa tatashi da tsayawa dana sakar mai murmushi cikin nuna jin dad’inta da ganinsa da tayi.
K’arasowa yayi gareta da rungumarta yace… “Nayi farin ciki da ganinki cikin kwanciyar hankali
Qara kusanta kanta garesa tayi da cewa.. “Nafi kowace mace farin ciki awannan lokacin saboda naga mijina ya dawo gida cikin k’oshin lafiya
“Gaskiya na dawo cikin k’oshin lafiya ammafa Zuciyata babu dad’i.
Nan take tazare jikinta daga nasa tace.. “Ayya.. Har yanzu Aunty NUFAISAT bata gane qaddarace ta had’ani dakai ba.
“aa bance miki. Kawai ki share zancen nan. Komai zai tafi daidai insha Allah.
D’an b’ata fuska tayi alamun nuna damuwa. Ganin hakan da yayi saiya qara janta jikinsa da cigaba da cewa. Ban yarje miki kisaka wannan lamarin cikin ranki ba. Saboda bana san natsinci kaina cikin matsala biyu gatata gataki. Dan Allah ki sake nasamu nutsuwa agunki. danna tabbatar natamma na d’an wani lokaci ne..
Jin hakan sai yasa TAUDHAT sakin murmushi tace.. “Muje dining kaci abincin dana girkama. “Kamar ko kinsan tun break d’in danayi d’azu banci komai ba. Saidai kamar bai dace kifara girki tun yanxu ba.
“Duk abinda zanyi wanda zai zama farin ciki agareka bana duba dacewa. Kawai Zuciyata gaya min take nayi shi.
Gaskiya yaji dad’in amsar data bashi hakan yasa ya kama hannunta sukayi dining d’in yana me gaya mata suna ci zasu kwanta dan haka kawai yake jin gajiya yau.
Murmushi tayi mai kawai da fara zuba mai abincikan datayi mai tana sakawa aranta saita kwace zuciyar Adams ya dena damuwa da wata NUFAISAT…

Itako NUFAISAT tana jin dawowarsa da ganin kiran da yake mata taja tsaki da cewa "Allah kasaka min. Tana fad'in hakan taja bargo abinta.. Asuba tagari ADAMS TAUDHAT & NUFAISAT ????

Rahma Nalele Auntyn luv. Ina gasuwa y’an hanuna????????

[6/26, 8:17 PM] ®????◾◼▪official Auntyn Luv.: ☆´-☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾☆• ❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH* *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ☆´-☆´- ☆“˜•☆• ¸☆“☆ª☆_☾☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story
April.. 2018

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh’md Rufa’i Nalele..☆

© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM????
☆We the best ☆

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&tn=H-R

” بسم الله الرحمن الرحيم

☆page 13☆

Koda wasa washe gari NUFAISAT batayi tunanin ta had’a musu breakfast ba. Qarfe takwas daidai tagama dukkanin abinda zatayi tashiga wanka.
Bayan ta fito daga wankan tad’auki wayarta taturama da Adams text message kad’an haka????????. Kana tagyara kanta nan tafito fes da ita. Doguwar riga tasaka me kalar ja. Ta yane kanta da d’ankwalin rigar da saka takalminta med’an tudu.
Sannan ta d’auki wayarta da key d’in motarta tama masu yimata hidima sallama ta ficce daga gidan.. Bata dire ako ina ba sai’a gidansu.
Da Dadynta taci karo lokacin dazata shiga falan nasu. Ya kalleta ad’an nazarce yace.. “Mamana kece agidan haka da sassafe. ( dake da haka yake kiranta kasancewar sunar mamansa yasa mata )
Turo baki tayi da durqusawa tace.. “Ina kwana Dady. Murmushi yayi da bata da amsa da. “Lafiya lau. Saidai baki ban amsata ba mamana.
Qara turo baki tayi da cewa. “Momy ce tace nazo saboda na gaya mata ADAMS ba wata bace wacce ya Aura face TAUDHAT aminiyata. Dady ADAMS bai kyauta min ba Sam.
Wallahi ban hanasa Aure ba. Saboda nasan dalilinshi nayin hakan. Sannan duk mata ta gari idan tana San taqara samun kusanci da ubangijinta to ya zaman mata dole tayima mijinta biyayya taso abinda Allahn ya halatta mishi da yayi. Sannan tadinga bashi gudun mawa idan taga zai kauce hanya.
Dady kun bani tarbiya wacce nataso akanta har ake sha’awata dan ita.
Saidai ina ganin kamar bazan iya yima Adams biyayya ba ayanxu. Dan ina mishi kallan munafuki azzalimi wanda ya aikata abinda bai dace ba…. Taqarashe maganar tata da sakin kuka.
Murmushi Dadyn nata yayi da cewa aransa.. Mata mata halinsu sai su. Banda haka miye abin tada hankali dan kawai mijinki ya Auri aminiyarki.
Afiliko ce mata yayi. Tashi mamana kukan ya isa haka nan. Muje falo
Haka tatashi tabishi har falan nasa. Anan yayi mata nasiha da nuna mata wannan ba komai bane. Ita dai ta riqe sirrin gidanta. Taci gaba dayi mai ladabi da biyayya. Wallahi komai zaixo mata da sauqi idan har tasaka Allah agabanta…
Godiya tayima Dadyn nata sosai sannan ta nufi gun momyn nata lokacin tana kan sallaya da alama warha tayi.
Tana jiranta ta idar d’inne saiga Zainab yayarta taxo. Aiko nan tatashi ta rungumeta sai yaxo da dai dai da lokacin da mommy d’in nasu tashafa addu’ar da takeyi…
Aiko bayan sun gama gaisawa NUFAISAT ta gyara zama tabasu kaf labarin abinda ya faru…
Ran mommy ya b’aci amman bata nunama NUFAISAT d’in ba
Zainab kam tausayin y’ar uwar tatane ya kamata.
Mommy tayi shuru tana nazari can tace da NUFAISAT d’in… “Ki bud’e kunnanki da kyau ki saurareni kiji abinda zan gaya miki.
Tattaro dukkan hankalinta NUFAISAT tayi tana sauraranta..
Mommy taja numfashi daci gaba da cewa.. Sirrin zama da kishiya uku ne NUFAISAT.. Nafarko kisaka aranki zaki zauna da ita tsakaninki da Allah. Bazaki munafunceta ba. Bakuma zaki cutar da ita wajen aikata mata wani mugun abu ba. Sannan bazaki danne mata hakk’inta ba.
Na biyu . ki rungumi danginta da y’ay’anta da qawayenta runguma ta tsakani da Allah wacce babu batun kai qararta ga d’aya daga cikinsu ku zauna kuna munafuntarta. Saboda duk yanda kikai da abinki saiya koma mata kunnanta wata ranah..
Karkisa aranki zaki cutar da y’ay’anta agaban idanta ko’a bayan idanta. Dan bakisan alkairin dake tafe dasu ba. Ko wata rana sune zasu temakeki. Koki mutu suna masu yi miki addu’a. Ki riqesu amana ba ruwanki da nuna musu wani hali na mugunta.
Na uku shine uwa uba..
Kisa aranki bazaki dena yima mijinki ladabi da biyayya ba dan kawai ya aurota. Ya zamana lokacin ne zaki ninka ladabin da kike masa da zak’ulo duk wani abu da kikasan zai faranta ransa
Ya kasance kowane lokaci cikin bincike kike akan San sanin me yafi so. Meyafi d’aukar hankalinsa. Meyafi tafiya da tunaninsa. Meye idan kika masa yake tsayawa aransa wanda idan ya kalleki zaisa ya sakar miki murmushi.
Idan kika san way’annan saiki kasance cikin yimasa su. Gefe guda kuma kina yaqi da zuciyarki wajen San zak’ulo abinda idan kika masa zai bashi mamaki.
Idan kika gama karantar way’annan saiki koma lura da abinda bayaso. Idan kika gama lura da abinda baya so. Sai kiyi yaqi da zuciyarki wajen nisantar wannan abun..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button