LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL
Yarda wayarta da key na motarta NUFAISAT tayi akan gadanta. Kana tad’an zauna agefen gadan tana me nazarin maganganun da momyn nata tayi mata..
Sai yanxu kanta ya bud’e tagane wasu abubuwa dadama. Sam idan kirsa na magani bai dace tafito ta nunama TAUDHAT tsana haka afili har ADAMS ya gani ba..
Idan zata nuna mata ya dace ta nuna mata ita da ita ne. Saboda idan ta nuna hakan ita TAUDHAT d’in kwantar da Kai zatayi agunsa.
Kuma tasan halin mijinta sarai dasan abashi kulawa da tattalinsa. Duk da bai cika d’aukar iskancin mace barkatai ba.
Toh mezai hana ta danne zuciyarta tayi kamar batasan ya Auri TAUDHAT ba. Idan ya ficce sai suci junansu ita da ita.
Murmushin jin dad’i NUFAISAT tayi saboda tanad’e komai na makaman yaqi da TAUDHAT akan duk abinda zata zo mata dashi. Sai tayi nazari kafin ta yanke mata hukunci. Ta saka aranta Wallahi bazata tab’a barma TAUDHAT d’in shi ba..
Dan haka yamma nayi tashirya kanta kamar yanda tasaba. Sam bata kulle kofarta kamar yanda takeyi a kwanaki biyun nan ba
Aiko da misalin qarfe shidda da rabi tana kitchen tana had’a complex taji qamshin mijin nata ya daki hancinta. Bata juya ba dan tana da tabbacin shine ya shigo kitchen d’in…
ADAMS dake bakin kofar kitchen d’in shigowa yayi yana jin dad’i aransa na ganinta da yayi. Gaskiya yayi missing d’inta sosai. Da’ace zata gane ko kad’an baya jin dad’in TAUDHAT da mu’amala da ita.. Da Ita kawai yake san rayuwa dajin dad’in mu’amala. yasan da zatafi kowa jin d’adi. Saidai bazai iya gaya mata ba. Ita da kanta zata gane hakan. Dan shi ya dad’e da yima zuciyarsa hud’uba akan taji maganganun kowa akan soyayya saidai tafi d’aukar na NUFAISAT da mahimmanci. Dan da ita yafara soyayyar. Wannan dalilin shiyasa duk yake jinsa wani iri idan yana kallan TAUDHAT tana zuba masa kalaman soyayya. Shi dai bazaice bata iya ba. Amman yafi jin na NUFAISAT fiye da nata aransa. Kodan yanxu ya fara sabawa da ita ne ta wannan fannin????…..
A hankali yaje ya rungumi NUFAISAT d’in ta baya yana ne sauqe ajiyar zuciya. Cikin wani salo yake shaqar qamshinta yana cigaba da sauke ajiyar zuciyar..
A hankali NUFAISAT tafara juyawa garesa ta rungumesa tsam. Dan nan take taji abinda takwana biyu bataji shi ba. Wato d’umin mijin nata. A hankali taji ranta na mata dad’i dasan su kasance ahakan.
Shima yaji mafificin dad’i da hakan data mai. Kamshinta kawai da yayi sabo dashi yana saukar masa da nutsuwa da kwanciyar hankali.
Cikin sanyin murya tace da shi. “Kayima Zuciyata illa da yawa mijina. Tunda karaba fatata dajin d’uminka kullum. Karaba idanuna da San ganinka cikin dare kullum. Karaba kunnena da sauraranka kullum. Kagayamin wane hukunci ya dace dakai
Murmushi ADAMS yayi da d’ago da hab’arta yace.. “Wallahi ganinki yanxu da nayi ji nake kamar na cinyeki d’anye. Dan komai naki nayi missing d’inshi da yawa my luv.
Dan Allah matata kiyima Zuciyata gata kidena kullemin kofa.
“Yanxu ka gayamin hukuncin daya dace na yanke akanka.. Wato zan hana ganinka da zuciyarka ganina. Zan hana kunnuwanka da fatar jikinka saurarona da jina…
“Haba matata dan Allah kimin aikin gafara wallahi bazan qara yimiki wannan kuskuran cikin hankalina ba. Nayi nadama nayi dana sani nayi Allah wadai da wannan tunani nawa daya kitsamin na rasa wacce zan auro miki sai TAUDHAT..
“Kadena Allah wadai da tunaninka mijina. Dan abinda kayi shine ya dace dani. Shed’an ne ya shiga Zuciyata har yakaini dayi muku wannan borin.
Sanda naje gun mommy na tabani haske akan manufarka da dalilinka da kuma nufinka.
Nagode Allah daya bani kai amatsayin mijina mesan ganin farin cikina akowane lokaci.
Tabbas kayi gaskiya TAUDHAT itace ta dace da zama abokiyar zama. Agareni. dan baza tata aikatamin abinda bai dace ba
Haka nima nasanta bazan tab’a aikata mata abinda bazai dace ba.
Na yarda da TAUDHAT yanxu mijina d’ari bisa d’ari. Kuma ina San rayuwa da ita rayuwa tahar abada.
Yanxu muje na ganta na kama hannunta na gaya mata ita qawata ce kuma y’ar uwata ce har yanxu. Fatana takulamin dakai kamar yanda nake kula dakai..
Qara rungumarta yayi dan yaji dad’in bayanan nata. Ya tabbatar mahaifiyarta uwace dan ta’iya gyara masa gida..
Ahankali ya fara neman bakinta amma taqi dana nuna masa yanxu ba lokacinta bane lokacin TAUDHAT ne dan haka ya kula..
Baiji abinda ta gaya masa ba. Dan bai barta ba sanda yaji bakin dakyau…
Aiko tana manne ajikinsa suka nufi part d’in TAUDHAT d’in zuciyarta na bugawa dan baqaramin tsanar ganin TAUDHAT d’in take ba.
Aha dai suka samu TAUDHAT d’in a falo taci riga da wando kayan sun matseta ainun dan komai nata ya bayyana ya fito fili qara qara.
Hankalin NUFAISAT ya tashi matuqa???? danta tabbatar lalle TAUDHAT so take ta kwace mata mijinta acikin lokaci qanqani tabarta can baki sake tana kuka da ihun aminiyarta ta cutar da ita ta aure mata miji.
ADAMS ko dagaske har cikin ransa kwalliyar TAUDHAT d’in ta birgesa amman yaga saurinta nayin hakan. Dan NUFAISAT sanda tayi sati biyu kafin tafara saka mai qananun kaya. Koda yake zamanine yazo da hakan. Dan kullum dad’a wayewa ake. Nan ya qara kallanta dakyau Saiya fad’a tunanin dukfa da hakan idan da kayan ne ajikin NUFAISAT ya tabbatar saiyafi d’aukarta. Saboda tad’anfi TAUDHAT abubuwan d’aukar hankali.
Ita kuma TAUDHAT ganin NUFAISAT da murmushi gata kuma manne jikin Adams ba qaramin fad’uwar gaba taji aranta ba. Nan take ta dibibice dan ranta b’aci yayi ainun.
Ba qaramin yaqi da zuciyarta NUFAISAT tayi ba wajen cewa.. “Nagode ma Allah dayasa nasameki cikin koshin lafiya haka. Takai qarshen zancen nata da sakarma Adams kiss a gefan kumatunsa shima ya sakar mata cikin kulawa kana ta zare jikinta daga nasa taje takama hannun TAUDHAT d’in daci gaba da cewa… Dama nazo nakama hannunki ne nanemi afuwarki daga takaicin dana nuna miki akan kyakkyawan udirinki na auransa da kikayi wajen San faranta min. Nagane gaskiyar mijina nufinsa akanki na aurokin da yayi. dan haka dan Allah kicire komai aranki kici gaba da d’aukata a matsayin qawa aminiya y’ar uwa. Dan muhad’u mu bama mijinmu farin ciki me d’orewa.
Kallan Adams taudhat tayi da maida kallan nata ga NUFAISAT tace “La.. karki damu. Ai dama nasan da wuri zaki gane manufarmu….
Galla mata harara NUFAISAT tayi tunda ta fahimci ta juyama Adams baya bayi ganinta sai tayi saurin bata amsa da cewa.. “Ina jin dad’in yanda kike da sauqin kan nuna komai ba komai bane
Cikin muryar qasa qasa TAUDHAT tace mata. “Hmm.. Wane saban shiri ne kuma wannan. NUFAISAT ta wurga mata kallan tsana itama cikin muryar qasa qasa tace.. “Irin shirin da kika d’auki lokaci kinayi wajen aure min miji.
“Idan ko haka ne kidena yinsa tun yanxu dan bazaki iya irinsa ba!
“Na rigada na shirya makaman yak’i dake taudhat. Wallahi ko’ana ha maza ha mata saikin gane ADAMS na irinmu ne mu kad’ai ba irinku karuwai mushirikai ba.
“Ni kuma saina nuna miki da irinmu ya dace bada irinku shashashai banzaye dolaye ba
“Idan da gaske na riqi Allah ke kuma kin riqi boka zanga tsakanin nidake wayake dacin galaba..
“Kasancewar ni ce nake fuskantar mijinmu ayanxu na lura ya fara zargin wani abu muke kullawa akansa. Dan haka ki adana kalamanki yanxu idan gobe tayi bayan ya fitta zanzo shashinki kifad’i maitarki ni kuma na baki amsarki
“OK. Ina nan ina jiranki me zuciyar maciya amana….
Kan TAUDHAT ta batama NUFAISAT amsa sai Adams yace.. “Wai me kuke fad’ama junanku ne haka naji kuna magana qasa qasa da alama akaina kuke maganar…
Murmushin yaqe TAUDHAT tayi da saurin figge hannunta daga na NUFAISAT tana niyar bashi amsa sai NUFAISAT tayi saurin juyawa garesa tace. “Hud’uba nake mata akan takulamin dakai. Dan idan tabarmin kai haka ba kulawa zan hukuntata irin sosai d’innan. Shine fa take ban hakuri… taqarashe maganar da kallan TAUDHAT d’in tana cigaba da cewa. Ko ba haka bane.
D’aga mata kai TAUDHAT tayi da cewa. “Haka ne man. hmm haka.
Murmushi ADAMS yayi da qarasowa ya kama hannun NUFAISAT ya sakar mata kiss da cewa.. “Nagode matata. Sannan kulamin da kanki. Ina miki fatan ALKAIRI akan kitashi lafiya.
Mayar mishi da kiss d’in tayi itama a hannunsa tace… “Tare dakai mijina. Kana taje ta rungumi TAUDHAT dacigaba da cewa.. Tare dakema Yar uwata… Tana fad’in hakan ta ficce daga d’akin tana jin wani iri aranta
Ko ba komai taji dad’in aranta. Yanxu ta fahimci agaban kowa Adams zai iya bata kulawa. Kuma Wallahi saita nunama TAUDHAT iya karta.