LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

“Assalamu-alaikum MESONA
Ya shigo falan da Murmushi akan fuskarsa yana me leqen ta’inda zaiga masoyiyar tasa…
Aiko canya ganota da qawarta suna masu hira cikin farin ciki da qaunar juna….
Lokacin da NUFAISAT tayi ido hud’u da Mijin nata tashi dayi da Sauri tazo ta rungumesa tana me nuna murna da farin cikin dawowarsa…
“Amma sweety banji shigowarku ba…
“Tayaya zakiji. Bayan kina tare da wannan wacce tabi ta kanannad’eki da zaqin baki….. Ya bata amsa da fad’in hakan yana me nuna mata qawarta TAUDHAT..
Da wani yanayi.. da wata shagwaɓa.. Da wani kallo.. tace… “Zaƙin bakinta agareni. bazai tab’a shagaltar da ruhina daga lura da jinka ko kuma ganinka ba…
Kawai kaidai kayarda banjika bane da gasken gaske. ????
Murmushi yayi da zareta daga jikin nasa ya nufi part nasa yana cewa. “Na yarda sweetyna.
Murmushi tayi da binsa da kallo. Kana takoma ta zauna sukaci gaba da hira da qawarta tata TAUDHAT BATARE DATA BISHI DAN TATEMAKA MISHI WAJEN CIRE KAYA BA.????
Can yafitoh falan da wata sabowar shiga. kallo d'aya zakamai kasan yayi wanka ne..
ADAMSY kenan mekatu….
Zama yayi a dining teble
Ga mamakina sai naga TAUDHAT tataso da Murmushi zuwa garesa tana cewa…. “Sannu da dawowa MIJIN K’AWA.. Fatan kadawo lafiya.. Allah yasa ba wani Wanda ya b’ata maka rai awannan ranah.. Wajen zaman ka wajen kasuwancinka. Konace a asibitinka..
Da Murmushi yace da ita… “Ba Wanda ya b’atamin rai. Kuma lafiya lau nadawo ga matata.. Fatan dai girkinki agareni yau yafi na jiya d’and’ano..????
Wani shuqumin Murmushi ta kai masa???? da fara zuba masa abubuwan data b’ata lokaci wajen girka masa tana cewa… “Ai akullum qara Neman sani nakeyi. Indai akanka ne. Nayi alƙawarin bazan tab’a bari kakawoma K’AWATA Kishiya akan girki ba……
Lumshe ido yayi lokacin daya kai farfesun kayan ciki bakinsa… Gaskiya yayi dad’i sosai.. Hakan ne yasa daya bud’e idan nasa ya sakar mata murmushinsa me tsada da furta kalmar… “Ki daure ki rayu da qawarki dan bani San nayi missing girkinki
Murmushi taƙarayi da zubamai drink a cup tajuya da nufar aminiyar tata tana cewa…. “Karka damu.. zan rayu da ITA da KAI.. har izuwa qarshen rayuwata…
Rungumarta NUFAISAT tayi da fad'in... "Nagode Aminiyata. Kina kula min da Mijina. Kina kulamin da cikinsa fiye da tunanina...
Nagode sosai fah
“La???? karki damu Aminiya.. Ai hidima ga Mijinki dani ya dace Idan da kara… Shine fa abin sanki abin qaunarki Wanda kikaso kashe kanki saboda shi. Idan ban kulam miki dashi ba dawa zan kula.
Kawai damuwata d’aya. kyautatawata agaresa. Allah yasa ta maqale cikin zuciyarsa. yaƙi mantawa dani. ta dami zuciyarsa hakan yasa yaqi qara miki abokiyar zama dan ina kishin wata Y’a mace tarab’ar miki miji sanadin girki kawai.????… TAUDHAT ce me fad’in hakan..
Qara Rungumarta NUFAISAT tayi da cewa. “Nagode… Alamu sun nuna zashi gun Dady… Dan haka kijirasa ya gama saiya sauke ki agida. Tunda yanxu kin fara qin tawowa da motarki…
Jan numfashi TAUDHAT tayi da fad’in “Toh Qawa…☆´-
☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾☆• ❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH* *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆
☆´-☆´- ☆“˜•☆• ¸☆“☆ª☆_☾
☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story
Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•RAHMA MUH’MD RUFA’I NALELE..☆
© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM????
☆We the best ☆
Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com
” بسم الله الرحمن الرحيم
☆page 03☆
Yana jinsu ahaka ya gama da tashi ya goge bakinsa da tishu yana fad’in.. “Toh my luv. Kamar yanda kikayi harsashe. Zani gunsu Dady. Kina da buqatan wani abu ne natawo miki da shi…
“Bana da buqatar komai.. Saidai kawai kasauke Y’AR UWA agida dan Allah.
“Angama my luv. Ya fad’i hakan yana me kallan TAUDHAT kana ya ficce daga falan.
“Toh Y’AR UWA Ni zan tafi. Sai Allah ya tashemu lafiya
“Nagode Y’AR UWA.. Ki gaishe min dasu mamah.
“insha Allah zataji.. TAUDHAT tabata amsa da ficcewa dana sakar mata Murmushi
Itama Murmushin tasakar mata..
Sanda taji tashin motarsu sannan tanufi dining da kwashe kayan kai. Takai kitchen. Tadawo tagoge wajen. Sannan takoma kitchen d'in tawanke kayan da adanasu a inda ya dace Sannan tanufi bedroom nata tana nazarin qara yin wanka..
ADAMSY da TAUDHAT ko. Kamar yanda suka saba. Idan bataxo da motarta ba.. Toh Idan ya d’auketa atashi motar bamema wani magana
Kasancewar shi d’in miskiline kuma me Aji
Dama Ita kanta tasan ba wani dalilin da zaisa yayi hira da ita imba tana tare da matarsa ba
Kawai zai kulatane da hira ne idan tana tare da NUFAISAT matarsa
Dan tasan shi mata basa gabansa
Kawai matarsa itace agabansa
Wannan dalilin yasa Idan tana tare dashi takan d’auki wayarta tata danne dannanta..
Dama shi yasan kansa ba wata hira da zaiyi da ita. Dan baisan me kuma zasuce ba
Shiyasa kawai yake maida hankalinsa kan tuqinsa dan baya tafiya da masu tsaransa zuwa gidansu
Wannan tsarinsa ne!!!
Ahankali ta kallesa da lankwashe harshenta tace dashi… “Nagode Mijin Qawa
Da Murmushi ya bata amsa da cewa… “Kinfi qarfin hakan. Kuma har yaushe zaki dena godemin Idan nakawoki gida..
Itama da Murmushin tabashi amsa da.. “Ai kaima kullum cikin godemin kake..
Da zaka dena da naji dad’i
“Hidima dani fa kikeyi Kullum.. Idan ban gode miki kullum ba. Me kikesan nayi
“Alamu dai sun nuna ba wanda zai dena godema juna a tsakaninmu….
Kan yabata amsa wayarsa tayi qara.. Koda yaga me kiran nasa. Murmushi yasake da d’auka yana cewa… “Hankalinki ya kwanta my luv. Yanxu na sauke miki qawa..
Murmushi NUFAISAT tayi dai-dai lokacin da take d’aura tawul ajikinta dan shiga wanka tace da shi… “Hankalina kuma bazai qara kwantawa ba. Harsai najika kaje gasu Ammee lafiya kadawo gareni lafiya.
“Fatan alkairi kawai matata
“Na kwana inayi maka Mijina
“Toh kiqara gyaramin kanki da kyau. Dan gajiyar yau.. ta Musamman ce..
“Kace na shirya karb’ar dukkanin tarin gajiyar..
“Abinda nake nufi kenan
“Toh ka kulamin da kanka..
“Naji my luv
Sanda ya ajiye wayar gefansa Sannan ya kalli TAUDHAT da sakar mata Murmushi yace… “Haka kawai kin zauna kina jin sirrina da matata..
Murmushi TAUDHAT tayi da ficce daga motar tana cewa.. “Amin afuwa bansan lefi nayi ba.. Kuma mah banji komai da kuke cewa ba..
Jan motarsa yayi kawai da Murmushi
Ita kuma tad’an cije harshenta da shigewa gidan nasu
Bata tarar da kowa a falan nasu ba. Dan haka saitai jifa da jakarta..
Ta zube akan kujera tafad’a tunani
Ahaka mamah mahaifiyarta taxo tadafata tana cewa… “Niko zanga ranar dazaki dawo daga gidan NUFAISAT ba tare da tunani ba
Murmushin yake tasakarma Maman nata da cewa. “Nima ina fatan naga ranar dazan dawo daga gidanta da farin ciki.
“To Wai meyasa hakan take faruwa dake
“Wallahi mamah San mijinta nakeyi????
Ina San ADAMSY
Danya tara duk wani abun da mace me aji takesan samu agun Mijin Auranta..
Duk da cewar yanxu kin manyanta.. Amman hakan bai hanaki cewa ADAMSY ya had’u ba
Dan Allah kiyarda mu had’a kai nashiga gidansa matsayin matarsa ta biyu…
Mamah ko kin manta ranar da kika gayamin cewar ya had’u..
“Ban manta ba TAUDHAT.. Kuma yanxu ma zan qara nanata miki..
ADAM ya had’u.. Dan ban tab’a ganin yaro Wanda ya had’e komai na rayuwa irinsa ba
Amman hakan dace da kamata yasa ki soshi aranki ba..
Saboda matarsa Y’AR UWA ta d’aukeki.
Wannan cin AMANA ne
Ina rokwanki daki dena San ADAM.. Dan kwata kwata baku dace da juna ba.
Duk da cewar ke Y’ata ce.
Bazanso kici amanar ADAM da NUFAISAT ba..
Saboda shi nagari ne
Shiba walaqantacce bane
Shi mutum ne me kamun kai
Bai kyautu da had’in kaina kizama mata a garesa ba
Kefa karuwace.. Wacce take karuwanci da manyan y’an iska..
Ko kin manta hakan ne
Shekarunku ashirin da biyar da NUFAISAT.. Amman bata tab’a sanin hakan ba
NUFAISAT bata tab’a sanin kina da wasu mugayan d’abi’u ire iran waƴannan ba…..
Cikin fusata da tsawa TAUDHAT tatashi tare da katse mahaifiyar tata da hannu tana cewa… “Ya isa haka mamah.. Bansan har sai yaushe zaki fara sona ba
Dalilin halin rayuwar da muka shiga nafad’a wannan halin da kike fad’a
Ke wacce irin uwace Mara imani
Kin tambayeni damuwata nagaya miki ita. Mazaisa bazakibi bayana ba
Saikace bake kika haifeni ba..
Sai kace bani kad’ai bace y’arki aduniya..
Ina ganin iyayan da suke bin ra’ayin y’ay’an su. suna jinjina basira irin tasu. Idan sunxo musu da wata shawara. Ko wani abu da suke san aiwatarwa kuma su qarfafa musu gwiwa..
Daga yau idan har zanzo miki da wani batu kuma bazaki bi bayana ba. Saidai kibini da mugayan maganganu.. Toh ina farawa kicemin bazaki iyaba..
Idan har kika barni nakai qarshe kafin kikace bazaki iya ba. Wallahi ba abinda zai hanani hukuntaki…