LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

NUFAISAT najin azabar rod’a mata kwalbar da TAUDHAT tayi nan taje tararomo wata bishiyarta dake gefan TVstan d’inta tanufo TAUDHAT da ita gadan gadan da nufin ta caka mata aciki kasancewar bakin bishiyar yayi sirisiri tsini tsini haka. amman TAUDHAT ta kauce aiko sanda NUFAISAT ta caketa agefan mazauninta… Nan ko jini ya fara fitta daga wajen kamar yanda jini ya wanke fuskar NUFAISAT…
Ai bashiri Zainab da Asiya suka kwalla qara da rabtaba salati suna masu neman akawo musu agaji. Dan ahakan ma ba denawa sukayi ba..
Dan NUFAISAT yar da bishiyar tayi da niyar cakamo wiyan TAUDHAT saidai kamar TAUDHAT d’in ta ankare nan ita tafara kamo wiyan NUFAISAT suka zube kan tiles duk jini ya b’ata musu jiki… Dai dai nan Adams ya sawo kai cikin falan dan anan yaji hayaniyar…
Taqer ya iya rabasu ransa yayi matuqar b’aci basoda yanda jini ke fitta daga jikinsu amman dan bala’i basu sararama junansu ba…. (Shed’an la’ananne daya had’a futunar yana gefe yana musu dariya.)
Allah ka karemu daga sharrinsa Ameen

Haka Adams ya danne zuciyarsa yasamu suka lallab’asu suka shiga cikin mota harda shi direban yajasu yana cema Zainab dan Allah tad’an jirasu yanxu zasu dawo.. Toh tace mai cikin damuwa.

Dr Aryan ne dai ya dubasu..
NUFAISAT tasha nani wajen saman kunnanta Yayinda TAUDHAT tasha gyara a gefan mazauninta
Adams baice musu komai ba. haka suka qara shiga motar wannan karan shiya jasu.

Ababban falan nasu ya had’asu yana me tambayarsu meya tayar musu da wannan futunar..
Duk shuru suka mai. Ransa ya qara baci afusace yace da NUFAISAT… “Ke nakeso ki fara bani amsar tambayata…
Shuru tamai.. Ya maida kallansa ga TAUDHAT yacigaba da cewa.. Ke fad’amin
Jan numfashi tayi da cewa.. “Kawai kayi hakuri..
Qara maida kallansa ga NUFAISAT yayi da wurga mata wani kallo Yace.. “Wato ban isa ba ko..
Jan numfashi tayi da tashi taje ta kama qafarsa da marairaicewa tace. “Dan Allah kayi hakuri mijina. Wallahi ba yanda zanyi da ita ne dole saina kulata..
Nasan kana sane da canjin dana samu jiya akan na amince da zama da ita matsayin abokiyar zamana kuma y’ar uwata.
Ashe abin bai mata dad’i ba dan taso na dauwama cikin jin tsanarta saboda tana San yin amfani da Wannan damar dan kawai kadinga ganin lefina
Wannan dalilin yasa kana fitta d’azu tabiyoni part d’ina akan wai munafuncine yasani canjawa ba canjin Allah da annabi bane..
Raina ya b’aci mijina hakan yasa nace mata ita batakai matsayin dazan canja mata dan munafunci ba.
Waime zaisa nace mata haka. Kawai saiji nayi ta fallamin mari.
Kaima kasan bazan iya jure hakan ba Gaskiya. shine na rama fad’a kuma ya kaure tsakaninmu.
Ina ganin shigowar Aunty Zainab naso barin fad’an amman nakasa saboda TAUDHAT d’in taqi barina…
Na rigada na yafe mata mijina kawai fatana tayarda da abinda nace mata adaran jiya dan musa ma maka farin ciki.
Ban iya qarya ba mijina. Toh akan me yasa zanma TAUDHAT bayan nasan tafi kowa sani nah…. NUFAISAT na kawowa nan azancenta tafashe da kuka tana meci gaba da cewa “Wallahi ina sanka mijina.. Dan Allah ka gaya mata ina San zama da ita lafiya tunda mommy tamin magana akan bada niyar ta bak’anta min rai ta aureka ba. Dan tasan TAUDHAT bazata ta tab’a cutar dani ba. Ashe ba gaskiya bane da wani abu aranta. Pls ka gaya mata har gobe bazan dena qaunarta ba… Saboda qaunar da nake mata ta jinice hakan yasa bazan iya jure zaman tashin hankali da ita ba…

Jan numfashi Adams yayi da d’agata daga durqushen da tayi ta zauna a gefansa kana ya kalli TAUDHAT da cewa… “Kinji abinda tace..
Shuru TAUDHAT tayi dan bata tab’a tunanin cikin lokaci qanqani NUFAISAT zata iya sharara qarya cikin makirci haka ba
Kanta ya kulle sosai.. kodai dama kallan biri take mata ita kuma tana mata kallan ayaba..
Hmm idan ko haka ne dole tatanadi makaman yaqi ta nunama mata ruwa ba sa’an kwando bane
Kwata kwata yanxu bata San mema zatacema Adams d’in ba
Shiko ganin tayi shuru sai kawai ya yarda itace bata da gaskiya saboda hakurin data bashi tun da farko. Dama kuma bai tab’a kama matar tashi NUFAISAT da qarya ba.
Ji yayi ya gamsu da abinda tace mai..
Dan haka ya kira Zainab yayar NUFAISAT dake falan NUFAISAT d’in awaya ya tambayeta akan me tasani akan fad’an nasu. Ta tabbatar mai ita kawai zuwa tayi tasamesu suna yi wallahi batasan meya had’asu ba…
Jin hakan yasa ransa ya qara b’aci da TAUDHAT dan ya yarda itace bata da gaskiya
Wato kamar yanda NUFAISAT d’in tafad’a ita TAUDHAT tafisan taga tashin hankalin NUFAISAT d’in ita kuma ta dinga binsa bin munafunci…
Hmm mata mata… Ahankali ya kalli TAUDHAT d’in da cewa.. “Banyi tunanin hakan kuma daga gareki ba. Watoh da wani abu aranki..
To bari kiji zan iya yimiki komai akan NUFAISAT matuƙar zaki cutar da ita. Danna aureki ne saboda iyayena da suka sani qara Aure
Sannan na zab’eki ne dan ina da tabbacin bazakiba NUFAISAT matsala ba
Ada tayima Auran namu kallan bamuyi mata adalci ba
Hakan yasa tayi mana buri cikin rashin fahimta
Yanxu kuma data gane gaskiya me yasa kika d’auki hakan amatsayin munafunci tayi….
Kallansa TAUDHAT tayi da niyar yin magana amman yayi saurin katseta da cigaba da cewa. “Bana San kicemin komai
Danna fiki sanin matata duk da atare naganku.
Bata tab’a zama tayi min qarya ba. Haka kuma na tabbatar bazata fara min akanki ba
Dan haka kinutsu karna qarajin kinje shashinta kin nemeta da fad’a dan ina San rayuwa da ita sosai sannan ina San rayuwa dake saboda ina fatan nasamu abinda iyayena suke fata daga gareki…
Yana kaiwa nan ya ficce daga falan zuwa ga motarsa direba ya jasa cikin sauri…

Tashi NUFAISAT tayi da kallan TAUDHAT kallan tsana tace. “Shegiya annamimiya ina zaman zamana da mijina kika wani kama kika shigo rayuwarmu danki b’ata tunaninmu. Tota ALLAH ba taki ba
Kuma wallahi yanxu mukasa qafar wando d’aya dake. Cikin ni dake zanga waye zaije yace yabashi takaddarsa. Tsananniya me jin d’and’anan maza.. Tana gama gaya mata hakan ta ficce daga falan zuciyarta cike da farin ciki dan ganin yanda ran TAUDHAT d’in ya b’aci kamar tad’auki bindiga ta harbeta..
Haka ne kuwa dan da sanyin jiki TAUDHAT d’in tatashi dayin part d’inta tana tuna mezatama NUFAISAT itako ta wucce arayuwarta…

Na gaida kowa kyauta????????‍♀
[7/1, 10:18 PM] ®????◾◼▪official Auntyn Luv.: ☆´-☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾☆• ❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH* *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ☆´-☆´- ☆“˜•☆• ¸☆“☆ª☆_☾☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story
April.. 2018

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh’md Rufa’i Nalele..☆

© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM????
☆We the best ☆

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&tn=H-R

” بسم الله الرحمن الرحيم

☆page 15☆

Zainab na ganin NUFAISAT taje ta rungumeta tana cewa… “Masha Allah. Nagode ma Allah dayasa bata cutar min dake da yawa ba.. Taqarashe tana me sakar mata kiss a kunci..
Zama sukayi NUFAISAT ta kwashe abinda ya jawo musu fad’an dayanda sukayi da Adams kaf tagayama Zainab d’in. Sannan taqara da cewa.. “Wallahi Aunty Zainab natsani TAUDHAT tsana mafi muni.. Kuma wallahi nashirya karb’an kowane irin sak’o daga gareta.
Zan bata mamaki matuqa ta gane NUFAISAT d’in data sani me sanyi ba itace yanxu ba..
Jan numfashi Zainab tayi da cewa.. “Bana San tashin hankali NUFAISAT.. Dan haka ki barta haka nan. Dan nafi buqatar rayuwarki fiye daki kulata..
Kinga taso nakasamin ke aka.. Gaba bamu San ina zata kai miki hari ba.
“Kar wannan ya dameki Aunty Zainab. Hakan ma daya faru qarin ilimin zama da itane nasa muh.
Dan haka karki gayama mommy saboda bani San hankalinta ya tashi..
“Bazan gaya mata ba. Amman dan Allah karki qara kulata..
Murmushi NUFAISAT tayi da cewa.. “Toh zan kiyaye..
“Kinga Asiya ta share miki ko ina tsaf. Sai idan Allah ya kaimu gobe zan tawo miki da wasu kwalaban turaran kimaidasu wajen da way’ancan suka fashe..
“Ba damuwa aunty Zainab nagode
Janyo jakarta Zainab tayi da bata ingantaccun magungunan da mommy ta bata ta bata
Nan tashiga mata bayanin yanda zatayi amfani dasu. Sosai NUFAISAT taji dad’i aranta..
Zainab ma sanda ta’ibi nata raban tana me cema NUFAISAT d’in.. “Na lura momy tafi ji dake aduk cikinmu…
Murmushi kawai NUFAISAT tayi mata dan da gaske mommy tafi bata kulawa..
A haka agurguje sanda Zainab ta qara bata haske kan girki kafin tabar gidan zuwa ga office d’inta dan yau kam tayi latti over.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button