LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

“Malam Isma’il kenan. Idan da sabo yaci ace nasaba da wannan gyaran naka
Danna lura Sam baka iya ganina babu komai jikina kabarni ta hanyar lallami. Har sai munyi fad’a hankalinka yake kwanciya. Duk duniya ban tab’a cin karo da mutumin daya ke d’aukar sama da awanni bakwai yana jina ba saikai da mijina.. Da nayi tunanin daga kai babu wani. Ashe akwai maza asamanka. Danna mijina yaci uwar naka..
Saidai kayi hakuri ayanxu babu maganar gyara tsakaninmu.. Idanko kaci gyaranka katabbatar gaba idan nazo babu kai babu jina…
Murmushi yayi ganin takai qarshen zancen nata yace. “Yanda na qara kwad’aituwa dake ayanxu. bani tunanin iya barinki. Dan haka komai ma ya faru nan gaba…
Ba kunya ba jin tsoran Allah haka sukata aikata masha’arsu..

Bashi ya barta ba sai kusan biyu da rabi na narah
Dan haka tsasashi agaba kan ya gaya mata komai d’in daya gano..
Jan numfashi yayi da cewa.. “Gaskiya TAUDHAT kishiyarki ba qaramar hatsabibiya bace.. Wato kallan kitse kikeyima rogo.. Dan NUFAISAT ta wucce dukkan tunaninki..
Kawai kibar kaza acikin gashinta.. Dan tsefeta ba qaramin wahala zakici gaba ba
Yanxu dai ki fuskanci matsalarki kawai dazan gaya miki..

“Ban gane me kake nufi ba. Kana nufin cin mutuncin da tamin da abinda mijina yamin agabanta nabarshi ya tashi abanza kenan..
“Eh haka nake nufi
“Toh wallahi bazai yuhu ba
“TAUDHAT kina da taurin kai akan abubu da dama. amman tunda so kike na tsefe miki komai kiji dalla dallah tobara kiji kyau. Bazaki tab’a cin galaba akan NUFAISAT wajen asirce asirce ba.
Dan aranar da kukayi fad’an ba qaramin dafa’i uwarta ta aiko mata dashi tasha ba. Sannan kin Santa da ibada akan lokaci da tsayuwar dare. Bata zuwa wajen boka ko malam akan lamuranta Allah d’aya tak tasa agaba.
Ina tabbatar miki Idan kikace zaki mata wani mugun abu wallahi kanki zai dawo. Bar kuri da cika baki akan kinyi wani babban kamun boka idan kikaje wajansa ya miki wani mugun abu akanta wallahi TAUDHAT koba jima ko ba dad’e saiya dawo kanki..
Dan haka kisama kanki kwad’an mutunci ki kasheta da kirsa da kisisina irin taku ta mata. Sannan zan baki wani magani ki saka agabanki wanda idan mijinki ya kusanceki bayan kin saka maganin? Wallahi bazai qara jin dad’in Kishiyarki NUFAISAT wajen auratayya ba..????
Idanko kikaga yaji dad’inta ba qaramin aiki taje aka mata ba..
Amman kina da damar da zaki iya sawa amata wasu qananun abubuwa saidai su d’inma ba tasiri zasuyi sosai akanta ba.
Jan numfashi TAUDHAT tayi cikin matuqar jin haushi. Ta yarda da malamin nata akan fad’a mata gaskiya da yake yi.
Kuma ba wani abu bane yake sawa yake gaya mata gaskiya tasani dan baya San yayi missing d’in jikinta ne.
Tasan ita kad’aice take iyawa dashi kamar yanda ya tabbatar mata..
Ita yanxu babban baqin cikinta d’aya shine yanda bazata iya aikatama NUFAISAT wani mugun abu ba.
“Kai gaskiya da sake… Ta fad’i hakan abayyane tana me kallansa taci gaba da cew.. “Hmm nasan kana da dabara akan abubuwa da dama na mugun abu ga wani. Ina San na musguna rayuwarta pls ka taimaka min mana.
Dariya yayi da cewa. “Ke wani zubin kamar baki da wayo Sam.
In banda abinki ai babbar cutarwa dazaki mata d’ayane shine kisa mijinta ya dena kusantarta. Ina akan abinda kukema kishi kenan mata. Idan kika mata haka kin kasheta da ranta. Dan zata zama photo ne agidan kece matar gida. Dan azahiri ADAMS zai dinga nuna miki kulawa dan kin d’auke madarajarta agaresa.
Amman idan kikace zaki haukatar da ita ko kisaka fad’a atsakaninsu ko kizama kece kyentattatciya agidan ko yarabu da ita ko ya dinga wulaqantata da sauransu nagaya miki hakan dawowa kanki zaiyi..
Shuru TAUDHAT tayi tana nazarin maganar tashi..
Can taja numfashi da kallansa tace nayarda da abinda kace. Kuma na gamsu.. Yanxu bani maganin na qara gaba..
Miqa mata wani kulli yayi da cewa.. Ki kwab’a da jinin al’adarki ko ruwan ni’imarki.
Karb’a tayi da cewa “nagode bara naje..
“Ai bakiji qarashen zancen nawa ba.
“Toh kuma menene yanxu.
“Kishiyar sirikarki Hajjiya Rukayyat tayi miki illa fah.
Waro ido waje TAUDHAT tayi cikin tsoro tace.. “Metayi min????
“Tabaki wani abinci kinci wanda yake d’auke da magani..
Gyara zama TAUDHAT tayi da cewa.. “Eh haka ne. Dan sunzo kawo kayan aure na tabani nama me d’auke da magani akan maganin mata ne. Wai tabama kishiyata mah? Shiyasa take juya Adams yanda take so. Dan haka gashi nima naci danta d’aukemu duk d’aya ne..
Murmushi yayi da gyara zama shima yace.. “Toh ba gaskiya bane.
Kinsan maganin me tasaka miki aciki..
Girgiza mishi kai TAUDHAT tayi.. Yaci gaba da cewa. Maganin hana d’aukar ciki ne..
Maganin dabazaki tab’a haihuwa da ADAMCY ba tabaki. Ammafa shi kad’ai. Zaki iya haihuwa da wani amman banda Adams. Wannan shine gaskiyar zance…
D’ora hannu aka TAUDHAT tayi ta zambad’a ihu dana cewa.. “Kutumar bura’uba.. Meyasa tamin haka.
Tab’e baki malamin nata yayi da cewa.. “Nima ban sani ba. Dan nayi duba nagane meyasata yi miki hakan banga komai..
Da b’acin rai TAUDHAT ta katseshi da cewa. “Hmm lalle ta ibo ruwan dafa kanta.. Dubamin kagani itama banda ikwan yi mata komai kamar na NUFAISAT ne..
Gayara zama yayi dayin zane zanansa can yayi murmushi dace mata.. “Kina da ikwan yimata komai dan tana wasa da sallah.. Sannan itama ai biye biye takeyi sosai.. Qilama tafiki yi. Dan daga dukkan alamu tayi mugayan abubuwa sosai akan jama’a..
Sheqewa da dariya TAUDHAT tayi da cewa.. “Kasan me zaka mata.. Girgiza mata kai yayi.. Taci gaba da cewa. So nake kajefeta yanxu ka kwantar min da ita yanda zata kasa komai arayuwarta..
“Kai TAUDHAT. Ayi haka
“Mezai hana kuwa. Kashe min rayuwa tayi fah.
“Kuma fa haka ne.
“Ashe kagane. Maza jefe gangan jikinta naji sanyi araina.
Ba b’ata lokaci yahau yin wasu surkulle nan take ya jefa wani dutse sannan ya kalleta da cewa.. “Tashi kije gida zakiji tana asibiti. Kuma ba abinda zasu iyayi mata..
Dariya TAUDHAT tayi da cewa.. Tukwicin wannan abun daka min shine zan had’a kai dakai kamin ciki mijina ya raini d’an malam..
Washare baki yayi cikin matuqar jin dad’i yace.. “Kai amma TAUDHAT kin biyani dan naji dad’i sosai..
Tashi tayi da yafa gyalanta ta sab’a jakarta tace.. “zaka jini bayan kwana biyu.
“Ina nan ina jiranki sarauniyar mata.. Takawarki lafiya. Ba wata mace daza tasha gabanki Hajjiya TAUDHAT..

“Kwad’awar taka ta isa haka. Kaidai kaga tafiyata..
Cije baki yayi cikin matuqar jin dad’i. Shi kad’ai yasan abinda yake ma murnah

Sam bata wucce gidansu ba gidanta ta wucce. Amman takira Adams ta gaya mai ta wucce gida basai yaje gidan nasu d’aukarta ba.. Dan tayi baqi ne. “Ok. Yace mata.. Sannan takira mamanta tagaya mata ta wucce gida..

Da misalin qarfe tara na dare NUFAISAT ce kwance kan d’aya daga cikin kujerun falanta. Tunani take meya hana ADAMS dawowa gida da wuri Yau
A hankali tad’auki wayarta dan takirasa sai kuma taji dawowarsa damasu tsaransa…
Da sauri taje ta bud’e mai kofar falanta dan tasan nan zai fara murd’awa..
Aiko haka ne. Dan part d’inta ya fara nufa kamar yanda ya saba.
Ganinta a bakin kofar ya bashi mamaki. Kan yayi mata magana ta rungumesa tana cewa.. “Haka kawai naji gabana na fad’iwa na rashin ganinka da banyi ba lokacin daka saba dawowa. Duk dako. Bayau bane karo na farko daka tab’ayin hakan.
Murmushi yayi da d’ago da fuskarta da yayi ya manna mata kiss da cewa.. “Wallahi momy Rukayyat ce bata da lafiya.. Wai tana shiga kitchen sai qarar fad’uwarta akaji..
Salim ne ya kawota asibiti. Saidai duk binciken da doctors sukayi basuga abinda ya haifar mata da hakan ba..
Cikin damuwa NUFAISAT tace.. “Ikwan Allah. Toh yanxu me yake damunta.
“Komai fa najikinta yanxu ya dena aiki.. Kawai bakinta ne yake aiki wajen magana da idanunta da suke ganin mutane
NUFAISAT taja numfashi tace.. “Toh dama mutane sunayin irin wannan ciwan ne..
“Gaskiya ban tab’a gani ba. Ki kwantar da hankalinka zata samu lafiya..
Cikin damuwa taraba jikinta da nashi tace.. “Toh Allah ya yarda..
“Amiin yace daci gaba da cewa. Bara naje nayi wanka naga qawar tamu dan kwata kwata a gajiye nake..
Murmushi tayi da cewa. “Kadai fara cin abinci danna hango yunwa cikin kwayar idanka..
Shafa gefen fuskarta yayi da bata amsa.. “Dama anan nake danafi jin dad’i danfa gaskiya kinfi TAUDHAT kula dani.
Murmushi taqarayi da fad’in. “Zan koya mata komai wanda zaisa kaji tafini kula dakai.
“Bana tunanin hakan. Nadaifi yarda dazaki koya mata daidai da yanda kike min
“Toh idan nayi mata hakan aizata qara da tata basirar. Kaga kenan dole tafini kula dakai
“Kawai dai naji saida safe.
“Dan Allah katashi da wuri dan musamu zuwa duba momyn akan lokaci..
“Murmushi yayi da cewa.. “Kema kinsan bana wucce lokaci..
“Nafa fad’ane kawai dan naji dad’in bakina
“Idanko haka ne nayi miki alqawarin bazaki ganni ba.. sai qarfe goma na safan..
“Wayyo Allah mijina dan Allah karkamin wannan horan.. Duk da cewar a d’akin y’ar uwata kake zanji ba dad’i sosai idan nakai wannan lokacin banga kyakkyawar fuskarka ba..
“Alk’awarifa nayi. Dan haka ki kwantar da hankalinki dan saina cika.. Yana fad’in mata hakan ya ficce daga falan yana murmushi..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button